Sashe 10
Garkuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kullum ana dukansu ina kuka.
Idan an tafi sai manya biyun su taru kan karamin cikinsu, suyita mishi tofi dan shi irin mutanen nan ne da basa jurar wahala lokuta da dama yana sumewa in an dakeshi sai daga baya ya farfaÉ—o, sukanyi ta kuka ina tayasu.
Daga nan muka fara sabawa, ina mamakin rauninsu kan iyaye da yar uwarsu mace da kullum suke tunota nakan ruggume karamin inyi ta kuka dan yana tuna min yarana.
A haka dai har ranar wata jumma'a nace musu dan Allah zan tambayesu me sukayi aka kawosu nan.
To anane sukayi ta rantse min da Allah suna cewa wlh tallahi su basu san me sukayi ba, kawai an kamosu daga wurin kiwone aka kawosu nan,
Babban cikinsu ya ƙara da cemin.
"Yanzu shekararmu É—aya a nan harda watanni, kullum in an zo an dakemu da dare akan dawo ace mana mu amsa cewa mu yan kinnafin ne, sukance mu yarda kawai cewa mu yan kinnafin ne za'a dena dukanmu, mu kuwa bamu ma san menene hakan ba sai daga baya muka fahimci masu sace mutane suce a basu kuÉ—ine Æ´an kinnafin É—in.
Yace min wlh tallahi summa tallahi mu ko gyadar gonon wani bamu taɓa sacewa mu bawa dabbobin bama, bare mu sace mutane ta yaya zamu yarda da laifin da bamuyi ba.
Har ace muyi bayani a saka a gidajen tv da Radio, to nima a ranar na basu lbrin abinda ya kawoni nan ga mamakina sai sukayi ta kuka wai sun tausaya min gwara su basa da yara sai iyaye."
Cikin rauni Sulaiman ya É—an tsagaita kana ya É—ago kanshi ya kalli Sheykh da sai yanzu hawayenshi suka samu zubowa.
Cikin kukan yaci gaba da cewa.
"Inda na tabbatar da cewa,
sharri akeyi musu basu san komaiba.
Saida aka fara batun belina.
Randa aka kai kuÉ—in sukazo sukace an kawo belina amman ba kuÉ—inane zai fiddani ba.
Dole sai an samu wanda za'a liƙa sharrin sune suke kawo min kayan satan ina saya ta hakane za'a nunawa duniya an kama ainihin masu satan shiyasa ni za'a sakeni.
Hankalina ya tashi ina zan samo wasu ayi musu sharri a banza tunda asalin waɗanda suka saida min saraƙunan can dai sun gudu su kansu hukuma sun kasa kamosu.
Cikin tashin hankali nace.
"Musu ni kam babu wanda zan nuna ince shike kawo min kayan sata ina saya.
Sai suka cemin to asheko zanci gaba da tabbata a cikin magarƙamar babu belin.
Ga mamaki na, sai yaran nan sukace.
To su sun amince in nunasu su, da dai ace su masu satan mutanene gwara satan sarƙa kuma zasu samu a dena dukansu dan haka gwara su yarda su ɓarayin sarƙane, sabida su dai basu san darajar gold ba, basu kuma san saraƙunan matar gwamna bane.
Haka yasa nace musu a a ni kam bazan iyaba bazan bari a ɓata musu sunanba."
Hawayensa ya share tare da cewa.
"Sai babban cikinsu ya matsoni cikin rauni yace.
Kada mu zauna damu da kai duk mu ƙare rayuwarmu a nan.
Mu dai bamu da gatan kowa a duniya sai Allah da iyayenmu, kuma mu yanzu iyayenmu su sadakar dan zasuyi tunanin kashemu akayi.
Kuma mu bamu da yara, kai kuma kana da mata da yara da ƙanne da yayu waɗanda kaine gatansu.
Mun amince zamuce duk abinda sukeso a fidda kai.
In ka fita in ka samu dama ka nunawa duniya halin da muke ciki, kasa makusantanka su samu a Addu'o'insu tabbas munsan watan wata rana gsky zatayi aikinta, mu mun É—aukeka matsayin É—an uwanmu."
