← Book details Garkuwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 45

Sashe 19

Garkuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A can É—akin Sheykh kuwa cikin tsananin hatsala da gajiya da dariyar muguntar da Hajia Mama ke kerketa mishi cikin kunnensa tsawon lokaci a tsale yaja tsaki tare da cewa.
"In kin san bazaki gaya minba meyasa kika kirani ina tambayarki me kikasa cikin fatar ragon sunan kina tamin dariya".
Cikin dariyar mugunta tace.
"Hahahahahhh madarar fiyafiyar mai surke da garin sukudaye na turbuÉ—a cikin fatar da nasan yanzu ana can an naÉ—e musu Æ´ar tasu a ciki, kafin miti biyar da za'ayi ana garata ta zama gaw..."
Cikin wani irin tashin hankali ruɗani da firgici da gigita ya cilla wayar ya liƙata da jikin gini a take ta buɗe batir ɗin ya rabu da wayar.
ba tare daya bari ya ida jin me zata ceba.
Cikin tsananin tashin hankali ya fito da gudu.
Gaba É—aya jikinsa tsuma da karkarwa yakeyi tamkar mazari namfashinsa tamkar zai bar gangar jikinsa.
Daga falonshi yake rabkawa Shatu da Umaymah kira da ƙarfi yana cewa.
"Aysha! Aysha!! Umaymah! Umaymah!!! Ummi! Kada ku bari asa Ƴarinyar nan cikin fatar nan".
Da sauri Aunty Rahma da Aunty Juwairiyya da Haroon da Jannart suka miƙe tsaye.
Da sauri Haroon ya nufi falonshi su Jamil ma kan tashi tsaye sukayi jin yadda yake mgn da azaban ƙarfi.
Kiciɓis sukayi da harun.
Da ƙarfi yace.
"Haroon ina Aysha ina Baby Ina Umaymah?".
Cikin tsoro Aunty Rahma tace.
"Suna É—akin Shatu ana al'adar fata".
Da ƙarfi ya ture Haroon dake gabanshi.
Cikin tsananin masifar tashin hankali da ruÉ—ani ya nufi Bedroom É—in Shatu.
Wanda haka yasa suka kab suka bishi a baya.

Da sauri Shatu ta miƙe tsaye tare da cewa.
"Na'am Yah Sheykh".
Sabida jin yadda yake abka mata kira tare da cewa.
"Aysha Aish Ina kike ina Æ´ata?".

Kiciɓis sukayi a bakin ƙofar shigowa ita zata fita shi zai shiga.
Da sauri tasa hannun shi ya tureta har saida ta faɗa jikin Umaymah sabida hango Sarkin Al'adun suna yana gara Afreen dake cikin fatar a ƙasa a tsakiyar ɗakin.
Cikin wani irin masifeffen tashin hankali yasa hannunshin da ƙarfi ya ture sarkin al'adun sunan
Ya faɗi ƙasa tib.

Cikin rawan jiki da tashin hankali Umaymah da Ummi sukayi kanshi.
Aunty Amina da Khadijah kuwa cikin mamaki suka zuba mishi idanu.

Su Aunty Juwairiyya kusa duk shigowa sukayi cike da mamaki.
Ita kuwa Shatu da sauri ta gyara tsayuwarta tare da nufoshi.
Ganin yadda gaba É—aya jikinshi ke karkarwar tamkar mazari.
A gigice ya sunkuyo ya zaro Afreen dake naÉ—e cikin fatar da sauri ya fara worwore fatar.
Gani yakeyi ma tamkar baya sauri murya na rawa hankali a tashe yake cewa.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun hasbunallahiwani'imanwakil Aish zasu kashe mana ita."
Dai-dai lokacin kuma ya gama woreta.
Cikin wani irin tashin hankali Ya juyo a gigice yace.
"Innalillahi Umaymah sun kashe min ita".
Jiki na rawa hankali a tashe Umaymah ta iso gabanshi da sauri tasa hannunta ta amshi yarinyar ganin yadda jikinsa ke karkarwar.
Da Sauri ta juyo gaban Gimbiya Aminatu tare da cewa.
"La'ilahaillaha Muhammadu Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallam.
Ta rasu."
Da ƙarfi Shatu tace.
"Innalillahi Umaymah me kikace kada kice haka dan Allah ku duba da kyau".
Cikin tsananin tashin hankali Gimbiya Aminatu ta amshi Afreen jujjuya yaya tayi da sauri tace.
"Ta...!

