← Book details Ba Ni Da Laifi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 32

Sashe 7

Ba Ni Da Laifi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Safeena taja daya babie din suka fice, duk da bana so amma saida suka sakani na fad'i bakaken maganganu....
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
*Update Of June, 2019*
In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen
*Assalam Alaikum sis, complete ne nayi maku shi a matsayin barka da sallah, tou idan kina akan what's app kiyi min magana inyi maki sending document dinshi, idan kuma facebook kawai kike, tou kiyi hakuri har kuzo karshen*
*barka da sallah mariam dabai, wish you all the best*
Page. 6
Na durkushe tareda fashewa da kuka, wannan wani irin abu ne duk da *BA NI DA LAIFI* amma an biyoni har gidanmu an zageni anci min mutunci, koda yake yanzu unguwarmu gulmata ake ko'ina suna cewa na samu mai kudi shiyasa na guji Mahmud yana neman mutuwa saboda sona amma ban damu ba, kudi sun rufe min idanu, duk zuwan da Aaryan yake wurina idanun magulmata yana a kai, the more yazo wajena suka ganni tsaye dashi the more zasu ce mayyar kudi, taga mai kudi mai kyau ta fasa auran talaka, tou ayi dai su gani idan tusa zata hura wuta, wai ita nan mai kyau, farin ne kawai ya ceceta, gulma iri-iri, da yawa maganganun suna dawo min amma ban damu ba, Aallah ya sani ba haka nike ba, ni kudi basu rufe min idanu ba, first wanda ya fara cewa yana sona babanshi mai kudi ne sosai shima yana dasu har kuka yayi min amma sam lokacin bana san auran mai kudi, ina ganin zai dauka na aureshi ne saboda kudinshi, gashi nan yanzu shi yaje yayi auranshi ni kuma ina nan talaka yana neman janyo min ciwon zuciya, yayi min k'arya amma kowa laifina yake gani bayan NI *BA NI DA LAIFI* sam, tunda na shigo Ummy ta shiga makotanmu, dawowarta kenan ta d'ago labule ta dubeni tace,
"Kukan mey kike?".

Nace, "K'anwar Mahmud ta rako cousin dinsu ta ci min mutunci".

Gani nayi ta saki labulen ta wuce, ina yawan tambayar kaina wai mi yasa kowa yake ganin laifina bayan k'arya yayi min, nikam bazan auri makaryaci ba, wuni nayi ina kuka saida nayi chatting da Aaryan sannan da salon barkwancinsa ya sakani farin ciki, shima wannan farin cikin washe gari tunda safe aka yi min spoiling dinshi, abun da ya faru shine takwas na safe nike da lecture din farko don haka tunda safe na wuce national ina tsaye gefen school bus ina waya da Jalila, abun da ya faru shine tun kafin in baro gida nayi waya da Jalila, shine na kirata take cemin tana cikin keke napep ta kusa zuwa wannan yasa naki shiga bus ina jiran tazo mu shiga tare, wannan babie din, ina nufin cousin din Mahmud, itace tazo wucewa ta hangoni, parking expensive car dinta tayi ta fito da alama da bala'i ta tashi, with anger ta tsaya gabana tareda rik'e kugu tace,
"Ke d'iyar talakawa....".

Na d'age niqab dita ne shiyasa ta ganeni, yadda tayi magana da karfi ya jawo hankalin tsirarun mutane dake wurin kasance da sassafe ne babu mutane da yawa, kallo ya dawo kanmu, nayi shiru kawai ina kallonta ta cigaba da cewa....

"Ke baki isa ba...

Kudi ko?

Don't worry you got it...".

Sai kuma ta zaro wrapper din en one thousand ta watsa min a fuska, I feel in fashe da kuka, Jalila ce ta shiga tsakaninmu tareda d'aga hannu ta kwasheta da mari, amma babie din ta maru sosai ta dafe cheek tana kallon Jalila, Jalila tace,
"How dare zakiyi mata haka?

What did you think?

Zaki ci bulus...

Never...

I said never...".

Sai kuma Jalila ta duk'e ta dauki kudin ta nuna mata sannan tace,
"Kin watsa mata su da wulakanci, yanzu zatayi kyauta dasu ta samu lada ke kuma kin k'are da mari".

Ta mik'awa wani mutum sannan taja hannuna muka wuce muka bar babie din tsaye tana dafe da kunci, muka wuce bus muka wuce inda napep suke parker, ina ji wani yana cema Jalila shine a layi ya nuna mata napep dinshi muka shiga, tace,
"Miye...".

Yace, "Akwai sauran wurin mutum biyu...".

Tace, "Muje, zan biya baki daya".

Ya shigo ya ja napep din, ni dai shiru nike ina shedding tears from inside cox na janyo niqab na rufe fuskata dashi, Jalila ranta ya b'aci sosai, tace,
"Mariam shiru-shiru da kike yayi yawa, kika sake sai wata ta janyo maki ciwon zuciya, yanzu banda nazo da barinta zakiyi ta wuce taci bulus...".

Shedding tears kawai nike babu sauti....

