← Book details Ba Ni Da Laifi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 32

Sashe 20

Ba Ni Da Laifi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan Abba ya dawo, Inna ta tusashi gaba ta zayyana mashi komai, ina ji ya rufe Ummy da fad'a, hakuri kawai ta bashi, Inna ta sanar dashi kwana biyu zatayi sannan ta koma....

Zaune nike a dakina nayi zuru, Ummy ta shigo ta zauna kusa dani ta dubeni da damuwa tace,
"Mariam kin san dalilin da ya saka nayi shiru?

Tou saboda idan nayi magana sai ya zamo cewa tawa tafi zafi amma duk da hakan ban tsira ba saida nayi laifi, don Aallah baby kiyi biyayya ga mahaifinku kadda kiyi silar da saboda rigimar wannan auren ni in rasa igiyoyin aurena wadda nayi shekaru sama da talatin ina tattalinsu...".

Na gyad'a kai kawai, Ummy ta mik'e ta fice, wayata tayi ringing na duba Yaa Mustapha ne, nayi picking yace,
"Baby why are you doing this?".

Nace, "Am doing the right thing ne, bazan bari ina gani innocent Aaryan ya rasa ranshi saboda ni ba, ai bashi da laifi, ai na yarda zan auri Mahmud, ai at least an barni da wannan".

Nayi hanging call din, dukkaninsu wurin Ayan ne kawai nike samun sauki, Nadiya gani take ina neman d'aurawa Ummy ciwo ne inyi silar da zamu rasata, kallonsu kawai nike, ace dukkaninsu mutum daya ne ya fahimceni....
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
*Update Of June, 2019*
In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen
*Eid mubarak our greatest mariam, tou ina nufin masu suna mariam, tou mariam, maryama, mairo, mariya, maryoyi, tou wish you all the best....*
*Hope kinyi sallah lafiya Zaynerb, our greatest zeezee, wish you all the best....*
Page. 18
Washe gari muna zaune wani yaro d'an makotanmu ya shigo wai ana kirana, nace,
"Inji wa?".

Yaron yace, "Mahmud yace...".

Nace, "Je ka kace gani nan fitowa".

Na mik'e zan suri hijab, Inna tayi sororo tana kallona sannan tace,
"Kee dakata ina zakije a haka...".

Sai kuma ta kwalawa yaron kira tace,
"Kace yayi hakuri zata shirya".

Sai kuma ta dawo kaina tace,
"Da ace ba ni kusa a haka zaki fita, tou wuce maza kiyi wanka ki shirya, saura kuma inga kin zunbula hijab...".

Saida nayi wanka sannan na shirya nayi applying lipstick gudun kadda ta koroni tace sai nayi kwalliya, na saka wasu riga da zani na atamfa tareda yafa veil na zura takalma flat, tou vaseline kawai na shafa na goge fuskata na shafa powder nayi applying kwalli then lipstick amma nayi kyau sosai, na wuceta a tsakar gida tace,
"Ko kefa saura kije kiyi mashi rashin kunya ki dawo in casaki a gidan nan".

Na fice na hangoshi jingine da mota yana sanye da kananan kaya, jeans da shirt mai wani irin neck, ina yawan ganinta a series, shirt din design ce mai kyau, na karasa tareda tsayawa gefenshi nayi mashi sallama ya amsa, nace,
"Ina wuni?".

Mahmud yana kallona yace,
"Lafiya lau...

Ya kike?".

"Lafiya lau....".

"Shopping zan kaiki...".

"Saidai bana hawa motar samari".

Mahmud ya ware idanu sannan yace,
"Shi kuma da kike shiga tashi...".

"Wannan kuma daban...

Kayi kyau...".

Smile ne ya sub'uce akan fuskarsa yace,
"Na gode...

Kema kinyi kyau...'.

Nayi dariya kawai, yace,
"Ina son wannan dariyar...".

Nayi murmushi sannan nace,
"Idan kana so kawai kayi min magana zanyi maka".

Yace, "Ya su Ummy?".

Nace, "Suna nan lafiya lau, Inna ma tazo...".

Gani nayi ya dafe goshi, yace,
"Ohhh gashi kuma kananan kaya na sanyo amma da daddare zan shigo in gaidata...".

Nace, "A'a yanzu dai, bari kaga inyi mata magana...".

Ya ware idanu na kwashe da dariya, yace,
"Rufa min asiri....".

Nace, "Asirinka a rufe yake...".

Ya bud'e mota ya zaro kwalin waya iPhone 8 tareda mik'o min yace,
"Gashi na sawo maki...".

Na kalli gefe kawai, yace,
"Amsa.....".

Nace, "I like sumarka, tayi kyau".

Mahmud yayi murmushi, mun jima sannan ya wuce na juya na koma gida, bayan sallar isha'i sai gashi yazo gaida Inna, fita nayi na shigo dashi, lokacin da ya fita ta hau ni da fad'a kamar zata dokeni....

"Yaron kirki, bashi da damuwa amma kike mashi wulakanci saboda wani can shashasha....".

Saida naji babu dadi akan abun da ta fad'a akan Aaryan, wani yaron makotanmu ne ya shigo da katuwar leather na amsa na mik'a mata nace,
"Naki ne, inji Mahmud...".

