← Book details Ba Ni Da Laifi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 32

Sashe 9

Ba Ni Da Laifi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na amsa na duba wai ashe bindawa yake nufi, ai ni har mantawa nike da sunanta haulat saboda kowa da bindawa yake kiranta, ai kamar nice idan mutum zai kwana yana cewa mariam ba za'a gane ba har sai idan yace baby ko kuma yayi describing dina da wacce tafi en course dinmu haske, mutane da yawa suna describing dina da haskena, wasu suce ai tafi kowa haske ga kyau, sai kuji ance hasken ne kawai ya ceceta, ai idan bak'a ce ba zata kallu ba, miye, daga farin fatar sai idanun sai dogon hancin shikenan, tambaya tou wai mey ake buk'ata a kyau bayan wadannan abubuwa, mutanen mu kenan, tou b'arb'ela dai tun taltala take da farinta na tabbata banda haka da wasu sunce wanka da sabulu ne yasa tayi haske ko kuma suce bilicin tayi....

Muryar Yaa Ahmad naji a bayana, da sauri na juya na dubeshi ya kalleni nace,
"Wayarshi na kawo mashi...".

Nayi crossing dinshi na koma ciki....

Washe gari tunda safe na wuce school, abun mamaki ina had'uwa da bindawa tace min d'an unguwarsu yana gaidani, ni abun dariya ya bani, tou ni da ya gani jiya da daddare wai kuma har da aiko min da sakon gaisuwa ya gaisheni da kansa mana....

Bayan kwana biyu muna zaune ni da Ummy da Affan wanda ya mak'alk'alewa Ummy, ina mik'a hannu ba ya zuwa amma idan na mik'a mashi wayata sai ya tafo ni kuma bazan bashi wayata ya karasa min da ita ba, tou dama ya lafiyar giwa ballantana kuma tayi ciwo, ina lallab'awa da wayata ai ina bashi zaiyi pieces da ita, akwai lokacin da na saka charge na dawo na tarar ya cireshi yayi ma wayar pieces, Aallah ya taimaka bata samu damuwa ba, diramarmu muke muna shan dariya abunmu, yana taking steps zuwa inda nike amma ina janye wayar sai ya juya ya gudu wurin Ummy, nayi dariya nace,
"Yaro bazan baka wayata ba, hakanan kayi mata daya-daya...".

Mukayi dariya, Ummy tace,
"Kuma yana amsa kangawa zaiyi a kunne yana kiran hello, hello, hello, Abba, Ummy, Baby, Ayan...".

Yaa Ahmad ne ya shigo ya daukeshi yace,
"Ai ni sai in baka tawa".

Ya zaro wayarsa android ya mik'a mashi, nace,
"Ai kai mai kudi ne, ni kuma idan ya b'ata min tawa sai nayi er murya".

Yaa Ahmad ya tangare min k'eya na saki k'ara sannan cikin shagwab'a nace,
"Ummy...".

Ummy tace, "Mey?

Babu ruwana, ai kunfi kusa".

Nace, "Babu ruwana da kai, mun b'ata...".

Kallona yayi yace,
"An baku assignment...".

Da sauri na dubeshi na zaro idanu nace,
"Aallah?".

Ya harareni yace,
"Daina kulani, ai mun b'ata".

Haka muke kamar abokan wasa, dariya ya kunshe ya amshi wayarsa daga wurin Affan ya mik'o min, yace,
"Duba ki gani...".

Na amsa nayi tsuru-tsuru da ni, ya kwashe da dariya sannan yace,
"Je ki dakina ki gani...".

Na mik'e na fita, da murna na dawo nayi hugging dinsa tareda mashi peck a kumatu, nace,
"I love you shiyasa duk nafi kama da kai...

Ummy next week ake bikin wani course mate dinmu kuma Jalila ta matsa akan dole sai munyi attending programs da za'ayi...".

