Sashe 32
Garkuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Zaune suke Umaymah Mamey LamiÉ—o Galadima Abba
A hankali LamiÉ—o ya gyara zamanshi tare da cewa.
"Toh Alhamdulillah komai ya wuce ya zama tarihi.
Manufar taruwarmu anan a kan Masarautar JoÉ—a ne.
Na gama zama da duk manyan fada mun gama tsaida zance duk kowa ya gamsu da batun Jabeer ya mulkin Masarautar JoÉ—a.
Toh amman inda gizo ke saƙan kun san ɗan naku, na kira sarki Jalaluddin akan batun to shi mgn ɗaya yayi cewa yasan Jabeer mai biyayya ne ga Khadijah da take ƙanwar mahaifiyarshi ma bare ke Aisha da Habibullah da kuke iyayensa yace ya sani tabbas in kuka cewa Sheykh ya mulki masarautar Joɗa ku bashi umarnine ba shawaraba tabbas zai yarda".
Cikin gamsuwa Galadima yace.
"Haƙƙun wannan haka yake tabbas zai yarda bisa dole bisa umarnin iyayenshi".
Cikin sanyi Mamey tace.
"In kuna son in bashi umarni zan bashi kuma nasan zai min biyayya to amman meyasa baza'a bawa wani cikin ƙannen mahaifinshi ba sai shi".
Shiru sukayi baki É—ayansu jin LamiÉ—o na cewa.
"Sabida ina son masararutar JoÉ—a ta tsarkaka ta rabu da duk wata al'ada daba addiniba.
Na sani babu mai iya sarrafa Masarautar JoÉ—a ya juyata daga bahahuwa zuwa ba damiya ya kauda al'adar bidi'a ya wanzar da sunna sai shi.
Zai gyara masararutar ta yadda za'a dena zalama da son cutar da juna bisa kujerar zai sauyata ta yadda sai mai cikekken ilimin addini ne zai iya mulkarta."
Cikin gamsuwa Mamey tace.
"In sha Allah zaku sameni mai biyayya bisa umarnin ku na in bashi umarni kuma na sani zai min biyayya".
Cikin jin daÉ—i sukace to.
"Allah ya shige mana gaba".
Amin Amin sukace.
Sai kuma suka nitsu jin LamiÉ—o na cewa.
"Alhamdulillah yanzu Ita matarshi ta kusa gama wonka tana gamawa zukjne Rugar Bani suyi kwana ɗaya daga nan su dawo su shirya suje Ƙasar Cameroon wurin iyayen Shatu kuma zasuje da Aliyu (Dr Aliyu) kenan da Basiru da Galadima domin su nemawa Jamilu auren Khadijah ƙanwar Shatu".
Cikin jin daÉ—i Mamey tace.
"Alhamdulillah to Allah ya kaimu".
Amin Amin sukace.
Sai kuma Abba yace.
"Jalal kuwa mun gama mgna da Abban Haroon kan batun Jalal da Hibba".
Cikin tsananin jin daÉ—i sukace.
"Alhamdulillah daga nan suka watse taron.
Washe gari su Umaymah suka koma.
Alhamdulillah yau Shatu ta gama arba'in.
Sosai Afreen tayi kuɓul-kuɓul da ita gwanin burgewa ta cika tayi kyau in ka ganta kamar yar wata biyu.
Sosai kuwa Shatu tasha gyara na musamman daga wurin Ummi da Mameynta.
A can ƙasar Cameroon kuwa.
Ba'ana ya gama shirin dawowarsa kab.
Wanda da azatonsa zai kaishi watanni uku sai gashi cikin wata biyu ya gama shirinsa.
Kana ya kamo hanya.
Yau Alhamis da misalin ƙarfe tara na dare yayiwa Rugar Bani diran miki...!
Ban samu nayi editing ba
By
*GARKUWAR FULANI*
4/6/21, 4:15 PM - &: Dirar mikiya tare da tawagar shi wanda Baroon na ciki.
