← Book details Garkuwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 45

Sashe 21

Garkuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai kuma yace.
"Jamil ne yazo ya daukomu a airport to yanzu mun biya mun sauƙe Yah Sulaiman da Malam Abubakar.
To gani tare dasu GiÉ—i É—in yanzu su ina zamu kaisu, umarni nake jira Hamma?".
Cikin sanyi yace.
"Alhamdulillah Affan ku dawo dasu masarautar Joɗa ku wuce dasu Part ɗinsu Jalal a sauƙesu a can.
Bawa Jamil wayar".
Da sauri yace.
"An gama sir yadda kace haka za'ayi ga Jamil É—in".
Ya kare mgnar yana miƙawa Jamil wayar.
Saƙale wayar yayi da kafaɗarsa tare da cewa.
"Assalamu alaikum Yah Sheykh".
GyaÉ—a al'kyabbar jikinshi yayi tare da cewa.
"Wa alaikassalam Jamil ka kaisu part É—inku É—akinka ka nuna musu Bathroom suyi wonka.
Aunty Rahma zata kawo musu abinci ka tabbatar sunci sun ƙoshi.
Sannan Jalal zai É—auki Dr Kabir zaizo ya dubasu in sunada matsalar lfy zai kula da komai".
Cikin gamsuwa Jamil yace to yana kallon kekyawar fuskar GiÉ—i ta madubin motar.

Shi kuwa Sheykh a hankali yace.
"Toh Umaymah a hakan ta yaya zan tozarta mahaifiyar Affan wanda duk munin halinta uwa dai uwace."
Cikin rauni Umaymah tace.
"Wannan hakane Jazlaan amman Hajia Mama tanayi mana illa a rayuwa".
Sosai jikin Haroon yayi sanyi.
Shi kuwa Sheykh Jalal ya kalla tare da cewa.
"Kaje Valli ka taho da Dr Kabir".
Jiki a mace Jalal yace to kana ya miƙe ya fita.

Umaymah na biye dashi a baya, har taje bakin ƙofar fita a hankali yace.
"Ayyah Umaymah ÆŠiyar taki ta kawo min É—iyar tawa mana in ganta".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Toh".
Shi kuwa Haroon da sauri yace.
"To bari in baka wuri dan nasan dai uwar É—iya za'a gani ba É—iyaba".

A hankali yace.
"Mutun da abinsa".
Dariya Haroon yayi kana ya nufi ƙofar da zata sadashi da Garden.

A hankali ta turo ƙofar Bedroom ɗinsa.
Tare da cewa.
"Assalamu alaikum".
Cikin wani irin happy yace.
"Wa alaikissalam".
sai kuma ya juyo ya fuskanceta tare da buÉ—e mata hannunshi.
Cikin sauri ta faÉ—a jikinshi ruggume da Afreen haÉ—e su yayi ya ruggume tare da cewa.
"Alhamdulillah ya Allah ka tsare min ahlinna ka cika mana farin cikinmu".

"Amin ya Allah". Ta faÉ—a a hankali sai kuma ya jawo hannunta suka zauna a bakin gadon.
Cikin narke fuska yace.
"Nayi fushi Aish tun É—azufa na aika kizo baki zoba sai yanzu".
Cikin sanyi tace.
"Ayyah Malam sallan la'asar nakeyi".
Cikin sauri ya kalleta tare da cewa.
"Kai haba dai Aish da gaske shine baki gaya minba yaushe kika fara salla".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Yoh ai dama ina salla".
Lakace hancinta yayi tare da cewa.
"Batun gsky dai my dear yaushe kika samu tsarki?".
Cikin nitsuwa tace.
"Yau da safe, nai wonka naci gaba da salla tunda naga jinin biƙin ya ɗauke na samu tsarki".
Kanshi ya gyaÉ—a tare da cewa.
"Masha Allah, jego yayi kyau kenan BoÉ—É—o na, dama wasu matan kafin satin sunama sun samu tsarki sun fara salla, kinga kema kina É—aya daga cikinsu wasu kuma sai anyi arba'in ma, wasu har hamsin suna likin.
Koda yake ke dama al'adarma kwana uku kikeyi ko".
Kai ta gyaÉ—a mishi.
Hannunshi ya cusa ƙasan pillow'nshi tare da zaro key ɗin sabuwar mota dal a leda.
Kamo hannun ta yayi ya danƙa mata key ɗin tare da cewa.
"Al'ada kwana uku baƙi kwana bakwai kai naji daɗi na, na more".
Da sauri ta buÉ—e tafin hannunta tare da kallon key É—in sai kuma ta lumshe idonta jin ya manna mata tattausan lips É—insa a goshi ya sake mata sassayan kiss.
Tare da cewa.
"Taki ce motar sai dai bani son kiyi tuƙi nafi son a jamin ke, sai daifa bana miji zai jamin keba.
Sara taki zata zama yar rakiyarki mai jan mota da tayaki kula da Babynmu, duk inda kuke in bana kusa daku.
Gimbiya Aminatu zata bamu wata mai girki".
Cikin wani irin farin cikin ta ruggumeshi gam-gam a jikinta.
Da sauri yace.
"Wayyo Aish zaki danne Mimi na".
Da sauri ta kwantar da Afreen gefe, kana ta faÉ—a jikinshi ta rungume shi.
Murmushi yayi mai cike da farin ciki cikin wasa yace.
"Zaki bani abin daÉ—i?".
Da sauri tace.
"Ban workeba".
Dariya mai É—an sauti yayi tare da haÉ—e bakinsu wuri guda.

