← Book details Exiled Prince Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 61

Sashe 27

Exiled Prince Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gyada mishi kai mama ta yi kafin ta ce " ko da malam na raye ba abun da zai iya fada maka a kan su dan shi ma bai san da su ba , amma bari na fara ba ka tarihina tukunna , a kauyen Illori a ka haife ni , lokacin da na cika shekara biyar mahaifiya ta ta rasu kuma ni kadai ta haifa , bayan mahaifina ya kara aure kawai matar shi ta shiga gallaza min , ba irin azabar da ba ta yi min ba , amma na jure a haka har na tasso cikin wannan azabar amma duk mahaifina bai sani ba , akwai wata rana na tafi debo ruwa a rafi , janyowar farko da na yi wa ruga ta kawai na ga wani dan karamin box a ciki , box din na zallar zinare ne , har wani kyali ya ke , haka na fara bin wajen da kallo na ga ni kadai ce sai wannan box din a hannu , wata zuciyar na ce min na bude na ga abun da ke ciki , wata kuma na ce min na fara kai ta wajen mai gari kar mai ita ya zo cigiya , haka dai na tsaya tunanin ya zan yi da ita , da ga karshe dai kawai sai na bude ta , ina bude ta lokaci guda garin ya koma duhu kamar cikin dare , kamar kiftawa haka ya sauya ya koma fari kal fiye da farko , ina tsaye a wajen wata guguwa ta tashi ta mamaye ni , har box din hannuna ta kubce min ta shiga cikin guguwar , cike da tsoro na yi kokarin fita guguwar nan amma na kassa , ga shi sai ihu na ke ina neman taimaka amma kamar babu wanda ke ji na , ina a haka kawai na ga wani farin abu ya fito da ga cikin guguwar da suffar mutum , mutum din ma tawa siffar kamar ina kallon kai na cikin madubi , lokaci guda abun nan ya bace sai ga wani irin shi amma wannan shi kuma bakki ne , shi ma ya bace lokaci guda , da ga haka ban san abun da ya faru ba kawai sai bude idanu na yi na gan ni cikin daki na , ina bude idanu matar mahaifina ta rufe ni da fada wai na je na yi zama na , na kyale ta da ayukan gida , abun da ban taba yi ba wannan karan na rufe ta da fada ni ma ina ta kyale ni , ni kai na abun ya ba ni mamaki dan ko so guda ban taba tunanin zan iya bude baki na mayarwa wani da magana bare ita matar mahaifina , kai sannu sannu har ya kai duk wanda ya yi min magana cikin kauyen sai na keta mishi rashin mutunci , kullum ni ce fada da yaran mutane har na ji musu ciwo , kullum sai sun kai kara ta wajen mahaifina shi kuma ya yi min fada wani lokaci ya cilas ta min na je na bawa yaran hakuri , har ya kai ya daina bari na fita kullum ina cikin gida gudun kar na janyo wani fadan , wata rana ina tsaka da barci na kawai na ji hannun mutum a jiki na , ina bude idanuna su ka sauka kan yaron matar mahaifina , dama ta taba yin aure har da yaron ta guda wanda ya ba ni kusan shekara biyar haka , cikin tsoro na mike ina tambayar shi me ya kawo shi daki na , kawai ya shiga ce min wai na bashi hadin kai ya biya bukatar shi da ni dan ya jima da wannan burin a ran shi , ni kuma na ki yarda , hakan ko ba karamin bata mishi ya yi ba kawai sai ya yi kokarin cin zarafina , ni kai na ban san ya hakan ta faru ba kawai sai bude idanu na yi na ga gawar shi konce a gefe na babu kai a jikin shi , lokaci guda na fita cikin hayacina dan abun ba karamin tsorata ni ya yi ba , lokacin da matar mahaifina ta shigo dakina dan ta tashe ni kawai sai ta ga yaron ta konce ba kai , nan take ta shiga kira na da mayya wai na kashe mata yaron ta , ko tsayawa ba ta yi ba ta fice gidan ta kiran mayya mayya ta kashe mata yaron ta , a haka har mutane su ka fara taruwa cikin gidan , duk irin magiyar da na yi musu ina cewa ni ban san abun da ya faru ba amma su ka ki yarda , sa'a ta guda kora ta su ka yi da ga cikin kauyen ba su kashe ni ba , bayan sun kore ni mahaifina ya biyo baya na ba tare da sanin kowa ba ya kai ni wajen wani dan uwan shi da ke zaune a kaduna , bayan ya kai Kaduna ne na hadu da Abban Abdoul , da sannu sannu har mu ka fara soyayya mu ka zo mu ka yi aure , na san ka abun da ya faru lokacin da ka karbi budurcin ta , to ni ma hakan ce ta faru , ba karamar razana Abban Abdoul ya yi , shi a tunanin shi aljana ce ma ni , ni kuma ban ma san maganar me ya ke min ba , sai dai kawai na yi zaune na yi ta yi mishi kuka , da ya ga kukan nawa ya fara yin yawa zan iya cutar da kai na , kawai ya hakura ya danne abun da ke cikin zuciyar shi ya dinga rarrashi na , a haka har na samu cikin Abdoul , lokaci guda na haife shi ko nakuda ban yi ba , haka zalika Nesrine , amma na Inaya , sai da na yi kamar zan mutu dan har suma na dinga yi kafin ta shigo duniya , lokacin da ta fara tasowa irin jarabar ta , kawai ta ke jan Nesrine fada kuma ta ba ta kashi duk da ita ce karama , ta sa sha Nesrine kuka ba dalili , bayan kuma wani lokaci ta daina kamar ba ta taba yi ba , kawai ta shiga yin wasu abubuwa kamar mara hankali , bayan Abban Abdoul ya bude makarantar islamiya ne kawai mu ka samu saukin abun da ke damun ta , na san ka sha yin mamakin yadda ta ke wasu abubuwa wanda ba dai'dai shekarun ta ba ne , ba ita ba ce aljanun da ke jikin ta ne su ke birkita mata kwakwolwa , duk cikin yarana ita kadai ce ta yi gadon aljanuna Abyad da Aswad , idan sun ga dama su sakin min kwakwolwa idan kuma su ka so su rufe ta na manta komai na rayuwata ta baya , ni ko yanzu na yi mamakin yadda a ka yi na ba ka wannan labarin " ta na gama fadar haka ta ja wani dogon nunfashi

