← Book details Garkuwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 45

Sashe 20

Garkuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su kuwa saura kab ajiyan zuciya sukayi tare da cewa.
"Alhamdulillah"..
Sai lokacin ya É—an kalli Aunty Rahma dake gefen Shatu tana zubda hawaye a hankali yace.
"So sorry my Aunty in Sha Allah babu komai likita yace, da shayar da ita shi akayi zaifi mata illa yanzu kuma shaƙane an mata duk wani taimakon gaggawa daya kamata".
Cikin gamsuwa ta gyada kai.
Sai kuma ya É—an taso tsaye sai lokacin yaga yawansu.
A hankali ya É—an sunkuyar da kanshi cikin sanyi yace.
"Gimbiya Aminatu in sha Allah daga yau wannan al'adar zata kau a masarautar JoÉ—a dama duk wasu tarkacen al'adun daba addiniba ki gayawa LamiÉ—o".
Cikin jin daÉ—i tace.
"Ai ba ita kaÉ—ai ba in dai ka yarda ka mulki masarautar JoÉ—a duk wata al'ada na masarautun gargajiya kana da damar datsesu ka wanzar da Sunnah".
Wani irin dogon ajiyan zuciya mai nauyi ya sauƙe.
Tabbas masarautar Joɗa tana buƙatar sabon Sarki sabon tsari sabon zubi bisa koyarwar musulunci da sunnar manzon Allah a kauda bidi'a a kawo sunna.
To amman shi baida ra'ayin mulki.
Cikin sanyi yace.
"Gyaran ba lallai sai ni É—aya zan yi shi ba ai, kuma ko bani ke mulkiba zan iya bada shawara in an yarda a amsa".
Cikin sauri Umaymah tace.
"Idan dai har kana son kauda al'adun a wanzar da sunna to dole ka mulki masarautar JoÉ—a da kanka".
Kanshi kawai ya jingina jikin kujerar kana a hankali ya sunkuyo yana kallon Shatu dake cewa.
"Baiyi mulki Bama Umaymah ana neman ransa da na ahlinsa".
LamiÉ—o da Galadima dake shigowa ne dan jin lbrin abinda ya faru a bakin Jalal ne.
Suka haÉ—a baki wurin cewa.
"Ƙi gudu sa gudu, Shatu ke muke zaton zaki bashi ƙarfin guiwa kuma sai ki karaya da wuri haka."
Da sauri su Umaymah kab suka ja da baya suka basu wurin zama.
Suna zama dai-dai lokacin kuma Shatu ta zare mamanta daga bakin Afreen ɗin cikin tsoron ganin yadda ta ke ɗan yunƙuri tana kwaro amai.
Da sauri Sheykh ya matso tare da cewa.
"Innalillahi".
Ita kuwa Shatu ɗagota tayi da sauri ganin yadda taketa yunƙirin kakarin amai ba ƙaƙƙautawa.
Da sauri Gimbiya Aminatu ta matso tana cewa.
"Subahanallahi"
Shi kuwa Sheykh wayarshi dake cikin al'jihun rigarsa ya zaro da sauri ya kira Dr Lukman Ibrahim yana É—agawa yace.
"Dr Baby fa sai amai takeyi ba tsayawa".
Da sauri Dr Lukman Ibrahim yace.
"Alhamdulillah tasha Mamanta ko?".

"Eh tasha, tana shane ma ta fara aman".
Ya bashi amsa.

"Yauwa haka akeso Sheykh ba komai yanzu duk kaifin gubar ya karye ta harar dashi yanzu zatayi bacci kuyi mata wonka da ruwan sanyi.
Tana farkawa kuyi mata wonka da ruwan sanyi kuma zata dawo dai-dai da izin Ubangiji".

Da sauri ya katse kiran bayan yace.
"Ok thanks Dr".

