Sashe 41
Garkuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin Shatu kuwa ya girma ya fito ras, sabida yayi watanni takwas.
Afreen kuwa Alhamdulillah tana gudu ko ina yanzu ga gwarancinta ras.
Watanninta goma sha É—aya amman in ka ganta zakayi zaton Yar watanni goma sha biyar ne.
Alhamdulillah su Shatu sun kammala karatun su lfy, komai yayi yadda ake buƙata.
Hajia Mama kuwa duniya tayi mata atishawar tsaki.
Sabida kuturta ya kuma shiga yatsunta na tsuntsayen.
A hankali take tafiya Afreen na riƙe da yatsarta.
Tana ta gwaranci.
"Abba! Abba! Abba!".
Murmushi yayi tare da buÉ—e mata hannunshi da sauri ta tsaki yatsar Shatu ta nufi inda Sheykh ke tsaye, cikin tarin farin ciki yace.
"Oyoyo Mamina".
Kana ya É—agata sama.
Murmushi Affan yayi tare da cewa.
"Afreen sarkin wayo ita kowa natane".
Jamil ne yace.
"Hmmmm ai ni jiya ta bani mmki.
Wai Ance Abbanmu na kiranta zai bata sweet wai sai tace.
“Bata so Abbanta a kawo mata".
Dariya Ummi tayi tare da cewa.
"Kuma daga baya ta bishi da gudu tana Abba cha ciwiut".
Murmushi Sheykh yayi kana ya sauƙeta, tare da kallon Shatu dake zaune ta tasa cikinta gaba.
Cikin wasa ya kalli Jalal daya shigo yanzu yace.
"Jalal ko dai zamu É—aga bikin kun nanne sai Aish ta haihu zatafi sakewa".
Da sauri ya katse wayar da yakeyi da Hibba tare da cewa.
“A'a me yayi zafi, tasha zamanta a ɗakinta mun hutasshe ta zuwa bikin".
Jamil kuwa kwaɓe fuska yayi tare da cewa.
"Uhumm wai a É—aga".
Dariya Affan yayi tare da kallon Sheykh dake musu murmushin wasa nan dai sukaci gaba da tattaunawa kan bikin.
Alhamdulillah yau bikinsu Jalal saura mako É—aya rak.
Komai ya kankama.
Tuni baƙi sun fara cika masarautar Joɗa tako wani yanki.
Hotels din Æadamaya LamiÉ—o da Sheykh sun kama fiye da rabinsu sabida, sauÆ™ar baÆ™in da suke tsastsafowa tako wani yanki.
Yau jumma'a wanda ya kama sauran kwana bakwai cin a nawa Sheykh rawani jumma'a mai zuwa kenan.
Wanda ya kama kuma ranar za'a É—aura aurensu Jalal tuni su Umaymah da tawagarta sun iso.
Tun da safe kuwa yau Shatu ta tashi da ciwon mara, kaÉ—an-kaÉ—an.
A haka take ta sabgoginta, sabida tana tare da amare duka uku.
Sha ɗaya dai-dai na safe Allah ya sauƙeta lfy ta haifi ɗanta na miji santalele.
Farincikin a ahlin Sitti ba'a mgn.
Bayan an gama kimtsa mai jego da jaririnta kato fari ƙal dashi.
Suna kwance Sheykh ya shigo.
Cikin tarin farin ciki dan yana gidan Malam Abubakar ne Yah Jafar ya kirashi ya masa al'bishir.
Cikin jin daÉ—i ya zauna gefen Shatu.
Tare da miƙawa Safiyyah hannu ta miƙa mishi jaririn murya cike da zallan farin ciki yace.
"Alhamdulillah masha Allah. Allah na gode maka, da wannan kyauta da kaimin. Ya Allah kasa baÉ—i iwar haka mu samu tagwaye".
Dariya sukayi baki É—ayansu ganin yadda Shatu ta zaro idonta cikin alamun tsoron tace.
"Wayyoooooooo Allah na. Yah Sheykh sai kace wata inji".
Aunty Rahma ce tace.
"Ato ai da alamar hakan zakuyi tunda gashi a shekara É—aya an samo irin tagwayen Nana FaÉ—ima".
Ummi ce dake gefe tana fifitawa Shatu tea tace.
"Ko Æ´an ukune Allah ya kawosu akwai masu tayaki rainon su.
Inji gashi yanzu Afreen tunda aka yayate, sai dai tazo ta leƙaki tayi gaba abinta".
Da sauri yace.
"Uhumm yauwa Ummi na gaya mata dai".
Ya ƙare mgnar yana sumbatar goshin yaron cikin tsananin farin cikin da son yaron.
