← Book details Exiled Prince Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 61

Sashe 21

Exiled Prince Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta na fita shi ma doctor Asheem ya fice , daya bayan daya sojojin nan su ka dawo cikin dakin , duk abun da su ke Malik ya na jin su amma ba shi da bakin yin magana sai kifta idanun shi kawai ya ke , sai da ya share wajen good one hour a haka kafin ya lumshe idanun shi a hankali allamun barci ya ke ji

bangaran MALIKAT INAS kuwa , ba ta koma part din ta ba sai da ta tafi wajen MALIKAT AL'UMU
bakin ta da sallama ta shigo dakin , nan ta ga MALIKAT AL'UMU konce saman gado idanun ta a lumshe

a hankali INAS ta karaso wajen gadon ta janyo chair ta zauna ta saki wani dan karamin murmushi ta ce " Moussina , yaron mu fa ya tashi , yanzu haka da ga room din shi na ke , amma doctor ya ce bai gama dawowa cikin hayacin shi , sai gobe zai iya zuwa ya gan ki , ina Fatan da kin jin Muryar shi za ki tashi " ta kai karshen ta na sakin dan karamin kuka

da sauri ta kai hannu ta fara goge hawayen ta ta na cewa " na san duk cikin jarabawar ubangiji ce , kuma in sha Allah sai mun lashe wannan jarrabawar , kamar yadda yaron mu ya tashi haka kema za ki tashi in sha Allah , za mu ci gaba da yin addu'a Allah ya tsare ahalin mu baki daya , dan ina ga makkiyan mu su na da yawa , Idan mun san wasu , wasu kuma ba mu san su ba , kawai kariyar ubangiji ya kamata mu nema , bari kar na cika ki da surutu zan tafi amma in sha gobe zan dawo , ki kula min da kan ki " ta na gama fadar haka ta kai lips din ta saman forehead din MALIKAT AL'UMU ta manna mata kiss kafin ta tashi ta baro dakin

bangaran su Inaya kuma , da sallama a bakin ta RIANNA ta shigo parlourn MALIKAT INAS
nan ta tardo Tesnim zaune waje guda ta yi zugum allamun ta tafi duniyar tunanin ta , har sai da RIANNA ta kai Inaya bedroom din ta , ta dawo cikin parlourn ta zauna geffen ta ta na yi mata magana ba ta sani ba

a hankali RIANNA ta kai hannu ta dafa shoulder din ta ta na fadin " Tesnim lafiyar ki kuwa ? "

a razane Tesnim ta dawo cikin hayacin ta ta juya ta kali RIANNA ta ce " ummm , wani abu ki ka ce ? "

" tunanin me ki ke yi haka tun dazu ina yi miki magana kin kyale ni " RIANNA ta tambaye ta ta na yi mata irin kallon tuhuma

girgiza mata kai Tesnim ta shiga yi ta na cewa " ba komai , ya jikin momy ? "
wani kyawatencen murmushi RIANNA ta saki kafin ta ce mata " Malik ya bude idanu "
wata yar karamar kara Tesnim ta saki ta mike tsaye da ta na fadin " da gaske Malik ya tashi , bari na je na gan shi " ta fada da sauri ta na shirin takawa

da sauri RIANNA ta riko hannun ta ta na cewa " to uwar zumudi dawo zauna , doctor ya ce kar wanda ya yi mishi magana sai gobe dan bai gama dawowa cikin hayacin shi ba , in kuma ki ka je , zai tambaye ki ke wacece , da ga nan ki sume mana kamar dai baby " ta kai karshen ta na yar karamar dariya

a hankali Tesnim ta koma ta zauna ta na murmushi ta ce " Allah na gode maka , na san tun da Malik ya tashi , ita ma momy za ta tashi da ga ta ji Muryar shi "

" in sha Allah " RIANNA ta fada ta na murmushi
da sauri Tesnim ta fada jikin RIANNA ta rungume ta , ta na sakin murmushi mai dan sauti kamar ta dariya
su na a haka MALIKAT INAS ta shigo ta same su
wani kyawatencen murmushi ta saki kafin ta karaso cikin dakin ta zauna saman sofa one seater ta na kallon su ta ce " tun da yanzu komai ya yi sauki , ku shirya gobe za ku koma dakunan mazajen ku "

a tare Tesnim da RIANNA su ka juya su ka kali MALIKAT INAS har su na hada baki wajen cewa " no gaskiya Ammie sai momy ta tashi "

tsuke fuska MALIKAT INAS ta yi ta na fadin " ba na son shirme , ba shawara na ke ba ku ba , umarni ne , da aure a kan ku amma ku ke nan zaune tare da ni , ko ita baby da na bata dama wlh tare da Malik za ta dinga kwana a cen likita , dan haka kuma ku shirya ku tafi wurin mazajen ku , in ku na son ganin Momy ai ku na iya tafiya ganin ta har ku biyo ku gan ni , ai duk cikin gida guda mu ke "