Ita kuwa Shatu ajiyan zuciya ta sauƙe tare da meda kanta ta jingina da kujera ganin ta bar aman.
Shi kuwa Umaymah ya kalla tare dayi mata bayanin da Dr yayi mishi.
Da sauri ta iso garesu ta amshi Æ´ar kana ta wuce Bathroom.
Wonka tai mata da ruwan sanyi É—an kwalinta ta wore ta naÉ—eta a ciki.
Tuni tayi bacci kafinma ta fito da ita.
A hankali ta zauna bakin gadon Shatu gefen Aunty Amina da Khadijah dake waya da Abboi Appansu kenan tanai mishi bayanin duk abinda ya faru.
Cikin tashin hankali da mamaki Abboi yace.
"Subahanallahi, kai wannan gida nasu akwai sarƙaƙiya.
yanzu ina Parvina?".
A hankali tace.
"Tana falo can naji kamar harda LamiÉ—o ma yazo da kanshi, amman yanzu yarinyar gata nan ta farfaÉ—o harma tayi bacci".
Cikin kula da son ahlinshi especially Parvina a hankali yace.
"In sha Allah nida Dedden ku da Al'ameen zumu zo gobe gobe da izinin ubangiji, dama tun tuni ma shiryawa hakan, in Parvina ta shigo kice ta kirani".
Da sauri tace.
"Toh Appa".
Guntun murmushi Umaymah tayi tare da cewa.
"Babanku kika gayawa ne?".
Cikin alamun karaya da lamarin gidajen sarauta tace.
"Eh Umaymah".
Kai kawai ta gyaÉ—a tare da gyarawa jaririyar kwanciya.
Aunty Amina kuwa sunkuyowa tayi tana kallon fuskar Babyn.

A falon Shatu kuwa sosai LamiÉ—o ya kwantar mata da hankali kana suka tafi Gimbiya Aminatu na biye dasu a baya.
Bayan ta shiga ta ƙara duba Babyn.

Umaymah kuwa fitowa falon tayi suka zauna a nan.
Ita kuwa Shatu bedroom ta koma ta konta tasa yarta a gaba tofi takeyi mata tana kallon fuskarta Allah ya sani ji takeyi kamar bata tsiraba shiyasa har yanzu hanjin cikinta ke kaÉ—awa.

A hankali ta jawo wayarta.
Abboi ta kira, bayan sun gama gaisa ya alhinta abinda ya faru ya É—aura da cewa.
"Dama can gobe zamu zo ko ba komai zanzo inga amryata, inga mummunace ko kekyawa".
Ya ƙare mgnar da ƴar raha da son kontar mata sa hankali.
Murmushi tayi tare da cewa.
"Allah ya kawomku lfy Appa na, da Ummey na da Junainah take kamafa".
Tayi mgnar cikin jin kunya duk da yawan shaƙuwa dake tsakaninsu.
Murmushi yayi tare da kallon Dedde dake jin duk tattaunawar da sukeyi yace.
"Ato kekkyawace sadaki ta garken shanun Bappa zai bata".
Dariya sukayi baki É—ayansu kana sukayi sallama da juna.
Daga nan kuma Bappa ta kira, wanda tun É—azu Abboi ya shaida masa abinda ya faru yana É—agawa yace.
"Shatu na ya jikin Aisha ƙaramar dai?".
A hankali ta É—an shafa kan Afreen tare da cewa.
"Alhamdulillah Bappa na ba komai ta samu lfy gatama tana bacci".
Cikin jin daÉ—i yace.
"Alhamdulillah ga Ummeynki tun É—azu hankalinta a tashe yake".
Amsa Ummey tayi cikin kula tace.
"BoÉ—É—o na me sukayi miki?".
Cikin yin ƙasa da murya tace.
"Ummey na so sukayi su kashe miki jikarki tun baki ganta ba, dan Allah da Manzonsa Ummey na kizo gobe".
Cikin kaÉ—uwa da begen son ganin Shatu da Æ´ar tata tace.
"In Sha Allah Gobe za muzo tare da Abboi da izin Ubangiji".
Cikin jin daÉ—i tace.
"Alhamdulillah naji daÉ—i na, Gobe ina cikin gatana".
Su kuma ta kalli Umaymah da ta shigo yanzu tare da cewa.
"Alhamdulillah Umaymah na Gobe Ummey na zatazo da Bappa na da Deddena da Abboi".
Cikin wani irin masha'hurin farin cikin alamun son tabbatuwar wani abu Umaymah tace.
"Alhamdulillah Allah ya kawo mana su lfy".
Amin Amin sukace baki É—ayansu.

