← Book details Garkuwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 45

Sashe 33

Garkuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Shin kina son Mijinki ya mulki masarautar JoÉ—a?".
Ta jefa mata tambayar kai tsaye.
Da sauri Shatu ta zubawa Ummey nata ido ta karanci yanayinta na ƴan wasu daƙiƙu kana a hankali tace.
"Mamey in dai kuna so ya mulka to nima zanso, hakan sai dai ina tsoro kada a sabautamu".
Da sauri Abba dake shigowa yace.
"A'a Shatu in sha Allah babu komai babu abinda zai faru sai al'khairi.
Burinmu ya mulki masarautar Joɗa ne dan ya gyara ta zama Tsarkakkiyar masarauta mai wadatar sunna da ƙarancin al'adun bidi'a".
A hankali ta gyaÉ—a kanta tare da cewa.
"Shi kenan Abba Allah ya sanya al'khairi yasa hakan ya zama ci gaba ga Musulunci da musulmai".
Amin Amin sukace.
Kana ta ɗan yunƙura zata tashi.
Ganin Abba ya shigo yana amsar Afreen tare da cewa.
"Ƴar lukuta".
Murmushi tayi kana ta kalli Mamey dake cewa.
"Ki fara nuna mishi amfanin ya mulki masarautar bisa hikima ta yadda zaki sa mishi abin a ransa ba tare da yaji dole akayi mishi ba".
Da sauri tace.
"Toh Ummeyna".
Har ta isa bakin ƙofar kuma sai ta tsaya jin Mameyn na cewa.
"Umurnine fa Shatu ki fara daga yau".
Ajiyan zuciya mai sauƙi ta sauƙe tare da cewa.
"In sha Allah kuwa Mamey".
Tana fita Ummi na biye da ita a baya.

A bakin ƙofar shigowa suka haɗu da Sheykh shida Affan.
Wuce sukayi kana su kuma suka fita.

Kai tsaye har bedroom É—in suka wuce.
Suna hira ta tsakanin iyaye da yaransu.
Da sauri Sheykh ya É—an É—ago ya kalli Mameynshi tare da sakin murmushi jin tana cewa.
"Jabeer wannan gemun haka ka É—an rageshi mana ga saje ga gemu".
A hankali yace.
"Mamey bai min kyau bane?".
Da sauri tace.
"A'a wlh yayi maka kyau sosai ma fiye da zaton mai zato sai dai yasa kayi kwarjini da yawa ni kaina sai inji kana min kwarjini".
Dariya mai sauti yayi tare da cewa.
"Uwa mai daÉ—i Allah ya bar mana ke Mameynmu".
Dariya Abba da Affan sukayi tare zubawa Sheykh É—in ido jin yana cewa.
"Toh gemu da saje ku kiyayi kanku da sa Mameyn Jabeer ganin kwarjini mai yawa".

Jamil da Jalal da Yah Jafar Imran dake shigowa ne suka haÉ—a baki wurin cewa.
"A to a haÉ—a harda mu dan muma kansu mana kwarjini yana mana yawa Hamma Jabeer".
Murmushi yayi kana suka shigo suka zauna suna hira cikin jin daÉ—i.
So a nanne yaji kaso 30 cikin 100 na azabebben kishin daya cakeshi É—azu ya ragu.

Ita kuwa Shatu suna shiga kai tsaye bedroom nashi ta wuce.
Ta gyara komai ta killace komai ta ɗan ƙara gudun AC kana tasa turaren ɗaki Tuch me mai sassayan ƙamshi.

Kana ta dawo É—akinta, kamar kullum bayan tayi wonka ta fitone.

Ummi ta shigo riƙe da kasko da rushi kaɗan a ciki.
Gaban gadon ta ajiye kaskon tare da jawo kujerar ƴar tsuguno mai rami ta turaren gyara ta ɗaura kujerar kana ta jawo wani kolba dake kan mirror ta buɗe tasa hayaƙi mai ƙamshi ya fara tashi.
"Zauna". Tace tana fita.
Da sauri Shatu ta zauna bisa kujerar tana mai jin yadda ƙamshin yake game jikinta,
Tabbas wannan turaren tana jin daÉ—in shi ita da kanta da kanta.
Dan ko fitsari tayi sai taji yana ƙamashi sai dai tana ji yana tsuketa.
Bayan kamar 30 minute Ummi ta kuma shigowa riƙe da cup da madarar gongoni a ciki mai sanyi da haɗin *Garin maɗi.*
Motsashi tayi da cokali tare da cewa.
"Yauwa amshi ki shanye".
Ba musu ta amsa sabida tana masifar jin daÉ—in haÉ—in.
Bayan ta shane ta ajiye cup ɗin kana ta matso gaban dreesing mirror'n humra mai sanyin ƙamshi ta murza a jikinta tare da zura wata tattausar rigar bacci royal blue mai ɗigo-ɗigon fari.
Rigar iya karya guiwa.
Turaren laylaytul sahrah ta fesa.
Kana ta zura jibajinta har ƙasa.

Su Sheykh kuwa bayan sun gama hirane.
Yasa hannunshi ya amshi Afreen da Mamey ke miƙa mishi tare da cewa.
"Kaita tasha mama".
To yace.
Tare da amsarta ruggume ta yayi a jikinshi tare da cewa.
"Sai da safe".

"Allah ya bamu al'khairi".

Amin yace yana mai fita, sai kuma ya tsaya jin Abbanshi na cewa.
"Kaje wurin LamiÉ—o akwai takardun aiken masarautu da yakeso ya baka".
Cikin bin umarni yace.
"Toh".