ta na gama rufe bakin ta Tesnim ta ce mata " amma fa Ammie....... "
ba ta kai karshen maganar ta ba MALIKAT INAS ta katse ta da cewa " ku rufe min baki , wlh duk wadda na gani cikin part din nan gobe a irin wannan lokacin sai na saba mata " ta na gama fadar haka ta tashi ta nufi corridor ta shiga bedroom din

ta na shiga Tesnim da RIANNA su ka juyo su ka kalli juna , a tare su ka sakin wa juna murmushi kafin Tesnim ta mike ta na fadin " shikenan , ni na tafi sai da safe " ta fada ta na fara takawa ta shiga corridor ta shiga bedroom din Inaya su ka bar RIANNA ita kadai a parlour

❤⚘E X I L E D P R I N C E⚘❤

(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )

STORY & WRITTEN BY : MEERAH ⚘🕊

BOOK ________3 👑✌

P A G E 12 🌹🕊

babu ko sallama Tesnim ta shigo bedroom din Inaya , nan ta tardo ta konce kamar gawa
wani dan karamin murmushi Tesnim ta saki kafin ta karaso bakin gadon ta zauna ta na kallon Inaya ta saki wani cool murmushi kafin ta juya

ta na shirin tashi idanun ta su ka sauka kan wayar Inaya , da ta Malik ajiye saman bedside drawer
a hankali ta juya ta kali Inaya kafin ta kai hannu ta dauki wayoyin
ta Inaya ta fara kunnawa , ta ga wallpaper din ta pic din Malik ne a sama , daya da ga cikin pics din da RIANNA ta turo mata
a hankali ta saki wani dan karamin murmushi kafin ta kunna wayar Malik , shi ma wallpaper din shi pic din Inaya ne , ta na konce saman gado , ta na sanye da wasu kananan kayan barcin pink color , gashin nan nata duk a tirje ta na barcin ta cikin konciyar hankali har wani dan karamin murmushi ta saki gwanin burgewa

wani cool murmushi Tesnim ta saki , ta na ci gaba da latsa wayar Malik amma sai ta ga ta na da Password ba dan ta so ba ta meda ta saman bedside drawer ta ajiye , sannan ta shiga latsa ta Inaya ta shiga messenger din ta , ta fara karanto Text din da Malik ya turo mata
sai da ta yi zaune ta karance su tsab sannan ta kashe wayar ta ajiye saman bedside drawer
sannan ta juyo ta kali Inaya ta saki wani cool murmushi murya kassa kassa ta ce " Gaskiya , yayana ya na matsanancin son ki , na san da ya son ki , amma ban taba tunanin soyayyar da ya ke miki ta kai haka ba , kamata ya yi a kira ku da Romeo & juliet , Allah ya sa ni ma wanda na ke so ya so ni haka , fiye da rayuwarshi "
ta na gama fadar haka ta tashi ta shiga toilet

▪AYMANE

" why ? why ? why ? why bai mutu ba ? ta ya a ka yi ma ya tashi wannan banzan Malik " Aymane ya ke fada cike da bacin rai

wani dan karamin tsaki Rouksar ta yi kafin ta ce " ka na tambaya ta , yo ni sani na yi , ko ni Tesnim da RIANNA na ji su na maganar , na zo shiga part din MALIKAT INAS ne na ji RIANNA ta na cewa Tesnim wai Malik ya bude idanu "

" na san wacen banzar yarinyar ce ta ta tashe shi , sai da na ce miki ki kashe ta , ki kashe ta , ki kashe ta amma kin kassa , yanzu ya ki ke so na yi , Rouksar duk abun da ya faru laifin ki ne " ya fada ya na nuna ta da yatsa

hannu Rouksar ta kai ta buge hannun shi ta na kallon shi cikin ido ta ce " no , laifin ka ne , lokacin da Hakim ke shirin harbin Nawfel , kai ka juya kwakwolwar shi ya harbi Malik , why ba ka kyale shi ba ya harbe shi , da yanzu wannan ba ta faru ba , ba ka tunani kafin ka aiwatar , Malik da ka ke ganin shi ya fi mahaifin shi wayo , da tun farko shi ka bari Hakim ya kashe da yanzu kai ne a kan kujerar Malik , yanzu Ruhin MALIKAT AL'UMU da ka sa na boye cikin bishiyar nan da me zai anfane ka ? a sani na ba MALIKAT AL'UMU za ta nadda ka a matsayin Malik , son da ka ke wa mulkin Saudiya ya sa ka daina anfani da kwakwolwar ka , ka ce min idan na yi abun da ka ke so za kyale ni , na yi abun ka ke so dan haka da ga yanzu kar ka sake nema ta " ta na gama fadar haka ta bace bat
Chapter 21 · 0% Book details