By
*GARKUWAR FULANI*
4/6/21, 4:15 PM - &: "Ta Suma ne!". Da sauri Sheykh É—in ya taso, tare da sa hannunshi ya amsheta, da sauri ya juya.
Itama Umaymah da sauri tabi bayanshi.
Side É—insa ya koma da sauri key É—in motarsa ya É—auka Umaymah na biye dashi a baya kana Haroon ma na biye dasu a baya.

Shatu kuwa cikin wani irin kuka mai rauni daya kubce mata ta koma bakin gado ta zauna gaba É—aya jikinta kerma yakeyi.

Shi kuwa Sarkin al'adun suna, da rarrafe ya fita ya bar ɗakin yana fita falon ya miƙe a guje ya bar Part ɗin da sauri Jalal ya mara mishi baya, kafinma ya bar Part ɗin ya damƙeshi Part ɗinsu ya wuce dashi.

Mamma kuwa da Gimbiya Aminatu gefen Shatu suka zauna.
Hannunta tasa bisa kafaÉ—arta a hankali tace.
"Kiyi haƙuri Aysha in sha Allah babu abinda zai samu ƴarki da izinin ubangiji, zata samu lfy".
Cikin rauni murya na rawa ta juyo ta kalli Mamma ido cike da hawaye tace.
"Mamma me tayi musu, da zasu cutar da ita ba tare da haƙƙinta ba, shike nan yanzu duk magautan Yah Sheykh sai su dawo kanta, kawai dan ta kasance ƴarsa, Mamma ya zamuyi".
Da sauri Gimbiya Aminatu tace.
"Babu komai Shatu da izin Ubangiji baza suci nasara a kankuba".

Aunty Rahma da Aunty Juwairiyya da Jannart kuwa jiki a mace suka koma falon Shatu suka zauna.
Gaba É—aya jikin kowa yayi sanyi.

Khadija da Aunty Amin kuwa tsoron al'amarin masarautar JoÉ—a ne ya rufesu.

Da sauri Mamma ta miƙa ganin Shatu ta zabura ta miƙe tsaye da sauri tare da tallabe breast ɗinta.
"Aysha zauna".
Murya na rawa tace.
"Mamma maman Afreen na tsastsafo da ruwa,
Ina Yah Sheykh ya tafi da ita? Ni kam zanje inga halin da take ciki".
Ajiyan zuciya mai nauyi Hajia Kubra dake tsaye gefen Mamma tace.
"Asibiti suka tafi, kuma insha Allah zataji sauƙi".
Kai Gimbiya Aminatu ta gyaÉ—a tare da cewa.
"Sosai ma kuwa tunda har kikaji haka to ta farfaÉ—o ne".

Dai-dai lokacin kuma Umaymah dake tsaye bakin ƙofar ɗakin da Sheykh da wasu manyan likitocin su na Valli Hospital Suka shiga da Afreen a sume.
Ta sauƙe wata ƙaƙkarfan ajiyan zuciya jin kukan da Afreen ta cillara da ƙarfi.

A cikin É—akin kuwa.
Kusan a tare sauran likitocin suka sauƙe ajiyan zuciya tare da ɗagowa suna kallon Sheykh daya ruggumeta jikinshi tare da cewa.
"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!".
Sai kuma ya juyo da sauri ya kalli Dr Lukman Ibrahim babban likitan yara kenan na asibitin na cewa.
"Ina Maman baby a yi maza a bata mama tasha shi zai taimaka wurin ƙara ƙarya ƙarfin gubar".
Da sauri Sheykh yace.
"To".
Kana ya juya.
Yana fitowa Umaymah tabi bayanshi.
Tana tambayarshi.
"Ta farfaÉ—o ko?".
Cikin ƙara saurin tafiyarsa yace.
"Eh Umaymah".
Suna shiga motar yaja da sauri ya nufi masarautar JoÉ—a a guje.