Na wuce daki ina ji tana zunduma mashi albarka, yanzu kam na ware da Mahmud, idan ya kira zan dauka idan yazo zan fita kuma bana mashi magana mara dadi saidai bana amsar abun hannunshi, indeed ni ba mayyar kudi bace, bayan kwana biyu Inna ta wuce, damuwa tayi min yawa amma tun daga wannan lokaci na yanke shawarar bazan k'ara sawa kaina damuwa ba, gab nike da fara zana jarabawata ta karshe a jami'a ga project da nike rubutawa, idan na saka wasa zan lalata CGPA din da nayi shekaru ukku ina tattalinsa, wannan yasa na cire kowace damuwa daga raina, dukkanin abun da ya faru a inda ya faru a nan nike barinshi, tou the more Aaryan yazo gidanmu the more zan fita the more kuma idan Yaa Ahmad ya gammu zai kwasheni da mari, nasha maruka marassa adadi amma ban damu ba, Aaryan ba ya jin dadin abun da yake faruwa amma koda yayi niyyar kasancewa away from me bazai iya ba, wani lokacin ji yake idan bai ganni ba yana iya mutuwa, ni idan har ya kirani yace yazo tou zan fita saidai na lura idan yaga ina tareda Mahmud komawa yake ko kuma yayi parking gefe, yana kirana a waya musha hira, gulma iri-iri a unguwarmu, unguwa ta dauka cewa ga wanda aka saka min biki dashi amma har yanzu ban daina kula saurayina ba, ko'ina surutun ake, nikam ta exam dake gabana nike ga kuma project da nike rubutawa....

Ranar wata laraba Nadiya tazo mamu wuni, muna zaune tace,
"Baby abun da kike sam bai dace ba, ai at least tunda kin san Mahmud zaki aura sai ki daina kula Aaryan, haba, abun yayi yawa, kina sakawa mahaifiyarmu damuwa, ai koni da nike k'anwarki ba zanyi haka ba".

Na dubeta na saki murmushi sannan nace,
"Nadiya na ce ke wanda kike so kika aura?

Ni kuma anyi min dole kuma na yarda zan auri Mahmud...

Ummy kuma gatanan saboda ita na kwantar da hankalina akan wannan auran...".

Daurin kirji ne kawai a jikina, wayata ce tayi k'ara ina dubawa naga Aaryan ne, picking nayi tareda kangawa a kunne, nace,
"Ina jinka Aaryan...

Shikenan gani nan fitowa...".

Nadiya ta zaro idanu tana kallona, na mik'e tareda shiga daki na zura long hijab na fito, Nadiya tace,
"Baby ina zakije?".

Nace, "Wurin Aaryan...".

Sannan nayi mata wani kallo na fice, lokacin da na dawo na tarar da Yaa Ahmad a tsaye fuskarsa a murtuk'e, kallonshi nayi zan wuce daki ya jawoni tareda kwasheni da mari saida hijab dake jikina ta d'age....

Yaa Ahmad ya ware idanu yace,
"Yanzu saboda baki da kunya haka kika fita daga ke sai daurin kirji".

Sai kuma ya cigaba da jera min mari a baya, Nadiya tace,
"Baby ki bashi hakuri mana...".

Nayi banza da ita, tace,
"Yaa Ahmad kayi hakuri...".

Yayi banza da ita, dakyar ta shiga tsakaninmu, yayi kwafa sannan ya wuce dakinshi, Ummy kam idanu ne nata, ina durkushe ina kuka, Nadiya tace,
"Ai kinga abun da kika jawa kanki...".

Ta wuce kitchen ta kawo min ruwan zafi, tace,
"Ki saga kuncinki...".

Wani kallo nayi mata na suri kwanon na wuce dakina, nayi zuru ina gasa kuncina, abunku da farar fata, fingers dinsa suka fito suka kwanta tareda appearing akan both cheeks dina....

Bayan kwana biyu ina sanye jeans da shirt ina duba note, Aaryan ne ya kirani nayi picking yace,
"Please baby ki fito ina akan titin unguwarku...".

Na mik'e da sauri na zura long hijab na fice a rud'e gani nike wani abun ne ya sameshi, ina fitowa bakin titi na hango motarshi na karasa tareda bud'eta na shiga, Aaryan ya dubeni cike da damuwa yace,
"Kiyi hakuri Baby I feel....".

Sai kuma yayi shiru yana kallon wani wuri, nima da sauri na kalli inda yake kallo zaro idanu nayi ganin Yaa Ahmad ya nufo motan, da sauri na fito nayi santarmu ina taking steps da sauri-sauri, ina shiga gida nayi tsaye ina maida lumfashi, Yaa Ahmad ne ya shigo tareda kwasheni da mari, ya k'ara min wani, na fashe da kuka, salati yayi yana kallona sannan yayi kwafa yace,
"Nasan maganinki...".

Ya wuce ya barni a durkushe ina kuka....

Washe gari ina zaune nayi picking call dinshi, Aaryan ne, daga daya bangaren yace,
"Baby kiyi hakuri amma ke kawai nike son gani, bana son in k'ara jawo maki damuwa, ina son ganinki amma bazan iya zuwa gidanku ba...".

Sai kuma naji yayi hanging call din, nayi shiru ina tunani, ji nayi Ummy tana kirana na amsa sannan na fito da sauri tareda zama kusa da ita, tace,
"Baby ya kamata ace kin lek'a gidan Nadiya tana yawan min korafin bakya son zuwa gidanta...".

Nace, "Kuma gobe zan shiga school in kai project dina amma bari in shirya yanzu in wuce sai inyi mata wuni...".

Ummy tace, "Hakan yayi....".
Chapter 20 · 0% Book details