Ummy tace, "Indai tareda Jalila zakije, ba ni da damuwa".

Washe gari bayan mun fito daga tutorial din wani course, Jalila tace,
"Baby...

Suhail ya bani ankonmu amma yana gida, dinkin ya had'u, kayan masu tsada, ohhh koda yake biki ne na arziki".

Nayi murmushi kawai, dinner ce aka fara, tou ita muka fara attending, tou a gidansu Jalila na shirya, expensive less ne brown da golden head amma abun mamaki kayana sunyi daban da na Jalila, duk yadda bana san yafa veil amma saida Jalila ta matsa min na yafa, dinkin fitet gown ne wadda tayi suiting dina amma bata matseni ba, simple make-up nayi applying amma nayi matuk'ar kyau kamar wacce zataje contesting din beauty, looking breathtaking....
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
*Update Of June, 2019*
In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen
*Eid mubarak our greatest sofi, sofinmu I just imaging a ranar sallar nan sweety ya amshi handbag dinki ya cika maki ita da dollars don haka ina jiran nawa share din, ko kuma aradu inyi ma sweety sending picture dinki kina kwasar loma, hhhh, lols....*
*Baby d'iyar rubber cikin dare take kashe y'ay'anta murus...

Baby d'iyar rubber cikin dare take kashe y'ay'anta tumus...

Baby d'iyar rubber cikin dare take kashe y'ay'anta kurus rumus...

Eid mubarak to you baby fans all over the world, ina jiran barka da sallah na....*
Page. 8
Da sauri na kalli high heel shoes dake jirana nace,
"Kin san Aallah Jalila bazan iya tafiya a wadancen takalman masu tsini ba, hakanan in fad'i in broken kafafu...".

Na nufi shoes rack dinta....

Jalila tayi dariya sannan tace,
"Dawo ai guda biyu ya sako maki heel shoes da flat shoes".

Sai kuma tayi min pointing flat shoes din na saka, tace,
"Ma shaa Aallah...

Baby you look cute...".

Ni da kaina nasan nayi kyau babu k'arya, saida ta kashe mamu selfie mukayi snapping picture sannan muka fice muka sauka kasa mukayi sallama da Mami muka wuce compound, muka shiga wata dalleliyar mota direba ya jamu, mahaifin Jalila yana da kudi sosai, gidansu babban mansion ne, direba ne yayi parking muka fito tunda daga inda muke muna jiyo kidi da yake tashi daga ciki, Jalila tace,
"Baby muje...".

Na kalli hall din na girgiza kai, tace,
"Sai in tafi in barki...".

Nace, "Bismillah...".

Dariya na bata tace,
"Wato don kin san bazan tafi in barki ba, wai ke mey yasa kike da tsoron mutane, miye na tsoro kamar wacce za'a cinye, kina da kyau, kina da haske, aikuwa dole a kalleki, wadanda basu kaiki kyau ba an kallesu ballantana ke kuma...".

Nayi mata banza, ta jawo waya ta danna call, tayi jim sannan tace,
"Gamu nan a bakin hall...

Baby ce kasan halinta...

Tou shikenan...".

Jim kadan suhail ya fito looking breathtaking, kun san dai yadda groom suke shan kyau, da smile ya karaso yace,
"Baby you look breathtaking ai koda amaryar ba zata nuna maki kyau ba...".

Kallonshi nayi yace,
"Cheese...".

Sai kuma ya kashe mamu selfie, yayi min snapping picture sai kuma ya rik'e hannuna ya jani ciki yayinda Jalila ta biyo bayanmu, kallon hannunshi da ya rik'e hannuna nayi I feel kamar ina sonshi, yana da hali mai kyau kuma yana matuk'ar sona sannan yana da kyau kuma yana da ilimi and yana da brain, tou first class ne mai security wanda small wuru-wuru bazai saka ya sauka ba, saidai har lokacin ba na nadamar rashin accepting dinshi da nayi, sai yanzu da nike tunani sannan na fara nadama, tou kamar yadda kuka sani yana sona sosai kuma yana da hali mai kyau amma nace a'a, naqi mai kudi gashi talaka yana neman janyo min hawan jini, both a cikin masu kudin da talakawa akwai na kirki hakanan kuma akwai na banza, tabbas ba duka aka taru aka zama daya ba, sai yanzu na fahimci komai amma a wancen lokacin babu abun da na gane....

