← Book details Exiled Prince Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 61

Sashe 57

Exiled Prince Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bari na dan takaice labarin , a ranar Friday a ka yi duk wasu shirye shiryen dan sake nada Malik , amma wani abun mamaki kawai sai ya ce shi bai dawo dan ya zauna saman kujerar nan ba , kawai ya dawo ne dan ya kwace ta da ga hannun Aymane kuma ya yi nassara , yanzu kuma zai nada wanda ya cancenta sa wannan kujerar bayan shi , da ga haka ya nada Diya da kanshi a matsayin Malik , kuma babu wanda ya yi mishi ja , har ya kammala , sannan ya nada Abdoul a matsayin na hannun daman Diya , nan ma babu wanda ya yi mishi ja
a haka har a ka kammala taron , kowa ya koma part din shi
a misalin karfe takwas na dare duk ahalin Malik su na cikin parlourn shi na part din shi a floor na uku dan har yanzu bai bude floor na hudu ba
a haka ya sanar da su zai koma US dan dama ziyara ce ya kawo musu yanzu lokacin komawarshi ya yi
RIANNA ta sha kuka ta rokon shi ya zauna amma fir ya rufe ido ya ce ta yi hakuri shi dai sai ya tafi
babu yadda su ka iya haka su ka yi mishi bankwana su na yi mishi addu'a Allah ya tsare shi tare da Familyn shi , su na fadin sun yi kewar shi sosai , ya ce duk ranar Friday su dinga zuwa a nan parlourn a karfe takwas su yi video call ya ga in kowa ya na cikin koshin lafiya
da ga haka har karfe goma sha biyu na dare ya yi kowane ya koma part din shi
bayan sallar asuba misalin karfe 5 , su ka raka Malik da Inaya da Nayel har airport , su na yi musu bankwana , da ga nan su ka shiga jet din su ya daga ya nufi US

THE END ............

🤣🤣🤣🤣🤣🤣✌✌✌✌✌✌ WASSA NA KE

▪AFTER FIVE YEARS

▪UNITED STATE OF AMERICA ( WASHINGTON DC )

wani kyakyawan yaro ne ya sauko stair , Fari kal da shi kamar ka taba jini ya fito , ya na da kananan idanu Hazel , ga dan karamin hancin shi a tsaye , da bakinshi , lips din shi red color shape din na sama kamar heart , ya na da smooth hair ya zubo mishi bayan keya , sai wasu kananan da su ka zubo mishi a gaban goshi har zuwa wajen eyebrow , ga tambarin masarautar Saudiya a wuyanshi
ya na sanye da wandon Jeans white color , da T-shirt blue color , ya daura wata jacket a sama White color , kafafun shi na cikin wasu sneakers Navy blue , da gani renon madara da ice cream

da gudu ya ke sauko stair din ya na wata yar karamar dariya
ya na gama sauko stair din Malik ya shigo parlourn ya na sallama
yaron nan na ganin shi ya nufe shi da gudu ya na fadin " Daddy , tun dazu fa na ke jiran ka , har na yi fushi " ya fada cike da shagwaba

a hankali Malik ya sa hannu ya dauki yaron nan ya na fadin " I'm sorry my Prince , tell me kun gama shiryawa mu tafi ? "

da sauri Prince ya ce " yeah , kai kadai mu ke jira , na matsu na ga Ammie , da mamie , da mama , da Uncle " ya fada cike da shagwaba
( hmmm , ko da ga ina ya dauko wannan shagwabar ? 🤔🤔 )

" okay , where is your mom ? " Malik ya fada

" wait " Prince ya fada kafin ya juya ya kalli Stair ya ce " Momyyyyyyyyy ! " ya fada da mugun karfi sai da Malik ya lumshe idanunshi ya na fadin " Prince slowly mana , ka fasa min kunne "

ya na gama fadar haka Inaya ta fara sauko stair ta na sanye da wata Abaya fara kal mai mugun kyau an yi mata zanen flower kamar rainbow , ta yafa veil din ta fari shi ma , ta na sanye da wasu sneakers pink color a kafa , ta na rataye da wata yar bag pink color ita ma
ta cika ta yi bul bul abunta , da ga gani ta samu hutu , har wani haske ta yi kumatu sun fito , gaskiya US ta zauna mata

tun da ta fara sauko stair Malik ya tsare ta da ido babu ko kiftawa , sai magana prince ke yi mishi amma ba ya jin shi
a hankali Prince ya kai hannu saitin fuskar Malik ya kyasta mishi yatsu ya na fadin " Daddy , tun dazu ina maka magana ka kyale ni , sai kallon momy ka ke kamar ba ka san ta ba "

a hankali Malik ya sauke ajiyar zuciya dai'dai lokacin da Inaya ta karaso gaban shi ta na fadin " mu tafi ko ? "

gyada mata kai Malik ya yi a hankali ya na murmushi kafin ya riko hannunta , ya juya su ka fita parlourn , su ka fito harabar gidan ,
su na fitowa sai saman motar Malik , kai tsaye ya budewa Inaya wajen mai zaman banza , ta shiga sannan ya rufe kofar

ya zagayo ya bude wajen driver ya shiga tare da Prince ya zaunar da shi saman cinyoyinshi ya yi tukin a haka har su ka bar gidan su ka nufi hanyar Airport