Sai kuma ya kalli Mamey dake shigowa yace.
"Mamey da waye yake kamane?".
Matsowa gabanshi tayi ta kalli fuskar jaririn kana tasa hannunta ta tallabo tashi fuskar.
Cikin jin daÉ—i tace.
"Da kai yake kama".
Cike da jin daÉ—i yace.
"Alhamdulillah".
Nanfa akaci gaba da hidima.
Yau kwana biyu da haihuwar Shatu.
Zaune yake agaban Mamey da Abbanshi, kai ya É—an É—ago ya kalli Abbanshi tare da cewa.
"Ummm Abba nace wanne suna za'a sawa yaron?".
Murmushi mai cike da jin daÉ—i Abba yayi tare da cewa.
"Na baka zaɓi zaɓawa ɗanka sunan da kafi so".
Murmushi mai cike da jin daÉ—i yayi tare da cewa.
"Mamey kefa, ko Jadda kikeso inyi mai suna".
Yayi mgnar cikin raha.
Da sauri tace.
"Mutun da É—an shi mun baka damarka a matsayinka na uba".
Kanshi ya sunkuyar tare da cewa.
"Ngd matuƙa da wannan damar".
Daga nan ya sallamesu ya miƙe ya fita.
Bedroom É—insa ya wuce.
Yana shiga ya kira Shatu a waya, ta kawo mishi É—an.
Yayi mishi huÉ—u ba.
Ido ta É—an zuba mishi tare da cewa.
"Me sunanshi?."
Murmushi yayi tare da kashe mata ido a hankali yace.
"Sai ranar suna zakiji".
"Abinma sirrine kenan".
Ta faÉ—i tana murmushi.
"Ina da wani sirrine bayan ke, Y.M.D.G na".
Ido ta zuba mishi tana mai nazartar baƙaƙen da yake yawan faɗi wasu lokutan.
Kiranshi da akayi a wayane yasa ta bar zancen.
Ranar jumma'a, da safe bayan an fito sallan asabu, aka raÉ—a sunan yaron kana suka nufi cikin gida kowa na mamakin sunan da Sheykh ya sawa É—ansa.
A tare suka shiga falon shida ƙannensa.
Da sauri Mamma tace.
"Affan me sunan É—an naku?".
Murmushi Affan yayi tare da nuna Sheykh dake wucewa Side É—insa Haroon da Ibrahim na biye dashi a baya.
Da sauri Umaymah tace.
"Affan me sunan ana tambayarka kayi shiru".
Cikin dariya yace.
"Uhumm Yah Sheykh da abun mmki sunanshi fa ya sawa É—an, duk zuriyar mun nan ya rasa wanda zaiwa takwara sai yayiwa kanshi".
Cike da mamaki su Ummi sukayi salati, shi kuwa Sheykh murmushi yayi tare da juyowa jin yadda suke salati yana dariya yace.
"Yoh duk zuriyar mu, nuni wanda sunanshi ya kai nawa daɗi Muhammad Jabeer, kuma kafin in burge wani gwara in burge kaina da kaina. Kuna ina son yaron yaji daɗin da nakeji a duk sanda naji an kirani da sunan sabida iyayena sunmin kekkyawan zaɓi".
Murmushi Mameyn tayi tare da cewa.
"Allah ya raya Muhammad Jabeer ƙarami yasa ya gaji halayyar mahaifinshi".
Amin Amin sukace baki É—ayansu.
Ita kam Shatu murmushi takeyi tana shafa kan jaririn.
Tare da kallon Afreen dake zaune gefenta.
Oh Allah mai iko wai itace dai Shatu da yara har biyu.
Nan dai sukaci abinci.
Kana duk mazan suka fara shirin fita É—an sha biyu dai-dai za'a naÉ—a Sheykh.
Ƙarfe ɗaya saura.
Duk illahirin manyan Masarautar Joɗa, da baƙin sarakuna.
Da duk maza ahlin masarautar JoÉ—a, hatta Jabeer da yau aka fita sunansa.
Jalal yazo dashi.
Gaba ɗaya ɗakin rantsawar ya cika maƙil da bani Adam.
Babu abunda ke tashi sai sarewa da tambura da al'gaita da kakafi.
A hankali LamiÉ—o ya tashi bisa kujerar, kana ya matsa.
Sarkin naÉ—i, ya kamo hannun Sheykh dake cikin shiga ta al'farma shigar limancin.
Ya matso dashi gaban kujerar, kana a hankali yasa hannunshin ya zare hiramin kansa.
Sannan ya sunkuyo ya amshi.
Rawanin da Lamiɗo ke miƙa mishi.
Yana daga tsayen ya naÉ—a mishi.
