← Book details Garkuwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 45

Sashe 26

Garkuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Littafin GARKUWA na kuÉ—ine Special Group 1k Normal group 300.
A yawan posting ne babban cinsu 0005388578 Jaiz Bank Aisha Aliyu Garkuwa in kin tura sai kiyi screenshort na Debit Alert ki turo min ta whatsApp 09097853276 Æ´an 3oo in naki da halin biya ta Account zaki iya sayan katin mtn na É—ari uku ki copy numbers É—in ku turo min ta whatsApp É—in 09097853276.

By
*GARKUWAR FULANI*
4/6/21, 4:15 PM - &: "Aranar wata jumma da da wanna Zazzafar ƙaddara ta rufta damu shekaru goma sha uku baya."
Sai kuma ya É—an tsakaita
tare da jan
sassayan numfashi ya gyara
zamansa tare dasa tafin hannunshi ya share hawayensa.
Yayin da gaba
É—ayansu kacokam
suka mai da hankalin su kansa,
Duk sun ƙagu suji yadda a kayi a wannan ranar da basu manceba.
Shi kuwa Yah Jafar wani numfashin yakuma.
Saukewa kana yaci gaba da cewa.
"Ranar da dare bayan anyi sallan isha'i duk muna falon Mamey dani dasu Jalal Jamil Affan da Ummi da Imran yana É—an sheksru takwas lokacin.
Anan mukaci abinci kana muka zauna muna hira.
Kasan cewar akwai shaƙuwa mai tarin yawa tsakanin Mamey da Affan da yake tana da son yara.
Amman son Affan da banne a wurinta har su Jamil kance wa Affan na hannun daman Mamey.
Takanyi Dariya tace.
"Eh É—in ai ya fiku nitsuwa".
Muna zaune sai hamma Mamey keyi tare da miƙa da lumshe idonta hakane yasa tace mana.
Duk ta sallamemu saida safe tanajin bacci.
Ummi tace.
To.
Still Kuma sai mukaci gaba da hira.
Da ido muka bita ganin ta miƙa cikin sanyi tace.
"Kai zanje inyi bacci wlh wani irin bacci mai nauyi nakeji yana fuzgata tamkar zan faÉ—i.
Ni na shiga saida safenku".
Allah ya bamu al'khairi mukace dukanmu kana ta shiga.
Tana shiga kwanta ko second uku batayi da kwanciya ba tayi bacci.
Mu kuwa muna gama hira muka watse.
To su Jalal ne ƙarshen fita ashe basu tasheta ta rufe ƙofarta ba a famintata kenan fa?".
Ya ƙare mgnar yana kallon su Jamil.
Da sauri Jamil yace.
Eh.
Cikin sanyi ya kalli su LamiÉ—o kana yaci gaba da cewa.
"Ina komawa É—aki na kira Juwairiyya muka fara hira a waya kamar kullum.
To bayan mun gama
waya da Juwairiyya
har na kwanta sai na mike na nufi
É—akin Mamey dan
inaso nayi mata magana a kan Juwairiyya fa tasanar wa mahaifin su maganar auren mu da ita, tun da lokacin takammala
karatun ta dan haka itama ta gayawa Abba na ayi batun aurenmu dan nima tuni lokacin na gama karatuna har na fara aiki.
Kuma a kwanakin ne aka bani sarautar Galadima wanda da mijin Gimbiya Saudatu ce mai matsayin to daya rasune LamiÉ—o ya maida mulkin kaina.
A zatonshi ta hakane zaisa yaranshi bazasuyi faÉ—a da junaba tunda bazasuce ya baiwa wane ya hana waneba.
Ni a lokacin dagani har Mamey da Jabeer da baya ƙasar ma ba son wannan mulkin mukayiba bisa dole aka bani ita.
Sai kuma ya jingina bayanshi da kujera kana yaci gaba da cewa.

Ina isa bakin kofar
Mamey natura kofar da sallama nashiga É—akinta.

