← Book details Ba Ni Da Laifi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 32

Sashe 31

Ba Ni Da Laifi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yace, "Nima bazan maida ba...".

Nace, "Please....".

Yace, "A'a....".

Na dubeshi kamar zanyi kuka nace,
"Tou na yarda...".

Smile ya saki ya kanne min ido guda sannan ya maida glass din yayi pillow da cinyata yana kallona ina kallonshi, the more nike kallonshi the more yake appearing more cute, hot and sexy, can ya mik'e ya sureni yayi sama yana taking steps ina kallonshi, tou nayi shiru dai, ai bance komai ba....

Satinmu biyu muna jin dadinmu ya kaini gidansu muka wuni kuma ya kaini gidan Mom, gaskiya naji dadin wannan ziyara sosai, sun nuna min kauna marar adadi, Umma har godiya tayi min akan kalubale da na shanye akan Aaryan, tace,
"Haka zaizo yana kuka yana fad'a min bai jin dadin abun da ake maki saidai bazai iya barin zuwa wurinki ba, wani lokacin ji yake kamar idan bai ganki ba zuciyarshi zata buga, yasha kwana akan cinyata yana kuka ina rarrashinsa, ban da kika cigaba da kulashi da watakila mun rasashi....".

A lokacin ji nayi kamar inyi hawaye, rayuwa kenan yanzu komai ya wuce kamar ba'ayi ba, naso ince mun tafi da Abba saidai na lura Umma tana jin dadin zamanshi shiyasa nayi shiru, daga baya ne mukaje gidanmu har ciki ya shiga nayi mamaki sosai akan yadda naga ya saki jikinsa, ya jima don har abinci yaci sannan ya wuce, da marece Abba yana dawowa yace in shirya in koma gidan mijina, nace shine zaizo ya daukeni, sai bayan sallar isha'i sannan Aaryan ya dawo ya daukeni muka wuce kuma ohhh ashe na daina fad'i saidai inyi sub'utar baki, Mom ta bani expensive car hakanan Umma itama ta bani expensive car, shima ya siya min mota kirar Benz da system kirar kamfanin apple da kuma waya latest version din iPhone tareda iPad, time to time yana min depositing din kudi, tare muke bitar hardarmu, idan tawa ta samu damuwa ya tusani gaba in gyara hakanan idan tashi ta samu damuwa in tusashi gaba ya gyara....

Ranar asabar yana zaune a garden yana karanta news paper yayinda nike kwance nayi pillow da cinyarsa ina kallo a iPad dita, a hankali na zare earpies dake kunnena nace,
"Heartbeat ya labarin Ummu-Abba (Aalima) har yanzu shiru?".

Aaryan ya dubeni yace,
"Wai Aalima?".

Na gyad'a kai, yace,
"Aalima ta wuce london medical checkup daga nan zata wuce Dubai tayi shopping tana sone ta bamu lokaci muyi enjoying amarcimu...".

Nace, "Uhmm...

Uhmm...".

Yace, "Kilbabba kamar ba d'azu ta gama min...".

Na ware idanu, yace,
"Tou na fasa bazan fad'i ba, kiyi farin ciki...

Aalima jiya nayi waya da ita tana tare dasu Adla...".

Nace, "Aallah sarki twins dinmu Adila da Adla, our greatest doctors to be, ina waya dasu amma ita har yanzu bani da numbarta, ka bani...".

Yace, "Ko jiya saida nace in baki tace a'a tafi son sai ta dawo sannan ku gaisa yadda ya kamata, mu zauna muyi having hilarious moment...".

Saida gabana ya fad'i, wasu lokuttan har mantawa nike da ina da kishiya aw abokiyar zama, koda yake our greatest soffi tace wata ce kishiya wata kuma abokiyar zama ce, wasu ne suka b'atawa wasu suna, sai kiji ana cewa kishiya this and that, maganganu dai daban-daban, duk da na kirkin suna da yawa amma na banzan sunfi kaurin suna, mik'ewa nayi tareda ajiye iPad dina akan table na dauki igiya ina tsallen igiya (after) ina murmushi ko lokacin da nike yarinya ina son tsallen igiya, tun brothers dina suna kad'a min ina yi har na koma ina kad'a abuna da kaina, nifa har kad'a taya nayi kuma nayi wasan dokin icce da jan mota amma cikin gidanmu, ina son buga game a lokacin kuma brothers dina ne suka siya min, tou ina wasa irin na mata amma nafi son na maza, k'awayena sukan ce min idan na sake zan zama ta maza, na kance naji tou miye ai brothers dina duka maza ne, brothers dina suna yawan goyani a baya, wani lokacin har maka wuya suke min, suyi min doki, dukkaninsu sun iya er carafke saboda ina sonta, wasu lokuttan da gangan suke faduwa suna bari ina cinyesu, ina son wasan jirgin leather musamman wanda ake sakawa asaberi, wow, saidai su tadashi kololuwa su bani idan ya samu damuwa tou babu b'ata lokaci zasu sauya min wani....

Ina tsallen igiya ina murmushi a dalilin tunawa da nike da happy moment da na samu tareda brothers dina a lokacin da ina yarinya, the more nike tunawa da wadannan lokuttan the more nike smile more and more.....
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
*Update Of June, 2019*
In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen
*Eid mubarak to you all Muslim all over the world, Aallah ya albarkaci rayuwarku, wish you all the best....*
*Hope kunyi sallah lafiya dearies, wish you all the best....*
Page. 28
Last page
Aaryan ne ya ajiye news paper dake hannunsa yayi taking steps zuwa inda nike tareda rik'e hannuna kallonshi nayi ya kalleni idanu cikin idanu sai kuma ya amshi igiya dake hannuna, muna kallon juna idanu cikin idanu yayinda yake kad'a mamu igiya muna tsalle a tare a lokaci guda, can ya saki igiyar ya sureni yayi ciki, tou an dai hanani fad'i....

