← Book details Ba Ni Da Laifi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 32

Sashe 23

Ba Ni Da Laifi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yaa Mustapha ya dubeni sai kuma ya amshi paper din ya saka a pocket din wandonsa sannan ya zaro wayarshi tareda jawoni na kwanta jikinsa ya kashe mamu selfie sannan yaja hannuna muka koma....

Mahmud ya kama hannuna na fizge yayi hugging dina, bayan sun tafi nayi zuru ina tunanin yau ne za'a rabani da gidanmu, na fashe da kuka, wuni nayi ina kuka....

Da daddare bayan nasihohi daga iyayenmu da en uwa, dakyar aka banbareni daga jikin brothers dina na makalkalesu ina kuka suna rarrashina, wata cousin dinmu tana ma Yaa Ayan recording, Aunty Usaina sister din Ummy dake aure a Kaduna ta jani sukayi waje dani ina waiwayen brothers dina ina kuka ina turjewa, ina ji ina gani aka rabani da gidanmu aka sakani mota za'a wuce dani gidan wani, motoci ne jere akan road din wata bayan wata, wasu saidai empty suka tafi, a cikin mota kuka nike har motar tayi parking aka fito dani, katon mansion ne mai girma, komai yaji, an zuba kudi babu k'arya, ina kuka aka jani aka wuce manya-manyan parlours dani aka wuce dani sama aka bud'e wani door aka shiga dani, shine bedroom dina kenan, aka yi min masauki akan gado nayi zuru ina sharar hawaye duk na b'ata heavy makeup da aka yi min applying, ni da k'awayena ne da en mata cousins dinmu muka rage a bedroom din, na d'age lullubi dake kaina, en matan suka kwashe da dariya, na kallesu da mamaki, tou kallona sukeyi suna dariya, Jalila ta mik'o min madubi na duba fuskata ta cikinshi zaro idanu nayi ganin yadda kwalliya ta zazzago ta maidani kamar horror, wani kallo nayi masu na duro daga saman royal bed din na wuce wani door wanda nike tunanin shine bathroom, ware idanu nayi ina kallon bathroom din wanda aka kashewa kudi ba kadan ba, yadda yake kamar a london, na shiga da addu'a na tsaya wurin madubi tareda bud'e famfo na tari ruwa a hannuna ina wanke fuskata saida na wanke makeup din tas sannan ta fito na kwanta akan doguwar kujera, Mahmud ya aiko min da waya, Yaa Ayan ne yake kira, video call yayi min, d'an uwa kenan mai dadi, raba dare mukayi muna video call idan yace zai tsinke ince a'a, saida na fara gyangyand'i sannan yayi hanging call din, na mik'e tareda fadawa bathroom nayi wanka tareda alwalla na fito na bud'e akwati daya da aka zo min dashi don sauran sai daga baya tukunna, wata doguwar gown mai hawa biyu na zura, short sleeves ce, tana da umbrella sannan kamar yadda nace a baya hawa biyu ce saida na saman daga wurin umbrella din a tsage yake, nayi kyau sosai, na had'e gashina nayi mashi gammo na tamke kaina da veil sannan na koma saman doguwar kujera nayi kwanciyata, su Jalila suna akan gado suna hira abunsu suna catching fun, Affan ne ya fad'o min a rai, Aallah sarki lil brotherna lokacin da zanyi bankwana da Ummy da yaga ina kuka shima sai ya fashe da kuka, ina jin en matan suna cewa ga chicken ango ya kawo nayi banza dasu, bacci ne yayi awon gaba dani....

Washe gari muna gama sallar subh na shiga bathroom na murje jikina da sabula masu kamshi sannan na sakarma kaina shower na jawo towel na d'aura tareda karasawa gaban madubi nayi brush sannan na fito na goge jikina tareda drying long gashin kaina na had'eshi da mayuka daban-daban masu kamshi mai sanyi, na shafa cream na goge fuskata nayi applying kwalli kawai, wasu riga da zani na atamfa Super English na saka, dinkakkarta aka sakata cikin lefe, style din ya tafi dani, early in the morning Safeena da wasu en mata suka kawo mamu breakfast mai rai da lafiya, bayan munyi breakfast kowace tasha wanka muka kashe selfie, muka fita balcony dake wajen wani door dake lullub'e da curtain muka sha selfie, wajen karfe sha biyu na k'ara wanka na saka wata bubu ta wani material mai sulbi amma daga gani yana da tsada sosai, abinci mai rai da lafiya suka k'ara kawo mamu, nikam kadan naci....

Da marece nayi wanka na saka wani expensive less, makeup artist tayi min applying makeup na koma kamar wata aljana saboda kyau, nayi alwalla before tayi min kwalliyar, wow amma nayi matuk'ar kyau duk wanda ya kalleni sai ya k'ara, da motoci aka daukemu aka wuce damu gidansu saboda a can ne za'ayi walima, a kuryar Ammi aka wuce dani, ita kam bani da damuwa da ita amma sauran dangin Mahmud tun daga kallon da sukeyi min nasan akwai damuwa don babu wacce takeyi min kallon rahama, wani kallo na daban suke min, suna ganin duk ciwon da Mahmud yayi laifina ne, yana neman mutuwa amma ban tausaya mashi ba, wannan cousin dinshi ce ta shigo da fara'a ta zauna kusa dani tace,
"Our greatest bride kinyi kyau, bari inyi mamu selfie".

Wani kallo nayi mata, ta ware idanu sai kuma ta mik'e ta fice, can ta dawo tana tafiya tana rausaya jiki tace,
"Amaryar Mahmud kinsha kamshi...".

Wani kallo nayi mata ta karaso kusa dani tace,
"Ohhh so sad, tou ya kika iya?

