Sashe 6
Exiled Prince Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gyada mata kai kawai Zulaihat ta yi ba tare da ta ce komai ba
wani cool murmushi Inaya ta saki sannan ta ce " Shikenan yanzu fada min ba ki son shi ? "
girgiza mata kai ta yi ta na cewa " da ba na son shi ba zan yarda na aure shi ba "
" to minene matsalar , why za ki ce a raba auren ku bayan ki na son mijin ki "
" Ina son shi amma gaskiya ba zan iya zama tare da shi ba , ba zan iya zama da mutumin da zai iya daga hannu ya dake ni , wanda zai iya halaka ni babu ko tsoron Allah a idanun shi ni gaskiya a raba auren nan "
" Inallillahi , ki na nufin Dukan ki ya ke ? "
gyada mata kai Zulaihat ta yi kafin ta ce " kullum sai ya sa hannu ya dake ni , ko da ban yi mishi laifi ba , har ya kai na rasa cikin shi da ke a jiki na saboda Dukan da ya ke min , Idan na fadawa yan gidan mu , sai su ce na yi hakuri mu rufawa juna asiri , ko karar nan da na kawo babu wanda ke da labarin ta saboda na san za su yi kokarin hana ni , Don Allah ina rokon ki , ki yi wa adalin shugaban mu magana ya raba ni da shi , duba ki gani irin azabar da ya ke min "
ta kai karshen ta na sa hannu ta warware veil din da ke a kan ta
ga shaidar belt nan konce a kan fatar ta , saman shoulder , saman wuya har a kirji , sun ni jazir kamar jini zai fito
cike da takaici Inaya ta ce mata " ki yi hakuri na yi miki Alkawari ba ke ba shi a yau , kuma zai fuskanci hukunci dai'dai abun da ya yi miki "
a hankali Zulaihat ta meda veil din ta ta yafa ta na yi wa Inaya godiya
a hankali Inaya ta mike ta juya ta na kallon mutanan fadar da su ka tsare ta da idanu
" na san dukkan ku kun ji abun da ta fada , shin wane hukunci zai fi dacewa da mutumin da zai iya daga hannu ya daki matar shi bayan ba ta yi mishi laifi ba , har ya kai ta rasa babyn da ke jikin ta , Tabas maza sun fi mata karfi saboda a haka Allah ya hallice su , amma ba ya bawa maza wannan karfin ba dan su dinga cin zarafin mata sai dan su dinga kare su , namijin da zai iya daga hannu ya daki mace , macen ma mai ciki sam bai kamata a kira shi da namiji " ta na gama fadar haka ta fara takawa a hankali ta koma saman chair din ta ta zauna
mutanan wajen ban da kallon ta ba abun da su ke yi har shi kan shi Malik , sam maganar ta ba ta yi kama da shekarun ta ba , da ga ji ka san akwai hankali tare da ita
a hankali Malik ya sauke ajiyar zuciya kafin ya juya ya kali Diya , ya ce " Ka sa a rufe shi a yi mishi bulala dari ko wace safiya , ya kuma rubuta mata takardar ta sannan ku ba ta abun da za ta kula da kan ta "
" an gama ran ka shi dade " Diya ya fada cikin girmamawa sannan ya dago kai ya kali wasu dogarai , da hannu ya musu allamun su dauke Hadi
da sauri dogarai uku su ka karaso wajen su ka dauke shi , sai kara ya ke ya na ba da hakuri wai su kyale shi a haka har su ka fice fadar da shi su ka nufi prison
su na fita Malik ya ce ma Zulaihat " gobe za ki iya dawowa ki karbi takardar ki "
ya na gama rufe bakin shi Rafik ya ce " amma ranka shi dade ta ya za mu raba auren su bayan ta na son shi , may be shi ma ya son ta kuma watarana zai iya yin nadamar haka har ya daina daga hannu saman ta , gargadi ya kamata mu yi mishi "
a hankali Malik ya juyo ya kali Rafik ya ce " wane irin gargadi za mu ba wa mutumin da zai iya kashe babyn shi tun kafin ya shigo duniya , a bar ma zancen bugun ta da ya ke yi , kisan kai fa ya yi , ko kuma sai ita ma ya kashe ta zai yi nadama ? "
dan sunkuyar da kai Rafik ya yi ya na cewa " An yi min afuwa ran ka shi dade "
Malik bai ce mishi komai ba ya juya ya kali Zulaihat ya ce " Tashi ki je a mayar da ke gidan ku "
