← Book details Garkuwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 45

Sashe 18

Garkuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A hankali Jalal ke tafiya tana riƙe da yatsarsa manuniya tana ɗigirgire da sawunta.
Wanda takalmanta ke hannun Jalal É—aya cikin yawan surutunta tace.
"Yah Jalal lallena zai ɓaci fa.
Ni mu zauna a nan sai ya bushe mu tafi".
Sunkuyowa yayi ya É—an kalleta fuska É—auke da murmushi yace.
"Mun isofa Junnu saura kaÉ—an".
Tura baki tayi dai-dai lokacin da yasa hannunshi ya tura ƙofar tare da sallama a bakinshi.
"Ni dai bana son Junnu Hamma Jabeer yace ba kyau ace Junainah yafi daÉ—i".
Tayi mgnar tana ƙara riƙo hannunshi.
Da sauri Umaymah ta kalleta ta kuma juyo ta kalli Ishma dake lafe jikin Shatu.
Ita kuwa Junainah da sauri ta saki hannun Jalal tare da rugowa a guje tare da cewa.
"Lah oyoyo Ummey na".
Tayi mgnar tana nufo gaban Aunty Rahma data hango tamkar Ummey'nta.
Da sauri ta tsaya tare da cewa.
"Laah".
Sai kuma ta juyo ta kalli Ishma kana ta kalli Aunty Rahma.
A hankali ta É—an matsa kusa da Shatu cikin yanayin jin kunya tace.
"Ina kwana".
Ta ƙare mgnar tana kallon Aunty Rahma da suma duk ita suke kallo.
Da sauri Mamma tasa hannunta ta kamo hannun ta jawota kusa da ita kusan a tare sukace.
"Ikon Allah kenan dan Allah kalli kama".
Murmushi Shatu tayi tare da cewa.
"Ai natama dana Ishma wasane na Ummey na da Aunty Rahma shine gaske".
Cikin sauri Jalal yace.
"Dan Allah yaushe Ummeynki zata zo mana ne kam".
Murmushi Aunty Amina tayi tare da cewa.
"Ai kam zata zo wata rana amman ba yanzuba".
Da sauri Aunty Rahma tace.
"Ai kuwa in sha Allah mu kam zamuje mu ganta".
Junainah ce ta É—an lafe jikin Mamma tana kallon Umaymah a hankali tace.
"Itama ai zata zo taga Baby".
Murmushi Umaymah tayi tare da shafa fuskarta.

Hibba kuwa Jawo Ishma tayi ta ajiyeta kusa da Junainah hota ta fara É—aukansu tana cewa.
"Masha Allah tagwayen kamanni".
Murmushi Aunty Juwairiyya tayi tare da cewa.
"Wlh kuwa".

Ranar dai haka suka wuni.
Anata hira da raha.

Ranar suna bayan sallan asuba, aka raba goro da dabino.
Kana akayi yanka yarinya taci sunan Ummey kuma Mamey Aisha.
Jamil na shigowa ya faÉ—awa Umaymah dasu Mamma dake cike a falon.
Da sauri Hibba tace.
"To da wanne sunan za'a kirata?."
Shiru Shatu dake cikin shiga ta al'farma tayi tana kallonsu.

Khadija ce ta É—an gyara zama tare da cewa.
"Afreen yayi".
Da sauri Jamil yace.
"Sosai ma kuwa kin iya zaɓi mai kyau kamar yadda kike mai kyau".
Murmushi tayi tare da sunkuyar da kanta ƙasa cikin kunya, sai kuma ta tashi da sauri tayi falon Shatu jin Jamil ɗin na cewa.
"Umaymah tayi ko surkaki ce".
Ya ƙare mgnar yana kallon Shatu.
Murmushi sukayi tare da cewa.
"A tayi sosai ma kuwa".
Sai kuma yace.
"Ko dai baza'a bani ita bane Adda Shatu?".
Da sauri tace.
"A a ni kam banceba ba ruwana, ai ina ganinku bini-bini kuna tare".
Sheykh da yanzu shigowarsa ne yace.
"In ka nitsu mu baka ita in Kuma baka bar ƙelle-ƙellen idoba da kallon mata mu habaka its".
Ƙeyarshi ya sosa tare da cewa.
"A ai yanzu na girma na bari ko Yah Haroon."
Ya ƙarashe mgnar yana kallon Haroon dake bayan Sheykh.
Dariya sukayi baki É—ayansu.
Shi kuwa Haroon zama yayi gefen Mamma tare da cewa.
"Ai kam yanzu ka girma".

