Sashe 36
Garkuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ai kuwa kamar da fari, suka sake ganin Jalal yayi sama-sama yayi ƙasa har saida Ummey tayi kansa da gudu hannu tasa ta dagoshi.
Tare da juyowa tana kallon gaban Shatu cikin sanyi tace.
"Ayyah Ba'ana kayi haƙuri kada ka cutar min da ahlina nasan kai mai al'khairi ne a gareni.
Bappa ne ya matso shima a hankali hakama su Affan da Yah Jafar.
Shi kuwa Sheykh jingina kanshi yayi da jikin bishiyar CeÉ—iya dake gefenshi.
Hannunshi na dama yasa ya tallabe haɓarshi yana mai bin inda Shatu take da wani irin kallo.
Sabida da fari zatonshi ko makaranta ne suka dawo.
So yanzu ya fahimci ba makaranta bane.
Hatsabibancin Ba'ana ne,
Nazari yakeyi yadda zai fito mishi ta sigar da dole ya karya lagonshi da takwabin addu'a.
Da sauri su Ummi duk sukace.
"Innalillahi".
Sabida ganin Ba'ana ya baiyana kansa garesu.
A take kuma ya ɓace.
Sai ya kuma sake baiyana ya kuma bace, saida yayi haka sau uku kana ya ɓace sai muryarsa ke tashin cikin rauni yace.
"Baroon kaci amanata ina sane na Barka.
Nayi hakane dan ka jawo shi wannan mai jajayen kunnuwa ya kawo min ita har nan.
Ku a zatonku tarkonku na faÉ—a baku san cewa nawa tarkon kuka faÉ—a ba sa'ansu É—aya nayi tuba na gaske bazan sake kashe raiba."
Sai ya kuma bayyana still hannunshi riƙe da hannun Shatu cikin rauni murya na rawa tace.
"Ayyah Yah Ba'ana dan Allah ka sakeni kada ka rabani da Æ´an uwana da Æ´ata".
Wani irin jujjuya kai yayi tare da cewa.
"Bappa kun kasa cika min al'ƙawarin da kukayi min ko.
Kai kuma Baroon kaci amanata ka muna furceni.
Shatu ke kuwa kin yiwa soyayya ta ta gsky riƙon sakainar kashi.
Wani abu kuke tunanin zaifi min ciwo da zafi sama da rabuwa da Shatu".
Sai kuma ya kalli Sheykh daya zuba mishi ido yana takaronto addu'o'i babu ƙaƙƙautawa ido cikin ido ya tsare Ba'ana da ido.
Shi kuwa Ba'ana murya a mace yace.
"Ko na bar barun a raye kaima watan wata rana zai ci amanarka tabbas zaici amanarka maci amana kuwa gubane".
Cikin sauri suka juyo kan Baroon daya saki wata iriyar gigitaciyar ƙara tare da komawa bayan Sheykh.
Shi kuwa Sheykh ido ya zubawa inda Shatu take tana nufoshi alamun Ba'ana na matsowa inda yake.
Da sauri sojojin dake wojen suka shigo da gudu
Lokaci ɗaya mutane suka fara tururuwan shigowa gidan sabida ihun da Baroon yakeyi yana kiran sunan Ba'ana yana bashi haƙuri.
Jalal kuwa da sauri ya kuma nufo inda Shatu take wanda da ita suke gane inda Ba'ana yake.
Cikin tsoron kada ya cutar da Sheykh ya nufosu.
Gib ya kuma ture Jalal tare da cewa.
"Ummey ki gayawa wannan yaron zan illatashi fa ya dena matsowa inda nake".
Gaba É—aya tsoro ya rufesu jin furucinsa.
Jalal kuwa hatsala iya hatsala ya hatsalo allurar ta motso to amman kuma faÉ—a da Ba'ana tamkar faÉ—a da iska mai kaÉ—awa ne ko kuma duhu.
Da sauri Ba'ana ya juyo kawai sai ya fara dukan sojojin nan baki É—ayansu.
Ya bugi wannan ta nan ya bugu wan can ta can.
Kana ya haɗa da shaƙo wuyan Baroon.
Kurma ihu da kakarin mutuwa Baroon yakeyi da ƙarfi.
