← Book details Exiled Prince Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 61

Sashe 52

Exiled Prince Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wata yar karamar kara Inaya ta saki ta na janye forehead din ta , ta kauda kai gefe , da karfi ta cije lips din ta kamar za ta fashe su

da sauri Malik ya kalli doctor ya ce " wai har yanzu ba ku fiddo mata wannan abun ba ? "

" don't worry , ga kanshi nan na fitowa , ranki shi dade , last working , ki turo da karfi " doctor ta fada ta na kallon Inaya

da sauri Inaya ta shiga girgiza mata kai idanunta a lumshe
da sauri Malik ya daura hannunshi saman kumatunta , ya juyo da face din ta , ya sauke forehead din shi saman nata murya kassa kassa ya ce " okay , zan kirga zuwa uku , da ga nan ki ka dogon nunfashi ki sauke , kin ji ko ? "

a hankali ta gyada mishi kai allamun Eh
" Okay , one , two , three let's go "

wani dogon nunfashi ta na sakin wata siririyar kara karfin ta sauke wata nanauyar ajiyar dai'dai lokacin da kukan baby ya gauraye wajen

wata nanauyar ajiyar zuciya Malik ya sauke ya na fadin " Alhamdoulilah " cikin zuciyar shi har lumshe idanunshi ya yi ya na sakin murmushi kamar shi ya yi aikin

ya na bude idanunshi ya ga Inaya ta yi tsit kamar an yi ruwa an dauke
Dum ya ji zuciyar shi ta buga da karfi , a dubu dari ya kai hannu ya fara jijiga ta ya na fadin " Cuti , Cutie , please ki bude idanunki , Cutie , please ki bude kar ki min haka mana "

da sauri Doctor da ke rike da babynsu ta karaso wajen ta na fadin " ka kontar da hankalinka , ba mutuwa ta yi ba , suma ce ta yi " ta na gama fadar haka
ya ga ta sauke babyn hannun ta saman kirjin Inaya ta kontar da kan shi saitin zuciyarta
wani irin sanyi ne ya ji lokacin da idanunshi su ka sauka saman babyn , kyakyawa da shi fari kal kamar ka taba jini ya fito har wani ja ya yi , ya na kama tak da Malik kamar an tsaga kara , sai dai idanun shi a rufe su ke sai in ya bude mu ga kalar su

kawai sai ya ga babyn ya rage kukan da ya ke yi , doctor na ganin haka ta dauke shi ta mikawa Malik ta na fadin " za ka rike shi , ko mu tafi ? "

bai ce mata komai ba ya dago hannayan shi a hankali ya mika mata
ba musu ta daura mishi babyn a sama
nan take ya kara sautin kukan shi ya na wuntsila Kafafu kadan ya kubcewa Malik
da sauri Doctor ta karbe shi ta na fadin " Nurse , ku je a yi wa mai martaba dress , ya samu rauni a jikin shi ta fada ta na juyawa da babyn

sai da ya sunkuyo ya mannawa Inaya kiss a saman forehead din ta , sannan ya kai bakin shi saitin kunnen ta ya yi mata rada kafin ya mike ya juya
ya bi bayan nurse din nan su ka baro dakin

su na fitowa kawai ta ga Malik ya yi gaba abun shi , ya nufi su MALIKAT AL'UMU da ke zazzaune sun yi zugum

su na ganin shi su ka mike a tare su na tambayar ta sauka lafiya
gyada musu kai kawai ya yi kafin ya ce " za ku iya komawa part din ku , doctor ta ce ta na bukatar hutu " ya kai karshen ya na shirin takawa

da sauri MALIKAT AL'UMU ta taro shi ta na fadin " me ta samu ? mace ko namiji ? "
slowly ya juya ya kalli MALIKAT INAS , cikin sanyin murya ya ce " Nayel ne "

wani kyawatencen murmushi MALIKAT INAS ta saki har hawaye na zubo mata
a hankali Malik ya juya ya fice word room din ran shi fari tas kamar an yi mishi albishir da gidan Aljanna

a haka su ma su MALIKAT INAS su ka baro Word room din , kowace ta nufi part din ta na asali

shi ma Diya da Nesrine su ka koma part din su , haka Abdoul da Tesnim
Rafik kuma ya nufi fada ya bude ta , ya kira duk wani na fadar ya fada mishi ya dawo Ranar Friday za a sake nada Malik Nawfel Hicham Bin Jaabar

bangaran Malik kuwa kai tsaye part din MALIKAT HOUDA ya koma ,
babu ko sallama ya shigo parlourn , nan ya tardo ta zaune , sai faman addu'a ta ke yi
ta na ganin shi ta sauke ajiyar zuciya ta tashi da sauri ta nufe shi ta na fadin " masoyina , ba abun da ya same ka dai ko ? Allah na gode maka "

wani dan karamin murmushin geffen fuska ya sakin mata kafin ya ce " kin ga , ki daina kira na da masoyinki , so ki ke papi ya tardo ni , ya ce na kwace mishi matar shi "

wata yar karamar dariya ta saki ta na fadin " kai dai ka sani , mara kunya kawai "

