Sashe 22
Garkuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jamil ne ya É—an kallesu tare da cewa.
"Shine babban yayanmu Sheykh da yasa aka fito daku".
Da sauri suka É—an gyara zama suka matsoshi tare da cewa.
"Allah sarki bawan Allah mun gode Matuƙa Allah ya saka da al'khairi ya kula da ahlinka fiye da yadda ka kula damu".
Cikin jin daÉ—i yace.
"Amin ya rabbil izzati, amman kuma duk haka ya farune sanadin Sulaiman da aka rufeshi tare daku".
Cikin gamsuwa sakace.
"Ayyah".
Sai kuma GiÉ—i ya É—an share hawayen da suka zubo mishi tare da cewa.
"Ayyah bawan Allah yaushe zamu koma Rugar Bani muga Bappa da Inna da Ummey da Shatu da Junnu".
Cikin gamsuwa da tausayinsu Sheykh yace.
"In sha Allah nan kusa amman nafi son sai naga kunyi aski kun ƙara hutawa, gobe zuwa jibi da kaina zan medaku".
Cikin wani irin masifeffen jin daÉ—i sukace.
"Allah ya kaimu".
"Amin Amin". Yace kana ya musu sai da safe.
Daga nan wurin Abbanshi da LamiÉ—o da Galadima yaje suka É—an yi wata mgnar kana ya dawo.
Ranar dai haka suka kwana gaba dayansu babu wanda yayi isasshen bacci sabida masifar bugawa da ƙirazansu keyi.
A can Rugar Bani kuwa.
Ko abincin dare Ummey bata iya ciba.
Haka nan sai taji zuciyarta na tsinkewa yana bugawa.
Tun abun bai damunta har ta gayawa Bappa, so ya bata ƙarfin guiwa da yin addu'a.
*Ba'ana*
Zaune yake gaban yaransa cikin rauni da yanayin damuwa yace.
"Nanda wata uku masu zuwa zan koma ƙasar Nigeria zanyi yaƙin neman Shatu koda zan rasa rainane, zan koma gareta.
Zan gaya mata ko mutuwa nayi sonta ne ajali na".
Cikin bashi ƙarfin guiwa ɗaya daga cikinsu yace.
"Zama kayi nasara".
A hankali yace.
"Babu tabbas, domin tunda na rasa Shatu nakega nayi rashin babbar nasara".
Sai kuma ya miƙe ya shiga cikin ƴar ƙaramar bukkarsa.
Murmushi Baron yayi tare da katse kiran da yayi Sheykh yana jin duk bayanan Ba'ana.
Dan shi Baroon yanzu ya zama É—an aikin Sheykh dan tun zuwansa lokacin ciwon hannun Shatu.
Da fari har yasa a kirasa daga baya yasa aka dawo dashi.
Ya biyashi kuÉ—i masu tarin yawa, yayi mishi duk bayanin É—aya nema, kana yasashi ya koma wurin Ba'ana kuma ya naÉ—o mishi rahoto da duk wani motsin Ba'ana yana turo mishi.
Alhamdulillah kuma yanzu duk shirin kama Ba'ana yakeyi.
Washe gari ranar asabar yau babu aiki.
Da misalin Æ™arfe goma na safe jirginsu Abboi ya sauÆ™a cikin birnin Æadamaya.
Kai tsaye Salmanu yayi musu jagora zuwa Rugar Bani dan a take suna sauƙa wasu tsala-tsalan motoci guda biyar suka iso wanda dama su tun jiya suka iso.
A ƙasan plate number motocin akwai tambarin hatimin kan shanu a ƙasa ansa Abboi, irin tambarin dake jikin jiragen Abboi kenan.
Suna zuwa kuwa babu ɓata lokacin suka isa har cikin gida.
Inda nan ArÉ—o Bani da kanshi da sauran dattawan sukazo.
Bayan sun gaggaisane Abboi ya É—an yi gyaran murya tare da cewa.
"Toh Alhamdulillah lallai komai yayi forko to tabbas yana da ƙarshe, to bayan bincike da bin diddigi dai mun gama fahimtar inane asalin wannan baiwar Allah'n kuma munada yaƙinin daga masararutar Joɗa ta fito.
To yau dai kam ranar data kamata mu shiga da ita ciki da yardar ubangiji tazo.
Kamar yadda muka tsara, yanzu zamu tafi".
Cikin tsananin jin daÉ—i da kuma fargabar ko ya al'amarin zai kasance Bappa yace.
