← Book details Ba Ni Da Laifi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 32

Sashe 29

Ba Ni Da Laifi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon gefe nayi tareda maida hawayen dake neman zubo min sannan na juya na dubeshi nace,
"Idan kana ganin ya kamata inyi auren tou zanyi amma na baka zabi, ka zabar min da kanka, na tabbata ba zaka zaba min mijin banza ba".

Kallona yayi sai kuma ya mik'e ya fita, Yaa Ayan ne ya shigo nayi pillow da cinyarsa nayi kwanciyata, bacci ne yayi awon gaba dani, Yaa Ayan yanzu babban likita ne wanda ake ji dashi a kasarmu nageria da sauran kasashen duniya, ya kware sosai, kudi sun zauna mashi, komai nike so babu b'ata lokaci yake yi min, shima Yaa Mustapha kwararren likita ne sosai, fiye da tunani, shima kudi sun zauna mashi, shi kam ba ya jira ince ina so yana ganin abun da zaiyi min zai siya min komai tsadarshi kuwa, shima Yaa Ahmad bashi da damuwa, sakar man kudi yake sosai, yanzu su ukkun sune suke komai na gidan nan, shekarar data wuce suka biya ma Ummy da Abba aikin Hajji (pilgrim), nima cikin ramadan naje Umrah tare dasu har da Nadiya, nasan dalilin da ya saka Yaa Ahmad yayi min wannan maganar saboda mutane suna ta fitowa har da samari amma bana kula kowa....

Bayan kwana biyu ina zaune ya shigo, yace,
"Baby maganar da mukayi na samar maki mijin, yaushe zaizo ki ganshi...".

Da sauri na girgiza kai sannan nace,
"A'a ni bani da damuwa akan sai na ganshi, idan har don nice tou yayi zamanshi na hutar dashi, idan kuma shine zai ganni tou...".

Yaa Ahmad yace, "A'a ai shi ya sanki, daman saboda ke ne...".

Nace, "Then na hutar dashi...".

Yace, "Alright then, good girl, babynmu...".

Mahmud ne ya fado min a rai, yana yawan kirana good girl ko kuma yace baby rigima zo in baki madara in rirrigaki kiyi bacci, duk sai naji babu dadi amma duk da haka saida na saki murmushi zuwa yanzu idan naga hotonshi ko kuma na tuna happy moment da muka samu sai inji na saki murmushi, shiyasa wani sa'in hakanan saidai a ganni na saki murmushi, bayan sati biyu ya sameni yake sanar dani biki nan da wata daya, hidimar biki ake sosai, tou Yaa Ahmad ya fada min angon yace yana da komai, tou ni dayata za'a kaini, koda aka kawo lefe ina daki, lefe kamar na budurwa akwati rabin seti, akwati shidda kenan, akwatu nan expensive ne irin masu high price din nan kuma latest, kayan dake cikinsu dukkaninsu expensive ne, kowa ya gani saidai yace Maa shaa Aallah, wannan biki no party no bidia, wa'azi kawai za'ayi a gidanmu, tun before satin ciki nayi gyaran jiki in side and out side tareda sauran abubuwan da suka dace, tou ni koda invitation card ban gani ba, tou koda sunan angon ban sani ba (our greatest fans wa kuke tunanin Baby zata aura?)....

Ranar jumuah aka d'aura min aure da angon da har yanzu ban sanshi ba, ban san waye ba, tsoho ne ko yaro ban sani ba, saurayi ne ko babban mutum ban sani ba, matanshi nawa ban sani ba, tou a ranar ne aka wuce dani, gidan part ukku gareshi amma dayan karami ne da alama na mai gidan ne, aka wuce dani part dake gefe babba ne sosai don yafi wanda aka fara kaini, banbancin a bayyane yake, wani katon bedroom dake saman bene suka wuce da ni, ina ji ina gani kowa ya watse aka barni ni daya, gidan yayi shiru, can na soma jiyo sautin takon takalma sannan ya turo kofa ya shigo da sallama, zaro idanu nayi jin muryar da tayi sallama, Aaryan ne tsaye yana kallona, da sauri nayi baya jikina yana rawa, tsoro nikeji, gani nike abun da ya faru laifina zai gani, zaiga nayi broken heart dinshi ne, muryata tana rawa nace,
"Don Aallah kayi hakuri sam ni *BA NI DA LAIFI* a lokacin ban san maganar auren tana nan ba shiyasa na kulaka...".

Aaryan ya kalleni sai kuma ya juya ya fice, na zauna ina maida lumfashi, a tsorace nike sosai, duk da mun rabu lafiya amma gani nike laifina yake gani yana jin haushina, gidan shiru babu motsin kowa, dukunkunewa nayi a gefen gado jikina yana rawa, can na kwanta tareda dukunkunewa wuri guda naja blanket idan bacci ya figeni na farka sai inji tsoro ya k'ara kamani in dukunkune jikina yana rawa, tunda asuba na tashi nayi sallar subh sai kuma nayi zuru ina kallon wall watch can na mik'e na shiga bathroom nayi wanka ina fitowa....
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
*Update Of June, 2019*
In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen
*Eid mubarak our greatest auta umarsanda, Aallah ya raya mamu kai...