▪DAULAR SAUDIYA 👑🔥

zaune MALIKAT AL'UMU ta ke cikin parlourn tare da MALIKAT INAS sai murmushi su ke saki
su na a haka RIANNA ta shigo ta na sallama ta na fadin " Ammie , momy mu tafi sauran ten minutes jirgin su ya sauka " ba ta jira amsar su ba ta juya ta fice da sauri ta na sakin murmushi

a tare MALIKAT INAS da MALIKAT AL'UMU su ka fito part din , su na fitowa sai saman wasu motoci a jere bakin part din , a tare su ka shiga motar da ke gaban su , su na shiga motocin su ka tada su ka bar masarautar da mugun gudu su ka nufi airport

a jere motocin su ka shiga airport , kai tsaye wajen saukar jirgi su ka nufa , sannan su ka yi parking ,
daya bayan daya su ka fara sauko motocin , Diya da Nesrine su ka fito da ga cikin motar su tare da Junior din su
RIANNA kuma ta fito da ga cikin motarta tare da mama da MALIKAT HOUDA
MALIKAT AL'UMU da MALIKAT INAS kuma cikin mota guda
sannan Abdoul da Tesnim su ka fito cikin mota guda tare da wata kyakyawar yarinya a shekaru ba za ta wuce 3 or 4 years ba , kyakyawa ce gaskiya kamar an tsaga kara da Abdoul dan ta na kama tak da shi , sai dai ta dauko farin Tesnim dan kamar ka taba jini ya fito ta ke har wani ja ta yi

ta na ganin MALIKAT AL'UMU ta nufe ta da gudu
wani cool murmushi MALIKAT AL'UMU ta saki kafin ta durkusa ta dauki yarinyar nan ,
a hankali duk su ka karaso wajen motar su MALIKAT AL'UMU su ka tsaya
da sauri MALIKAT HOUDA ta ce " wai har yanzu ba su iso ba ? "

wata yar karamar dariya duk mutanan wajen su ka yi kafin Diya ya ce " mamie , mu ma duk mun matsu mu gan su "

har ta bude baki za ta yi magana su ka jiyo karar jirgi
a tare su ka kai kallon su wajen da su ka jiyo sautin su na fadin Alhamdoulilah cikin zuciyoyinsu
a hankali jirgin nan ya sauka , ya tsaya ya na fuskantar motocin su

sai da ya yi two minutes a haka kafin kofar jirgin ta bude a hankali
a tare Malik da Inaya su ka fito da ga cikin jirgin Malik ya na dauke da Prince duk jikin shi ya yi sanyi allamun barci ya ke

a tare duk su ka nufe su su na yi musu barka da zuwa , da sauri MALIKAT INAS ta kai ta karbe shi nan ta ga ashe barci ya ke , amma duk da haka sai da karbe shi
da ga haka su ka shiga rungumar juna , specially Diya , da ya rike Malik sai da RIANNA ta shiga ce mishi ya sake mata dan uwa ita ma ta rungume shi , ita dai Inaya tun da ta rungume mama ba ta sake ta ba har kowa ya hakura ya bar ta dan sun San yadda kewar uwa ta ke

da ga su ka shiga motocinsu su ka bar airport din su ka kama hanyar Daular Saudiya
ko da su ka isa kai tsaye Diya ya wuce da Malik building din shi tare da Abdoul
MALIKAT INAS kuma ta tafi part din su da Prince tare da MALIKAT AL'UMU da RIANNA da Tesnim
Inaya kuma ta bi mama tare da Nesrine su ka nufi part din MALIKAT HOUDA tare da Junior

▪MALIK

tsaye ya ke a cikin parlourn part din shi a floor na uku sai bin wajen ya ke da kallo kamar bakwon shi
ya na a haka ya jiyo Muryar Diya a bayan shi ya na fadin " mu tafi ka yi wanka , ka huta , amma gaskiya abokina US ta zauna maka , ka na cen ka na shan dadinka ka kyale ni nan da aiki "

wani dan karamin murmushi Malik ya yi ya na fadin " ai ni zuwan tsaye na muku , dan gobe zan yi gaba da Cutie " ya kai karshen ya na fara takawa ya nufi corridor

cikin rudu Diya ke ce mishi " ban gane ? "
ko sannu Malik bai ce mishi ba ya shige corridor
sai da ya shiga sannan Diya ya juyo ya kalli Abdoul da ke tsaye gefe ya ce " har yanzu dai na miskilancin nan su na nan "
Chapter 57 · 0% Book details