← Book details Exiled Prince Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 61

Sashe 40

Exiled Prince Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kallon ta kawai Malik ya ke , yanayin da ta yi shagwabar ta ya yi mugun tuno mishi Cutie din shi
a hankali mutumin nan ya dago kai ya ga irin kallon da Malik ke yi wa matar shi
bai ce mishi komai ba ya kwace hannayan shi da ya juya a hankali ya ce mata " Mrs Aylan , tafi ina zuwa , bari na gama magana da shi "

cike da shagwaba ta ce mishi " da gaske za ka ciwo min plush ? "
daga mata gera guda ya yi ya na fadin " bayan wadda ke cikin cikinki ? in bai ishe ki ba zan ba ki wani " ya kai karshen ya na kashe mata ido guda

turo dan bakin ta ta yi ta na fadin " ni dai plush na ke so , kuma dole ka amso min yawwa "

wata yar karamar dariya ya yi ya na fadin " yanzu dai bari na yi mishi magana , in ya so ko me plush din ne ma za ki samu "

wani cool murmushi ta saki kafin ta juya ta koma inda ta fito
ta na barin wajen ya juyo ya zo gaban Malik ya tsaya ya ce " lafiya ka tsare ta da ido ? , she is my wife "

cikin sanyin murya Malik ya ce mishi " i'm sorry " ya kai karshen ya na shirin rabawa ta geffen shi zai wuce

da sauri ya riko hannun shi ya na fadin " ta yi maka kama da wata ce ? "
a hankali Malik ya bude baki ya ce " Cutie "
wani dan karamin murmushi mutumin nan ya saki kafin ya ce " hmm , ka ga, ga banci cen , mu je ka fada min wacece wanan Cutie , zan so na ji labarin soyayyar ku in ya fi namu dadi , let's go ? " ya kai karshen ya na daga mishi gera allamun ya sunan shi

" Nawfel " Malik ya fada a takaice

gyada kan shi mutumin nan ya yi kafin ya ce mishi " General Aylan " ya kai karshen ya na mika mishi hannu
ba musu Malik ya riko hannunshi , su ka yi musbaha , sannan Aylan ya ja shi su ka nufi wani hanci su ka zauna ya na cewa " tell me now , wacece Cutie ? "

" My wife " Malik ya fada ya na kallon hannayanshi

" waw , we are maried , yaran ku nawa ? , ni ina da Twins , na uku na kan hanya " ya kai karshen ya na wata yar karamar dariya

ba tare da ya dago kan shi ba Malik ya ce " ko guda , ina ga kuma ba za mu taba samu ba " ya kai karshen a sanyaye kamar ya na shirin kuka

" oh , i'm sorry , what happened ? we are sick ? a kassar US fa ku ke , in matsalar haihuwa gare ku za ku iya samun solution , cikin sauki ma kuwa " .

girgiza mishi kai Malik ya yi a hankali ya na fadin " ba matsalar haihuwa gare mu , we are okay "

cikin rudu Aylan ya ce mishi " and ? why ka ce ba za ku taba samu ba ? ko ba ka son samun baby ? ni ma da farko haka na ke , ko mace ba na so kusa da ni , amma lokaci guda ta shigo rayuwa ta , kuma ba na fatan ta fita "

cikin nitsuwa Malik ya katse shi da cewa " ni ma ba na son ta tafi , i don't know what to do , ba ta jin magana ta , na ce mata ta zubar da cikin amma ta ki , sai illa ya ke yi mata ya kokarin raba ni da ita amma ta kassa gani , i can't live without her " ya kai karshen a sanyaye

" okay , calm down now , ina ga wani abun na damun ka , tell me , may be i can help you "

girgiza mishi kai Malik ya yi ya na cewa " ko na fada maka ba abun da za ka iya yi min "

" just tell me , za ka gani "

ba musu Malik ya ce mishi " she is Pregnant , but her pregnancy is risked za ta iya rasa rayuwarta wajen haihuwa , ko yanzu ba karamar illa ya ke yi mata ba , bayan fruits ba ta iya saka komai a cikin ta , imagine two months da fruits kawai ta rayu , Idan ya fara yi mata ciwo har sai ta fita hayacinta ba ta sani ba , duk doctor din da na yi wa maganar , ce min ya ke wai mu zubar da cikin , ko kuma a cire mata yaron idan ya kai wata bakwai ko takwas , shi ma it's not sure baby ya rayu , na ce mata mu zubar da cikin amma ta ki yarda , she just want to leave me , i can't live without her , i can't " ya kai karshen idanun shi na cikowa da ruwa