"Alhamdulillah mu duk a shirye muke, fatanmu Allah yasa ina munje ta tuna baya, ta tuno ita wacece".
Da sauri ArÉ—o Bani yace.
"In Sha Allah ma zata tuna Malam Babayo".
"Allah yasa haka".
Al'ameen ya faÉ—a.
Amin Amin sukace kana duk suka miƙe suka fito.
Kana Bappa yazo yacewa Ummey da Dedde su fito.
Nan suka mara musu baya.
Mota É—aya Bappa da Abboi da ArÉ—o Bani suka shiga.
Ummey da Dadde da Al'ameen kuwa suma mota É—aya suka shiga.
Sauran kuma ƴan tsaronsu ne a ciki sai motar Yah Salmanu da Hafsi ƙanwar Shatu a haka suka fito daga Rugar Bani suka nufi Masarautar Joɗa.
A hankali Ummey ta jingine kanta da jikin kujera tare da dafe ƙahon zuciyarta a hankali ta furta innalillahi wa innailaihi rajiun".
Sabida tsananin tsinkewar da zuciyarta keyi Dedde kuwa hankalinta naga makiyayan dake zirya.
A nan cikin birnin Æadamaya a tsakiyar Masarautar JoÉ—a kuwa.
Gaba É—aya su Umaymah suna falon Shatu.
Aunty Rahma ce da su Sara a kitchin, Aunty Juwairiyya tana part É—inta da Hibba.
Junainah da Ishma kuwa suna kitchen tare da Aunty Rahma.
Kowa sabgar gabansa keyi.
A hankali Shatu ta miƙe ta nufi ƙofar falon Sheykh da sallama a bakinta.
Shiru ba kowa a falon tray'n breakfast É—inshi shida Haroon ta ajiye bisa Dinning table.
Ganin ba kowane yasa ta turo kanta cikin bedroom É—in.
Shiru ba kowa a hankali ta ƙara so ciki tana cewa.
"Salam Yah Sheykh". Ƙofar bathroom ta matso a hankali ta tura ba kowa a ciki komai yana kimtse tsab-tsab.
"Toh ina yaje kuma yau Lahadi kuma ai babu inda zaije".
Shiru tayi tare da juyowa ta matso tsakiyar É—akin jujjuya kanta tayi ba mutun ba alaman mutun a É—aki.
Har ta juya zata fita, sai kuma tayi sauri ta juyo tazo bakin gadonshi, abun data hanƙo ƙasan pillow'nshi ne yasa ta sunkuyowa da sauri hannunta tasa ta zaronshi.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun".
Ta faÉ—a jiki na rawa tare da sakin fuskar robar da Sheykh ake amfani da ita a matsayin Jahan.
Da sauri ta juyo da nufin zata fita, sabida tsoron daya rufeta.
Sai kuma tayi sauri taja da baya tare da zare idanunta dai-dai lokacin da ta iso jikin marfin wodurob É—in sa
Wanda yayi dai-dai da lokacin da Sheykh ya turo marfi ya fito.
A gigice take jujjuya kai tare da zaro ido.
Sai kuma ta juya da sauri ta kalli fuskarnar da ƙarfi ta buɗe baki tare da cewa.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun Yah Sheykh".
Da sauri yasa hannunshi ya kamo nata ya fizgota jikinshi cikin haÉ—e fuskarsu wuri É—aya yace.
"Na'am Aysha please kada kiyi ihu tsaya nitsu nine Muhammad Jabeer Yah Sheykh mijinki Abu Afreen".
Cikin yanayi kaÉ—uwa tace.
"Yah Sheykh kai mutum ne ko al'jan".
Da sauri ya kamo hannunta suka iso gaba durowar.
Buɗe ƙofar yayi, kana a hankali yasa hannunshin ya ture, al'kyabbas ɗin shi dake jere a hanga a saƙale, sai ga wani ƙofa mai kamar glass.
A hankali yace.
"Aysha nitsu ki jini kinji ko".
Cikin sauƙe numfashi tace.
"Toh".
Kanshi ya gyaÉ—a kana a hankali yace.
"Kinga wannan wurin ko?".
Da sauri tace.
"Eh naga kamar ƙofa ne".
Jawota yayi suka ɗan matso hannunshi yasa ya tura ƙofar da sauri tace.
"Lahh".
Sabida ganin wata Æ´ar siririyar hanya mai tsawo.
A hankali yace.
"Ni mutum ne Aish yanayin tsarin masararutar JoÉ—a ne yasa dole nake amfani da wasu ababen.