A bakin titi motar ta sauƙesu kana suka ƙaraso cikin Rugar tasu da ƙafa.
Dai-dai bakin mashigar Rugar Bani É—in suka tsaya, sabida ganin uban gayan tafiyar ya tsaya.
A hankali ya lumshe idonshi, tare da shaƙan sassayan iskan garin dake kaɗawa yana ratsa jiki.
Hannunshi ya buɗe ya waresu, ya tanƙwashe kansa bisa wuyanshi cikin muryar dake nuni da gskyar abin dake binne can ƙasan zuciyarsa yace.
"Uhummmmmmm ko wani É—an adam yanada yanki na musamman da yake cikin bugun zuciyarsa.
Ni kuwa Rugar Bani ce bugun zuciya ta.
RUGAR BANI itace mahaÉ—in soyayya da Mata. Allah ka sani kaine ma sannin sirrin zuciyata ina son Shatu son da ni kaina ban san adadinshi ba.
Son da bana yiwa kaina shi.
Mata itace cikon farin cikina ban taɓa son wani abu a duniya sama da Shatu ba ya Allah ka yafe min kura-kuraina na baya, ka bani ikon samun Shatu, ka tsare min imanina duk da nasan.
Ban fiye aikata aiyukan gsky ba a rayuwata.
Amman son Shatu gsky ne a cikin zuciyata kuma tuban da nayi gsky ne.
Ya Allah ka jiƙaina ka tausaya min ka cika min burina ka ƙaddara Mata ta tabbata matar aure na, in rayu da ita inuwa ɗaya.
Domin itace sanyin idaniyata in ka samar min ita rayuwata zata inƙanta."
Ya ƙarashe mgnar cikin rauni da rawan muryar kana wasu irin tafasassun hawaye suna masu kwarya mishi.
Sheykh kuwa dake jin duk abinda Ba'ana yake faÉ—a bisa kiran da Baroon yayi mishi.
Da ƙarfi ya rumtse idanunshi, yana mai jin wani irin azabebben kishi mai masifar zafi da ƙuna yana caccakar zuciyarsa.
So yake ya tashi yaje suyi hira da Mamey'nshi Amman gaba É—aya yanayi shi ya hautsine kishi ajalin maza.
Domin in mu mata kumallonmu ne tofa su maza yakan iya karsu.
A can Rugar Bani kuwa, cikin rauni Ba'ana yaci gaba da magana cikin sanyin jiki da raunin da bai taɓa riskar shi ba yace.
"Na sani na yarda akan komai ni bazan amsa sunan mai gsky ba ko mai tausayi amman akan tubana da Shatu ni mai gsky ne! Ya Allah ka mallaka min Shatu na yarda na gane babu wani sihiri ko tsafi ko boka ko dodon tsafin da zai mallaka min ita sai kai sarkin da bashi da tamka sarki buwayi gagara misali sarkin kowa na Annabi baban zara".
Kawai sai ga hawaye shar-shar suna kwaranya daga idanunsa rusunawa yayi ya durƙusa bisa guiwowinsa ya kafa kanshi cikin sassayan yashin garin.
Ya saki wani irin raunataccen kuka.
Gaba ɗaya yaran nashi shiru sukayi cikin tarin mamaki da tsantsar gaskata soyayya ba ƙarya bace shirya kuma ta Allah ce dan tuni sun san yabar komai na tsafi saidai wasu abubuwan dake jikinsa basu karyeba kamar ɓacewa har yanzu yana iya ɓacewa.
Saida yayi kuka mai tarin yawa kana suka miƙe suka nufi cikin gari.
A tsakiyar wurin garken al'ummar Rugar Bani É—in ya tsaya ya juya gabas da yamma kudu da arewa.
Kana a hankali yace.
"Duk da son hanaku ci gaba da nakeyi, ya rigada Allah ya lamunce muku kuna ci gaba da izininsa."