Ina enjoying zama tare dashi, yanzu kam matsewata nike in saka guntun skirt, in saka guntun wando, in saka guntuwar gown, tou mey yafi raina ai gidan mijina ne, a wasu lokuttan muna fita tare....

Aalima ta dade abroad sannan ta dawo, har part dinta naje nayi mata sannu da zuwa kuma ta tarbeni da fara'arta....

Aaryan ya had'a mu yayi mamu nasiha tareda raba kwana, tou kwana biyu-biyu zai rinkayi, kowace zatayi girkinta ne amma duk wadda ranar girkinta ya kama ranar jumu'ah tou tare zatayi mu hadu a sashensa muci a tare sannan zamu rink'a fita ziyara, lokacin da zai wuce wurinta da daddare kuka na saka mashi saida ya lallab'ani nayi bacci sannan ya tafi, ina farkawa tsakar dare naji ban ji ni a jikinsa ba, na laluba inda yake kwanciya naji wayam yayinda komai ya dawo min a brain, fashewa nayi da kuka, saida nayi nafila da karatun Alk'ur'ani mai girma sannan na samu na dawo daidai, babu b'ata lokaci bacci mai dadi yayi awon gaba dani....

Da asuba ya lek'o ni hakanan da zai wuce wurin aiki kamar kadda ya tafi har so yayi ya makara, kun san wani abun dariya har uhmm naso inyi mashi ya gudu, aw ashe na daina fad'i koda yake ai ban ambaci suna ba, kuma babu wacce zata iya guessing....

Ina zaune a parlour ina kallo, Aalima ce ta kawo min kaya, ashe komai biyu ta sawo ni da ita hakanan har Ummy tayi ma tsaraba, sai duk naji kunya ta kamani ni da na rinkayin shopping dina ni daya, zama tayi muka sha hira abunmu mukayi having hilarious moment yadda ya kamata daga baya ta koma sashenta, cikin wadannan kwanaki nayi missing Aaryan sosai aiko har henna nayi, idan ya dawo daga aiki zai shigo girkina ya fara kenan wannan itace ka'idar don haka delicious food na girka kuma favourite dinshi kuma bazan fad'a maku girkin ba ballantana wata tayi min snatching, hhhh lols, na jera komai akan dinning table, na cire apro na wanke abubuwan da na b'ata na jerasu sannan na dauraye hannuna na fito na wuce sama na jima cikin kumfa mai kamshi ina wasa dashi sannan na dauraye jikina na daura towel nayi brush before na fito na shirya naci gayu cikin riga da skirt en kanti tareda jawo jelar kitso guda da yayi min ta kwanta akan kirjina kamar dai yadda yake son ganinshi, saida na feshe jikina da perfumes different design sannan na suri veil na zura takalma flat na sauko kasa tareda hakincewa akan doguwar kujera very stylish....

Aaryan ne ya shigo yana sanye da suit yasha zanzaro ga wani cute necktie yana rataye da briefcase a shoulder, he look cute, na saki murmushi tareda mik'ewa na ruga da gudu na d'ane jikinsa yayi sama dani yana jujjuyawa dani muna dariya, ya wuce staircase yana dauke dani, nace,
"Abinci...".

Aaryan ya ware idanu sannan yace,
"Wani abinci kuma?

Kilbibi kawai...

Ni baby rigimarki ba zata bari inci abinci hankali kwance ba, sai na sakaki bacci sannan kuma idan kin manta tou sai nayi wanka sannan nike cin abinci ko?".

Ya wuce sama yana dauke dani, saida ya kwana biyu sannan ya komawa Aalima, zaman lafiya muke ba ya nuna banbanci a tsakaninmu, yana kwatanta yi mamu adalci saidai dole a wani wurin a samu damuwa, Aalima bata nuna damuwa akan wasu abubuwan, ko ta ya abu zai b'ata mata rai bata nuna damuwa, kau da kai take tana hakuri, har mamakinta nike, tana hakuri kuma bata nuna damuwa koda kuwa ba'ayi mata adalci ba, itace jigon wannan zaman lafiya, koda abu ya siyo mamu sai idan ta bani na zab'a sannan ta dauka, daga baya nace mashi ya rink'a sawo iri daya saidai abun da zaiyi ma fari kyau amma ba zaiyi ma chocolate colour ba, ina kwatanta bata girmanta saidai wasu lokuttan ina kwafsawa ita kuma tana hakuri, wasu lokuttan idan ya wuce wurin aiki ina shiga sashenta musha hira, wani lokacin tana rigani zuwa ko kuma mu hadu a garden, idan kuma yana nan sometimes a sashensa muke haduwa, idan Ummy tazo sai ta fara shiga sashen Aalima sannan ta biyo sashena kuma duk abun da zata kawo min tare take bamu kuma iri daya, little Abba kam ya zama d'an gidan Umma tou yafi zama a can, idan yazo kwanaki yake mamu yana komawa, yana kiran Aalima da Ammi while ni kuma yake kirana da Mami, while yake kiran Aaryan da Abbu, ni kuma ina kiran Aalima da Ammin-Abba, while nike kiran Aaryan da yadda little Abba yake kiranshi sometimes ince heartbeat....
Chapter 31 · 0% Book details