← Book details Garkuwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 45

Sashe 29

Garkuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

By
*GARKUWAR FULANI*
4/6/21, 4:15 PM - &: Ya sauƙe idanunshi kan Giɗi Seyo Gaini.
Cikin wani irin yanayin tarin farin ciki mai sanya rauni.
Wasu zafafan hawaye suka kwaranyo mishi.
Da sauri ya yunƙura ya juyo ya fuskanci al'ƙibila. Sujjadar godiyar Allah yayi kana ya ɗago yana mai zubda hawaye.
Ita kuwa Shatu da sauri ta ƙarasa garesu, kawai sai ta faɗa jikinsu baki ɗayansu, tare da sakin raunataccen kuka.
Cikin rauni da yanayin kula Seyo wa mai tausayi kamar uwa yace.
"Shatu dena kuka, mu godewa Allah".
Sai kuma ta kalli Yah GiÉ—i cikin sanyi ta ruggume shi tare da cewa.
"Tunda na rasaka kusa dani na rasa abokin faɗa da tsama, shiyasa lokuta da dama ina jin daɗin inyi taƙaddama da Gimbiya Saudatu dan sai yana tunamin ta ƙaddamar mu, da Yah Giɗi na abokin faɗana".
Cikin zubda hawaye shima GiÉ—i yayi murmushi tare da janyeta jikinshi kana yace.
"Nayi kuka a lokuta ma banbantan da bazan iya ƙididdiga ba sabida tunoki da rayuwarmu".
Hannun tasa ta share hawayenta kana ta kalli Yah Gaini wa mai matsayin Uba cikin kulawa da yanayin rayuwarta yace.
"Shatu ina Ba'ana ko mun samu nasarar rabuwarki dashi".
Da sauri tace.
"Yah Gaini Allah ya rabamu da Yah Ba'ana".
Cikin tarin jin daÉ—i yace.
"Alhamdulillah".
Dai-dai lokacin suka isa gaban Bappa daketa zubda hawaye.
Zama sukayi a gabanshi gaba dayansu huÉ—u.
A hankali GiÉ—i ya sunkuyo ya kwantar da kanshi bisa cinyar Bappa tare da sakin sassayan kuka a hankali yace.
"Bappa mun ganka kaida Shatu ina Innarmu ina Ummey ina Junainah ina Yah Lado?".
Da sauri Ummey tasa hannunta ta rufe bakinta jin kuka zai kubce mata.
Sai dai tuni sautin kukan ya fito.
Da sauri GiÉ—i ya rarrafo gabanta murmushi yayi still Ido na zubda hawaye a hankali yace.
"Alhamdulillah Ummey Junainah ina Innarmu da Yah Lado".
Cikin kuka Junainah ta faÉ—a jikinshi tare da cewa.
"Arnan Ɓacama sun kashe Innarmu sun kashe Yah Lado sun kashe mutane da yawa na rugarmu".
Da sauri GiÉ—i ya juyo ya kalli Ummey cikin tashin hankali da kubcewar kuka.
Gaini da Seyo suma kuka mai rauni suka sake ganin Bappansu yana jinjina musu kai alamun zancen Junainah hakane".

Shiru falon sukayi baki ɗayansu sai sutin kukan Giɗi, Shatu, Junainah, Ummey, Seyo, Gaini. Raunin da kukansu ya sauƙar a zuciyar Bappa ne yasa shima sakin kuka dan yau sai sukaji gaba ɗaya rasuwar Yah Lado da Inna ta dawo musu sabuwa.

Sosai Shatu keyin kuka tana durƙushe ta tanƙwashe sawunta, hakama Ummey.

Gaba ɗaya kab falon saida idon kawa ya ciko da ƙwalla.