Kinga wanan hanyar har cikin bedroom É—in LamiÉ—o da Abba na duk akwai su.
Muna haÉ—uwa dasu a É—akin LamiÉ—o lokuta da dama.
In kina so anjima zan nuna miki, dan yanzu Lamiɗo ya rufe ƙofarsa ne da yanzu zamuje".
Da sauri tace.
"Me kukeyi a ɓoyen".
Jawo ƙofar yayi ya rufe kana a hankali yace.
"Ina wani aikine Aish Kuma aikin sirrine, tsawon shekaru inayi babu wanda ya sani sai LamiÉ—o da Abba na da Umaymah sai yau kuma da kika zama ta uku".
Ya ƙarashe mgnar yana jawota suka zauna bakin gado.
A hankali ta sauƙe numfashi ido ta zuba mishi a hankali tace.
"Kai SS ne ko Yah Sheykh?".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Ba'a faÉ—a kiyi shiru kada wani yaji kinji ko sirri ne BoÉ—É—o na".
Murmushi mai cike da jijjina tayi mishi.
Shi kuwa ruggume ta yayi ya koma baya ya kwanta.
Dai-dai lokacin kuwa motar Salmanu dake gaban motocin su Abboi ta kusa kai cikin matsarautar JoÉ—a bayan an wangale musu gate.
Wani irin rumtse ido da ƙarfi Ummey tayi tare dasa kanta bisa guiwowinta sabida wani irin masifeffen tsarawa da kanta yayi da azaban ƙarfi.
Kai tsaye bakin part É—in su Sheykh Salmanu ya nufa dasu sai dai Motar Abboi da sauran duk a can baya bakin fada suka tsaya inda Bappa ya nuna musu.
Yadda suke ƙara kusanto Part ɗin su haka sarawa da bugun zuciyar da Ummey keyi yake ƙaruwa.
A can cikin falon Shatu ma, da sauri Umaymah da Mamma Suka kalli juna sabida masifar bugawa da ƙirazansu sukayi.
Sheykh kuwa da ƙarfi ya ruggume Shatu sabida ji yayi tamkar zuciyarsa zata faso ƙirjinsa ta fito woje.
Jalal da ke Part É—in Yah Jafar da sauri ya rumtse idanunshi shida Yah Jafar É—in.
Hakama Jamil dake tare dasu Gaini.
A hankali motocin sukayi parking.
Ummey kuwa wani irin ƙara rumtse idanunta tayi da masifan karfi.
Dedde kuwa a hankali ta buɗe ƙofar.
Ta sako ƙafarsa cikin shigarta ta al'farma.
Shi kuwa Al'ameen da sauri ya zagayo ya buÉ—e wa Ummey kofar tare da cewa.
"Ummey mun iso bismillah".
Cikin tsananin danne sarawar da kanta keyi ta ɗago jajayen idanunta a hankali ta zuro ƙafafuwan woje.
Ras ras Din dab din dab haka zuciyarta ta bada wasu tagwayen bugu.
Da sauri tasa hannunta ta dafe ƙirjinta.
Dedde kuwa a hankali ta zagayo inda take.
Shi kuwa Al'ameen a hankali yace.
"Bismillah ku shiga ga ƙofar".
A hankali Dedde tace to kana ta nufi ƙofar.
Ita kuwa Ummey cikin rawan jiki ta ɗaga ƙafarta ta dama ta ɗaura kan barandar tare da ƙara dafe ƙirjinta da rumtse idanunta sabida jujjuyawan da kanta ya fara.
Shi kuwa Al'ameeen bayansu yabi.
Shi kuwa Salmanu a hankali ya kalli Hafsi ƙanwar Shatu dake bin Khadijah.
Cikin yin ƙasa da murya yace.
"Ko in É—agaki ne in kaiki".
Cikin jin kunya tace.
"A a Yah Salmanu zan shiga da ƙafata".
Su Bappa kuwa Sarkin ƙofa ne yayi musu iso zuwa cikin fada.
A hankali Dedde ta kai hannunta ta kama handil ɗin ƙofar falon ta murɗa tare da turawa kana tasa ƙafarta ta dama ciki bakinta ɗauke da sallama.
Aunty Rahma dake fitowa daga kitchen Junainah na biye da ita da sauri ta É—an juyo ta kalli Dedde tare da cewa.
"Wa alaikassalam".
Ta ƙarashe amsa sallamar tana matsowa dan ganin wani irin fitinenne kama da Dedde keyi da Shatu.