Yana fita Part É—in LamiÉ—o ya nufa.

Gefenshi ya zauna ruggume da Æ´arsa cikin kula Gimbiya Aminatu tace.
"Kai É—a da daÉ—i ko Sheykh".
Murmushi yayi tare da kallon Afreen dake jujjuya ido tana lumshesu alamun bacci zatayi yace.
"Uhumm sosai ma kuwa É—a kam da daÉ—i Gimbiya Aminatu".
Dariya sukayi baki É—ayansu.
Shi kuwa kissing goshinta yayi tare da sa mata al'barka.
Kana ya kalli LamiÉ—o a fakaice yace.
"Abba yace akwai takardun da zaka bani".
Eh yace tare da miƙo mishi wasu takardu liƙe cikin wani, kekkyawan mazauni tare da tambarin hatimin masarautar Joɗa a jiki.
Hannu yasa ya amsa tare da cewa.
"Toh na menene?".

Cikin tsareshi da ido LamiÉ—o yace.
"Aiken Masarautar JoÉ—a ce zuwa ga sauran masarautun gargajiya na Arewacin Nigeria, zaka kai musu É—aya baya É—aya".
Da sauri yace.
"Yaushe kuma aiken menene?".
A daƙile Lamiɗo yace.
"Gobe sai kaje ka dawo zan gaya maka na menene.
Waziri, Wambai, Galadima, Chiroma, Durbi, duk sun sa hannun".
Taɓe baki yayi tare da cewa.
"Sai dai kuma ai kai ba ubana bane da zaka wani tirsasani ka sani abu dole.
Harda wani wai gobe".
Ya ƙarashe zancen yana miƙewa tsaye riƙe da takardun.

Shi kam LamiÉ—o murmushi kawai yayi ya bishi da ido.

Kai tsaye Part É—in su ya nufa.
Ba kowa a falon haka yasa ya rufe ko ina ya kashe duk kayan wuta.
Kana ya wuce Side É—insa ruggume da Afreen.

A hankali yaja sassayan numfashi tare da shaƙar ƙamshin ɗakin.
Wutan ya kunna,
ido ya lumshe ganin komai fes-fes.

A can tsakiyar gado ya kwantar da Afreen tare da gyara mata kwanciyarta dan tuni tayi baccinta.

Addu'o'in yayi ya tofa a tafin hannunsa ya shafa mata.
Bathroom ya wuce.
Wonka yayi mai rai da lfy kana ya kimtsa cikin wasu tattausan riga da wondo pink guava color da ratsin Royal blue masu É—an karen taushi.
OudKareem É—insa ya fesa kana ya fito.

A hankali ya É—an zauna bakin gadon ba tare daya kashe wutanba.

Miƙe sawunshi yayi bisa gadon tare da ɗan zamewa ya kwanta rigingine.
Ido ya rumtse a hankali tuno kalaman Ba'ana a kan Shatu.

Ita kuwa Shatu a hankali taja ƙofar ɗakinta ta rufe Sannan ta nufi Side ɗinsa.

A hankali ta tura ƙofar tare da cewa.
"Assalamu alaikum".
buÉ—e idonshi yayi tare da zuba mata su.
Murya can ƙasa yadda bata jiba yace.
"Wa alaikassalam".
A zahiri kuma sai ya haÉ—e fuska tare da tsuke bakinshi.

Motsowa ta inda yake tayi tare da cewa.
"Yah Sheykh kayi bacci ne?".
Bai kulata ba kuma bai É—auke idonshi a kanta ba.
Ƙara matsoshi tayi tare da zare hijabin ta ninkeshi tana cewa.
"Hamma Jabeer yau ba mgna ne".
Bakinshi ya taɓe mata.
Wanda hakan ya tabbatar mata yana fushi da itane wanda tasan fushin bai rasa nasaba da yadda yake buƙace da ita take kauce mishi.

Ajiye hijabin tayi a gefe. Sannan ta É—an matso gaban shi.
Yatsun ƙafarshi ta ɗan ja tare da cewa.
"Nooryat".
Idonshi ya cire a kanta, yana mai ji kamar ya ruggumeta.
Fahimtar dafa gaskene fushin yasa ta É—an hauro saman gadon.
A hankali ta sunkuyo kanshi tabi tsawon shi.

Hannunta ta cusa cikin rigar tashi, ta fara mishi tafiyar tsutsa ta gefe da gefen cikinsa.

Kana ta haÉ—a fuskarshi da nata.
A hankali ta kamo lip ɗinshi na ƙasa ta tsotsa tare da fidda sautin.
"Shyyyyuuyyh Yan Sheykh na tuba".
Miƙa mai tsawo yayi jin yadda takeyin ƙasa da hannunta.
Kana ta haÉ—e bakinsu wuri guda.
Wani irin lasa tayiwa harshensa wanda yasa yaji.
Sheykh ɗin shi ya amsa amo ya miƙe cike da zalama.
Da sauri yace.
"Barni".
Cikin raÉ—a tace.
"Naƙi".
Kanshi ya É—an É—ago tare da tsareta da ido.
"Sai kuma ya tashi zaune yana riƙo hannunta jin tana kwance mishi zariyar wondo.
Da sauri yace.
"Wai menene hakan?".
Cikin tura baki tace.
"Abuna zan nema".
Bai san lokacin da dariya ta kubce mishi ba ganin yadda tayi mgnar cikin dariyar yace.
"Abun naki kuma babu inda zaki nemo shi sai cikin wondona?".
Ya ƙare mgnar tare da jawota jikinshi ya ruggumeta gam-gam yana kissing wuyanta.
Chapter 33 · 0% Book details