← Book details Ba Ni Da Laifi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 32

Sashe 26

Ba Ni Da Laifi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Na rik'e kugu sannan na kalleshi idanu cikin idanu nace,
"Samuna tayi har gidanmu ta jefeni da kudi bayan ta fad'a min bakaken maganganu ta zageni sannan yanzu ta biyoni har gidan mijina tana min gadara shiyasa nayi mata dukan tsiya, tsaya ai har bina tayi bus stop ta jefeni da kudi ta zageni, Alhamdulillah wancen karon an shigar min tasha mari, hot one kuwa...".

Mahmud ya daka min tsawa yace,
"Keh wannan wacce maganar banza ce, kina hauka ne zaki kama d'iyar mutane ki jibga, nace uban mey tayi maki kika doketa...".

Haushi ya bani nace,
"Kai daina min ihu a kai, ita da na buga kaje ka tambayeta mana ai itama zatayi maka bayani tunda itama ai tana da bakin magana...".

Ya d'aga hannu kamar zai dokeni yace,
"Nace uban mey tayi maki kika doketa".

Nace, "Kai tsaya idan kai ubanta yayi maka wankan arziki ne kana tsoron kadda don na bugeta ya amshe abunsa, tou ni bana buk'atar komai a wurinshi don haka duk er iskar da tazo gidan nan tayi min iskanci sai na casata...".

Yace, "Kehh...".

Nace, "Ehh....".

A tsawace yace,
"Tambayarki nike...

Uban mey tayi maki kika doketa?".

Saida na dubeshi idanu cikin idanu sannan da karfi nace,
"Ubanta ya saka na bugeta, mai dirty cap...".

Mahmud ya dubeni a fusace sannan ya d'aga hannu ya kwasheni da mari, na durkushe tareda fashewa da kuka, ya juya kawai ya fice, ina kuka har da majina na mik'e na wuce sama tareda jawo wayata na dannawa Yaa Ahmad call, yana picking na k'ara sound din kuka na, kuka nike har da majina, ya rud'e yana tambayata abun da aka yi min, saida naci kukana na gaji sannan nace,
"Tunda kun nuna mashi ya fini a wajenku ai duk abun da ya gadama yi min zaiyi, ka mareni a kanshi gashi yanzu shima ya dora a kai, cousin dinshi har gida ta bini tayi min rashin mutunci ta jefeni da kudi sannan ta bini har bus stop tayi the same thing amma daga yau tazo tayi min rashin kunya na nuna mata iyakarta shine ya mareni kamar yadda kasha marina a gabanshi kuma saboda shi, ai dama tunda yaga baku sona aikuwa sai abun da na gani a gidanshi, wato er uwarshi itace d'iya ni kuma daga bishiya aka tsinkoni".

Nayi hanging call din tareda fashewa da kuka, ina gani yana danno call nayi banza da wayar banyi picking ba, ashe kiran Mahmud yayi sukayi mahad'a, Yaa Ahmad yana zuwa ya d'aga hannu ya kwashe Mahmud da mari sannan yace,
"Na bugeta na mareta saboda nasan kai mutumin kirki ne zaka riketa saboda Aallah amma wannan bazai baka damar wulakantata ba, ina sonta, muna matuk'ar sonta itama d'iya ce".

Sai kuma ya juya ya wuce yabar Mahmud tsaye yana dafe da kuncinsa abunka ga fari har yatsu sun fito tar akan kuncinsa, nikam a lokacin ina zaune daki ina kuka can na mik'e na wuce bathroom na tara ruwan zafi na gasa cheek dina sannan na koma parlour ina matsar hawaye, Mahmud ne ya shigo ya zauna, kallo daya nayi mashi na lura da yatsu da suke kwance akan fuskarsa, a nan take abun da ya faru yazo min a brain, na fashe da dariya tareda mik'ewa na wuce toilet dake parlour na wanke fuskata na fito na tusashi gaba ina dariya har da rik'e ciki, nace,
"Aaahhh wato kai mai er uwa na bugeta ka mareni, tou ai nima ina da d'an uwa kuma ya rama min...".

Yayi shiru, na k'ara fashewa da dariya sannan nace,
"Aaahhh yasha mari, wai da a tunaninka ka mareni ka mari banza ka mari wofi, impossible, Aaahhh kato dashi yasha mari...".

Kanshi a kasa har yanzu baiyi magana ba, ina d'agowa na hango k'anwarshi Safeena a tsaye tana kallona idanu a waje, d'agowa yayi ya kalleta sai kuma ya ware idanu yana murmushi, nayi mata wani kallo na mik'e na wuce kitchen tareda bud'e fridge na dauko drinks da apples na jera a tray na wuce garden na zauna akan shillo ina kallon comedy ina kwasar dariya ina gutsirar apple ina korawa da drinks, can Safeena ta fito tareda karasowa inda nike tana kallona tace,
"Aunty Mariam na tafi...".

Na dago ina kallonta nace,
"Ohhh har zaki tafi, tou ki gaida gida kinji, idan direba yana nan kice mashi nace ya kaiki gida...".

Safeena ta kalleni sai kuma ta juya ta wuce, haushinta nikeji, cikin raina nace,
"Kema kin ci sa'a ne, da yanzu nayi maki dukan rakawa da kikayi aka yi min rashin mutunci...".

