← Book details Exiled Prince Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 61

Sashe 38

Exiled Prince Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wata yar karamar dariya Diya ya yi ya na kallonta , ta na kuka ta shan fruits ba karamin burge shi ta yi ba

ya yi nisa duniyar tunanin shi kawai ya ga ta tashi da gudu har sai da tray din fruits din ta ya fadi , ta toshe bakin ta da hannu guda
a hankali ya mike ya bi bayan ta

❤⚘E X I L E D P R I N C E⚘❤

( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )

STORY & WRITTEN BY : MEERAH ⚘🕊

【THE ROYALTY LOVE ❤🌹】

【 BOOK ________3 📚✍💌 】

______________________🕊🌸🕊🌸🕊🌸🕊🌸🕊🌸🕊🌸🕊🌸___________________

{ P A G E ………20 🌹🕊}

▪AFTER SOME DAYS

sannu sannu lokaci na tafiya yanzu wajen sati biyu da tafiyar su Malik US , a cikin satin a ka nada Aymane Malik din Saudiya , RIANNA kuma MALIKAT , a cikin satin kuma Diya ya dauki Nesrine su ka koma Qatar da zama dan a ganin shi ba zai iya zama cikin Saudiya da Aymane a matsayin Malik , dama Saboda Malik ne ya ke zaune a Daular Saudiya tun da ba ya nan ya kama hanyar gaba ne
Aymane kuwa farin ciki kamar ya kashe kan shi , burin shi na zama Malik ya cika , yanzu kuma su shirya sabon mulkin shi dan ina ji a jikina ba zai mulki bisa gaskiya ba
idan mu ka leko mutanan US kuma , kullum ciwon cikin Inaya kara tsananta ya ke amma sai ta danne dan kar Malik ya lura , har ya kai yanzu ta na faman da matsanincin ciwon kai har wani dishi² ta ke gani idan ya fara yi mata ciwo , ga kuma tashin zuciya , har ya kai qamshin turaren Malik kadai ya isa ta yi amai , duk abun da ta ci sai ta amanyo shi , bayan fruits ba ta iya shan komai , har wata yar rama ta yi , duk abun da ta ke Malik ya na sane kawai ya na kokarin dannewa ne dan ya faranta mata , amma har cikin zuciyar shi ba ya jin dadin ganin ta cikin wannan halin , shi ya sa kawai ya yanke shawarar zubar da cikin tun kafin ya rasa ta

▪US ( WASHINGTON D.C )

▪INAYA

zaune ta ke tsakiyar gadon su sai dafe ciki ta ke ta na lumshe idanunta , da allamun ciwo ya ke mata
ta na a haka ta jiyo Muryar shi ya na sallama kassa kassa
da sauri ta janye hannunta , ta bude idanunta sannan ta amsa mishi sallamar shi a ra'rabe

a hankali ya karaso bakin gadon ya mika mata wasu drug guda biyu , da glass din ruwa kai tsaye ya ce mata " karbi ki sha "

kallon drug din ta yi kafin ta dago kai ta ce mishi " yaya Zayd maganin minene ? "

" maganin abun da ke damun ki ne , karbi ni sha "

da sauri ta girgiza mishi kai ta na cewa " ni ba abun da ke damuna yaya Zayd "

" No Cutie , wannan abun da ke cikin cikinki shi ya ke damunki , ki karba ki sha ya tafi kawai , Allah zai ba mu wani babyn amma ban shirya rayuwa babu ke ba , duk abun da ki ke cikin gidan nan ina sane da shi kawai na sa miki ido ne na gani "

marairaice mishi fuska ta yi kamar za ta yi kuka ta ce " yaya Zayd da gaske ba abun da ke damuna please ka bar maganar nan wlh ba zan iya zubar da cikin nan ba "

cikin bacin rai ya ce mata " ba tambayar ki na ke ba umarni na ke ba ki , ki karba ki sha , a sani na , ni ne uban yaron na kuma ce ba na so dan haka ki karba ki sha ko so ki ke ki bata min rai ? "

da sauri ta girgiza mishi kai ta na hawaye ta na fadin " yaya Zayd ka bari don Allah "

" No , na bari sai ya kashe min ke sannan ? ban shirya yin rayuwa babu ke ba , saboda ke na hakura na bar kassar Saudiya , na bar kujerar Malik kawai dan mu yi rayuwar mu cikin konciyar hankali , amma ki na neman ki ruguza komai , ki karbi maganin nan ki sha please "

kuka ta sakin mishi ta na fadin " yaya Zayd "

da sauri ya katse ta da cewa " please Inaya ki sha maganin nan ? "

dan zaro idanu ta yi ta na kallon shi jin ya kira sunanta kai tsaye , a iya sannin ta duk zaman da su ka yi ko so guda bai taba bude baki ya kira sunanta kai tsaye ba , ba shi ba har Diya bai taba kiran sunan ta kai tsaye , yanzu kuma ga shi ya kira sunanta hakan na nufin yau ranshi ya baci