Suhail yana jaye dani ne yayinda muka bada wani perfect match, indeed I feel kamar ina sonshi, tunda muka shiga idanu suka dawo a kanmu, sai lokacin na lura ashe kayan da ya bani ba anko bane, wadanda Jalila take sanye dasu sune anko, expensive less din dake jikina yafi match da kayan dake jikinsa, har zuwa wannan lokacin yana rik'e da hannuna yana tafiya ina biye dashi kuma high table yake nufa inda bride dinsa take zaune, da smile yace,
"Baby ga mai sona...

Suhailat ga wadda nike so...".

Suhailat ta yaye veil dake kanta tana kallona, saida gabana ya fad'i, kamarta daya sak da suhail, kallo za'ayi mata a gane jininsa ce, kallonshi tayi ta kalli hannuna da yake rik'e dashi, smile yayi, tace,
"Mariam ko?...

Sannu...

Ohhh baby...".

Ni rasa abun da zance mata nayi sai kuma nace,
"Congratulation, I wish you all the best Mrs suhail to be, suhail bashi da damuwa, hope zaki kula mamu dashi, muna sonshi...".

Suhail ya ware idanu sannan yace,
"Aahhh ashe baby kina sona...".

Na kai mashi a baya nace,
"Zanyi maganinka...".

Suhail ya turo lips yace,
"Zuciyata zaki sace ne...".

Nayi shiru kawai, tou babu bakin magana, yasa dariya yana kallona, Jalila ce ta raba hannuna da nashi aka daukemu hotuna muka wuce wurin en course dinmu, bayan da na baiwa bride abun da ya saka min a cikin anko ina ganinshi na gane abun da yake nufi, amma lokacin da na bata har da cewa....

"Mun gode wacce nike so...".

Duk wanda muka gaisa sai ya yaba kyan da nayi, wasu suce tubarkallah wasu kuma saidai ni ince a cikin zuciyata, bindawa tasha rawa hakanan Jalila, nikam saida suka matsa min sannan nayi aikuwa na sha liki, suhail yayi min wanka da wrapper din dollars, a hanyarmu ta komawa gida, Jalila tace,
"Baby duba ki gani...".

Sai kuma ta mik'o min wayarta na amsa naga suhail ne ya saka selfie din da yayi mamu akan dp, na duba wayata babu kudi nayi mashi please call me babu jimawa ya kira, nayi picking before inyi uttering koda word guda daya, yace,
"Baby i love you har yanzu...".

Naji kamar inyi mashi duka, nace,
"I love you din banza, ni kawai ka cire hotona daka d'aura akan dp...".

Daga daya bangaren suhail ya ja lumfashi sannan yace,
"Hotonmu dai, ai ni da ke ne a ciki, ko kin manta...".

"Whatever ma shi nike nufi...".

"Alright then, zo ki amshi wayar ki sauya da kanki, kin ganta nan a hannuna...".

Na biye mashi yana zaulayata ina cewa ni ya cire min hoto daga kan dp, koda kiran ya tsinke ya kara kira ya cigaba da zaulayata, sai bayan yayi hanging call din sannan na tuna da wani abu dole a wannan lokacin yana tare da amaryarsa zasu maidata gida, na ware idanu nace,
"Jalila na bani, yana tare da amaryarsa na kirashi kuma dole taji haushi, anya kuwa zan k'ara attending wani program".
Chapter 9 · 0% Book details