Da sauri naja natsaya nan bakin kofar.
Can na hangi Mamey na kwance.
Bisa gado tana bacci da alamun baccin mai nauyi ne.
Hajiya mama kuwa na tsaye a kanta da wata iriyar shiga da tafi kama data bokaye ko ince matsafa.
Da mamaki nake kallon
Hajia Mama dake tsaye bakin gadon sanye da wasu irin jajayen kaya tun daga samanta har ƙasa,
kanta babu ko É—an kwali
hannunta rike da wani ƙwarya.
Tana yayyafawa Mamey
wani ruwa dake cikin ƙwaryar tare da yin wasu surutai da sukafi kama da surkullen matsafa.

"Innalillahi wa'inanna ilaihirraji'un, nafurta da karfi.
Da sauri nanufo in da Hajia Mama'n ke tsaye cikin ruÉ—ani da kiÉ—ima ina faÉ—in.
Meye hakan Hajia Mama? me kike mata? me kike zuba mata a jiki haka?.
Dasauri tajuyo kaina tasaka hannunta cikin ƙwaryar taɗibo ruwan tashiga watsamin tana ƙara matsoni,
kaucewa nashiga yi ina matsowa in da Mamey take kwance kamar gawa ko matsi batayi,
itako Hajia Mama masoni tarikayi tana watsamin ruwan,
Baki na buɗe da karfi sabida wani irin masifeffen suka da naji duk inda ruwan ya taɓa a jikina yanayi.
Ƙara watsomin tayi wanda yasa na ƙara kaucewa da sauri tare da buɗe baki da nufin yin ihun zafin da nakeji da kuma fargabar halin da Mamey na ke ciki.
Sai kawai naji harshena yafurta Innalillahi wa'inanna ilaihirraji'un,wannan kalmar narika nanawata da karfi madadin inyi ihu."

Ita kuwa Hajia Mama da sauri tajuya cikin alamun tsoron tonuwar asirinta.
dan lokacin dare baiyi nisa sosai ba misalin ƙarfe goma ne,
da gudu tafita a É—aki dan jin yadda na kara sautin salatin da nake.

Ita kuwa Hajia Mama tana fita part É—inta ta nufa direct bathroom É—inta ta shiga gaba É—aya jikinta rawa yakeyi number'n bokan ta takira yana É—agawa cikin haki da fargabar a bin da zaije ya da wo tace.
"Boka yanzu nafito daga É—akin matarnan na samu tayi bacci kamar yadda kace, kuma na watsa mata ruwan bata farka a sai daifa wani yaganni lokacin danake yayyafa mata ruwan maganin nan babban É—anta Galadiman Masarautar JoÉ—a kenan ya ganni".
Wani irin dariya irin nasu na hatsabibai bokan yayi kana yace.
"Toh daya ganki me yakeyi? me kuma yake cewa?".
cikin rawar baki da soron da ya ziyarce ta gudun kada ai kin ya ɓaci tace.
"Sunan Allah yaketa ambata salati yaketayi babu ko kakkautawa da wasu addu'o'i".
Cikin É—an tsagaita dariyar mugayen bokan yace
"To aiki kam zaici amma dai akwai nakasu aciki, amma kada kidamu yanzu shi yaron zamu rufemasa baki zai dauwama kurma ba mgna a bakinsa bazai iya yin maganaba bazai iya furta komai ba haka zai dauwama ba mgn saidai yayi ta mai-mai-ta abinda yake cewa.
Sannan daga nan tagwayen kuma zamu haɗa ɗaya da bin mata ɗaya shaye-shaye shi kuma babban kinga zai zama kamar Mahaukaci, shi kuma wancan Jabeer ɗin na gaya miki tun yana ƙaramin akwai sihirin da wani yayi mishi kada ki damu dashi bazai taɓa yin aureba har gaban abadan ko an mishi bazai zauna da matarba, kinga kenan duk sun zama suna da matsalar da dole baza'a basu mulkiba sai dai a bawa ɗanki Affan tunda kinga shi Imran ɗan ɗaya kishiyar taki shine ƙarami kan Affan."
Cikin sauƙe numfashi tace.
"Yauwa boka na gode ni dama fatana É—ana yayi mulki dan bana son mulkin ya bar É—akina tunda dai kace min tabbas cikin yaran Habibullah ne mijin wani zai gaji kakansa sarauta.
Dariya yayi tare da cewa.
"Kada ki damu mulki na gareki da É—anki".
Wa iyazubillah kaɗan kenan daga sharrin tsinannun shaiɗanu maƙiya Allah da Manzonsa bokaye taɓaɓɓu masu sa mai binsu ya taɓe ya gaza sauri a ranar da muminai ke sauri a bisa siraɗi.