a hankali ta bude baki ta na shirin magana kawai ta ga ya saki drug din hannun shi da glass din ya fadi kassa ya watse , ya juya ya fice dakin

da sauri ta sauko da ga saman gadon ta ma manta da glass din da ke bakin gadon kawai ta taka su kafar ta ta fashe amma ba ta ji komai ba
da gudu ta bi bayan shi ta na kiran sunan shi , ya na jin ta amma ya kyale ta

sai da su ka karaso cikin parlourn ya nufi hanyar fita sannan ta riko hannun shi
da karfi ya juyo ya kwace hannunshi ya na fadin " kar ki sake ki min magana ! " ya fada da karfi ya na nuna ta da yatsa
ba karamar razana ta yi ba , ko so guda bai taba daga mata murya ba , yau ga shi ya na mata tsawa

nan take ta sakin mishi sabon kuka ta na fadin " yaya Zayd tsawa ka min ? "

cikin bacin rai ya ce " me ki ke so na yi Cutie ? kin fi kowa sanin irin son da na ke miki , yanzu in ki ka tafi ki ka bar ni ya zan yi da rayuwa ta , kashe kaina kawai zan yi "

da sauri ta ce mishi " in ka kashe kanka wa zai kula da babyn mu , ka sani zai bukace ka a kusa da shi "

da sauri ya katse ta da cewa " wai ki na tunanin zan iya kallon shi ma idan ya yi sanadiyar rabuwa ta da ke ? , bari na fada miki wannan cikin shi ne ma fi munin abu da ya samu rayuwata Cutie "

" yaya Zayd ka na jin abun da ka ke fada ? " fada cikin raunin murya

" Eh , ina ga ke ce ba ki ji abun da na ce ba , wannan abun da ke cikinki kashe ki zai yi , ni kuma ba abun da zan iya yi a kai , kin gwammace rabuwa da ni har abada a kan rabuwa da wannan abun , bayan kin san za mu iya samun wani bayan shi "

ya na gama fadar haka kawai ya ga ta dan lumshe idanun ta kamar mai jin barci ta yi baya kadan kamar za ta fadi allamun jiri ta ke ji

ya na ganin ta amma bai ce mata komai ba ya juya ya fice gidan baki daya
ta na ganin shi har sai da ya fita sannan ta juya a hankali ta nufi stair ta haye
kai tsaye bedroom din su ta koma ta haye saman gado , ta dunkule waje guda ta saki kuka mai cin rai
ko one minute ba ta yi ba da fara kukanta kawai ta fara rage sautin kukanta kawai jikin ta ya dauki sanyi da allamun ta sume dan ko motsi ba ta yi

bangaran Malik kuwa tuki ya ke cikin fitar hayaci ba ya maganin gaban shi duk idanun shi sun rufe
sai da ya share wajen good ten minutes ya na irin wannan tukin kafin ya ja wani mugun burki geffen titi

a hankali ya kai hannu ya fido wayar shi da ke faman ringing , dalilin ta ne ma ya ja burki
kallon screen din ya yi kafin ya dauki kiran ya kai kunne ba tare da ya ce komai ba

a daya bangaran kuma wata yar karamar dariya Diya ya yi kafin ya ce " haba abokina ka yi sallama dai ko ? "

wani dan karamin tsaki Malik ya yi kafin ya ce " lafiya ka kira ni ? "
" Haba , yanzu tsakani da Allah wajen kwana nawa rabonka da ni , ni na kira ka shi ne za ka ce lafiya na kira ka ? Ah dan na ji in ka mutu ne , dan rainin sens "

tsaki kawai Malik ya yi ya kontar da kan shi saman steering motar

wata yar karamar dariya Diya ya yi kafin ya ce " shikenan , yanzu fada min ya ka ke , ya kuma baby ? "

" Fine " ya fada a takaice ya na lumshe idanun shi

shiru Diya ya yi yanayin da Malik ya yi mishi magana sam bai konta mishi ba , ya San yanayin maganar abokinshi idan ya magana cikin damuwa cikin bacin rai ko cikin farin ciki

cikin sanyin murya Diya ya ce mishi " Malik , tell what's wrong with you ? "

a hankali Ya dago kan shi ya na tsaki ya ce " nothing " a takaice

da sauri Diya ya ce " wani abu ya samu baby ? " ya fada a razane

" ba abun da ya same ta yanzu , amma nan gaba zai same ta " ya fada kamar ya na cikin bacin rai

" calm down , yanzu ka fada min abun da ke faruwa cikin konciyar hankali " Diya ya fada

ba musu ya shiga bashi labarin abun da ya faru bayan zuwan su US amma bai fada mishi abun da ya faru yanzu tsakanin shi da ita ba
Chapter 38 · 0% Book details