A part É—insu Jalal kuwa.
Yah GiÉ—i Seyo Gaini ne zaune bayan duk sunyi wonka, sun saka sabbin kayan da Jamil ya zaro musu cikin durowarsa.

Cikin wani irin yanayin jin daÉ—in duniya da kuma bege da kewar iyaye da Æ´an uwa wanda da sun cire tsammani.
A hankali Yah Giɗi ya kalli Jamil dake miƙo mishi turare yana cewa.
"Kai masha Allah sai kunga yadda kukayi kyau, farinku ya ƙara fitowa".
Cikin rauni GiÉ—i yace.
"Dan Allah bawan Allah, nan ina muke ne? Kuma ina wanda muka dawo dashi? Sannan ina za'a kaimu? Wayasa aka fito damu?".
Da sauri Jamil ya zauna gabanshi kamo hannun shi yayi a hankali yace.
"Nan kuna cikin Ɓadamaya ne, cikin masarautar Joɗa, wanda kuka dawo dashi kuma Yayana ne Affan ya tafi ƙofar matarshi.
Wanda ya taimake ku yasa aka fitar daku kuma babban Yayanane Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero JoÉ—a.
Yana nan matarsa ta haihu yau akeyin suna. Sai in ya nitsu zaizo wurinku shi zai gaya muku ina za'a kaiku".
Wasu irin hawaye ne suka tsunkowa Gaini murya na rawa yace.
"Alhamdulillah kowa yace yaya zaiyi ya manta da Allahu wahidun ƙahharar sarki buwayi gagara misali mai badawa mai hanawa mai raya mai kashewa mai kawo sauƙi cikin tsanani mai yaye tsananin duhu ya wanzar da haske".
Ido Jamil ya zuba musu cike da so da ƙaunar su, sai kuma ya kalli Seyo da yake zubda hawaye cikin sanyi yace.
"Ko wanne hali ahlinmu ke ciki".
Da sauri Jamil yace.
"Yanzu muje falo kuci abinci kunji dan Allah ku bar kukan".
Kasan cewar ya haÉ—a su da Allah yasa ba musu suka tashi.
Amman badon hakaba farin cikin da suke ciki ya kori yunwa bare ƙishi.

A tsakiyar falon suka zauna.
Jamil da kanshi ya zuba musu abincin da Aunty Rahma ta kawo musu.
Sukaci suka sha.

Dai-dai lokacin kuma aka kira sallan magriba.
Nan sukayi al'wala kana Jamil ya jasu sukayi jam'i.

Shatu kuwa bata bar É—akin Sheykh ba saida ya tafi masallaci.
Ta fito cike da farin ciki.
Aunty Amina da Khadijah da Umaymah da Hibba ta samu a falonta Umaymah ta miƙa wa key ɗin tare da cewa.
"Umaymah Yah Sheykh ya saya min mota".
Cikin jin daÉ—i Umaymah tace.
"Masha Allah. Allah ya sanya al'khairi".
Amin Amin sukace baki É—ayansu.
Kana duk sukayi al'wala haramar salla.

