← Book details Garkuwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 45

Sashe 4

Garkuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shatu dake tsaye gaban dreesing mirror'n tana kimtsa kayyakin kolliyar ta, cikin yar ƙaramar jakane alamun shirin tafiya, jin wayarta na ringing yasa tasa hannu ta ɗago ganin sunan dake saman wayar.
Habibi Da'iman, murmushi tayi tare da amsa wayar kana ta kara a kunne, cikin sanyi tace.
"Assalamu alaikum Yah mu'allim".
Sassanyan numfashin ya fesar tare da sauƙe ajiyan zuciya kana yace.
"Wa alaikassalam Mar'atussaliha, kina lfy ko".
Kai ta gyaÉ—a kamar tana gabanshi kana a hankali tace.
"Lfy lau Alhamdulillah"
Da sauri yace.
"Baby nafa".
Murmushi tayi kana tace.
"Alhamdulillah Doctor duk muna lfy, sai dai muna kewarka Yah Sheykh".
Cikin lumshe ido yace.
"Ina nan tare daku".
Cikin ta É—an shafa kana tace.
"Hamma Jabeer nifa na gama shirina".
Ƴar karamar dariya yayi fahimtar duk sunan da zata kirashi dashi yanada ma'anarsa namusannan kuma ko wanne suna a gaɓar daya dace dashi take kiranshi.
Takan ce mishi Doctor a duk lokacin da yake bincikar lfyarta ko kuma takejin wani abu nata na mata ciwo, to kai tsaye da Dakta take kiranshi da yaji haka kuma yasan akwai abinda zatace mishi na damunta.
Kana duk sanda zata ce mishi Hamma Jabeer takanyi mgna dashi kai tsaye a matsayin Garkuwanta kuma Æ´aÆ´anta É—an uwa yadda da yaji haka yasan zatayi mishi mgn kan nuna shi matsayin Æ´an uwansa natane Æ´an uwanta nashine, kuma a kan danginshi zatayi mgn ko nata.
In Kuma yaji tace mishi.
Malam to yasan akan abinda ya shafi addini zatayi mishi mgn ko tambaya da dai makamantansu.
In kuwa yaji Yah Sheykh to yasan fagen da ake ya lura tana jin daɗin sunan, dan takan kira sunan ne cike da shauƙi mai ratsa zuciya.
A hankali yace.
"To BoÉ—É—on Ummey ki shirya da kyau, dan nima zaki shirya min dare nan ki bani kyautar kwana ukun da zakiyi".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Kai Hamma Jabeer bazan hutaba".
Da sauri yace.
"Zaki huta mana".
Uhum kawai tace.
Shi kuwa cikin nitsuwa yace.
"Aysha manna wayar a jikin cikin namu ko".
Da sauri tace.
"Toh Malam ayi addu'ar da ni".
Tayi mgnar sabida sanin addu'a zaiwa cikin.
Ai kuwa tana manna wayar a cikinta ya fara addu'o'in masu ratsa jiki.
Wani irin murmushi tayi tare da cewa.
"Laaah Malam kaji Baby tana motsawa".
Murmushi yayi shima kana yaci gaba da Addu'o'in.
Saida ya ida kana sukayi sallama.

Littafin GARKUWA na kuÉ—ine Special Group 1k wanda anfi yawan posting in kunaso kiyi min TRANSFER 0005388578 Jaiz Bank Aisha Aliyu Garkuwa sai kiyi screenshort na Debit alert É—in ki ki turomin 09097853276 ta whatsapp sai in saki a group akwai Normal group Kuma 300 ne kuma ta ac É—in zaku biya in baki da halin biya ta ac ki sayi katin Mtn na É—ari uku kacal ki copy numbers É—in ki turo min ta whatsApp 09097853276.

