← Book details Exiled Prince Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 61

Sashe 32

Exiled Prince Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya na zama Inaya ta shigo fadar ta na sallama
a tare duk su ka juyo su na kallon ta , har shi kan shi Malik
a hankali ta fara takawa cikin fadar duk inda ta wuce sai sun dan sunkuyar da kai su na gaishe ta cikin girmamawa dan a yanzu a matsayin MALIKAT din su ta ke

ita kuwa ba ta bi ta kan su ba , ta nufi Malik da ya tsare ta da ido babu ko kiftawa
sai da ta karaso tsakiyar fadar sannan ta tsaya cak ta na kallon Malik

wani dan karamin murmushin geffen fuska ta yi kafin ta ce " ina mika gaisuwa ta ga shugaban wannan kassar mai Albarka " ta fada ta na dan rinsinar da kai

har cikin zuciyar shi maganar ba karamar dariya ta so ta bashi ba , amma sai ya danne
ba shi kadai ba duk mutanan wajen sai da su ka saki wani dan karamin murmushi su na kallon ta

shi kuwa Diya sai da ya yi murmushi mai dan sauti kafin ya ce " mai martaba na amsa gaisuwar uwar gidan shi , sarauniyar kassar Saudiya har shi kan shi mai Saudiyar "

ba shiri Malik ya juya ya kalli Diya da ke ta faman qumshe dariya dama da gangan ya fadi hakan
sarai Diya ya lura da irin kallon da Malik ke yi mishi amma bai kula shi ba sai ma ci gaba da maganar shi ya yi ya na fadin " me ke tafe da shugabar mu a yau ? "

dan jinkirtawa Inaya ta yi kafin ta ce " ranka shi dade , akwai wata bishiya bayan masarautar nan , ita kadai ce a wajen , ina son a cire ta "

cike da rudu kowa ya ke maimaita abun da ta fada
har sai kanshi Diya sai da ya ce " bab.... ranki shi dade , bishiya kuma ? wace irin bishiya ? "

wani dan karamin murmushi ta saki ta na fadin " Bishiya dai , na san da wuya ku san da ita saboda cen bayan masarautar ta ke da ga yamma , babu komai a wajen sai wannan bishiyar , ina son a cire "

har Diya ya bude zai yi magana Malik ya daga mishi hannu ya na fadin " ku yi abun da ta ce "

cikin rudu Diya ya ce " amma ranka shi dade , me ye laifin bishiyar , a .... "

cikin nitsuwa Malik ya katse shi da cewa " ku yi abun da ta ce , yanzun nan "

gyada mishi kai Diya ya yi a hankali kafin ya bawa wasu dogarai umarni a kan su je su cire bishiyar da ke bayan masarautar da ga yamma , ba musu wasu dogarai har guda shidda su ka fice fadar dan cika umarnin Malik

su na fita Inaya ta saki wani kyawatencen murmushi ta sunkuyar da kai ta na fadin " na gode ranka shi dade "
gyada mata kai kawai Malik ya yi da allamun na miskilancin da izzar a sama su ke a yanzu

" zan iya tafiya ? " ta fada cikin sanyin murya
yanzu ma gyada mata kai ya yi ba tare da ya ce komai ba ya na kallon ta
wani cool murmushi ta sakin mishi kafin ta juya ta fice fadar

ta na fita Diya ya sunkuyo wajen Malik ya na fadin " Malik , ni fa ban ga dalilin cire bishiyar nan ba , yo ni ko zaman ta ban san da shi sai yanzu da ta yi maganar "

kassa kassa Malik ya ce mishi " ni kai na ban san da zaman bishiyar , amma tun da ta ce a cire ta , ita ta san dalilin ta na yi hakan "

" okay " Diya ya fada a takaice kafin ya koma ya gyara tsayuwarshi , da ga haka su ka ci gaba da aikin su

▪INAYA

a hankali ta turo kofar dakin da MALIKAT AL'UMU ke ciki ta na sallama
a tare Rouksar da Tesnim su ka juya su na amsa mata sallamar ta , Tesnim na ganin ta ta saki wani kyawatencen murmushi ta na fadin " baby ! "

da murmushi a face din ta Inaya ta karaso wajen Tesnim ta rungume ta , ta na fadin " barka da safiya Aunty Tesnim "

murmushi mai dan sauti Tesnim ta yi ta na fadin " barka baby , hope ki na lafiya ? "
" Fine " Inaya ta fada ta na raba jikinta sa na Tesnim

a hankali Rouksar da ke zaune baya ta mike ta na fadin " Tes , ni zan tafi "

da sauri Inaya ta ce mata " ina kuma za ki je ? ko dan na zo ne za ki tafiya ? "

wata yar karamar dariya Tesnim ta yi ta na fadin " no baby ba haka ba ne , gida za ta koma dama ta zo ta yi min bankwana ne "

dan tabe baki Inaya ta yi kafin ta tako gaban Rouksar ta ce "hmm kin gama aikin ki shi ne za ki tafi ko ? "

wani dan karamin tsaki Rouksar ta yi kafin ta juya ta kalli Tesnim ta ce " Tes , sai mun yi waya " ta fada ta na kokarin takawa

da sauri Inaya ta riko hannunta , ta medo ta baya da karfi ta na fadin " babu inda za ki je "