Sai kuma ya kife kansa a jikin kujera yaci gaba da kuka yana mai cewa.
"Yana gaya min haka ƙanne shi ma suka matsoni sukace su sun san tasu ta ƙare a ciki amma zasu tsaretar dani.
A haka a gabana inaji ina gani aka fitar dasu woje, aka jera bindigogi da makamai da kuÉ—aÉ—en a gabansu, kana aka dasa musu camera bayan an gaya musu abinda zasuce.
Anan ake tambayarsu ku su wayene.
Cikin bushewar zuciya ganin sharrin da akeyi musu ido na ganin ido sukace.
"Mu Æ´an kinnafin ne".
Kana aka sake cewa.
"Ku wanne yarene?".
Sukace.
"Mu fulanine".
Wlh sai gashi wanda suke ciki kusa dani suna dariya suna cewa.
"Shegu fulanin dole sai mun koreku a kasar nan mun hanaku jin daɗi mun ɓata muku sunan ƙabilar shugaban ƙasar namu hegen bafullatani".
Hankalina ya tashi dana gane wai ashe duk anayin hakane dan a ɓata sunan fulanin a dozarta ƙabilar shugaban ƙasar to amma. Alhamdulillah tun daga ranar aka dena dukansu da wahal dusu".
Wani nannauyan numfashi suka sauƙe gaba ɗayansu suna masu zubda hawaye.
Cikin rauni Sulaiman yace.
"To tashin hankali na yaune za'a haska video da kayiwa yaran a nuna duniya cewa sune ɓarayin mutane".
Tofa wannan al'amari yayi masifar tada hankalin Sheykh yayi kukan da shi kanshi bai san yaushe rabonsa da yinsa ba.
Ganin ƙarfe ɗaya ta wuce ne yasa ya sharce hawayensa, murya a disashe yace.
"Zan tafi Malam, amman in sha Allah zan meda hankali na kan batun yaran nan, in Allah ya yarda zan sasu cikin addu'o'i na.
Zan kuma roƙi duk limamen masallacin jumma'a su sasu a addu'a."
Cikin tsananin jin daÉ—i Sulaiman da Malam sukace.
"Allah ya yarda ya bamu sa'a, ya tsaresu al'farmar Annabi da al'ƙur'ani ya fito dasu lfy".
Amin Amin yace kana ya sallamesu ya tafi.
Daga nan kai tsaye makarantar su Shatu ya wuce ya É—aukota.
Ta lura yana cikin tashin hankali kuma duk jikinsa a mace.
To amma ganin lokacin salla yayi ne yasa batayi mishi mgn ba.
Suna dawowa ta shiga É—akin ta, shi kuwa al'wala yayi ya fita.
Bayan an idar da salla kuma wurin LamiÉ—o ya shiga ya mishi duk bayanin da Sulaiman yayi mishi.
Wannan ne yasa baiyi baccin tsakanin azahar da la'asar ba.
Kiran salla ne ya medasu masallaci.
Ita kuwa Shatu koda ta shiga wonka tayi kana tayi salla, akan sallayar ta miƙe, dan ta gaji.
Ummi kuwa jin motsinta ne yasa taje ta kai mata abinci.
To nanma da kyar taci kaÉ—an kana ta koma ta konta.
Itama Ummi ta koma É—akinta.
Saida tayi sallan la'asar ne ta fito ta nufi kitchen ita da Sara.
Ita kuwa Shatu cikin ɗan jin sauƙin gajiyar ta miƙe doguwar riga ta zura kana ta fito, falonta.
Har kamar zata wuce babban falonsu kuma sai taji ƙafarta ta riƙe wanda yafi wata da fara mata hakan.
A hankali ta ja ƙafar ta isa gaban kayan kallon, hannu tasa ta kunna TV inda ta samu tashar BTV a kunne anayin zabi sonka.
A hankali ta koma baya ta zauna bisa kujera 3 str, tana fuskantar tv murmushi tayi tare da cewa.
"Oh ikon Allah ashe har yanzu anayin zaɓi sonka".