" shikenan , bari na yi wanka , zan yi miki albishir me dadi "

" shikenan , ina jiran ka , mai martaba " ta fada cikin zolaya
bai ce mata komai ba ya nufi corridor ya shige bedroom din Inaya ke ciki , kai tsaye toilet ya wuce

❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤

( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )

STORY & WRITTEN BY : MEERAH ⚘🕊

【THE ROYALTY LOVE ❤🌹】

【 BOOK ________3 📚✍💌 】

_______________________♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡______________________

{ P A G E ________ 28 ✍💕🔥}

bai ce mata komai ba ya nufi corridor ya shige bedroom din Inaya ke ciki , kai tsaye toilet ya wuce dan ya yi wanka
jim kadan ya fito sanye da bathrobe
bed din ya nufo ya zauna , ya zauna a baki ya kai hannu ya bude bedside drawer ya fido A box

sannan ya ajiye a sama , sannan ya bude ya fiddo wata yar takarda
hannu ya sa ya rabata gida biyu , ya fido wata yar karamar allura irin ta dinki ta na da wani siririn zare blue

a hankali ya kai allurar nan wajen yankar da Aymane ya yi mishi , ya fara yi wa kanshi dinki , ya na lumshe idanunshi , ya na cije lips din shi na kassa dan ba karamin zafi a dakwai ba
amma a haka ya yi wa kan shi dinki , ya yi dressing wajen , sannan ya tashi ya nufi dressing room

jim kadan ya fito sanye da Trouser black color , da T-shirt sky blue , sai wasu sneakers farare a kafafun shi , ya daure wanan smooth hai din nashi a baya , sai tashin qamshi ya ke , sannan ya nufi kofar fita bedroom din ya fito

kai tsaye part din ya baki daya ya baro , ya nufi hanyar Fada
bakinshi da sallama cen kassan makoshi ya shigo Fadar , nan ya tardo duk mutanan fadar shi , su na zaune
su na ganin shi kowane ya saki murmushi ya na mikewa tsaye su na gaishe shi cike girmamawa

sai da ya karaso tsakiyar fada sannan ya juya ya kalli side din su
tsayawa ya yi ya kare musu kallo na dan lokaci kafin ya ce " na ji dadin ganin ku cikin koshin lafiya "

a tare duk su ka saki wani kyawatencen murmushi su na fadin suma sun ji dadin ganin shi a raye

dan sunkuyar da kai ya yi kafin ya dago ya ce " okay , zan so ku fara shirye shiryen nada sabon Malik ranar Friday , sannan Dalil ( sabon Sarkin bayi ) zan so ka mayar da bayan ki part din su , sannan gobe ka sa su je part din Malik su kwashe duk kayan da ke ciki za a zuba sabi , duk wani abu da ke bukatar gyara a cikin masarautar nan har ma wajen ta kawai ku aiwatar , kar ku damu da adadin kudin za a kashe , Idris ( shi ne sabon me kula da dukiyar Daular ) ka bude bankin masarautar , na ba da dama a fitar da kudin da su ka dace dan ganin an kyara masarautar , amma abu na farko da na ke son ku fara shi ne cire min wadanacen banzan status da a ka kafa min bakin Daula , General Abdallah , duk mutanan Fadar Aymane da ke hannun jami'an ka , ku yi executed din su kawai , ita kuma Hafsat a mayar da ita wajen mahaifiyar ta , sannan ku shirya min zama da yan JARIDA a matsayin Mr president ba Malik ba ran monday "

( Idan ba ku manta ba tun farko na ce muku Malik shi ne shugaban kassar Saudiya , kuma duk wata maganar administration a hannun shi ta ke , hakan na nufin shi ne sarki kuma president din kassar Saudiya , mutanan Fadar shi kuma duk yawwancin su ministers ne )

" an gama ya shugaba " su ke fada a tare sannan su ka shiga jero mishi addu'a

cikin zuciyarshi ya ke amsa musu da Ameen kafin ya juya ya sa kafa ya baro fadar
tafiyar shi ya ke cikin konciyar hankali ya na bin Daular da kallo , a haka har ya karaso cikin word room

kai tsaye dakin da ya kai Inaya da farko ya nufa , kawai sai ya ga babu kowa a ciki
da sauri ya juya ya koma reception ya na tambayar matar shi
cikin nitsuwa Wata nurse ta ce mishi " an sauya musu daki , su na cikin room 5 "
Chapter 52 · 0% Book details