← Book details Exiled Prince Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 61

Sashe 42

Exiled Prince Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gyada mishi kai kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba
shi ma bai ce mata komai ba ya ja hannun ta , su ka nufi wajen sofas din nan , ya zaunar da ita saman three seaters sannan ya zauna geffen ta , ya kara janyo table din gaban su

hannu ya kai ya dauki wani Dewar flask , sannan ya dauki wani Mug da ke geffen shi , ya bude flask din nan , coffee a ciki sai tiriri a ya ke
cikin Mug din nan ya zuba , sannan ya meda flask din ya ajiye ya mika mata Mug din

a hankali ta girgiza mishi kai ta na fadin " yaya Zayd , ni ba na iya shan wannan abun "

" coffee ne fa ? " ya fada cikin sanyin murya
girgiza mishi kai ta yi allamun ba ta so
" please my Cutie , ki sha mana , ki fara shan coffee idan ya so ki sha fruits da ga baya "

sai da ta dan jinkirta kafin ta kai hannu ta karbi Mug din
a hankali ta kai shi a baki ta dan surba
da sauri ta mika mishi Mug din ta na fadin " umm ba dadi , amshi kayan ka "

dan zaro idanu ya yi ya na kallon ta ya ce " kamar ya ba dadi ? No , wassa haba ki ke min kawai dan ba ki son sha , wlh sai kin shanye shi "

marairaice mishi fuska ta yi ta na fadin " yaya Zayd , ba na so please "
" Cutie , ina wassa da ke ? " ya fada ya na matse gera
a hankali ta girgiza mishi kai allamun a'a
" okay , shanye coffeen nan tun kafin rai na ya bacci "

turo dan bakin nan nata ta yi kafin ta kai mug din a baki ta ci gaba da sha
sai da ta shanye coffeen tas sannan ta sauko mug din ita kanta ba ta sani ba
kawai sai jiyo Muryar shi ta yi ya na fadin " ki ka ce ba shi dadi "

shagwabe mishi fuska ta yi ta na fadin " ni ai wassa na ke maka "

" na ji uwar rigima , yanzu idan sauran ina zuwa " ya fada ya na kokarin tashi da ga haka ya fice dakin ya bar ta nan zaune ta na shan fruits salad din da ya hada mata

sai da ta cinye baki daya abun da ke cikin tray din nan ba tare da ta sani ba , karan farko da ta ci wani abu bayan fruits kuma ba ta amanyo shi ba , da allamun shi ma babyn nata abun da mahaifinshi ya gyara mishi kawai ya ke son ci

bayan ta kammala ta tashi a hankali cikin ta ya cika dam , da kyair ma ta iya karasowa wajen gadon , ta haye ta zauna a tsakiya ta jinjina bayan ta a jikin forehead din gadon , ta lumshe idanun ta , ta na sauke ajiyar zuciya

ta na zaune a haka ya turo kofar dakin ya shigo ya na sallama
ba karamin dadi ya ji ba ganin ta cinye duk abun da ke saman tray
a hankali ya karaso wajen bed din , ya haye ya zauna geffen ta shi ma ya jingina bayan shi a jikin forehead din gadon ya na kallon ta kamar bai san ta ba

" you are so beautiful with your big belly you look like a watermelon " ya fada murya cen kassan makoshi kamar ya na yi mata rada

wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " ni ba na kama da watermelon "

" humm , na ji , ki na bukatar wani abu na kawo miki ? "

a hankali ta ware idanunta , ta kai hannu ta daga t-shirt din ta fara shafa cikinta ta na fadin " no , ba ma bukatar komai , ko ba haka ba baby ? " ta kai karshen ta na wani dan karamin murmushi

bai ce mata komai ba ya dago hannunshi a hankali , bai sauke shi ko ina ba sai saman cikin ta
a tare shi da ita su ka ji wani mugun sanyi a cikin zuciyoyinsu , nan take ya shiga shafar cikin nata ya na sauke ajiyar zuciya a jere

ita da kanta sai da ta sauke ajiyar zuciya , idanunta su ka ciko da ruwa

da sauri ya janye hannunshi ya na fadin " no kar ki min kuka , na daina in zafi ki ke ji "

a hankali ta girgiza mishi kai ta na cewa " no babu zafi , sanyi na ke ji , please ci gaba "

ba musu ya meda hannunsa , saman cikinta ya ci gaba da shafawa a hankali ya na kallon face din ta
a hankali ta lumshe idanun ta , ta sauke wata yar karamar ajiyar zuciya har da sakin murmushi
ta na haka kawai ta ji saukar lips din shi saman nata
a tare su ka sauke wata nanauyar ajiyar zuciya kafin ya cabko lips din ta na kassa ya fara sucked kamar ya samu sweet