Zama tayi tanajin ana gaishe-gaishe bayan minti biyar asa waƙa tayi minti biyar a cireta.
Ƙarfe biyar dai-dai aka gama shirin.
Shi kuwa Sheykh ana idar da sallan la'asar ya nufi gida,
tafiya yakeyi cikin yanayin tsantsar dauriya da danne tsananin halin da yake ciki.
Sabida wani irin masifeffen sarawa da ƙugunsa yake har sai yaji ƙahon zuciyarshi ya bada sautin ras-ras wata iriyar fitinenneyar zuface mai azabar zafi ce ta keto mishi tana tsastsafo mishi tako wani hudan gashin jikinsa.
Da sauri ya tura ƙofar falon ya shiga.
Ba kowa sai wulgawar Ummi daya hango ta shiga kitchen.
Yah Jafar kuwa gidanshi ya nufa.
Jalal kuwa yau kwana ukuma kenan baya gida.
Jamil kuwa tun safe daya tafi wurin aiki bai dawoba.
Wani irin azabebben karkarwa jikin shi ya farayi da tsuma sabida azabar ciwon da bai taɓa jin makamancinsa ba.
"La'ilahaillaha Muhammadu Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama".
Haka yake maimaita kalmar shahadar sabida jin tamkar ciwon zai É—auke ransa.
So yake ya zaro wayarshi ya kira, Shatu ko Umaymah ko Abbanshi ko LamiÉ—o ya gaza wani irin raunine ya rufeshi wanda yasa hawaye fara kwaranyo mishi, cikin zuciyarsa yake tunanin shike nan zai rasu ba tare da burinshi ya cikaba zai tafi matarsa bata haifuba zai bar É—ansa maraya.
Zai bar su Jalal cikin makirin masarauta.
Wani irin rumtse idanunshi yayi da azaban ƙarfi tare da taune lip ɗinsa na ƙasa.
Kar-kar haka jikinsa ke karkarwar.
Babu abinda yake cewa sai maimaita kalmar shahada, wani irin jujjuya kai yayi ya tafi luuu ya...!
Ita kuwa Shatu, a hankali ta sunkuyar da kanta ta É—aura hannunta bisa cikinta.
Tana jin yadda É—an cikin ke jujjuyawa.
Da sauri ta É—ago kanta ta zubawa tv Ido, jin É—an jaridar na cewa.
To masu kallo barkanmu da war haka yau dai gamu tare da SP Daniel tare da rahoton ƴan kinnafin ƴan bindiga daɗi, daga babbar het kotansu na babban birnin tarayya, zaku kalli video ƴan kinnafin ɗin kana muji ƙarin bayani daga SP Daniel
Ido ta zubawa allon tv lokacin da aka fara haske makaman dake jere gabansu Yah GiÉ—i Seyo Gaini da wasu matasan fulani waÉ—anda aka kamo kamar yadda aka kamosu.
Ana cikin nuna makaman, ana jefa musu tambaya.
"Wato wannan shine makaman da kuke amfani dasu a matsayin ku na masu GARKUWA da mutane?".
Dai-dai lokacin kuma ake haska camerar kan fuskar Yah Gaini wanda duk sauyin da zai samu a duniya bazata gaza ganeshi ba.
Ana ƙarasa haska fuskarshi da fuskar Yah Seyo da Giɗi.
Tayi wani irin yunƙura da azaban ƙarfi zuciyarta kuwa tayi wani irin azabebben tsinkewa da masifan karfi.
Wani irin azabebben juyi É—an cikinta, yayi gaba É—aya jikinta karkarwa ya farayi kamar wacce aka jonawa wutar lantarki.
Wani irin rumtse idanunta tayi da ƙarfi tare damke cikinta, ta buɗe bakinta da azabar firgita da karfi ta kurma wani irin azabebben kuka mai haɗe da ihu da kiran sunan.
"Yah Giɗi Seyo Gaini wlh ƙaryane. Sherri akeyi maku innalillahi wa innailaihi rajiun hasbunallahiwani'imanwakil wayyoooooooo Bappa wayyoooooooo Ummey na Yah Sheykhhhhhhhhhhhhh...!