← Book details Exiled Prince Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 61

Sashe 10

Exiled Prince Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

cikin nitsuwa ya katse ta da cewa " uhm me za ki fada mata ? " ya tambaye ta dai'dai lokacin da ya sauke ta saman gadon su , a hankali ya komo bakin gadon ya zauna ya kai hannu cikin aljihun ya ciro wayar shi ya fara latsawa

cikin shagwaba ta ce mishi " sai na ce mata ba ka bari na huta , ni gaskia yaya Zayd ka kyale ni na yi barci "

cen sai ta ga ya dago wayar ya kai ta a kunne ya yi sallama cen kassan makoshi sannan ya ce " Barka da wannan lokacin Ammie "

Inaya na jin ya ce Ammie ta zaro idanu ta na kallon shi
ta na haka ta jiyo Muryar shi ya na cewa " Fine Ammie , dama akwai wanda ke son magana da ke ne " ya na gama fadar haka ya sauko wayar
ya mika mata ya na cewa " karbi Ammie ce "

da sauri ta girgiza mishi ta na marairaice fuska
matse gera ya yi allamun babu wassa ya ce mata " karbi na ce ! "

wasu yawu ta hadiye kafin ta dago hannun a hankali ta karbi wayar , ta kai a kunne Murya na kerma ta ce " Hello Ammie "

a daya bangaran cikin fara'a MALIKAT INAS ta ce " Baby ya ki ke ? fatan ki na lafiya ? "

cikin sanyin murya Inaya ta ce mata " Ina lafiya Ammie , ya ku ke , da Aunty RIANNA ? "

" Alhamdoulilah baby , Allah ya sa dai lafiya mijin ki ya ce ki na son magana da ni "

a hankali Inaya ta dago kai ta ga shi ma ita ya ke kallo
" Oya , fada mata " ta fada ya na daga mata gera guda

" babu komai Ammie " ta fada da sauri ta sauko da wayar ta mika mishi
ba musu ya kai hannu ya karbi wayar ya kai a kunne ya ce " ta ce ne ta na kewar ki , shi ya sa na kira ki "

" kai dai Nawfel , na san Halin ka , anya ba takurawa yarinyar mutane ka ke ba "

" Ammie na takura mata ba matata ba ce ? " ya fada da larabci

wata yar karamar dariya MALIKAT INAS ta yi kafin ta ce " Allah ya huci zuciyar ka , ka dai yi mata a hankali na san halinka ba karamin jarabbabe ba ne , ka na gani fa yarinya ce , ba dan ta dauke ka sau guda za ka ci gaba da takura mata , ka dinga bari ta na hutawa kar ka ji mata ciwo "

shiru ya yi ya na sauraron ta , kenan ta gane maganar me Inaya ta so yi mata kenan ?
a hankali ya sauke ajiyar zuciya ya ce " Shikenan Ammie "

" yawwa dan Albarka , ka kula min da ita ka ji ? "
cikin sanyin murya ya ce " In sha Allah Ammie , ki kula min da kan ki " ya na gama fadar haka ya sauko wayar ya katse kiran sannan ya kai hannu saman bedside drawer ya ajiye ta

ya na ajiye wayar ya dawo da kallon shi kan Inaya ya ce mata " I love you "

wani kyawatencen murmushi ta sakin mishi har da sauke ajiyar zuciya , da sauri ta fada jikin shi ta rungume shi
A hankali ya zagayo da hannayan shi a bayan ta ya rungume ta tsam , kafin ya Haye saman gadon ya konta da ita a jikin shi , a haka har barci ya yi gaba da su

▪WASHE GARI

misalin karfe 8 na safe , fadar masarautar cike ta ke da mutane dan yau Malik zai yanke wa Hakim Hukuncin , musaman MALIKAT AL'UMU da MALIKAT INAS sai da su ka halar ta bisa Umarnin Malik

su na a haka General Abdallah ya ce wa daya da ga cikin sojojin shi ya je ya taho da Hakim
ba musu ya fice da gudu ya bar fadar

ya na fita Inaya ta matso kussan Malik ta ce mishi " Baby ciki na ciwo ya ke min " ta fada ta na marairaice fuska

slowly ya juyo ya kale ta , ya ce mata " Sorry my Cutie , da na Kamala za mu tafi "
wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta gyada mishi kai ta gyara zaman ta

su na a haka sojoji Biyar su ka shigo , biyu na rike da Hakim
biyu na rike da Miram da ke daure kamar goro , fuskar shi duk ta yi ja allamun ya sha bugu dan bakin shi har ya fashe

mutanan wajen na ganin Miram duk su ka shiga kananan magaganu
da sauri Diya ya ce musu " please keep quiet ! "
ba musu kowane ya yi tsit ya na kallon abun da ke faruwa
sai da sojojin nan su ka kawo su tsakiyar fadar , sannan su ka zubar da su saman guyiwowin su , su na fuskantar Malik

cikin nitsuwa Diya ya ce musu " Kamar yadda ku ka sani wannan shi ne Sniper din da ya harbe marigayi Malik , a yau mun dawo ne gaban Malik domin yanke mishi hukunci dai'dai abun da ya aikata , na san kowa zai yi mamakin ganin Miram a wannan yanayin , duk za ku samu amsar ku nan gaba "