Saida na shan dariyata da comedy sannan na koma ciki....

Da daddare ya kwana dakinshi na kwana dakina, I feel babu dadi ga kadaici....

Washe gari na tashi ban ganshi a gidan ba, ashe zuwa yayi ya samu Yaa Ahmad suka daidaita kansu....

Da rana ina zaune a parlour ina kallon series ya shigo ya kalleni yace,
"Zo mu je sama...".

Idanuna suna akan kallon da nike nace,
"Azumi nike...".

Ya ware idanu yace,
"Amma a matsayina na mijinki ai dole ne ki fara sanar da ni".

Nace, "Sorry mantawa nayi...".

Kallona yayi sai kuma ya juya ya fice, ashe tarani yayi saida ya bari na kai azumin nasha ruwa nayi both sallar magrib da isha'i sannan ya nuna min kurena yayi min nashi hukuncin, I feel banyi mashi abun da nayi mashi ba, wannan ai mugunta ce tareda fin karfi, nasha wahala....

Washe gari bayan na gama had'a breakfast ya sauko mukayi ya mik'e na rik'e hannunsa nayi rau-rau da idanu nace,
"Please kayi hakuri..."
Kallona yayi yace,
"Bamu da damuwa yanzu, kinyi min nayi maki, one-one".

Sai kuma ya juya ya wuce sama ya shirya ya sauko yayi min sallama ya wuce, ina zaune Jalila ta kirani tana fad'a min zasu shigo ita da en course dinmu, da murnata na shiga kitchen na had'a masu delicious food tareda zobo na zuba mashi ice cube sannan na jera komai akan dinning table na juya na haye sama nayi wanka tareda saka wata black arebian gown mai adon skin din damisa, na tamke kaina da veil na sauko kasa, suna shigowa na mik'e tareda rugawa da gudu nayi hugging dinsu ina ihu tareda tsallen murna, bindawa tace,
"Kai amarya kin sha kamshi kinga kuwa yadda kikayi wani fresh dake, da alama d'an unguwarmu yana kula dake yadda ya kamata, miye sirrin?".

Nayi rolling idanu nace,
"Sirrin na matan aure ne ke kuma en mata ce, tou bazan fad'a maki ba".

Muka kwashe da dariya nayi masu jagora ciki muka ci abinci muka kora da zobo muka sha hira mukayi sallah sannan na sake wani sabon wanka na saka wasu riga da skirt na atamfa, rigar wrapper ce and hannun d'an short ne sannan a gaban rigar daga sama a tsakiya zuwa gefe an ratsa wani design, while skirt din yake pieces, powder kawai na shafa nayi applying kwalli da lipstick, na daura kallabi tareda zura takalma muka wuce garden muka sha hotuna da selfie kala-kala, iri-iri, design daban-daban, naba bindawa wayata ta daukeni ni da Jalila muna tsaye, aka yi min da Bintu, akan chairs muka zauna mukayi having hilarious moment yadda ya kamata can naja Jalila muka wuce sama muka barsu a parlour suna kallon series, bedroom dina muka wuce muka zube akan gado, tace,
"Baby kinji dadinki, kinyi kyau...".

Nace, "Na gode...

Ya sweety?".

Tace, "Yana nan qalau yana gaidaki...".

Nace, "Ina amsawa, sweety mutumina...

Jalila kin san mey?".

Jalila tace, "A'a sai kin fad'a...".

Nace, "Ashe hakanan na dauki alhakin Mahmud bashi da laifi, bari in kunna maki recording din kiji, ki saurara da kyau, ashe wani yake ma magana bani ba".

Na jawo wayata na kunna mata recording din ta ware idanu tana saurare yana karewa tace,
"Hakane, ashe bashi da laifi, har na fara jin kunyarshi, Aallah yaso banyi mashi rashin mutunci ba...

Ya fita ne?".

Nace, "Ehhh tunda safe ya fice...".

Na kirashi na fad'a mashi zuwansu, nayi hanging call din, nace,
"Jalila kin san Mahmud bashi da kunya, don rashin kunya ya dauki bed sheet na first night dinmu ya kaima Ammi ta kira tana ma Ummy godiya, Ummy ta kirani tana tambayar dalili, ita kanta Ummy saida taji kunya da na fad'a mata...".

Jalila ta kwashe da dariya, nace,
"Wannan container din kunyar har ina...".

Jalila tace, "Baby...

Wai container din kunya...

Ahhhh....".

Ta fashe da dariya, saida naji haushi sannan ta daina muka sauko kasa na had'o masu kayan snacks da kayan makeup, Jalila ta sake sabuwar mota mai kyau muka fito na ganta na nuna masu motocina guda hudu, muka koma ciki, suna gab da tafiya Mahmud ya dawo, dukkaninsu mutanenshi ne, babu wacce bai sani ba, ya zauna aka sha hira da dariya, lokacin da suka tashi tafiya ya basu kudi muka rakasu har wurin motocinsu, tou da motoci ukku suka zo, saida motocin suka fita daga get sannan muka koma ciki ya zauna saman kujera tareda jawoni jikinsa ya kashe mamu selfie, na lura dashi yana son daukarmu hoto don the more nayi wanka the more zaice baby zo inyi mamu selfie....
Chapter 26 · 0% Book details