Kai tsaye garken Bappa ya nufa bayan duk ya sallamesu sai Baroon kawai.
A hankali yasa ƙafarshi ya ratsa tsakiyar garken cikin ɗan ɗaga murya yace.
"Bappa".
Cikin wani irin masifeffen tashin hankali da firgici Bappa ya miƙa tsaye.
Tare da cewa.
"Na'am Ba'ana".
Giɗi da Seyo ne dake gefenshi suma suka miƙe da sauri cike da tsoron me zai faru.
A hankali ya zame ya zauna gaban Bappa kana a hankali yace.
"A nan a tsakiyar garken nan na rayu da ita tsawon shekaru goma sha biyu, na rayu da sonta kan gsky.
Koda komai ƙaryane Bappa ka yarda ina son Shatu son da bana yiwa kaina".
Cikin sauƙe ajiyan zuciya Bappa ya zauna jiki a mace hakama su Gidi da Baroon.
Cikin nitsuwa yace.
"Ba'ana yaushe ka dawo?".
Murya na rawa yace.
"Bappa yanzu na shigo Rugar Bani ko gidanmu ban jeba, ina so ka yarda cewa da gaske ina son Shatu".
Yadda yayi mgnar yasa Bappa jin wani irin rauni da tausayinsa a hankali yace.
"Na yarda Ba'ana na sani kana son Shatu".
Da sauri yace.
"Bappa ka tuna kun min al'ƙawarin aura min ita".
Da sauri Bappa yace.
"Na tuna Ba'ana ban manceba to amman al'ƙawarin Allah ya ture namu ya rigada Allah ya tsara Shatu ba matarka bace."
Cikin sauri ya miƙe yana cewa.
"A'a a'a bana son jin haka".
Yana faÉ—in haka yana yarfa hannun a haka ya nufi cikin gari Baroon na biye dashi a baya.
Shiru Bappa da su GiÉ—i sukayi cikin tarin rauni.
Shi kuwa Ba'ana a tsakiyar gidansu ya zauna gaban Bukar da Bugulu mahaifiyarshi.
Cike da mamaki suke kallonsa jin yadda yake kuka babu sassauci.
Cikin tsananin tausayi da so irin na iyaye da yaransu.
Sukayi kanshi cikin kula Bugulu tace.
"Ba'ana yau ranar farin cikine a garemu ba ranar kuka ba.
Kada kayi kuka muna cikin farin cikin ganin juna".
Ba mgn sai kuka.
Da sauri Bukar ya jawoshi jikinshi tare da cewa.
"Gaya min me ya saka kuka haka?".
Cike da rauni yace.
"Karo na forko dai a rayuwata Baba zan roƙeku in kuna da hali ku aura min Shatu ku dawo da ita gareni".
Ganin tsananin tashin hankali da yake cikine yasa sukace.
"To kwantar da hankalinka ina shine kawai burinka zamu dawo maka da farin cikin ka".
Da sauri yace.
"Allah Baba?".
Kai ya gyaÉ—a mishi cikin tausayinsa.
Shi kuwa jin hakane ya zame ya kwanta ya ɗaura kansa bisa cinyar babanshi yana sauƙe numfashin kuka shima Baroon gefe ya zauna.
Sheykh kuwa cikin tsananin tashin hankali na kishi ya rumtse idanunshi da ƙarfi.
Kana ya taune lip ɗinsa na ƙasa.
Shatu ce zaune ita da Mamey har cikin É—akinta Afreen na hannun Ummi.
A hankali Mamey tace.
"Shatu".
Da sauri ta É—ago kanta ta kalli Mamey tare da cewa.
"Na'am Mamey na".
Gyara zama tayi tare da cewa.
"Shatu batun mijinki ne, nake son kisa baki a lamuransa".
A hankali tace.
"Mamey waÉ—annen lamuran ne?".