Dole kika aureshi, Ahhh har kin bani tausayi...".

Sai kuma ta mik'e tareda fadin....

"Alright then...

See you...

Bye...

Ki huta...".

Ta juya ta fice tana wani turo baki na kilbibi, an gudanar da komai lafiya, an basu korai wanda iyayena sukayi sannan aka damka masu amanata, murmushi kawai sukayi babu wacce tace ta dauka hakanan babu wacce take min kallon rahama, tunani nike, how zanyi surviving a cikin wannan dangin wanda bana ganin sona a tattare dasu, motoci hudu suka bani, daya Ammi, guda biyu wasu sunaye aka fad'i su suka bani guda daya-daya sai kuma uncle dinshi da ya bani katuwar Jeep, a can nayi both sallar magrib da isha'i sannan Aunty Usaina suka wuce dani gidan mijina, ashe en mata sun amshi kudadensu, dubara sukayi min amma kowace gidansu ta wuce, muna isa nayi wanka na saka wasu expensive kaya, makeup artist tayi min applying makeup sannan ta feshena da different design din perfume masu wani kamshi na musamman sannan ta wuce, Jalila ce muka zo tare itama Jalaludden ya kirata cewa yazo daukarta ta mik'e nayi rau-rau da idanu ta girgiza kai sannan ta wuce, nayi zuru ni daya tunda su Aunty Usaina sun wuce, can naji muryoyin maza har dariyarsu ina jiyowa, wani abu na tuna saida cikina ya bada kululu, yau kam na mutu, tawa ta k'are, Mahmud ne ya shigo yana sanye da wani expensive yard komai fari ya saka looking muah yana zuba wani kamshi mai sanyi, da sallamarsa ya shigo tareda haurowa saman gadon kusa dani, nayi baya da sauri, yace,
"Miye?".

Nace, "Bacci nikeji, ka barni inyi kaji...".

Mahmud ya kunshe dariya sannan yace,
"Naji amma sai idan kinyi duk abun da na umarceki".

Na kalleshi yace,
"Yeah...

Ohhh ashe har yanzu kallon makaryaci kikeyi min, bari in ajiye wadannan kajin, uhmmm fad'a min yadda aka yi na zama makaryaci don ban san mu fara rayuwar aure kina min wani kallo wanda bashi bane, ina son mu fahimci juna".

Na kalleshi sai kuma na jawo wayoyina guda biyu baby Nokia da kamarar waya mai gidan memory, d'ayar na dauka wadda take da memory, na kunnata tareda kunna mashi recording, wayar da mukayi ce wadda yace min shi staff ne, abun mamaki gani nayi ya kwashe da dariya sai kuma ya amshi wayar yace,
"Dama saboda wannan kika cemin makaryaci, *BA NI DA LAIFI* amma kika dauki alhakina, tsaya kiga, ki manta da muryata ki saurari wata murya dake magana kasa-kasa".

Sai kuma ya kunna, muryarshi ce ta soma fitowa yana cewa....

"Kullum ina ganin Abba...".

Then muryata ina cewa....

"Tou ai wurin aikinku daya...".

Then sai naji wata muryar namiji kasa-kasa yana cewa....

"Miye matsayin Muneer a ma'aikatar?".

Then Mahmud yace,
"Ai staff ne...".

Kusan lokaci mukayi magana ni da daya muryar namijin, nace,
"Ohhh kai staff ne?".

Yayinda daya muryar dake fita kasa-kasa tace,
"Ashe staff ne...".

Then Mahmud yace,
"Ehhh staff ne...".

Mahmud ya kashe recording din yace,
"Yanzu na wanke kaina, ni ba makaryaci bane, uhmmm".

Na zaro idanu ya ja kumatuna tareda sakin murmushi yace,
"Baby rigima....".

Sai kuma ya rik'e hannuna ya zubawa tafin hannuna idanu kamar wanda yake karanta handout mai kananan rubutu, na kalleshi, yace,
"I like this henna...".

Ya kalli kafata yace,
"Har da na kafar...".
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
*Update Of June, 2019*
In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen
*Eid mubarak our greatest twins, Hafsat and Ummulkhairi, Aallah ya albarkaci rayuwarku, wish you all the best....*
*Hope kunyi sallah lafiya dearies, wish you all the best....*
Page. 21
Na dubeshi ya d'ago ya saki murmushi yace,
"Kinyi kyau...

You look muah...".

Sai kuma ya yaye veil dake kaina tareda janye kallabin da na tamke kaina dashi, ya warware gashina yana wasa dashi, yace,
"Ina son gashin nan, ashe haka yake da tsayi sosai, da alama idan kika tashi tsaye zai iya wuce gwuwarki".

Ya jawo waya ya kashe mamu selfie, da wayo da dubara ya cire both jeweleries dake jikina, sannan ya mik'e yace,
"Wayarki tana bedroom dina, da safe zan baki ita...".

Ya cire kayan dake jikinsa ya rage daga shi sai d'an karamin wando (skin tide karami), ni kunya naji na rufe idanu, tou bashi da riga daga shi sai wannan d'an guntun wando, duk da brothers dina suna zama da boxer amma basu yawo babu riga, a rayuwata ban tab'a ganin babban namiji a haka ba, ji nayi ya sureni, idanuna a rufe na soma dukanshi a kirji ina mutsu-mutsu, ina bud'e idanuna ya bud'e bathroom ya shige da ni, duk rigimata amma saida ya danneni yayi min wanka, saida mukayi alwalla sannan muka fito ina turo baki daga ni sai guntun towel daidai kugu, farar jallabiya ya zura ya jawo wata farar half gown yayi min dropping dinta yace,
"Ki saka...".
Chapter 23 · 0% Book details