Wanda yasa gaba É—aya gidan ya cika da mutane.
Harda su ArÉ—o Bani.
Bukar da Bugulu kuwa gefen Bappa suka tsaya suna kekrketa dariyar mugunta.
Junaidu kuwa gefen Junainah dake ta kuma ta tsaya yana bata baki.
Gaba É—aya hankalin mutane ya tashi.
Su Bappa da Arɗo bani da sauran dattawan Rugar Bani duk sai haƙuri suke bawa Ba'ana sabida ganin yadda yaketa dukansu Jalal ba sauƙi.
Ita kuwa Shatu da gudu ta faÉ—a jikin Sheykh sabida saketa da Ba'ana yayi.
Ganin ta nufi wurin Sheykh ne ya sashi sakin wuyan Baroon tare da barin dukan su Jalal.
Ya nufo kansu Sheykh da Shatu.
Cikin tsananin ruÉ—ani Shatun ke cewa.
"Yah Sheykh mu gudu zai maka illa".
Jamil kuwa tuni ya fara aikinshi.
Affan kuwa da Yah Jafar Kara matsowa kusa da Sheykh suke gudun kada a cutar dashi.
Aunty Juwairiyya da Ummi da Sara da inna Amarya kuwa gaba É—aya jikinsu rawa yakeyi.
Shi kuwa Sheykh murmushi yayi jin Shatu tace.
"Wayyoooooooo Allah Yah Ba'ana ka sakeni".
Hakane yasa ya fahimci Ba'ana na kusa dashi.
Ido ya lumshe tare da É—ago hannunshi kana a hankali yace.
"Bismillahi".
Yana faɗin haka yaji hannunshi ya sauƙa kan hannun Ba'ana kuma ya baiyyana kowa na ganinshi.
Cikin nitsuwa Sheykh ya fara karanto Ayatulkursi'u yana mai kallon Ba'ana ido cikin ido wanda a take ya karya duk wani sihirin da Ba'ana ke tutiya da tinkaho dashi da ayar Allah. (Haske ya kori duhu)
Da sauri Shatu ta koma bayan Sheykh É—in.
Shi kuwa Sheykh juyowa yayi ya kalli su Jalal daketa haki cikin haki da tsananin tafasar zuciya suka nufosu.
Shi kuwa Sheykh ido ya zubawa Ba'ana ganin yadda yaketa fiffizgewa da buga ƙafarshi ta dama da ƙasa amman ina ya kasa ɓacewa.
Cikin sanyi yace.
"Jalal ku kamashi da sunan Allah bazai sake ɓacewa ba har abadan da izinin ubangiji".
Ai kuwa da sauri Jalal yasa hannunshi ya damƙo wuyan Ba'ana tare da cewa.
"Bismillahi".
Ai kuwa bai ɓace ɗinba.
Cikin wani irin tafasan zuciya da zafin yadda Ba'ana yayi ta libgarsu kamar shine sojan sune masu laifi cikin takaicin.
Yayi mishi wani irin azabebben shaƙa tare da kima mishi naushi a cikinsa tare da kalmar "Bismillahi".
Wani irin azabebben ihu mai rakaÉ—i da baiyyana azabar da yaji yace.
"Wayyoooooooo Allah na rana,".
Cikin haki Jalal ya kuma haÉ—a mishi wani naushin tare da cewa.
"Kasan Allah ne kafurin banza matsafi".
Dai-dai lokacin kuma sauran abokanshi sojojin suka rufe Ba'ana da azabebben duka da ammaton sunan Allah wanda hakan ke ƙara kwance duk wani ɗaurin sihirin dake jikin Ba'ana.
"Ya ilahi ya mujibadda'awati."
Mamey da Ummi ke faÉ—i sabida wani irin dukan zaban da su Jalal keyiwa Ba'ana.
Ita kuwa Shatu cikin tsananin tsoro da kerma ta ɗan leƙo.
Dai-dai lokacin Khalid ya murɗe hannun Ba'ana ɓas ya bada sautin karyewa.
Da sauri ta rumtse idanunta tare da sakin wani irin kuka mai ciwo a rai.
Da sauri Sheykh ya juyo yana kallonta.