a hankali ta zagayo da hannayanta a wuyan shi ta kara shigewa jikinshi
a hankali ya zame bakin shi da ga cikin nata ya na fadin " tsaya da wani katon cikinki , kar ki ji mishi ciwo "

marairaice mishi murya ta yi ta na fadin " ba abun da zai same shi pleaseeeee " ta kai karshen ta na neman ta kamo lips din shi

dan baya kadan ya ja ya na fadin " okay tsaya " ya kai karshen ya na juyawa ya kai hannu wajen box din bedside drawer ya bude ya fiddo wata remote , ya danna wasu button a ciki
ya na dannawa kofar dakin ta koma ta rufe kanta , duk lamps din dakin su ka mutu kamar da wassa Wall din glass din nan ya koma baki kirin ko haske ba ya iya shigowa , nan take duhu ya mamaye bedroom din

a hankali ya ajiye remote din saman bedside drawer sannan ya juyo ya sa hannu ya yi sama da rigar jikinta
sannan ya janyo ta jikin shi , su ka konta , a haka ya janyo duvet ya rufe su har zuwa kai
nan take su ka shiga sabon aiki , gaskiya sun yi missing juna specially shi , yadda ya jure wajen two months ko kiss bai yi mata ba ,
ita kanta ta yi kewar shi over , shi ya sa na fara yi mata kiss ya ji wata muguwar sha'awar shi ta rufe ta

🤣🤣🤣AH TO NI BARI NA TAFI NA BA SU WAJE , SU GAMA DEBE KEWAR JUNAN SU SANNAN MU CI GABA DA LABARIN 🤣🤣🤣✌✌✌

❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤

( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )

STORY & WRITTEN BY : MEERAH ⚘🕊

【THE ROYALTY LOVE ❤🌹】

【 BOOK ________3 📚✍💌 】

_______________________♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡______________________

{ P A G E ♡♡♡ 23 🌹🕊}

▪MISALIN KARFE 8 NA DARE

a hankali ta ke sauko stair ta jan kafa kamar wadda a ka zarewa lakar jiki , ta na sanye da wasu kananan kaya , cikin nan nata ya na a waje dan rigar ko saman cibi ba ta kai ba

sai da ta kawo tsakiyar stair sannan ta saki kukan shagwaba ta na fadin " yaya Zayd ka kyale haka ya isa , tun dazu ka ke ce min na hau na sauka , na gaji wlh "

a hankali Malik da ke zaune saman sofa ya mike , ya karaso bakin stair din ya matse fuska , ya nade hanayan shi a kirji ya na fadin " saura uku , da ga nan sai ki tafi ki konta "

har ta bude baki za ta yi magana ya riga ta cewa " idan ki kammala zan ba ki chocolate "

" da gaske ? " ta fada cike da shagwaba
a hankali ya gyada mata kai allamun Eh
wani dan karamin kukan shagwaba ta saki kafin ta juya ta haye stair din , ta sake saukowa har kassa sannan ta koma kuma

ya na tsaye ya na kallon ta har sai da ta hau ta sauko wajen sau uku sannan ya ce mata " okay , ya isa haka zo ki zauna "

ba musu ta karaso cikin parlourn ta nufi doguwar sofa ta haye ta konta ta na meda nunfashi
a hankali ya karaso ya zauna bakin sofar , ya kai baki saman cikinta ya manna mata kiss sannan ya dago ya na cewa " ba ga shi ba kema za ki ji karfin jikin ki , amma kullum ki na konce waje guda kamar buhu "

cike da shagwaba ta ce mishi " ni ka kyale ni , mun bata "
" tun da mun bata na rike chocolate di na kenan ? " ya kai karshen ya na daga mata gera
" ni gaskia chocolate na ke so " ta fada kamar za ta yi kuka

a hankali ya mike da ga saman sofar ya na kallon ta ya ce mata " Oya , sai ki tashi ki haye , ta na cen bedroom din mu "

kukan shagwaba ta sakin mishi ta na fadin " ni gaskia ba zan i........ " ba ta gama fadar maganar ta ba ta ji cikin ta ya murde , amma ba kamar kullum ba , wannan karan da dan sasauci

da sauri ya koma bakin sofar ya zauna a rude ya ke fadin " Cutie , me ya faru ? "

a hankali ta saki wani dan karamin murmushi ta ce " babu komai yaya Zayd , ya wuce ma "

" okay , tashi mu koma bedroom ki konta " ya fada ya na kokarin tashi
da sauri ta ce mishi " yaya Zayd ina son mu kalli film "
ba musu ya nufi Tv plasma ya kunna ta , sannan ya dauki remote ya dawo wajen sofar ta , ya daga kafafun ta , ya zauna sannan ya daura kafafun saman cinyoyinshi
Chapter 42 · 0% Book details