Wani dan karamin murmushi Diya ya saki ya na kallon Miram ya ce " Miram , ba za ka gaishe da Mai martaba ba ? "
ya fada dan su na son Miram ya yi magana Hakim ya ji yadda zai iya gane Muryar shi

wasu yawu Miral ya hadiye kafin ya bude baki a hankali ya ce " Barka da Safiya ranka shi dade mai girma Malik "

ko sannu Malik bai ce mishi ba da allamun yau na mulkin su na sama
gyada kan shi Diya ya yi kafin ya ce " Hakim , ka gane Muryar nan ? "
a hankali Hakim ya gyada mishi kai dan har yanzu bai samu karfin jikin shi ba

wani dan karamin murmushi Diya ya saki kafin ya ce " Hakim ina son ka fadawa mutanan wajen nan abun da ya faru tsakanin ka da wannan mutum "

ba musu Hakim ya ba su labarin da ya ba wa Malik a prison , sannan ya daura cewa " wannan shi ne wanda ya saka ni yin aikin , shi ne ya saka ni kashe Malik , sannan ya sace min matata , day BEFORE yesterday , ya tarda ni a cikin cell di ta ya yi kokarin kashe ni , ko da bai yi magana ba zan iya gane face din shi , saboda a ranar bai boye fuskar shi ba ya zo ya kashe ni , a tunanin shi ba zan yi rai ba " ya kai karshen ya na jan wani dogon nunfashi

nan take fadar kowa ya shiga fadin inallillahi wa'ina illaihi raji'un kowa da abun da ya ke fada
abun mamaki Malik kuwa ya tsare Mohammed da idanu , sai wani kauda kai ya ke , har wata zufa ke karayo mishi duk da ac din wajen ya na hadiye yawu

a hankali Malik ya furza iska da ga bakin shi kafin ya kali Diya murya kassa kassa ya ce " je ka taho da ita "

gyada mishi kai Diya ya yi kafin ya fara takawa da sauri sauri ya fice fadar
kowa ya na kallon shi har sai da ya fita sannan Rafik ya ce " Amma Miram ba ka kyautawa kan ka ba , me Malik ya yi maka ? tamkar dan uwa ya dauke ka am....... "

bai kai karshen maganar shi ba ya jiyo Muryar General ya na cewa " mai girma Rafik , please ka danne zuciyar ka , mu ji abun da Malik zai fada , da ga baya kowa ya yi maganar shi "

ba musu Rafik ya ja bakin shi ya yi shiru fadar ta yi tsit kowa ya na sake saken qui cikin zuciyar shi amma duk sai da su ka yi wa Miram tir da hali irin na shi

❤⚘ E X I L E D P R I N C E ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )

STORY & WRITTEN BY : MEERAH ⚘🕊

BOOK ________3 👑✌

P A G E 6 🌹🕊

jim kadan bayan fitar Diya ya dawo cikin fadar , kai tsaye geffen Malik ya koma ya tsaya sannan ya daga murya ya ce " za ki iya shigowa "

ya na gama fadar haka Wata kyakyawar budurwa ta shigo fadar ta na sanye da wata Abaya blue color ta yi Rowling veil din ta , da ga gani ciki ne da ita , dan ga shi nan ya fito at least zai kai 5 to 6 months , kai a sunkuye ta shigo fadar , hannayan ta saman cikin jikin ta , ta na taku a hankali

kai tsaye Geffen Hakim ta karaso ta tsaya cikin girmamawa ta ce " ina mika sakon gaisuwa ta ga shugaba "
gyada mata kai kawai Malik ya yi ba tare da ya ce komai ba

Hakim na jin Muryar ta ya ji zuciyar shi ta yi mugun bugawa , a hankali ya dago da kan shi dan a sunkuye ya ke tun lokacin da ya Kamala maganar shi
ya na ganin ta , Ya dan zaro idanu , ya ma manta da mutanan da ke wajen ya tashi da sauri ya rungume ta ya na sakin wani dan karamin kuka ya ce " Najoua , da gaske ke ce ? ba abun da ya same ki ? ba su cutar da ke ba ko ? "

ya kai karshen ya na raba jikin shi da nata , ya talabo face din ta da hannayan shi biyu
Dum ya ji gaban shi ya fadi lokacin da idanun shi su ka sauka saman shatin hannun mutum a face din ta , da allamun marin ta a ka yi ba guda ba dan wajen ya yi jazir
Chapter 10 · 0% Book details