*Yahunde International airport*

By
*GARKUWAR FULANI*
4/6/21, 4:15 PM - &: Ƙarfe huɗu dai-dai, na yamma, wasu irin motoci ne masu masifar kyau da tsaruwa.
Suke kutsa kai cikin airport ɗin, wanda a ƙalla sun kai bakwai.
bisa alamu duk akwai cikekken nasaba da dama, dan har can asalin wurin da jirgi yake biyu daga cikin motocin suka wuce.
Kana biyar kuma suka tsaya a ainihin harabar.
A hankali aka buÉ—e motocin.
Alhaji Abboi ne ya fara fitowa.
Sai Bappa kana Al'ameen da wasu matasa uku masu kama da Al'ameen sai wata kekkyawar budurwa mai kama da Shatu sak wacce take riƙe da hannun Junainah.
Sai Ummey da Inna Amarya da suka fito.
Bisa alamu duka, sauran rakiya sukayiwa su Bappa.
Gyara tsayuwarsu sukayi dan ganin matafiya nata shiga cikin jirgi, wanda yake É—auke da tambarin Abboi.
Cikin murmushi Appa ya miƙawa Bappa hannu sukayi musabaha kana a hankali yace.
"Toh Malam Babayo Allah ya maidaku lfy ya kiyaye hanya".
Cikin jin daÉ—i Bappa yace.
"Amin Amin Abboi Ubangiji ya saka maka da mafi kyawun sakamako".
Cikin jin daÉ—in Addu'a Al'ameen da saura zaratan samarin nan sukace.
"Amin ya Allah".
Sai kuma sukayi shiru jin Appa na cewa.
"In kun isa ka gaida min Parvina da kyau, kana aci gaba da ɓoye mata abinda mu muka fahimta,
har sai lokacin da ido zaiga ido muna da kekkyawan yaƙinin duk sanda taga wasu cikin masarautar Joɗa mu samman in ya shafi ahlinta in sha Allah zata iya tuno komai na baya".
Ya ƙarashe mgnar a hankali yadda ko su Al'ameen basu jiba bare su Ummey.
Cikin gyaÉ—a kai Bappa yace.
"Inama ji a jikina komai ya kusa zuwa ƙarshe da izinin ubangiji.
Dan yanzu dai nasan muna komawa Shatu zata zo, to inma batazo da waniba ina zaton zata zo da mijin nata, kuma inma bata zo É—inba idan ta haihu shine shirinmu ta sanadin haka Ummeynta zata shiga masarautar JoÉ—a ba tare da an zargi komaiba".
Kai Appa ya gyaÉ—a tare da cewa.
"Tabbas komai ya kusa zuwa ƙarshe".

Yar Kekkyawar budurwar nan kuma mai kama da Shatu hannun Junainah ta sake ganin Bappa na miƙo mata hannu alamun tazo su tafi.
Cikin sanyi Khadijah tace.
"Ayyah Junainah zamuyi kewarki."
Da sauri Junainah tace.
"Adda Khadijah ina in Adda Shatu na ta haihu zakizo keda Dedde ko?".
Kai Khadija ta jinjina tare da cewa.
"In sha Allah kuwa, zanzo ki gaida min ita da kyau kinji ko my Junnu kice mata duk Ahlin Abboi muna kewarta."
Da sauri tace.
"To zan gaya mata, bey-bey Adda Khadijah sai kunzo".
Tana faÉ—in haka ita da Bappa suka nufi cikin jirgi.
Ita kuwa Khadijah ruggume Ummey tayi tana zubda hawaye tace.
"Ummey zamuyi kewarki, dake da Junnu".
Hannu Ummey tasa ta share mata hawayenta kana tace.
"Nanda wata biyu dai Shatuna zata haihu zakuzo mu gana".

Da sauri Ummey da Inna Amarya suka nufi cikin jirgin bayan sunyi sallama da Abboi.

Basu tafiba saida sukaga tashin jirginsu.

Ƙarshe biyar da rabi jirginsu ya sauƙa cikin Ɓadamaya International airport. riƙe da jakukkunan kayansu suka fito, Junainah na gaba.
Tanata murmushin jin daÉ—i.
A haka suka iso asalin inda masu taryar matafiyan suke.

Yah Salmanu ku wanda shida Junaidu ne sukazo taryarsu cikin motar Yah Salmanu wanda tuni shima ya samu aikinsa, cikin Ɓadamaya an bashi gida da mota.

Wani irin tsalle Junainah tayi tare da rabkawa Junaidun kira wanda ta hangoshi yanata É—an dube-dube alamun neman ta inda suke.