"Sunana Mariam Yusuf amma kowa da kowa da Baby yake kirana kasancewar dukkanin brothers dina maza ne zalla, lokacin da Ummy ta haifeni ta samu damuwa har ana tunanin ba zata sake haihuwa ba, wannan yasa suka dauki son duniya suka d'aura man, tou da yake haihuwa ta Aallah ce bayan shekaru biyu ta haifi Nadiya sai kuma Affan data dauki shekaru sosai before ta haifeshi almost tare da Nadiya suka haihu, duka watanni biyu ne a tsakaninsu, a lokacin Ummy tana da tsohon ciki Nadiya ta dawo wanka har saida ta koma sannan Ummy ta haihu...

Both iyayenmu en katsina ne fulani farare sol shiyasa dukkaninmu muke farare sol don ni har naso in zama kamar zabayyana, Yaa Ayan dake karatu a london shi kadai ne chocolate kuma duk ya fimu kyau, ya fimu shiga mutane, kasancewar mu duk inda muka shiga idan aka kallemu sai an k'ara, if care is not taking wani ya sakar maka baki ka dawo kana fama, shi kuma skin dinshi normal ce shiyasa ba ya damuwa yake shiga inda yake so, duk a cikinmu nafi tsanar kallo na tsani inga mutum yana kallona shiyasa nike saka niqab...

Muna rayuwa tsaka-tsakiya, mahaifinmu yana da albashi mai kyau saidai duk kudin suna k'arewa ne akan karatunmu, ya yarda ya bamu ilimi koda zamu rayu babu wadata, muna rayuwa ne babu wadata sosai, babu sutura mai kyau amma dukkanin wannan lokaci ne, Yaa Ayan shine nike bimawa tunda ya tashi yake da brain sosai shiyasa Abba ya turashi karatu London, Yaa Ahmad ya fara aiki da albasi mai kyau shine suke had'awa suna biyan kudin karatun Ayan, kamar yadda kuka sani yana karantar medicine ne a can, wannan shine abun da zan sanar daku, sauran zakuji nan gaba a cikin labarina....
*Shin miye asalin komai?

Shin a ina na had'u da Mahmud?

Shin ya aka yi na fara soyayya dashi har aka saka mamu biki, yayi min k'arya?*
*ASALIN KOMAI*
Karfe hudu na marece na gama lecture don haka saida na tsaya nayi sallar asr sannan na biyo bus, macpolo ce don haka anyi tsaye-tsaye wajen sauke mutane kafin finally tayi parking a national, baki daya daliban da sukayi saura suka soma fitowa ciki har dani na matsa tareda tsaida kekenapep zuwa unguwarmu da yake akwai nisa, tun daga nesa na hango wani d'an saurayi jingine da bike (rubber-rubber) a kofar gidanmu ya bada baya da alama yaron da zai aika ciki yake nema, a hankali nace,
"Nan yayi.....".

Kekenapep din ta tsaya na zaro er poss dake cikin handbag dina na zugeta na zaro kudin mai napep na bashi sannan na maida poss din cikin bag tareda zuro kafafu na sauko, sanye nike da long hijab har kasa kalar duhu ce wadda ta kasance ta plain yard babu pattern babu design babu flower babu daukar hankali, fuskata tana rufe da niqab kuma na k'ara jawo ta saman ta saman kaina (linki biyu) don haka koda idanuna ba'a hangowa, saurayin dake kofar gidanmu na kalla, fari ne sosai don koni da haskena yaso ya zama kamar zabayyana da kadan zan nuna mashi haske, kallona yayi sai kuma ya kalli wani wurin da alama kwarjini nayi mashi, a hankali nike taking steps kamar iska zai kaini kasa kasancewar na gaji sosai, har na gotashi na dawo da baya tareda d'age niqab dake a fuskata, a hankali nace,
"Kana neman Yaa Ahmad ne...".

Jim yayi sannan yace,
"A'a sako ne daga mai gida...".

Sai kuma ya mik'o min leather dake hannunsa na amsa na wuce cikin gidan wanda ya kasance mallakin Abbana, gidan yana da girma, ginin kasa ne yana da fluster saidai yaji jiki, gida ne daidai na rufin asiri, ban zame ko'ina ba sai dakin Ummy inda Yaa Ahmad yake zaune yana ma autanmu Affan wasa shi kuma yana wangame baki, Yaa Ahmad ya d'ago da murmushi akan fuskarsa yace,
"Aaaahhhh babynmu an gaji...".

Na zube kasa nace,
"Kai dai bari, indeed na gaji, tun eight fa har four, yanzu ma ai five tayi, wayyo Aallah yunwa...".

Yace, "Bari kiga...".

Sai kuma ya mik'e ya ciko min kofi da ruwa masu sanyi ya mik'o min, nace,
"Yauwa na gode shiyasa nike k'ara sonka our lovely brother".

Yace, "Ke kuma our
lovely sister".

Mukayi dariya na amshi kofin na kafa lips na shanye ruwan tas, nidai a rayuwata ina ma ruwa one love musamman masu sanyi, before idan na dawo daga school kankarar loli nike siya in sha saida Ummy ta cashe min akan shan sanyi sannan na daina....

Ummy ce ta shigo na jawo leather da na amsa wurin saurayin nan, nace,
"Abba ne ya aiko wani mai kyau ya kawo".

Yaa Ahmad ya kalleni, nace,
"Yeah, tou kyanshi ne yayi appearing more shiyasa nace kadda ka fassara ni...".

Yace, "Baby ai ban ce komai ba".
Chapter 7 · 0% Book details