Ummi ce ta fito daga kitchen da akoshin cike da hanta gashin tukunyar da akayiwa Shatu.
Sai Jannart kuma riƙe da gashin da tayi musu nasu daban.
Sara da Larai kuwa da sauran duk riƙe da manyan Foodflaks suka shigo dasu a hannunsu.
Kana suka koma suka dauko plates da cups da spoons.
A tsakiyar falon suka ajiyesu.

Nan suka taru gaba É—ayansu suka zauna a falon.
Harda Junainah.

Aunty Amina kuma da Khadijah da Shatu falonta suka tafi.
Shi kanshi Sheykh a nan kusa da Umaymah ya zauna a plate É—aya sukeci shida Haroon.
Ishma da Junainah.
Jannart da Hibba da Aunty Juwairiyya.
Rahma Kuma ita da Mamma Umaymah kuwa ita da Ummi.
Jalal da Jamil.

Affan kuwa yana can Abuja bai dawoba shida Sulaiman da Malam Abubakar sai dai Alhamdulillah shariya tayi kyau babu jeka ka dawo kasan cewar akwai manyan shaidu kuma ga yawan Addu'o'in iyaye da yan uwa kan su Gaini da Addu'o'in masallatan jumma'a kana ga taimakon gskya. Da samun ƙwararren lawyer da kuma sa bakin babban mutum Lamiɗo da Jadda da kuma shi kansa Sheykh.
A ranar kotu ta wonkesu tsab.
Kana akayi ram da Dineal dama sauran ɓata garin jami'an tsaron kasar da suke da hannu cikin irin wannan kitimurmurar.

Shi kuwa Sheykh Affan ya gaya mishi komai amman yaƙi ya yardama suyi mgnar da Shatu da zaran ta fara mishi mgnar sai ya zille yafi son yayi mata ba zata.

Bayan duk sun gama cin abinci ne, kowa wacce ta fesa wonka da kolliya
Sosai sukayi kyau cikin shiga ta al'farma, Hajia Kubra ma tazo.
Dama sauran abokan arziki.

A hankali Sheykh ya meda ƙofar ɗakinshi ya rufe, tare da amsa kiran Hajia Mama.
Dariya mai sauti tayi tare da cewa.
"Hahaha shegu zanyi mgninsu yau.
Tuni fatar ragon sunan ya shiga hannuna na gama yin shirina har na meyar musu da ita.
Da sauri cikin tsoro yace.
"Toh me kikasa a cikinta".

Dai-dai lokacin kuma sairkin al'adun Sunan masarautar JoÉ—a ya shigo falon wurinsu Umaymah tare da Gimbiya Aminatu da
Yana riƙe da fatar ragon sunan.

Bayan sun zauna ne ya sun gaisa ya shimfiÉ—a fatar ragon sunan.
Tare da miƙowa Ummi dake riƙe da Afreen yace.
"Masha Allah kawo Aisha Æ´ar Aysha jikar Aisha mu cika mata masakinta".
Da sauri Ummi ta miƙa mishi Afreen dake naɗe cikin shawul fari ƙal mai taushi da ɗaukan, ido.