Cikin Rauni Sheykh ya matso inda Shatu ke durƙushe gaban yayun nata, cikin sanyi ya kalli Bappa Ummey murya a raunace yace.
"Tabbas bansan irin ƙunar da kakaji a cikin ranka ba Bappa amman nasan kwatankwacin kamannin ƙunan rashin ɗa, a suman da Afreen tayi naji ciwo da ƙuna a zuciyata tamkar ban taɓa farin cikiba, nasan zafin rashin uwa, amman ban san zafin rashin mataba dan kamin gatan bani Mar'atussaliha ta zame min GARKUWA tana sani farin ciki a duk lokacin da nake cikin baƙin ciki."
Shiru yayi sai kuma ga hawaye shar-shar a idanunsa cikin rauni yace.
"Na samu komai da nake nema a rayuwata daga gareka ka bani mata ta gari, Allah ya azurtamu da samun ƙaruwar arzin haihuwa sanadinka Ummey na ta dawo.
Inama! inama! ace Inna da Lado ɓata sukayi ba rasuwa ba, da tabbas zanyi iyakar iyawata in dawo maka dasu da izinin ubangiji.
To amman wannan hurumin ubangijin sammai da ƙassaine.
Kayi haƙuri Bappa Allah ne ya baka Inna matsayin mata ya ɗauketa ya sauyama da ƴar uwarta kuma Allah shi ya baka Lado ya ɗauke shi kuma ya killace maka Seyo Gaini Giɗi, wanda wata ƙil da suna Rugar ba'a sacesu ba da an kashesu.
Gashi yanzu Allah ya dawo maka dasu.
Bappa kace Alhamdulillah ka godewa Allah da ni'imar da yayi maka sai ya ƙara maka wata a kai.
Kayi haƙuri ka bar kuka kaga kukanka na ƙara ingiza nasu".
Ya ƙare mgnar yana sa hannunshi cikin tafin hannun Shatu yana murza a hankali.
Cikin gamsuwa da jin sanyi a ransa Bappa yace.
"Alhamdulillah".
Da sauri Su GiÉ—i suma sukace.
"Alhamdulillah". Hakama su LamiÉ—o kab falon sai suka fara mai-mai-ta hamdala.
Ai kuwa cikin ikon Allah duk ƙuna da ƙuncin da zuƙatansu keyi a take Allah ya sauƙaƙa musu shi.
Cikin gyaran murya LamiÉ—o yace.
"Alhamdulillah komai yayi forko zaiyi ƙarshe duk abinda yayi tsananin tabbas zaiyi sauƙi Allah mun gode maka daka ara mana rai da lfy".
Ya ƙarashe mgnar yana kallon Sheykh dake kallon agogon hannunshi sabida jin anyi kiran sallan azahar.

Cikin tarin jin daÉ—i Abbansu Sheykh ya matso kusa da Bappa da Abboi murya cike da tarin jin daÉ—i yace.
"Bappa Abboi dama duk al'ummar Rugar Bani da Rugar Arɗo Babayo ngd matuƙa Ubangiji yayi muka sakayya da gidan al'ljanna mafi ƙololuwa girma.
Shatu Allah ya dafa miki ya tsareki dake da ahlinka".
Amin Amin sukace baki É—ayansu.
Shi kuwa Bappa Sheykh ya kalla tare da cewa.
"Muhammad Ngd matuƙa Allah ya saka da al'khairi da kulawarka Alhamdulillah ga mahaifiyarku da ƙanwarku Allah ya bamu aron rai da lfy da ikon dawo muku dasu lfy".
Cikin jin daÉ—i Ummey tace.
"Bappa dani dasu ya kamata muyi godiya ba kuba kun gama min komai a duniya musamman Alhaji Abboi da matarsa Dedde sun min karar bani yar su duk da tarin son da sukeyi mata, suka amince muka dawo da ita nan, kana suka bawa Jabeer na aurenta."
Sai kuma ta juyo ta kalli Shatu tare da cewa.
"Kin min komai kin juya min Jabeer daga bauÉ—eÉ—É—en mutun zuwa dai-daice gashi yanzu har fara'a yakeyi ga Jalal na shima ya zama mai fara'a Jamil kuma ya nitsu.
Sai dai yanayin Affan nane ke min ciwo a rai, Affan ka dena kuka kajiko Shalelen Mamey".
Cikin rauni Affan ya matsota É—aura kanshi bisa cinyarta yayi tare da sakin kuka.
Gaba É—aya kowa yasan takaicin abinda mahaifiyarsa tayine yake sashi kukan.
A hankali LamiÉ—o yace.
"Kayi shiru Affan ita rayuwa kowa abinda ya shuka zai girba".
Daga nan dai kuma akayi gaishe-gaishe.
Kana mazan duk suka tafi masallaci.
Matan masarautar JoÉ—a kuwa irinsu Gimbiya Saudatu da Gimbiya Aminatu dasu Mom da Samira duk ko wacce ta koma part É—in ta cike da al'hinin sharrin É—an Adam.