da sauri ya lumshe su ya na kauda kai gefe

ya na a haka ya ji Aylan ya dafe shoulder din shi cikin sigar rarrashi ya ce mishi " bari na fada maka , lokacin da ta haife min Twins di na a ranar mutuwa kawai a ba ta yi ba , ba zan taba manta wannan ranar saboda a ranar na ji tsoron da ban taba ji ba a rayuwa ta , ga shi yanzu har sun girma sai shegantaka kala kala , ita kanta ta manta da wannan ranar kamar komai bai faru ba , yanzu a ka je wajen haihuwa ba ta mutu kuma fa ? ya za ka yi ? me za ka ce mata ? "

shiru Malik ya yi ya na tunanin abun da ya ke fada mishi

dan jinkirtawa Aylan ya yi kafin ya ce " kamata ya yi a ce ka na tare da ita a wannan lokacin , ko da shi ne last time din ta a duniya , ku yi shi a tare , yanzu ka sa kan ka cikin damuwa , ka saka ta cikin damuwa , hakan ko ba karamin hatsari ba ne ga mace mai karamin ciki , ka na neman ka kashe ta da kanka , shawara guda zan ba ka , ka je ka rungumi matar ka da babynku , why za ka juya mata baya a lokacin da ta fi bukatar ka a kusa da ita ? kai a ganin ka ka yi mata adalci ? kar ka bari son zuciya ya raba ka da ita tun kafin mutuwa ta raba ku "

slowly Malik ya dago kai ya kalle shi , cikin sanyin murya ya ce " i'm afraid , ba zan so na rasa ta ba , ita kadai ta yi min saura a duniya "

" in sha Allah ba abun da zai faru da ita , kamar dai ba ka san ikon Allah ba , ka kai kukanka gare shi , in sha Allah zai warware maka matsalar ka , bare kuma wannan dan karamin abu , mata nawa ne ke rasa rayukan su wajen haihuwa without her pregnancy was dared ? kawai lokacin su ne ya yi , idan lokacin ka bai yi ba ko cikin bakin lion ka ke ba za ka mutu ba , may be ita ma nata lokacin ba wajen haihuwa zai zo ba , kawai ka sakawa kan ka tsoro ne "

a hankali Malik ya sunkuyar da kai ya na kallon hannayanshi

murmushi mai dan sauti Aylan ya yi ya na fadin " na cika surutu ko ? "

" hmmmm , ai kai na ba ka ce komai ba , idan Cutie na magana sai ka ce an kunna radio sam ba ta gajiya da surutu "

wata yar karamar dariya ya yi ya na fadin " haka matan nan su ke da mugun surutu , ga shi yanzu ta koya min har ya kai ba na iya rufe baki na " ya kai karshen ya na wani dan karamin tsaki ya kauda kai gefe

shi dai Malik bai ce mishi komai ba ya tafi duniyar tunanin shi , har sai da Aylan ya tashi ya bar wajen bai sani ba

sai da ya share wajen ten minutes a haka kafin ya dago kan shi , ya na shirin magana ya ga wajen babu kowa
ya kalli dama ya kalli hagu , amma bai gan shi ba
kawai ya tambayi kanshi ko dai da aljani ne ya yi magana bai sani ba

a hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya jingina bayan shi a jikin bancin ya daga kai sama ya lumshe idanu , har ga Allah ya na matukar kewar Cutie din shi , specially wannan yar shagwabar ta , da wannan dan bakin surutun nata , ya na kewar komai nata , wajen two months ya kwaurace mata baki daya , sai yanzu ya ke nadamar biyewa son zuciyar shi , da yanzu tare da ita zai zowa park din nan , shi ma katari ne a ka yi ya zo wucewa kawai ya ga wajen ya burge shi shi ne ya shigo , ya San ita ma zai mugun burge ta , gaskiya zuciya ba ta yi mishi adalci ba , gashi yanzu ta na neman ta raba shi da abun kaunar shi guda , shi kan shi bai san ya a ka yi ya jure tsawan watanni ba ta kusan shi , bare kuma ita da ta fi bukatar shi fiye da komai , bisa hallacin da ta yi mishi , ta so shi a lokacin da ba shi da komai , kowa na yi mishi kallon makaho da kurma amma a haka ta so ta zauna tare da shi gaskiya bai kyauta mata ba

❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤

( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )

STORY & WRITTEN BY : MEERAH ⚘🕊

【THE ROYALTY LOVE ❤🌹】
Chapter 40 · 0% Book details