← Book details Exiled Prince Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 61

Sashe 26

Exiled Prince Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

bakin shi da Sallama cen kassan makoshi ya shigo parlourn MALIKAT HOUDA
nan ya tardo ta zaune tare da Muntaz , ta na ganin shi ta saki wani kyawatencen murmushi ta shiga yi mishi sannu da zuwa
gyada mata kai kawai ya yi kafin ya nufi MALIKAT HOUDA ya zauna geffen ta , murya kassa kassa ya ce " barka da wannan lokaci Mamie "

a hankali ta kai hannu saman kumatun shi , ta matso da face din shi ta manna mishi kiss saman forehead sannan ta ce " na fada maka wani abu ? ina matukar alfahari da kai , na godewa Allah da babu abun da ya same ka "

hannun ta ya riko ya kai saitin bakin shi ya manna mata kiss ya na fadin " ina son ki duk da kin tsufa "

wata yar karamar dariya MALIKAT HOUDA ta yi kafin ta ce " tsakani da Allah Nawfel ban fi MALIKAT din ka kyau ba ? "

" ko kusa ta fi kyau , duk duniya babu macen da ta kai ta kyau , har yanzu ban ga macen da ta kamo ko da kafar ta ce wajen kyau bare ke tsohuwa " ya kai karshen ya na kauda kai

da sauri Muntaz ta ce mishi " a'a gaskiya ban da ni , ko makaho ya kalle ni , ya kalle ta , ya San na fi ta kyau , ko Mamie ? " ta kai karshen ta na sakin murmushi

" ni dai ba ruwa na , tsakanin ku ne , kar ku sanyo ni cikin fadan ku " fadin MALIKAT HOUDA

har Muntaz ta bude baki ta na shirin magana Malik ya riga ta cewa " ina sirikata ta ke , wajen ta na zo "

hararrar wassa MALIKAT HOUDA ta wurga mishi ta na fadin " Ah , dama ba waje na ka zo ba ? shikenan tashi ka tafi , ta na cikin dakin ta "

" okay " ya fada a takaice ya na mikewa tsaye ya nufi corridor ya shige
da kallo Muntaz ta raka shi har sai da ya shiga corridor din sannan ta ce " wlh ni dai na fi wacen sakarar kyau , Ah to " ta kai karshen ta na turo dan bakin nan nata
murmushi kawai MALIKAT HOUDA ta yi ta na kallon ta , sai wahalar da kan ta ta ke yi , wanda ta ke yi wa bai ma san da ita ba

a hankali kai hannu ya tura kofar dakin mama ya shiga ya na sallama cen kassan makoshi

zaune mama ta ke bakin gadon ta , ta na fuskantar kofar shigowa
a hankali ta dago kai ta na amsa mishi sallamar shi , ta na ganin Malik ne ta saki wani cool murmushi ta ce " malam Zayd ne da kan shi a nan ? ko dai batan kai ka yi ? " ta fada cikin zolaya

girgiza mata kai ya yi ya na cewa " barka da wannan lokacin mama , fatan na same ki lafiya ? "

wani dan karamin murmushi ta saki ta na nuna mishi geffenta da hannu
ba musu ya karaso bakin gadon ya zauna ya na kallon ta
ya na zama ta shiga karanto mishi addu'o'in tsari da ga ubangiji ta na tofa mishi idanu a lumshe
sai da ta Kamala sannan ta ware idanun ta ta ce " ya jikin naka ? na ji an ce ba ka da lafiya "

cikin nitsuwa ya ce mata " Alhamdoulilah "
" Masha Allah " mama ta fada ta na dan karamin murmushi

dan jinkirtawa ya yi kafin ya ce " please mama ina son mu yi wata magana , a kan Inaya "
da sauri mama ta katse shi da cewa " Allah ya sa ba wani laifin ta yi maka ba ? "
girgiza mata kai ya yi allamun a'a , kafin ya mike a hankali ya nufi kofar dakin ya tura ta ya rufe sannan ya saka security kafin ya juya ya dawo inda ya tashi ya zauna

sai da ya dauki dan lokaci kafin ya ce " ba ta yi min laifi ba , kawai akwai wata magana da ta tsaya min a zuciya , tun da uncle ba ya nan , na san ke kadai zan iya fadawa wannan abun "

" Ina sauraron ka , kar ka ji tsoro za ka iya fadamin " mama ta fada ta na kai hannu ta riko hannun shi

a hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce " mama ni kai na ban san yadda zan yi na fada miki ba , saboda abun ya wuce tunanina , watarana uncle ya taba ce min ya na ji a jikin shi kamar ba ita kadai ba ce a cikin jikin ta , na kassa gane me haka ke nufi , ta sha fada min abu , kuma abun nan ya tabbata , na san ku na da labarin poison din da a ka zuba min a abinci , a ranar ni da ita mu ka sha fruits din , har ta ce min kar na hadiye abun da ke cikin bakina bayan ita ta hadiye kuma ni na konta ciwo ita ba abun da ya same ta wannan abun ya tsaya min a rai , ko jiya lokacin da na bude ido , na gan ta tsaye a gabana duk ta sauya min idanun ta sun koma farare kal har gashin kan ta , please mama idan uncle ya taba yi muku wata magana a kan ta ya kamata na sani " ya kai karshen ya na dago kai ya kali mama

cikin nitsuwa mama ta ce mishi " hakan na nufin wani abu ya shiga tsakanin ku ? " ta fada ta na sakin murmushi

dan zaro idanu ya yi ya na kallon ta , shi tambayar da ya yi mata daban ita tambayar da ta ke yi mishi daban

kamar ko ta san abun da ya ke tunani sai ta ce mishi " da a ce wani abu bai shiga tsakanin ku ba , babu yadda za a yi ka min wannan maganar " ta na gama fadar haka idanun ta su ka koma farare kal ko digon baki babu

ba karamar razana Malik ya yi ba har sai da ya shiga karanto kalmar shahada
lokaci guda idanun mama su ka koma dai'dai , da sauri ta ce mishi " kar ka ji tsoro ba abun da za su yi maka "

cikin rudu Malik ya ce " su wa kuma ? "

wani dan karamin murmushi mama ta saki kafin ta ce " Abyad & Aswad "

" white & black ? " Malik ya fada cike da rudu
Chapter 26 · 0% Book details