← Book details Garkuwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 45

Sashe 13

Garkuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummi ce tayi dariyar jin daÉ—i tare da cewa.
"Wlh kuwa Alhamdulillah Shatu ta haifo mana Kekkyawar ɗiyar fulani fara ƙal".
Kusan a tare Jamil da Affan sukace.
"Yesssss masha Allah Alhamdulillah".
Jalal kuwa wani irin murmushi yayi mai baiyana farin cikinsa a hankali yace.
" A a kai Alhamdulillah Allah mun gode maka, Allah ka raya mana ita bisa imani".

Yah Jafar kuwa da sauri ya juyo ya kalli Sheykh ga mamakinsu babu zato babu tsammani sukaji yace.
"La'ilahaillaha Muhammadu Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallam. Alhamdulillah Allah na gode maka, daka c nuna min wannan ranar Alhamdulillah ni Muhammad Jafar Allah na gode maka".
Wani irin juyowa da ƙarfi Sheykh da zai shige falonsa yayi cikin tsananin kaɗuwa da tarin al'ajabi da mamaki da rantsar kokonton shin muryar Yah Jafar ce kuwa da tsawon shekaru 13 baiyi mgnaba yake mgn?.
Jalal kuwa da sauri ya koma da baya ya faÉ—a kan kujera sabida rawan da jikinsa keyi.
Jamil da Affan da sauri suka matso kusa dashi.
Ummi kuwa da sauri ta saki kular dake hannunta.
Ita kuwa Juwairiyya cikin tsananin kaÉ—uwa da tsoro ta matso gabanshi bakinshi take kallo tamkar zata cire idonta ta mannasu jikin lips É—insa gaba É—aya sun kasa mgn.

Shi kuwa Sheykh da sauri ya iso gabansa hannunshi ya kamo ya riko gam gam tare da cewa.
"Yah Jafar mai-maita abinda kace Yah Jafar sake mgn inji maimata".
Yayi mgnar da ƙarfi cike da kaɗuwa.
Ga mamkinsu sai ga Yah Jafar É—in yayi shiru yana kallonsu Tamkar kurma.
Cikin wani irin tsuma da kaÉ—uwa duk suka zagayeshi.
Cikin tsananin farin ciki Sheykh ya ruggume shi gam-gam a jikinshi murya cike da al'hini da hamdala yake cewa.
"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!. Yah Jafar kayi mgna ka sake yin mgn dan Allah kayi mgn".
Ya ƙarashe mgnar yana mai janye jikinshi daga jikin Yah Jafar ɗin tare dasa hannunsa bisa kafaɗunsa duka biyu yana jijjigawa.
Itama Juwairiyya cikin rauni murya na rawa cike da kukan hamdala tace.
"Yah ilahi ya mujibadda'awati ya Allah idan mafarki nakeyi ka tabbatar min dashi".
Cikin sauri Jalal dake zaune yace.
"Ba mafarki bane Aunty Juwairiyya".
Affan ne ya matsosu tare da haÉ—e su duka ya ruggume sai kawai ya saki kuka.
Ummi kuwa cikin shassheƙan kuka tace.
"Sheykh ku barshi mu bishi a hankali tabbas mgn yayi kuma in sha Allah zai kumayin mgn".
Jamil kuwa gaba É—aya jikinshi kerma yakeyi wayarshi ya zaro Umaymah ya kira tana É—agawa ya fashe da sassayan kuka tare da cewa.
"Umaymah! Umaymah!!".
Cikin tsananin ruÉ—ani da kiÉ—ima tace.
"Innalillahi Jamil mene! Jamil gaya min meyasa ka kuka".
Da ƙarfi yace.
"Umaymah kukan farin cikine.
Yau Yah Jafar yayi mgna kuma ya maimaita Umaymah farin cikine ya samu kuka".
Cikin wani irin farin ciki mara misaltuwa Umaymah ta saki wayar tare da juyowa ta kalli Sitti da Jaddansu da sauran ƙannenta da babban yayansu baban Aunty Juwairiyya da Ibrahim kenan.
Cikin wani irin murmushi mai haÉ—e da hawaye tace.
"Sitti Jadda Jafar ya fara mgn".
Gaba É—aya salati suka É—auka a tare, suka direshi da kalmar.
"Alhamdulillah ala kulli halin, Alhamdulillah lallai tabbas dukkan tsanani yana tare da sauƙin."
Kawai sai kuma duk suka matso gaban Jaddansu da ya saki kuka kamar ƙaramin yaro cikin rawan murya yace.
"ÆŠaya daga cikin burukana ya cika, kafin mutuwata ko yanzu na kwanta dama nasan bakin Jafar ya buÉ—u.
Sai dai har yanzu ina da wani babban buri Yah Allah ka bani aron rai da lfy ka ka baiya na min ƴata Aisha ka tsare min ita a duk inda take ka dawo da ita kan ƴaƴan ta al'farmar Annabi da al'ƙur'ani".
Cikin zubda hawaye suka amsa da Amin Amin gaba É—ayansu.