Acan cikin É—akin Mamey kuwa.
Sosai sautin addu'a da karatun da Jafar keyi yatsanan ta yana kankame da Mamey, wacce ke ƙwance ida nunta a rufe, har lokacin bata farka daga.
Baccin sihirin da akasa takeyi ba saboda nauyin. Baccin da suka je fata ciki.
Sheko bakinsa baya iya furta komai sai addu'o'in sai kuma hawaye da keta tsatstsafowa daga cikin ida nunsa sabida fargarba da kuma zafin da yakeji,
Abba kuwa dake can part É—insa da yake Part É—in shi na natsakanin na matan nashi ne.
Yana cikin É—akinsa dake sama.
Haka yasa yarinƙa jiyo muryar Jafar da irin addu'o'in dayake cikin kiɗima, da kajin addu'ar kasan acikin tsananin firgici da tashin hankali yake yinsa,
Wuf yamike yanufo part in Mamey kasan cewar babu wata tazara sakaninsu.
Gudu-gudu sauri-sauri ya isa.
Cikin hanzari yatura kofar bedroom É—in Mamey cikin sananin tashin hankali da kaÉ—uwa ganin yadda Yah Jafar ke rungume da Mamey sai innalillahi yake da karfi hawaye yagama wanke fuskarsa idanunsa sun yi jazir saboda kuka da zafin da yakeji da fargabar ganin tamkar Mamey a mace take a kiÉ—ime yanufo in da suke yana faÉ—in.
"Subahanallahi kai Jafar meya farune me ya sameta?".
Yayi tambayar hankali a tashe, tare da miƙa hannu ya ɗago kan Mamey dake kan kafar Ya Jafar yashiga girgizata yana kiran sunan ta.
"Aisha! Aisha!! Ummu Jabeer!.
Gani shiru bata ko matsi sai dai tana numfashi ya tsananta firgicinsa.

Hankali a tashe yakuma kallon ya Jafar wanda keta addu'o'in babu ko kakkautawa.
Mai da kan Mamey'n yayi ya kwantar kan cinyar kafar Jafar.
Kana ya juya a kiÉ—ime ya fita a É—akin da sauri ya nufi sashin mahaifinsa LamiÉ—o.

Shi ko ya Jafar cigaba da maimata innalillahi yakeyi yana zubda hawayen.

A can ɓangaren Hajia Mama kuwa.
fitowar ta daga É—akinta kenan cike da jin daÉ—in yadda bokan ya karfafa mata guiwa tanajin daÉ—i a ranta yanzu komai zai tafi mata yadda take bukata zata rabu da zugar yayan Mamey da ita duk kowa ya huta, tana fita ta hangi Abba ta window yafita daga cikin part É—insa hankali a tashe.

Fuska ta É—an yamusa tazauna saman É—aya daga cikin kujerun parlour'n, can kuma tamike kamar an tsikareta tabi bayansa da sauri.

Acan shashin LamiÉ—o kuwa.
Da sauri LamiÉ—o da Galadima suka mike, bayan Abba yagama sanar musu abin da ke faruwa.
A tare suka fito suka nufi part É—in Mamey'n.

Lamiɗo na gaba Galadima da Abba na biye dashi suka shiga ɗakin, in da Abba yabar Yah Jafar a haka suka iske shi yana ganinsu ya miƙe da sauri Mamey yashiga nuna wasu Lamiɗo da hannu yana kuka yana nuna musu ita da kwatanta musu yadda Hajia Mama tayi mata.

Da sauri Hajia Mama ta turo kofar dan taga shigowar su LamiÉ—o'n.
Jafar kuwa yana ganinta yashiga nunata da hannu sai kuma ya nuna Mamey'n yana cigaba da ƙwatanta yadda tayi matan shidai baki kam babu shi sai dai addu'o'in da kuma kukan dayake tayi.
Chapter 26 · 0% Book details