Hannunshi yasa ya fara zare Shawul É—in yayi kana ya fara cire mata kayan jikinta ya rage daga ita sai Pampers.
Aunty Rahma ce ta É—anyi ajiyar zuciya tare da cewa.
"Kai wannan masarautar JoÉ—a taku tanada tsarabe-,tsaraben al'adu masu masifar tsauri.
Allah ya baku cikekken ahlul sunna ya mulki masarautar shine kaÉ—ai zai kauda al'adun ya wanzar da sunna, ina dalili a ninke yarinya cikin É—anyen fata ayi ta garata a tsakiyar É—akin mahaifiyarta ai ko ba'ayi hakaba dole zata san É—akin uwartace".

Umaymah ce ta É—an gyara zamanta tare da cewa.
"Toh ya zamuyi tunda abu nasune".
Gimbiya Aminatu ce tayi murmushi tare da cewa.
"Watan wata rana dai tabbas al'adun zasu kau sunna ta wanzu in wanda muke zaton ya yarda ya amshi masarautar".

Allah ya sa haka.
Umaymah tace.
Amin Amin sukace baki É—ayansu.
Suna masu kauda kansu kan fatar dan wani irin warin da basu gane kamsaba da fatar keyi wanda dole in kaji zakayi zaton ƙarnin ɗanyar fatarne.
Wanda fiyafiyen ya gauraye dashi sai dai shi kanshi sarkin al'adun sunan kauda kanshi yakeyi dan azabar warin fiyafiyar da Hajia Mama ta turbuÉ—a cikin fatar.
Kansu suka É—an kakkauda tare da cewa.
"Dan Allah kayi maza ka gama ka fito da baiwar Allah".
Cewar Umaymah da Mamma.
Shi kuwa Sarkin al'adun suna murmushi yayi tare da naÉ—a Afreen cikin fatar ragon sunan,
da Hajia Mama ta gama zazzaga mata madarar fiyafiya mai masifar ƙarfi.
Sai dai da yake fatar a ninke take yana kuma warewa ya naÉ—e da sauri to sai ya zama kamar a rufe yake, shiyasa basu ji wari sosai ba.
Dan duk wari shi ai in a rufe yake bakajin warin sosai.
Cikin murmushi mugunta ya haɗe yarinyar ya ninke ciki ya matse da ƙarfi kana ya ɗagata ya nufi Bedroom ɗin Shatu.
Zaune ya sameta bisa bakin gado.
Tayi masifar kyau cikin wata dakekkiyar Getzner Orange color mai masifar kyau da sheƙi.
Khadija na tsaye gefenta tana ninke É—an kwalin zatayi mata É—auri.
Da sauri ta É—ago kanta ta kalli Sairkin al'adun Suna cikin mamaki tace.
"A bawan Allah ya da kawo fatan rago kuma har cikin É—aki".
Cikin yin ƙasa da kai yace.
"Al'adar ranar suna zamuyi".
Hannunta tasa ta dafe kanta kana ɗaya hannun ta ɗaurashi kan ƙirjinta dake harbawa da azaban ƙarfi da sauri-sauri kuma.

Aunty Amina ce tace.
"Kai gsky yana wani irin wari fa".
Ummi dake biye dashi a baya da ita da Umaymah da Gimbiya Aminatu ne suka haÉ—a baki wurin cewa.
"Toh ka fara mana".
Juyowa Khadijah kam tayi ta zauna tana kallon ikon Allah.
Itama Aunty Amina hannu tasa ta dafe haɓarta tana kallon ikon Allah.

Dan dagasu har Shatu basuma gane cewa.
Afreen ce a naÉ—e a cikiba.

Shi kuwa a hankali yake komai yana mai jin yadda yarinyar take mutsu-mutsun neman ceton rai sai ƙara danneta yakeyi.
Ƙarshen ginin ɗakin yaje kana ya sunkuya ya ajiyeta tare da garata ta gangaro har gaban gadon.
Tuni zuwa yanzu numfashin yariyar in ya fita baya komawa.
Gaba ɗaya fatan jikinta yayi jazir idanunta sun ƙaƙƙafe.
Chapter 18 · 0% Book details