Kana ya juyo bayanshi da niyar zare al'kyabbar jikinshi.
Da sauri LamiÉ—o yace.
“A'a barshi da shirgarsa ta limancin, shigar sarauta bazata kori ta limancin ba.".
A hankali Sheykh ya lumshe idonshi yana mai jin wani irin masifeffen nauyi dake ratsa kanshi nauyin rawanin mulkin Masarautar JoÉ—a.
Shi kuwa Sarkin naÉ—i kai ya gyaÉ—a kana ya zaunar da Sheykh bisa asalin kujerar masarautar JoÉ—a da sunan Allah a bakinsa.
Kana aka miƙa mishi sandan ya amsa ya riƙe, sarkin fada ya matso kusa dashi.
Hakama É—an zagi.
Sauran fadawa kuwa duk sai suka matsa suka janye labulen da sukayi musu da manyan garunan su.
Lokacin É—aya gaba É—aya mutanen cikin hall É—in duk suka zauna
Tare da jinjina kai, dan ko kai sarkine in kazo Masarautar wani sarkin to shine a sama.
Sabida kalmar nan ta bahaushe.
(Kare ma a gidansa zaki ne)
Bare kuma sarki.
Nanfa makaÉ—a da mabusa duk suka É—auki amo.
Cikin wani irin rauni Sheykh ya lumshe idanunshi tare da ci gaba da tasbihin da yake abokin rayuwarsa.
Sabida wani irin tashi da tsikar jikinshi keyi.
Sarautar tana ratsashi.
Bayan an gama naÉ—a shi ne, aka naÉ—a Baba Basiru a matsayin Galadima.
Wanda dama anfi son Galadima yafi sarki shekaru.
Nan kuma aka naÉ—a Affan Chiroma.
Kana Jalal Wambai, Jamil Durbi.
Yah Jafar kuwa MajidaÉ—in Masarautar JoÉ—a.
Masha Allah komai dai ya tafi yadda ya kamata.
Nan aka naÉ—a duk sauran hakimai.
Kiran sallan Jumma'a ne ya tadasu a taron.
Nan kuma aka raka'a.
Inda Sarki Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero JoÉ—a ya kasance limamin kamar kullum.
Bayan ya tsaya ya dai-dai-ta tsayuwarsa bisa mimbari.
Ya fuskanci taron al'ummar Annabi dake cike maƙil a masallacin da harabar.
Gyaran murya yayi cike da rauni dan fara hudbar jumma'a kamar kullum.
Cikin taushin murya da lafazi.
Murya na rawa yace.
"Mulki, da sarauta".
Sai kuma muryarsa ya fara rawa, sabida nauyin abinda yake jin tsoro daya ratsa kanshi.
Hawaye na zuba yace.
“Da ace ɗan Adam yasan nauyin dake cikin kalmar mulki ko sarauta da bai ɗauke ta ƙaramar kalmaba.
Da daga cikinmu mun dena sha'awarta sabida nauyi da haƙƙin wanda kake matsayin shugaban su, da zai rataya akanka".
Sai kuma ya sunkuyar da kansa.
Cikin rauni da zubda hawaye ya fara zazzafan hudba kan sarakuna da kuma shugabannin.
Wanda gaba É—aya aka nitsu akayi cib.
Mafi akasarin mutane rauni da tsoro ya sasu zubda hawaye.
Bayan ya idane, akayi salla aka idar.
Sannan dubban al'ummar Annabi Sallallahu alaihi Wasallam suka shaida É—aurin auren. Jalaluddin da Muhibbar, (Jalal and Hibba) Khadijah da Jamil. Rafi'a da Al'ameen.
Al'amarin yayi armashi matuƙa gaya.
Nan aka fito, mafi akasarin manyan sarakuna da shugabanni da baƙi a take Airport suka fara wucewa, sabida komawa.
Jirage kuma a ranar tamkar a jidda Airport a lokacin aikin Hajji.
Haka jirage ke tashi. A Æadamaya International Airport.
Tuni mutanen Cameroon sun tafi da amryarsu.
Da duk mutane su.
Hakama su Aunty Rahma sun kai Hibba part É—in ta.
Mutanen Cameroon kafin su tafi sun kai.
Khadijah Part É—inta.
Sosai mutanen gidan suka É—an rarragu.
Sheykh kuwa hada-dadar jama'a ta hanashi shiga gida.
Sabida zaman fada.
Sai bayan sallan isha'i ya samu shiga gida.
Kai tsaye Part É—in Mameynshi ya wuce.
A can kuwa ya samu su Umaymah gaba dayansu.
Sai Shatu da Junainah dake Part É—insu suna gyarawa sabida mutanen sun tafi.