Ƙarfe goma da rabi.
Duk baƙi sun watse.
Sai su Umaymah da su Aunty Amina.
A falon Shatu suke suna hirarsu cikin salama Ummi na ruggumi da Afreen.
Umaymah kuwa na haÉ—awa Shatu tea da fifitashi da kyau.
Aunty Rahma kuwa kitso Khadija keyi mata.
Junainah da Ishma kuwa suna can babban falon da Hibba da Jalal.

Sara da Larai da indo hadimar Aunty Juwairiyya kuwa tattare kitchin sukeyi da kimtsa ko ina na gidan.

Sheykh kuwa a hankali ya jawo wayarshi daya tattare wacce yake waya da Hajia Mama da ita.
Kiranta yayi.
Tana amsawa yace.
"Ƴar ta mutu ko?".
Wani irin gigitaccen tsaki taja tare da cewa.
"Inafa ta mutu na dai ji ta suma amman wannan Shegen yaron duk abinda nayi a kanshi ko matarsa yanzu dama yar tashi abun baya tasiri.
Sannan babban tashin hankali na, shima Sarkin al'adun suna bai dawoba.
Kuma wayarshi na shiga baya É—agawa, tsorona kada dai sun ganeshi".
Cikin sauya muryarsa ih zuwa muryar Jahan yace.
"A a ba dai kamashi ba kam, sai dai ko in yana jin tsoron amsa kiran nakine sabida kada kiyi mishi faÉ—a tunda Æ´ar bata rasuba kada kice bai iya aikinsa bane a ganina fa shine yasa baya amsa kiran naki".
Cikin tashin hankali tace.
"Ni babbar matsala ma yau tunda gari ya waye hankalina yake a tashi zuciyata na tsinkewa gaba É—aya tsoro ya rufeni ji nakeyi wani mugun abu yana tunkaro rayuwata, naje gidan boka kuma ya koroni shima sai tsalle yakeyi yana kaÉ—e jikinsa
Wai komai na gab da dawo mana".
Murmushi mai cike da jin daÉ—i yayi a ransa yake zaton ko shiryace zata zo mata, haka yasa yace.
"Sai gobe zanzo muyi mgn in kaiki gidan wani sabon boka".
Da sauri tace.
"To".

Daga nan ya katse kiran.
Kana ya miƙe ya fito falo, a hankali ya kalli Jalal da Hibba tare da cewa.
"Jamil fa".
"Yana Part É—in mu".
Jalal ya bashi amsa".
To yace kana ya juyo ya kalli Yah Jafar da yanzu ya shigo kenan.
A hankali ya tsaya gaban Sheykh.
A hankali suka lumshe idonsu a tare, da sauri Sheykh da Jalal da Hibba suka matso kusa dashi sosai jin yana cewa.
"Jabeer zuciyata na tsinkewa tun jiya sai inji kamar wani abu zai faru".
Cike da mamaki Jalal yace.
"Wlh nima tun jiya zuciyata ke tsinke kirjina yaita bugawa".
Wani irin rumtse ido Sheykh yayi tare da cewa.
"Nima abinda naketa fama dashi kenan tun jiya, to da Aisha ta suma sai nai zaton ko abinne ke samin tsinkewar zuciya.
To kuwa still abin bai bariba saima ƙaruwar da yakeyi yana tsananta".
Cikin sanyi Hibba tace.
"To kuyi ta addu'a hakama Umaymah da Mamma da Aunty Rahma sukace suna ji".
Kai suka gyaÉ—a gaba É—aya.
Hannun Yah Jafar É—in Sheykh yaja suka nufi Part É—in su Jamil.

Su kuwa su Jalal zama sukayi suna kallon Ishma da Junainah daketa sabgoginsu.

A hankali Sheykh ya zauna tare da kallon Jamil dake zaune tsakiyarsu GiÉ—i a hankali yace.
"Ka barsu su huta mana".
Cikin sanyi Jamil yace.
"Allah ko Hamma Jabeer ina so in tafi wurin Khadijah ma sai inji zuciyata na tsinkewa kamar dai zan samu wani abu".
Cikin kula Sheykh yace.
"Uhmm duk haka mukeyi kaita mai-maita innalillahi wa innailaihi rajiun".
To yace.
Shi kuwa Sheykh nitse ya kalli Gaini da zai kai sa'an Affan.
Cikin kula yace.
"Sannunku da hanya".
A tare sukace sannu.
Chapter 21 · 0% Book details