← Book details Exiled Prince Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 61

Sashe 19

Exiled Prince Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" amma....... " ba ta kai karshen maganar ta ba ya daka mata tsawa ya na fadin " za ki fita da ga nan ko sai na tataka ki a nan ? " ya kai karshen ya na zaro mata idanu da kyau

ba karamar razana ta yi ba , ai ba shiri ta juya ta na rike da box din ta ta bar wajen
sai da ta bar wajen sannan wanda ya yi mata magana da farko ya saki wata yar karamar dariya ya ce " ko ni sai da ka ban tsoro wlh "

" na ga kamar ta na son ta raina min hankali , da tun farko tsawar ka yi mata da ba ta bata mana lokaci ba haka " ya fada ya na kauda kai
murmushi mai dan sauti Sojan ya yi kafin ya kauda kanshi shi ma

bangaran Nurse din nan kuma , kai tsaye Hospital din ta fito , amma ta kofar baya ta fito , babu kowa a wajen ko haske sosai ma ba bu
ta na fitowa ta tila box din hannun ta gefe cen cikin ciyayi
ta ja tsaki ta na fadin " why za su hana ni shiga ? gaskiya sai na zage damtse dan ganin na kashe Malik , dole na san abun yi game da wannan lamarin tun kafin ya tashi da ga saman gadon nan , ko kuma wacen sakarar yarinyar ta riga ni aiwatarwa , You just won a battle but the war has just begun "
ta na gama fadar haka ta ja wani siririn tsaki ta bace bat a wajen

▪WASHE GARI ⛅⛅⛅

a hankali Inaya ta ke tafiya cikin likita , ta na rike da wani basket a hannun ta , ta na sakin wani cool murmushi
ta na karasowa bakin dakin da Malik ke ciki duk sojojin da ke tsaye bakin kofar sai da su ka sara mata
da fara'a a fuskar ta ta ce musu " zan iya shiga ? "
a hankali guda cikin su ya kai hannu ya bude mata kofar ba tare da ya ce komai
wani dan karamin murmushi ta sakin mishi ta na yi mishi godiya kafin ta daga kafa a hankali ta shiga dakin ta na sallama

yanzu ma sai da sojojin wajen su ka sara mata cikin girmamawa sannan daya bayan daya su ka fice dakin
su na fita ta karaso a hankali bakin gadon shi ta janyo chair ta zauna bakin gadon ta na bin shi da kallo ta na murmushi , yanayin Skin din shi ya koma kamar yadda ya ke , ta rage wannan farin
a hankali ta dago hannun ta ta daura saman face din shi , nan ta ji jikinshi ya rage sanyin da gareshi jiya

wani kyawatencen murmushi ta saki ta na janye hannun ta ta ce " Baby , da ga gani ka na samun sauki , na fada maka wani abu ? Gaskiya ba na jin dadin kwana idan ba ka nan " ta kai karshen ta na turo dan bakin nan nata

a hankali ta juya ta kai hannu ta bude basket din da ke geffen ta , ta ciro wani dan karamin bowl da spoon , sannan ta cire Plate din da ke rufe da bowl din ta meda cikin basket din kafin ta juyo ta na kallon shi ta fara shan Fruit salad din da ke cikin bowl din , ta na ci ta na yi mishi hira , har wani dan jinkirtawa ta ke kamar ya na amsa mata

sannu sannu sai da ta share yinin ranar a cikin dakin shi ta na zuba mishi surutu , sai wajen kiran sallar Azahar sannan ta tashi ta ce mishi za ta dawo da yamma sannan ta baro dakin

▪ROUKSAR

zaune ta ke kassan bishiyar nan , Aymane na zaune geffen ta wannan karan bai rufe fuskar shi ba
ta yi irin zaman bokaye , ta na sanye da wasu kaya bakake da veil baki ta rufe fuskar ta shi
ga wasu kwallaye gaban ta sai hayaki ke fitowa da ga cikin su
a hankali wani wata guguwa ta fara tashi ta mamaye ta , har veil din ta ya fadi gashin ta ya fara tashi sama

sai motsa lips din ta ke yi da sauri sauri idanun ta sun koma farare kal
a hankali ta daga hannu sama , ta na haka kawai wata ball fara kal kamar lamps ta fado cikin hannun ta
lokaci guda ta juya da hannun ta daura shi saman bishiyar bayan ta , nan take Ball din nan ta shige cikin bishiyar

da sauri Rouksar janye hannun ta , ta yi baya ta na sauke nunfashi da karfi har da dafe saitin zuciyar ta da hannu guda

wata yar iskar dariya Aymane ya bushe da ita ya na fadin " Good job , kin yi aiki mai kyau "

wata nanauyar ajiyar zuciya Rouksar ta sauke kafin ta ce " Aymane , wlh idan wani abu ya same ni ba zan yahe maka ba , maci amana kawai "