shi dai Malik shiru ya yi ya na sauraron ta ya kassa cewa komai
sai da su ka share good ten minutes a haka kafin ya bude baki a hankali ya ce " it means da aljanu a jikin ta ? "

gyada mishi kai mama ta yi ta fadin " Eh da aljanu a jikin ta , lokacin da ka......... to a lokacin su ka tashi , kar ka ji tsoro ba abun da za su yi maka sai ma ba ka kariya da za su yi saboda kai da ita kun zama abu guda yanzu , Abyad ita ce me kula da lafiyar ta duk wani ciwo da zai iya shiga jikin ta sai ta kawar da shi shi ya sa da ta ci poison din nan ba abun da ya same ta , Aswad kuma gaskiya ban sani ba , sai dai nan gaba idan ta fito ka ga nata aikin , amma zan ba ka shawara , duk abun da za ta fada maka ka yarda da ita dan ba za ta iya fadin kariya ba , idan kuma ta ce maka ka yi abu kawai ka yi ita ta san dalilin ta na yin hakan "

dan lumshe idanun shi a hankali Malik ya yi ya ma rasa abun da zai ce , shi dama ya san akwai abun da ke damun babyn shi amma bai yi tunanin haka abun ya ke ba

ya na haka kawai ya ji hannun mama saman cinyar shi
slowly ya bude idanun shi ya na kallon ta hannun ta kafin ya dago kai ya kale ta
wani cool murmushi ta sakin mishi kafin ta ce " Zayd , ka san za ka iya fadamin abun da ke damun ka ko ? "

gyada mata kai ya yi a hankali kafin ya juya ya sunkuyar da kai ya na kallon hannayan shi
" shikenan fada min to , ko dai abun da na fada maka ne ya tada maka hankali ? don Allah ka kontar da hankalin ka , har yanzu Inayar ka ce b....... "

cikin nitsuwa ya katse ta da cewa " a'a mama , ni ba wannan abun ke tada min hankali ba , har ga Allah ina son na dauke ta mu bar wajen nan , mu tafi inda babu wanda zai yi kokarin rabani da ita , zama na a nan wlh babban hatsari ne ga rayuwar baki daya , yanzu ni kawai jira na ke momyna ta tashi na dauke ta mu bar wajen nan , amma doctor ya ce min shi bai san abun da ke damun ta ba , na rasa ya zan yi " ya kai karshen ya daura hannun saman forehead din shi

shiru mama ta yi ba tare da ta ce komai ba , da ga gani ka san ya na cikin matsananciyar damuwa , amma ya shanye kayan shi kar ya takurawa mutanan da ke zagaye da shi

wani dogon nunfashi mama ta ja kafin ta ce " na tambaye ka ? Inaya ta yi maka wata magana a kan ita momyn taka ? "
Chapter 27 · 0% Book details