Bappa kuwa dasu ArÉ—o Bani dasu Yah Jafar kab Bukar da Bugulu suke kallo wa É—an da suke wani irin kuka mai cike da tashin hankali.
Jamil da Affan kuwa sarawa su Jalal sukayi.
Mutanen Rugar Bani kuwa kab suna tsaye wasu tuni hawaye na zubo musu.
Da ƙarfi Ba'ana yayi wani irin azabebben ihu da kururuwa sabida taka hannunshi da Khalid ya karya.
Wanda Umar yayi É—aya sojan ya murza tare da buga mishi naushin da saida yayi birgiman kule ya iso har gaban Sheykh.
Cikin rauni da azabar raÉ—aÉ—i murya na rawa yace.
"Mata! Mata zasu kasheni!".
Cikin wani irin rauni da tsananin tausayi wani irin masifeffen kuka mai ƙarfi yan kwacewa Shatu.
Da sauri ta zame har ƙasa ta durƙusa.
Sabida wani irin azabebben tokara da guiwa da Jalal yayi mishi bisa tsakiyar bayanshi.
A take sai ga jini ta hancinsa da bakinsa.
Murya na rawa cike da rauni Shatu ta É—ago kanta.
Ta kalli Jalal dasu Khalid kana ta kalli jinin bakinshi daya ɗan tsallo ya taɓa farin gyalen jikinta.
Wani irin kukane mai cike da tsananin tausayi rauni ta fashe dashi tare da cewa.
"Ayyah Jalal dan Allah ku barshi kada ku kasheshi ku barshi dan Allah".
A hankali Jalal ya ɗan tsaya yana maida wani irin azabebben numfashin haƙi.
Sheykh kuwa wani irin kallo mai cike da azabebben kishi ya watsawa Shatu.
Tare da sa tafin hannunshi ya tallabe haɓarshi.
Kana ya jingina kanshi da jikin bishiyar yana mai kallonsu.
Mamey kuwa itama zamewa tayi tanamai sakin kuka.
Ummi, Inna Amarya, Aunty Juwairiyya, Sara, dama duk sauran matan dake wurin wasu irin hawaye ne masu zafi suka tsastsafo musu.
Junainah kuwa zuwa tayi ta durƙushe gaban Ba'ana gefen Shatu cikin wani irin azabebben kuka mai cike da rauni tace.
"Wayyo Yah Ba'ana Dan Allah Adda Shatu ki hanasu dukanshi."
Da ƙarfi Junainah ta faɗa jikin Shatu lokacin da Jalal yayi wani irin juyi ya kifawa Ba'ana wani irin masifeffen mari da tafin ƙafarsa.
Tare da cewa.
"Wato kai gaka shege har zaka sa hannu ka daki jamin soja".
Wani irin azabebben karkarwa jikin Ba'ana ya farayi tamkar mazari.
Wani irin kuka mai azabar ciwo da cin rai Bukar da Bugulu suka saki sabida ganin yadda hukuma ke azabtar da Ba'ana tamkar zasu É—auke ransa.
Cikin rauni murya na rawa ido na zubda hawaye Mamey tace.
"Jalaluddin ku bar dukanshi".
A hankali Jalal ya koma baya ya zauna bisa dakalin ƙofar ɗakinsu Giɗi.
Sabida yasan muddin Mamey ta kirashi da sunanshi kai tsaye to abu ya ta'azzara gareta.
Domin Babana take kiranshi, sai gashi yau full name É—inshi ta kira bama Jalal kawai ba.
Sai kuma ta kalli su Khalid kana ta juyo ta kalli Sheykh murya na rawa tace.
"Muhammad ka hanasu dukanshi".
Cikin wani irin yanayi Sheykh ya É—agawa su Khalid hannu.
Haka yasa suma suka koma gefen Jalal suka zauna suna haki da maida numfashi.
Shi kuwa Sheykh ido ya zubawa Shatu dake kuka tamkar ranta zai fita.
Gaba É—aya wurin babu wanda rauni bai darsu bisa zuciyarsa ba.
Yah Jafar da Bappa kuwa tuni hawaye suke zubdawa.
Bukar da Bugulu kuwa da rarrafe suka iso gareshi.