" za ki iya fadin duk abun da ki ke so , ni dai ba zan ja da baya ba a kan kudiri na , na gode da taimakon ni , idan kuma ki ka ce za ki yi wani abu against me , kar ki manta da hannu kadai zan iya kawo karshen ki " ya kai karshen ya na dafe bishiyar bayan shi da hannu ya na sakin mata wani makirin murmushi kafin ya bace ya bar ta a wajen

wata yar karamar kara Rouksar ta saki kamar za ta yi kuka kafin ta bace ita ma , dama an ce macuci shi ya san makontar macuci , yanzu Aymane ya saka rayuwar Rouksar a hatsari , dan ko da kuwa branch guda ce ta bishiyar nan ta fado , to sai Rouksar ta ji a jikin ta bare a ce za a cire bishiyar baki daya , Allah ne kadai ya san abun da zai faru , amma ni dai na san ba al'heri ne su ka aikata ba

▪BAYAN SALLAR ISHA

a hankali Inaya ta ke fitowa da ga cikin corridor ta na sanye da wata Abaya Pink color me mugun kyau , ta yafa veil din a kai ba ta yi Rowling din shi ba ,

❤⚘ E X I L E D ⚘❤ P R I N C E ⚘❤

(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )

STORY & WRITTEN BY : MEERAH ⚘🕊

BOOK ________3 👑✌

P A G E 11 🌹🕊

ta na tafiyar ta cikin konciyar hankali da murmushi a fuskar ta
bakin ta da sallama ta shigo parlourn nan ta tardo RIANNA rungume da Tesnim da ke kuka kassa kassa

a rude Inaya ta karaso wajen ta na fadin " Aunty Tesnim me ya faru ki ke kuka ? "

cikin nitsuwa RIANNA ta ce mata " kar ki damu baby , momy ce a ka kai likita jinin ta ya hau saboda halin da Malik ke ciki , amma kar ki damu za ki iya tafiya wajen Malik "

a hankali Inaya ta karaso ta dafa shoulder din Tesnim ta na cewa " ki yi hakuri kin ji Aunty Tesnim ? ba abun da zai samu momy in sha Allah "

wani murmushin karfin hali ta na gyada mata kai ba tare da ta ce komai ba
kamar da ga sama su ka jiyo Muryar Abdoul ya shigo wajen ya na sallama
Tesnim na ganin shi ta tashi da gudu ta nufe shi ta fada jikin shi ta na sauke ajiyar zuciya
a tare Inaya da RIANNA su ka saki wani dan karamin murmushi , kafin Inaya ta tako a hankali ta raba ta geffen Abdoul ba tare da ta ce komai ba ta fice abun ta dan ita ma yanzu ta na da burin kasancewa da nata masoyin

a haka ita ma RIANNA ta mike ta bi bayan Inaya amma ita wajen MALIKAT AL'UMU za ta je

su na fita Abdoul ya dago Tesnim da ga jikin shi ya ce " To rigimamiya , sake ni kare ki karaya min baya "

noke mishi kafada ta yi ta na turo dan bakin nan nata ba tare da ta ce komai ba
a hankali ya rage sautin Muryar shi ya ce mata " mu tafi garden to ? "
da sauri ta gyada mishi kai kafin ta sake shi a hankali ta na sunkuyar da kai

hannu ya kai ya riko hannun ta kafin ya juya su ka bar part din a tare
😂😂😂✌KU BARI NA BI BAYAN SU TUKUNNA , MUN NEMI INAYA DA GA BAYA 🤣🤣🤣

a tare su ka baro part din MALIKAT INAS su ka nufi garden
su na shigowa ya ce mata " me ya faru ki ka ce ki na son ganina ? " ya fada ba tare da ya kale ta ba su na ci gaba da tafiyar su

cikin sanyin murya ta ce mishi " kawai ina son kasancewa tare da kai "
wani dan karamin murmushi ya saki kafin ya ce " hmmm fada min gaskiya dai , da ga gani akwai abun da ke damun ki , za ki iya fadamin kin sani ko ? "

dan jinkirtawa ta yi kafin ta ce mishi " ban san abun mu ka yi musu , sun raba ni da Abbi , ga Malik cen konce rai a hannu Allah , yanzu kuma sun komo kan momy , yanzu da jimawa a ka tafi da ita likita ni na san doctor karya kawai ya ke mana , ba wani jini ta da ya hau , yanzu ga ta cen konce ko motsi ba ta yi " ta kai karshen kuka na kubce mata

shiru Abdoul ya yi ya na kallon ta ta na kukan ta , gwara ya bar ta ta gama kukan ta ta fitar da abun da ke cikin zuciyar ta da ga baya ya shiga rarrashin ta
Chapter 19 · 0% Book details