A nan masarautar JoÉ—a kuwa,
Cikin tsananin tarin farin ciki Sheykh ya kamo hannun Yah Jafar ya zaunar dashi bisa kujera kana da sauri ya juya ya nufi É—akin Shatu.
Konce ya sameta da alamun bacci takeyi.
Hannunshi yasa ya É—auki Jaririyar kana da sauri ya juyo ya fito.

Yana fitowa kuma dai-dai lokacin LamiÉ—o da Galadima da Abbanshi suka shigo falon.
Cikin sauri ya matso gaban Yah Jafar miƙa mishi ƴar yayi ga mamakinsu sai sukaji yace.
"Bismillahi".
Cikin tsananin kaɗuwa da mamaki Lamiɗo Galadima da Abba suka zauna, Lamiɗo da Galadima da Yah Jafar bisa kan kujeru sauran kuma duk kowa na ƙasa harda Abbansu.
Kallon kallo sukayiwa juna lokacin da suka ga yana shafa kan yarinyar tare da buÉ—e baki a hankali yace.
"Masha Allah. Allah ya raya mana ke bisa imani yayi miki al'barka".
Zuwa yanzu LamiÉ—o da Galadima cikin kaÉ—uwa suke cewa.
"Jafar".
Da sauri Sheykh ya juyo ya kalli Abbansu da tuni hawaye suke tsastsafo mishi ya kasa cewa komai sai tallabe haɓarsa yayi da hannu bibbiyu yana kallonshi.
A hankali Sheykh ya juyo kamar ƙaramin yaro haka ya iso da rarrafe.
Ya zauna gaban mahaifin nasu ya fuskanceshi da kyau hannunshi yasa ya kamo hannun Abban nasu ya zare mishi tagumin da yayi, kana yasa tafin hannunshi ɗaya ya share mishi hawayen da yakega suna zubo mishi cikin ƙarfin zuciya da tsananin farin ciki kan farin ciki murya cike da girmamawa yace.
"Abbanmu kace Alhamdulillah kada kayi kuka, Abba kaga ikon Allah ko Yah Jafar yayi mgn a yau yayi hamdala yace ya godewa Allah daya nuna masa wannan ranar muma muce mun godewa Allah mana sai ya ƙara mana wata ni'imar domin indan Allah yayi maka wata ni'imar ka gode mishi sai ya ƙara maka da wata, muce Alhamdulillah".
Kusan a tare gaba É—ayansu sukace.
"Alhamdulillah".
Harda shi Yah Jafar É—in.
Ya ilahi wannan shine kyautar Allah.
Juwairiyya kam hawayenta yaƙi barin zubowa.

LamiÉ—o kuwa a hankali ya dawo kusa dashi hakama Galadima, sai ya zama sun sashi a tsakiyarsu.
Abban da Sheykh kuwa suna gabansu da sauran Juwairiyya da Ummi kuwa suna gefe".
Cikin nitsuwa Abba yace.
"Jafar! Jafar!! Jafar!!!".
Shiru babu amsa.
Da sauri LamiÉ—o ya jujjuya mishi kai tare da cewa.
"A a barshi, dole sai a hankali komai zaiyi dai-dai."
Sai kuma ya gyara zamanshi ya kalli jikokin nashi ya juya dama da hauni kana cikin yin ƙasa da murya yace.
"Toh wannan al'amari ya zama sirri tsakaninmu har zuwa É—an wani lokaci kada ku gayawa kowa na cikin masarautar JoÉ—a".
Da sauri sukace "To".
Shi kuwa Sheykh a hankali yasa hannunshin ya ɗauki Jaririyar ya miƙa Lamiɗo ita.
Addu'o'in yayi mata sosai kana ya miƙawa Galadima ita, sannan Sheykh ya ɗauƙeta ya miƙa Abba ita cikin murmushi yace.
"Aisha ta tafi Aisha ta dawo".
Murmushi Ummi tayi sabida tuno irin tarin son da Abba kewa Mamey wanda shiga goma zai zaka jishi yana kira Aisha! kaxa Aisha kaza da kaza yayi kaza ko?,".
Shima addu'o'in yayi mata kana, suka É—an tattauna kaÉ—an suka tafi.