Jiyo muryar ta, A tare suka juyo shida Yah Salmanu.
Wani irin murmushi mai cike da tarin jin daÉ—in Junaidu yayi tare da nufo inda suke gadan-gadan.
Ita kuwa Junainah da gudu ta iso gabanshi, sai kuma ta tsaya tare da sakin murmushi bata abka jikinshi ba kamar yadda takeyi da can baya.
Wani irin murmushi Yah Salmanu yayi tare da cewa.
"Oyoyo My Junnu Allah sarki nesa mai raba masoya, watoma Junaidu kawai kika sani banda ni ko?".
Cikin jin kunya alamun shekara ɗaya nan data ƙara cikin shekarunta yanzu ta zama yar shekaru goma sha uku hankali da nitsuwa da kunya sun fara zuwar mata, cikin jin kunya tace.
"A a Yah Salmanu na ganka mana".
Sai kuma ta kalli Junaidu daya karkata kai yana kallonta cikin sanyi yace.
"I miss you very very sorry so much my Junainah".
Cikin rufe ido tace.
"I miss You to Yah Junaidu, ya jikinka ka worke ko?".
Da sauri yace.
"Alhamdulillah garauma kuwa".
Shi kuwa Salmanu da sauri ya isa gabansu Bappa jakukkunansu ya amsa, haka yasa shima Junaidu yayi maza ya amshi na hannun Ummey tare da cewa.
"Oyoyo Ummey na Bappanmu Inna Amarya sannunku da hanya".
Kusan a tare sukace yauwa.
"Sannu Junaidu".
Sai kuma Bappa ya kallesu tare da cewa.
"Masha Allah Junaidu na ya girma."
Ummey kuwa Salmanu ta kalla tare da cewa.
"Kai sannu Salmanu ya bayan rabuwa?".
Cikin girmamawa yace.
"Alhamdulillah Ummey na munata kewarku Rugar Bani gaba É—aya".
Bappa ne ya jinjina kai tare da cewa.
"Muma muna cannedai Amman munata kewarku".
ÆŠaga nan suka nufi inda motar Salmanu take.
Suna shiga suka nufi Rugar Bani.

Kafin a kira mangriba dai sun isa.

Anayin sallan magriba da isha'i matan Rugar Bani suka rinƙa shigowa sunayiwa su Ummey sannu da dawowa da ganin amaryarsu.

Junaidu kuwa ana idar da salla ya dawo nanfa yaja Junainah gefa kaÉ—an cikin gidan sunata hira, tana bashi lbrin ahlin Abboi yayinda sosai yanzu faransaci ya kama bakinta.

A nan masarautar JoÉ—a kuwa.
Ana idar da sallan isha'i suna fitowa a kan hanyar komawarsu cikin gidane.
LamiÉ—o keyiwa Sheykh batun zuwansu Rugar Bani da Umaymah ta gaya mishi.
ÆŠan juyowa yayi ya kalli LamiÉ—o jin yana cewa.
"In Allah ya kaimu goben da safe fadawa da bayi zasuyi muku rakiya, ka kuma É—auki Jalal da Jamil da Umminku".
Cikin kwaɓe fuska yace.
"Bana wani buƙatar rakiyar bayi da fadawa da hadimai.
Kuma Jamil da Jalal duk yanzu bana son yawonsu na aamu suÉ—an fara meda hankalinsu sosai kan aiyukansu sun rage zaman gida da yawace-yawace kuma ma ni tafiyata ta sirrice, bana ma son asan Aisha bata gida bare asan inda take, sabida gsky wanna Hankakar Hajia Mama mai farin gaba bakin baya sata iyasa aje can Rugar ayi mata komai, badon dole bama bazata jeba, sabida rugar ba tsaro."
Jinjina kai LamiÉ—o yayi cikin gamsuwa da zancenshi yace.
"Eh to wannan ma hakane ba matsala kuyi tafiyar sirrin ammanfa zakuje da Ummi".
Kai ya gyaÉ—a alamun to daga nan sukayi sallama.

Yana shiga falon ya samu ba kowa.
Falonshi ya wuce a nan ya samu Shatu kwance bisa kujera.
Matsawa kusa da ita yayi tare da cewa.
"Ya dai Aish lfy kuwa yau ba hira ina Ummi ina Juwairiyya?".
Ido ta lumshe tare da cewa.
"Wlh Ummi zazzaɓin mura ke damunta".
Cikin kula yace.
"Assha subahanallahi tasha mgni kuwa?".
Kai ta gyaÉ—a tare da cewa.
"Eh tasha har tayi baccima".
"Toh Allah ya sauƙa".
Yace yana zare al'kyabbar jikinshi.
Amin Amin.
Tace tana tashi zaune.
Gefenta ya zauna ganin haka ta É—an gyara zamanta tasa mishi abinci ya fara ci.
Chapter 4 · 0% Book details