Haka dai akayi wunin sunan jiki a mace da abinda ya faru.

Sai can da yamma ne da Afreen É—in ta farka daga baccin suka ganta lfy lau kafin hankalin kowa ya kwanta.
Nan Umaymah suka fito da kayan suna na gani na burgewa, da aka haÉ—awa mai jego da ÆŠiyarta.

Kayan da Sheykh yayi musu kuwa abin sai dai ace son barka.

Gaba É—aya wunin yau shima ya kasa fita ko nan da can tunda akayi sallan Jumma'a ya shigo ya wuce Side É—insa.
Bini-bini ya kira Shatu ko Umaymah ya tambayi jikin yarinya.

Bayan sun dawo sallan la'asar ne.
Jalal ya biyoshi har cikin falonshi, gefen Haroon ya zauna kana a hankali yace.
"Shima sarkin al'adun sunan harda shi a sahun Magauta sai dai biya shi Hajia Mama tayi da dubu É—ari bakwai daga baya yace min tace in Æ´ar ta rasu zata cikata mishi dubu É—ari uku ya zama one million".
Cikin mamaki Haroon yace.
"Ikon Allah ikon gaske, wai ita wannan shegiyar matar meyasa bazamu fito mata a fili bane mu nuna mata mun san komai mu kuma juyo kanta".
Cikin taune lips Sheykh yace.
"Uhumm bazaku gane bane,".
Da sauri Umaymah dake shigowa tace.
"Ni na gaji bazamu gane me É—in ba kuma".
Cikin wani irin yanayi mai rauni cikin sanyi murya na rawa yace.
"Affan ina ɗagawa Hajia Mama kafane sabida Affan ina jin takaici in na tuno a cikinta Affan ya fito, ku kun san waye Affan kun kuma san asalin zahirin gskyar so da ƙaunar da yake mana, kunsan yadda yake faman faɗa da yaƙin sauya mahaifiyarshi daga mummunan ɗabi'a eh zuwa kekkyawan ɗabi'a.
Ta yaya zanci zarafin ta al'halin Affan ya É—aukeni matsayin Uba ya É—aukeni ciki É—aya muka fito,kada ku manta son da Affan kewa Mameynmu Jalal ka duba tarin son da Affan yakeyi muku kaida Jamil.
Ko a lahira wani kanci al'barkacin wani.
Ina barine sabida ko Affan zai samu nasarar juya halinta".
Ya ƙarashe mgnar hawaye na zubo mishi.
Gaba ɗaya jikinsu yayi sanyi tabbas sun san waye Affan ko su Jalal basa so da shaƙuwa dashi kamar Affan.
A hankali yace.
"Duk abinda nasa Affan zaiyi minshi babu musu koda baya son abin duk inda na aikeshi zaije min duk abinda na bashi zaɓi zaɓina yake bi, Affan da kanshi ya fara nuna min baya son inci abincin Hajia Mama wacce take uwace a garesa, yayi hakane sabida zargin tana samin abu a cikin abinci.
Yasha yin kuka yana mgiya in ya tareta tana wani abun me zanyiwa Affan in nuna mishi halaccin É—an uwantaka banda in rufawa mahaifiyarshi asiri".
Shiru yayi ganin kiran Affan daya shigo wayarshi.
Jiki a mace itama Umaymah ta zauna.

A hankali ya kara wayar a kunne bayan a amsa kiran.
"Assalamu alaikum Hamma Jabeer".
Affan ya faÉ—a cikin tsananin so da ladabi ga É—an uwan nasa.
"Wa alaikassalam Affan kana lfy".
Sheykh yayi mgn yana mai jin wasu zafafan hawaye na tsastsafo mishi.
Murmushi Affan yayi cikin yanayin shi na Happy mood yace.
"Alhamdulillah Hamma Dr Akarmakallu Yah Sheykh, mun sauƙo lfy".
Jingina bayan sa yayi da kujera tare da cewa.
"Alhamdulillah Affan Allah yayi ma al'baka".
Da sauri yace.
"Amin Hammana".
Chapter 20 · 0% Book details