Su Jamil kuwa suma É—aya bayan É—aya suka amsheta.
Cikin murmushi da tarin son yarinyar Jalal yace.
"Masha Allah da Ishma take kama".
Da sauri Jamil ya amsheta tare da cewa.
"Kace da Mamey take kama tunda Ishma dai da Aunty Rahma take kama Aunty Rahma Kuma da Mameynmu take kama".
Da sauri Affan ya amsheta tare da cewa.
"Masha Allah wlh da Mamey take kama, Alhamdulillah Yusuf ƙarami yayi kamu".
ÆŠan shi kenan takwaran Hamma Yusuf É—in Zahra dariya sukayi baki É—ayansu.
Kana Aunty Juwairiyya ta amshi yarinyar ita da Ummi suka nufi É—akin Shatu.

Suna shiga suka sameta zaune bakin gado da alamun waya takeyi da Rafi'a.
"A a bazan gaya miki ba sai kinzo kiga mai aka samu".
Tayi mgnar tana amsar Babyn da Aunty Juwairiyya ke miƙo mata.
Ita kuwa Rafi'a cikin tarin jin daÉ—i tace.
"Ai kuwa gobe da sassafe zan muku sammako".
Da sauri tace.
"Rafi'a baza kizo mu kwana ba".
Cikin dariyar jin daÉ—i ta e.
"Zan dai zo gobe kam da wuri".
Daga nan sukayi sallama.
Ita kuwa Ummi abinci ta zuba mata mai rai da lfy cimar jegon gaske.
Tuƙeƙƙen tuwon shinkafa da miyar ɗanyar kuɓewa tasha man shanu da yajin daddawa da nama.
Sosai ta tasata gaba taci.
Ita kuma Juwairiyya tana riƙe da Ƴar.

Bayan taci tuwon ne kuma Ummi tasa mata gashin da yaketa tururi yaji yaji tana fifita matashi dan yayi sanyi.
Kana ta haÉ—a mata kunu da zuma ta bata, tanaci tana É—an korawa.
A hankali ta É—an jingina bayanta da gado a hankali tace.
"Ummi na ƙoshi".
Da sauri tace.
"A a Shatu ƙara sashi kada kice zakiyi jegonku na yaran zamani jego da soyayyan Arish da tea".
Cikin sanyi tace.
"Allah Ummi cikina zai fashe".
Jin hakane tace.
"To sai anjima ki ƙara".
GyaÉ—a kai tayi kana ta gyara zamanta.

A can falon kuwa su Jamil duk Dinning area Suka nufa, suka zauna suka fara cin abinci.

Yah Sheykh kuwa falonshi ya wuce, wayarshi liƙe a kunne wanda Bappa yake kira.

Shi kuwa Bappa a can Rugar Bani yana zaune a tsakar gida Junainah na gefenshi su Ummey na gefenta.

Da sauri Junainah ta miƙo mishi wayar da dama Game takeyi da ita.
Amsa yayi da sauri ya amsa kiran.
Gyara zamanshi yayi jin muryar Sheykh na cewa.
"Assalamu alaikum".
Cikin kulawa yace.
"Wa alaikassalam Muhammad".
Da sauri ya zauna bisa kujera cikin tarin jin daÉ—i da son tsohon da tausayinsa yace.
"Na'am Bappa na Ina wuni".
Fuska É—auke da murmushi yace.
"Lfy lau Alhamdulillah Muhammad ya su LamiÉ—o ya Abbanka dasu Jalal duk suna lfy koma?".
Chapter 13 · 0% Book details