❤⚘E X I L E D P R I N C E⚘❤

( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )

STORY & WRITTEN BY : MEERAH ⚘🕊

【BOOK ________3 👑✌】

______________________⚘⚘⚘⚘⚘⚘⚘___________________

{ P A G E ………17 🌹🕊}

a tare Tesnim da Rouksar su ka zaro idanu su na kallon Inaya
a hankali Tesnim ta karaso geffen Inaya ta na fadin " baby , lafiya ki ka tsayar da ita ? me ya faru ? "

da sauri Rouksar ta ce " Tes , ni fa ban san abun da na yi wa yarinyar nan ba , tun lokacin da na shigo masarautar nan duk ta dauki tsanar duniyar nan ta daura min kawai dan na ce ta rabu da Malik , ni da farko ban san abun da ke tsakanin su ba shi ya sa na yi mata wannan kashedin saboda ina son shi , amma kin gani yanzu na bar zancen , asali ma Daular Ottoman zan koma "

a hankali Tesnim ta kai hannu saman shoulder din Inaya ta na wani dan karamin murmushi ta ce " baby , na san kishi ki ke yi , kar ki damu kanki , Malik ba shi da wata mata a duniya bayan ke , please ki sake mata ku yi bankwana , may be shi ne last time za ku ga juna "

wani cool murmushi Inaya ta saki kafin ta ce " ba za ta bar wajen nan ba sai ta cire abun da ta yi wa momy , idan kuma ta dauka da wassa na ke bismillah ga hanya nan " ta kai karshen ta na nuna mata hanyar fita

cikin bacin rai Rouksar ta ce mata " ba ki da hankali wlh " ta kai karshen ta na fara takawa

da sauri Tesnim ta bi bayan ta ta na fadin " Rouksar , please ki ts....... "
ba ta kai karshen maganar ta ba ta ga Rouksar ta tsaya cak ta na sakin wata yar karamar kara ta dafe saitin zuciyar ta

" Rouksar , lafiya ? " Tesnim ta fada ta na nufar Rouksar
da sauri Inaya ta riko hannun ta , ta na fadin " Ki tsaya kar ki taba ta " ta kai karshen ta na janyo ta da karfi ta yo baya har sai da ta fadi kassa

a rude Tesnim ta mike ta na kallon Inaya ta ce " baby , lafiyar ki kuwa ? " ta kai karshen ta na fara takawa za ta nufar Rouksar da ta Zube a kassa ta na murkuso

da sauri Inaya ta riko ta da duk hannayanta biyu ta na fadin " Aunty Tesnim , kar ki taba ta , don Allah wlh za ta cutar da ke , asirin da ta yi wa momy ne na kare "

cak Tesnim ta tsaya ta na kallon Inaya irin kallon nan na rudu kafin ta juya ta kali Rouksar
a hankali Rouksar ta mike sai faman hakki ta ke yi , murya a disashe ta ce " me ki ka yi wa bishiyar nan ? " ta fada ta na kallon Inaya idanun ta cike da ruwa har wani lumshe su ta ke kamar mai jin barci

cikin ko in kula Inaya ta ce mata " na sa a cire ta , kuma na san yanzu haka sun kusa Kamalawa "
Dum Rouksar ta ji zuciyar ta ta buga wata yar karamar kara ta saki ta na fadin " No , me ya sa za ki yi haka , ba ki san abun da ki ka aikata yanzu , na tabbatar miki abun da zai biyo bayana ba za ki iya yaki da shi ba "

ba ta gama rufe bakin ta ba Tesnim ta daga murya ta na fadin " ya isa haka , wai maganar me ku ke yi haka ? na kassa ganewa "

Har Rouksar ta bude baki za ta yi magana kawai ta ga Ruhin MALIKAT AL'UMU ya shigo dakin ya nufi MALIKAT AL'UMU zai koma jikin ta
a dubu dari Rouksar ta yi kokarin kamo shi ta na sakin wata yar karamar kara
amma ina ko taku biyu ba ta yi ba ya shiga jikin MALIKAT AL'UMU

wani irin dogon nunfashi MALIKAT AL'UMU ta ja kafin ta ware idanun ta a dubu dari ta mike zaune ta na nunfashi da karfi

a dubu dari Inaya da Tesnim su ka nufe ta su na fadin " momy , momy "
a rude MALIKAT AL'UMU ta ke kallon wajen ta na fadin " Baby , Tesnim , me mu ke yi a wajen nan kuma ? "
Chapter 32 · 0% Book details