cikin girmamawa Zulaihat ta shiga yi mishi godiya ta na jero mishi aduo'i shi da Inayar shi mutanan fadar su na amsa mata da ameen sannan ta tashi ta fita
ta na fita Malik ya juyo ya kali Inaya , Da ta yi cak waje guda ta tsare waje guda da ido
cikin rudu ya juya ya kali saitin da ta ke kallo , nan ya ga ashe Miram ta ke kallo , sai faman kauda kai ya ke ya kassa kallon ta
a hankali Malik ya juyo gare ta ya kai hannu saman nata cikin rada ya ce mata " Cutie me ya faru ne ? "
wata nanauyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta juyo ta kali Malik cikin rada ta ce mishi " baby , wannan mutum shi ya yi kokarin kashe saurayin da mu je gani asibiti cikin dare "
Dum Malik ya yi zuciyar shi ta buga da mugun karfi har wani lumshe idanun shi ya yi ya na fadin " ya rahman " cikin zuciyar shi
ajiyar zuciya ya sauke kafin ya juya ya kali General Abdallah da hannu ya mishi allamun ya zo
ba musu General ya mike ya karaso gaban Malik ya tsaya ya sara mishi
da hannu Malik ya mishi allamun ya matso
a hankali General ya juya ya kali mutanan fadar kafin ya juyo ya daga kafa ya karaso dab da Malik ya sunkuyo
cikin rada Malik ya ce mishi " Ku yi bincike a kan lambar motar da na tura maka ? "
gyada mishi kai General ya yi kafin ya ce " eh ran ka shi dade mun yi , yanzu ma na ke cewa idan mun fita , na tarda ka part din ka dan mu yi maganar "
" no fada min , da sunnan wa a ka yi register din motar "
a hankali General ya saci kallon Miram kafin ya ce " ranka shi dade , da sunnan Miram ne , a cikin daren kuma na tura dan leken asiri kofar gidan Miram , a cikin daren kuma ya ce min ya ga shigowar wani mutum gidan Miram cikin motar , kuma bai yi ten minutes ba ya fita da motar sai dai mutum biyu su ka fita a cikin motar "
dan lumshe idanun shi Malik ya yi kamar mai jin barci sannan ya ce ma General zai iya tafiya
ba musu General ya koma saman chair din shi ya zauna
ya na zama Malik ya kali Inaya ya ce " Cutie tashi ki je wajen Momy ta ce ta na son ganin ki "
gyada mishi kai Inaya ta yi kafin ta mike , cikin nitsuwa ta fara takawa ta fice fadar
ta na fita ya juya ya kali Diya , da sauri Diya ya dan sunkuyar da kan shi dan jin abun da zai fada
ni dai ban ji abun da ya rada mishi ba , ya na gama maganar shi ya mike tsaye
da sauri mutanan wajen su ma su ka mike tsatsaye , cike da izza ya fara takawa ya nufi Hanyar fita fadar ya fice abun shi
ya na fita Kowane ya koma ya zauna , sannan Diya ya tako gaban Miram ya ce " Miram mai martaba na son ganin ka a part din shi "
cikin rudu Miram ya ce " To , why zai ce sai a part din ba zai iya yi min maganar a nan ba ? "
" ni ma ban sani ba kawai ya ce min na fada maka ya na jiran ka a part din shi , a floor na karshe " Diya na gama fadar haka ya juya ya koma saman kujerar shi ta wazirin Malik su ka ci gaba da aikin su
cike da Shakku Miram ya mike ya bar fadar ya nufi part din Malik
▪INAYA
bakin ta dauke da sallama ta shigo parlourn MALIKAT AL'UMU
nan ta tardo Tesnim da Rouksar zaune a parlourn su na hirar su
Rouksar na ganin Inaya ta tsuke fuska ta kauda kai gefe kamar ba ta gan ta ba ko sallamar ta ba ta amsa mata ba
Tesnim kuwa da fara'a a fuskar ta ta ce " My sister-in-low , sai yau ki ka tuno da ni ? "
wani dan karamin murmushi Inaya ta saki ta na karasowa gaban Tesnim sannan ta zauna saman sofa a geffen ta ta na fadin " Aunty Tesnim ina kwana ? "
" lafiya lau Baby , ya ki ke ? yanzu kin ba zuwa waje na ko ? " Tesnim ta fada ta kai karshen ta na yi wa Inaya hararrar wassa
yar karamar dariya Inaya ta yi kafin ta ce " Sorry Aunty Tesnim , Momy ta na nan ? "
" eh , bari na je na ce mata MALIKAT Inaya na son magana da ita " ta fada cikin zolaya har da yar karamar dariya kafin ta tashi ta bar wajen ta nufi corridor