A can part É—insu Jalal kuwa.
Wani irin gigitaccen mari Jalal ya yarfawa Sarkin al'adun suna.
Wanda yasa shi jin fitsari ya kubce mishi.
Ba tare daya gama dawowa hayyacisa ba ya kuma jin saukan wasu tagwayen maruka a gigice ya kurma ihu tare da cewa.
"Wayyoooooooo Allah na na shiga uku ni ilu Jalaluddin kayi haƙuri".
A fusace Jalal yasa ƙafarshi ya taɗe sawunshi har saida ya faɗi tib! A ƙasa hannunshi yasa ya tallabe ƙeyarsa tare da sakin wani gigitaccen ihu.
Da sauri Jalal yasa ƙafarshi ya taƙa yatsun hannunshi tare da cewa.
"Sheeeyyt rufe min baki, uban me kuka sa a cikin fatar ragon sunan?".
Cikin kerma da zare ido yace.
"Wlh bani ne na sakaba".
Ƙara taka yatsun yayi tare da murjesu da ƙarfi yace.
"Me akasa a cikin fatar ragon? kuma waya saka? Nawa kuma aka biyaka?".
Cikin sakin fitsarin azaba yace.
"Madarar fiyafiya ce aka saka cikin fatar. Hajia Mama ce ta saka! Dubu É—ari bakwai ta biyani".
Wani irin murza yasun yayi da ƙarfi tare da cewa.
"Okay bari in daddage yatsun hannun da zaiyi kisan kai da amsar kuÉ—in yin kisan kai É—in".
Zuwa yanzu ya gigice ihu kawai yakeyi, shi kuwa Jalal rufe Windows É—insa yayi ya mishi É—an karen duka.
Kana ya kira É—aya daga cikin ma'akatansu na jami'an sirri na soja yazo ya tafi dashi.

A nan falon Shatu kuwa, a hankali Jamil da Yah Jafar Suka koma suka zauna.

Yana gaba Umaymah na binshi a baya a haka suka shigo.
"Aish Aish Aysha!". Ya ɗan ƙare kiran da ƙarfi.
Da sauri Shatu ta miƙe da sauri ta nufo falon.
Ummi da sauran na biye da ita a baya.
Aunty Amina da Khadijah kuma suna zaune.
Da sauri ya kamo hannunta bisa kujera ya ajiyeta gefen Aunty Rahma da sauri yace.
"Bata nono yi sauri".
Da sauri tace to tare da fara kiciniyar É—ago rigarta.
Ina gani yake bata sauri shiyasa cikin sauri ya É—aura mata ita kan cinyarta.
Kana yasa hannunshi ta baya ya zuge zip ɗin rigar yayi ƙasa da ita.
Hannunshi yasa ya fito da breast É—inta na dama.
Tare da É—ago kan Afreen daketa fidda wani irin numfarfashi alamun har yanzu numfashin bai dai-dai taba.

Da sauri kuwa ta damƙi nonon tare da fara zuƙa.

Wani irin dogon ajiyan zuciya mai nauyi suka sauƙe a tare shi da ita.
Lokaci É—aya kuma hawayensu ya kwaranyo bisa fuskokinsu.
Cikin sanyin murya yace.
"Alhamdulillah Aish kada kiyi kuka kiyi mata addu'o'in samun lfy ke wuce addu'aki gareta bata da hijabi".
Hannunta tasa tana ƙara tallaɓe kan Babyn murya na rawa tace.
"Yah Allah ka bawa wannan baiwa taka lfy ka yaye mata wahalar shaƙar numfashi ka sauƙaƙa mata shi al'farmar Annabi da al'ƙur'ani."
"Amin Amin. Ameeeeeeen ya rabbil izzati my Dear".
Ya faÉ—a yana share mata hawayen fuskarta da hannunshi na hagu.
Chapter 19 · 0% Book details