Matan kuma duk kowa tai al'wala sukayi salla, kana suka sake fitowa falo suka zauna suna cin abinci.

Affan kuwa Part É—in shi ya koma ganin tashin hankali da yake cikine yasa Mami meda hankalinta gareshi.
Shi kuwa Rumaisa yayarshi ya kira tana É—agawa yace.
"Uhummm tunda kullum kece kike zuga Hajia Mama kuna cutar waÉ—anda basu damu da kuba sai ki shirya kizo kiga halin da Mama ke ciki na girbar aiyukanta data shuka".
Cikin tashin hankali Rumaisa tace.
"Affan m.."
Bai bari ta ida zancenta ba ya katse kiran.

Su Sheykh kuwa dasu Haroon falon Sheykh Suka wuce.

Bayan anyi sallan la'asar ne,
Dedde ta kalli Ummey cikin kula tace.
"Toh Ummeyn Shatu mu zamu koma Rugar Bani, sai jibi zamu koma Cameroon da izinin ubangiji Allah ya kiyaye gaba ya tsaremu".
Cikin sauri Umaymah tace.
"Yanzu-yanzu zaku tafine?".
Cikin nitsuwa Dedde tace.
"Eh ai su tuni ma sun shiga mota nida su Khadijah suke jira".
Da sauri Umaymah tace.
"Ayyah ni kuwa ina son ku gaisa da Sittinmu da Jadda kafin ku tafi".
Da sauri Mamma tace.
"Ai sun iso suna Part É—in LamiÉ—o.
Amman yanzu zasu iso".
Da sauri Shatu tace.
"Toh Dedde am ki É—an jira ku gaisa mana".

Suna cikin mgnar Sitti da Jadda suka shigo.
Allah sarki iyaye sai gashi Ummey a tsakiyarsu suna kuka gaba É—ayansu an rasa mai rarrashin wani.
A hankali Sheykh da Haroon suka shigo falon cikin tsiya Sheykh yace.
"Toh Alhamdulillah Jadda ni dai burina ya cika ko yau in kana son tafi ka gaida na gaba tunda kaga Mamey na ta dawo ta sameku cikar farin cikinta kusa mata al'barka".
Dariya sukayi baki É—ayansu kana su Dedde suka matso aka gaggaisa.
Sannan Jadda ya fita ya koma wurin su LamiÉ—o.

Cikin sanyi Shatu ta kalli Deddenta Aunty Amina Hafsi Khadijah waÉ—anda duk suke cikin shirin tafiya.
A hankali tace.
"Allah sarki da mu ƙara kwana mana, yanzu kuma in kun tafi shikenan sai yaushe ni na zama a nan ina gefe duk ƴan uwa suna Cameroon".
Da sauri Ummi tace.
"Kema kina tare da yan uwanki ga Ummeynki ta dawo kusa dake ga kuma Junainah gani ga Hibba".
Da sauri suka kalli Jamil da ke cewa.
"Kuma zan auro mana Khadijah ma ta dawo nan zaku bani ita ai ko Dedde".
Ya ƙare mgnar cikin yanayinsa na wasa da dariya da kowa.
Murmushi Dedde tayi tare da cewa.
"Ai an baka ma Jamilu".
Dariya mai sauti yayi tare da cewa.
"Alhamdulillah".
Junainah kuwa a hankali ta matso kusa da Ya GiÉ—i tare da cewa.
"Ummey ni dai zan tafi tare dasu Yah GiÉ—i ban gaji da ganinsu ba".
Cikin jin kewar juna Ummey tace.
"Kije Junainah nima in Sitti na da Jadda sun tafi zamuzo tasu Mamma".
Da sauri tace to.
Kana ta kalli Shatu da tai shiru tana kallonta tare da cewa.
"Kada ki damu Addana nima zanke zuwa masarautar JoÉ—a".
Da sauri Jalal yace.
"Zaki dawo dai Junnu gamu ga Abbanmu ga Adda Shatunki ga Ummey".
Da sauri ta kalli Sheykh tare da cewa.
"Toh Yan Junaidun fa".
Dariya mai sauti Sheykh ya É—an yi tare da cewa.
"Shima zai dawo nan".
Nan dai suka fito gaba dayansu dan yiwa su Dedde rakiya.
Jadda kuwa harda kuka yayi yana yiwa su Abboi da Bappa godiya.
Chapter 29 · 0% Book details