Aameen....*
*Hope kunyi sallah lafiya dearies, wish you all the best....*
Page. 26
Nayi jim sannan na karasa gaban mirror na shafa cream nayi applying powder sannan nayi applying kwalli da lipstick, na zura wata cute arebian gown purple kamar bubu take, na tamke kaina da veil, na juyo nayi tsaye ina kallon bedroom din duk da na shiga gidaje na alfarma naga bedrooms kala-kala amma ban tab'a ganin wanda yayi koda quarter din kyanshi ba, daga gani an zuba naira over, komai na bedroom din abun kallo ne, fitowa nayi na sauko kasa nayi tsaye ina karewa parlourn kallo, tabbas tunda nike ban tab'a ganin mansion mai kyau da girman wannan ba, na wuce kitchen na zage na had'a delicious breakfast na jera komai akan dinning table, nayi tsaye ina kallon stairs, Aaryan ne ya sauko yana sanye da farar jallabiya saida gabana ya yanke ya fad'i, ya karaso ya ja kujera ya zauna na juya nayi serving dinshi before nayi serving kaina sannan naja kujera opposite dashi na zauna, ina having breakfast ina kallonshi saidai har ya gama ya mik'e ya koma sama ban had'a idanu dashi ba, saida na tattara abubuwan da muka b'ata na wuce dasu kitchen na wanke sannan na koma sama na soma bud'e door ina neman bedroom din da yake, ina bud'e wani door na hangoshi kwance yayi relaxing akan kujera idanunsa a lumshe, a hankali na karasa tareda rik'e hannunsa nace,
"Please kayi hakuri...".

Aaryan ya bud'e idanunsa ya kalleni, wani kallo yayi min sannan ya maida idanunsa ya rufe, na dubeshi kamar zanyi kuka, nace,
"Please mana *BA NI DA LAIFI* ai ban san maganar auran tana nan ba shiyasa na kulaka...".

A hankali ya bud'e idanunsa yace,
"Baby wato so kike dole sai kin b'ata min rai, ai na san baki da laifi kuma na san kinyi min halarci, jiya na shigo da farin cikina amma kika b'ata min rai, kin san mey yasa na juya na fita saboda bana san ganinki cikin damuwa...".

Sai kuma ya maida idanunsa ya rufe, fadawa nayi jikinsa ina dukan kirjinsa, yasa dariya yana rikeni ina fizgewa sai kuma ya dafe kirjinsa, na zaro idanu tareda d'agashi, ya kwashe da dariya ya mik'e saidai ji nayi yayi sama dani yana jujjuyawa dani muna dariya sai kuma ya direni akan gado, ya hauro tareda pillow da cinyata, yace,
"Baby hira zamuyi amma idan karfe sha biyu da mintina arba'in tayi kiyi man magana...".

Na gyad'a kai, yace,
"Kin san mey?

Lokacin da Yaa Ahmad ya sameni tambayata yayi idan har zuwa wannan lokaci ina sonki sannan ya bani wannan takardar...".

Ya zaro wata takarda ya mik'o min na amsa na bud'e ina dubawa naga ashe takardar da na rubutawa Yaa Ahmad ne, abun mamaki gani da nayi duk wadannan shekaru amma har yanzu kamar sabuwa take, na dubeshi ya cigaba da magana....

"Wannan takardar ya bani sannan yace ya sani ina matuk'ar sonki ya bincika ya samu bani da damuwa, idan har zuwa wannan lokaci ina sonki tou zai bani auranki, ni kuma na amsa da ehh, kin san mey na tambayeshi?

Ce mashi nayi ina son sanin komai game dake saboda ina son sanin abubuwa da yawa a game dake, shekarun da suka wuce kinyi kuka saboda ni, bana san ya kasance yanzu kinyi kuka a kaina, tou ya sanar dani komai tun daga yarintarki...".

Da karfi nace,
"Ohhh no...".

Aaryan ya kwashe da dariya sannan yace,
"Ai ba zaulayarki zanyi ba...

Yanzu Yaa Ahmad friend dina ne sosai...".

Nace, "Ina Aalima?".

Saida yayi murmushi sosai sannan yace,
"Tunda kikayi aure ban k'ara lafiya ba, na kwanta asibiti a lokutta daban-daban, har abroad Umma ta fitar dani, daga baya na auri Aalima yaronmu daya Yusuf amma muna kiranshi da Abba...

Aalima ta tafi Umrah while Abba yana wurin Umma...

Adila da Adla suna karatu abroad amma a gidan wani uncle dinmu suke zaune, medicine suke karantawa...".

Mom ce ta fado man a rai, nace,
"Mom fa?".

Yace, "Mom tana nan lafiya lau, kin san mey?

Tare da ita aka kai lefe, baku hadu bane...".

Na jawo wayata na kunna mashi recording din call din nan, yana k'arewa yace,
"Ai wannan ba dake yake magana ba, akwai wanda yake magana dashi daban".

Nace, "Hakane sai bayan da mukayi aure yake fad'a man, amma ba kayi man gaisuwa ba".

Aaryan ya dubeni yace,
"Baby tare dani aka rufosu har ranar sadakar ukku saida na halarta...

Aallah yayi masu rahama...".

Nace, "Aameen...".

Ya mik'e zaune tareda yi min magana kasa-kasa, na zaro idanu sai kuma yayi min magana a kunne, na rufe idanuna da sauri, ya fashe da dariya tareda jawoni jikinsa yace,
"Uhmmm fad'a min...".

Idanuna a rufe nace,
"No...".

"Ai sai kin fad'a...".

"No...".

Sai kuma na fizge na duro daga saman gadon, shima ya duro ya bini muna zagaye bedroom din yana fadin....

"Kamota, Kamota...

Kamota, Kamota...".

Can yayi min kofar rago ya sureni ya jefa akan gado yabi ya danne yana min cakulkulo ina dariya, nace,
"Zan fad'a...

Zan fad'a...".

Aaryan ya turo lips yace,
"Miye?".

Saida na rufe idanu sannan nayi mashi rad'a a kunne, ya kalleni ya ware idanu sai kuma yace,
"Ai zan iya...

Worry not...".

Na tura kaina a kirjinsa, ya kwashe da dariya sai kuma yace,
"Baby kin san mey?".
Chapter 29 · 0% Book details