← Book details Ba Ni Da Laifi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 32

Sashe 3

Ba Ni Da Laifi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mukayi dariya, ta ciro gorar ruwa tasha ta rufe murfin ta maida a bag ta mik'e muka sauko kasa, muka wuce venue din da muke lecture din, muka zauna a seat daya, muna zama na d'age niqab dake fuskata, karfe sha biyu daidai muka fito daga lecture din, na fito tareda bindawa, tace,
"Baby dama ina son magana dake".

Na katseta da cewa....

"Babie you don't have to waste your energy na sani akan Mahmud ne, ki fad'a mashi bazan aureshi ba, wannan auren ya riga ya wargaje yaje ya nemi wata".

Na jawo Jalila muka wuce, ina ji tana cewa....

"Ai shima talaka mutum ne kuma arziki na Aallah...".

Jalila tace, "Mey bindawa take cewa ne?".

Nace, "Manta kawai, d'an unguwarsu take shigarmawa, watakila tausayi ya bata...".

Jalila tace, "Sweety ya shigo daukata bari kiga in kirashi...".

Ta danna mashi call, muka zauna a bus-stop amma ta baya muna tab'a hira, wata zukekiyar expensive mota mai matuk'ar kyau ce tayi parking, Jalaludden suitor din Jalila ne ya fito tareda wani breathtaking handsome saurayi fari, lokacin da na kalleshi saida gabana ya yanke ya fad'i, duk da gidanmu akwai maza masu kyau amma wannan kyanshi na daban ne, da smile suka karaso inda muke na d'age niqab dina tareda waving hannu nace,
"Sweety....".

Da yake haka muke kiranshi, Jalaludden yace,
"Yeah...

Baby....

Yane....".

Nace, "Normal....".

Cute saurayin da suke tare naji yana min magana....

"Baby babu magana ne....".

Nayi dariya sannan nace,
"Aaahhh tou ina mik'o gaisuwa...".

Yayi dariya har cute dimple dake mak'ale a both cheeks dinsa sukayi appearing, yace,
"Ina amsawa...

Kinsan mey ina sonki".

Nayi dariya kawai, yace,
"You look cute".

Nace, "Kana da barkwanci".

Yace, "Kina da daukar abu da wasa, kince mashi sweety ai nima sweety ne".

Jalila ta mik'e tareda dubana tace,
"Besty muje....".

Ya ware idanu sannan yace,
"Hira muke...".

Jalila tace, "Ni kuma gida nike son zuwa, ehe...".

Jalaludden yace, "Kuma dole akai gimbiya gida...".

A tare mukayi dariya mukayi baki dayanmu, yace,
"Alright then, ai nima ina da magana da ita".

Muka mik'e muka karasa, Jalaludden ya bud'e side din mai zaman hakanan, ya d'age seat, saida Jalila ta shiga sannan nima na shiga, ya maida seat din ya zauna while abokin nashi wanda har yanzu ban san sunanshi ba, ya zagaya bangaren direba, ashe motarshi ce, yana driving suna kus-kus, Jalaludden ya juyo yace,
"Baby....

Ina Mahmud?".

Kaina a kasa nace,
"Mun rabu...".

Da mamaki yace,
"Ban gane ba, kunyi fad'a ko kuma kun rabu?".

Jalila tace, "Sun rabu sweety, wacece zata yarda ta auri makaryaci...

Aaryan babu magana ne...".

A cikin raina nace,
"Ohhhh ashe sunanshi Aaryan...".

Idanunsa suna akan titi yace,
"Yeah...

Akwai...

Ai nemanki nike...

Kedai ki bari kawai, zamuyi magana ne...".

Ni suka fara saukeni a unguwarmu, Jalila tace,
"Baby ki gaida min Ummy...".

Nace, "Ai kusa kike da gidan...".

Mukayi dariya, Jalaludden ya fito tareda d'age seat na fito, ya koma suka wuce, tou a bakin titi ne sukayi dropping dina, na matsa tareda shiga santar gidanmu, tun daga nesa na hangoshi, Mahmud ne tsaye duk ya rame ya fita hayyacinsa ya koma wani iri, yana tsaye yana kallona, dauke kai nayi nai gaba domin bazai tab'a bani tausayi ba, shi makaryaci ne, crossing dinshi nayi, da sauri yasha gabana yace,
"Mariam ba kice komai ba....".

Ji nayi raina ya b'aci bayan duk abun da ya faru amma shine yazo gabana yana min wannan magana, don't he feel despair, wani kallo nayi mashi nace,
"Ohhhh so kake inyi magana...

Alright then, you got it...

Tabbas kai makaryaci ne, kuma bazan aureka ba, nace bazan aureka ba, kaje ka nemi wata, ai bani daya bace, akwai sauran mata a duniya, fara, bak'a, doguwa, siririya, budurwa, zawara, sai wadda ranka yake so...

Ka manta dani...".

Dafe saitin zuciyarshi yayi, nayi crossing dinshi na shige gidanmu...
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
*Update Of June, 2019*
In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen
*Assalam Alaikum sis, complete ne nayi maku shi a matsayin barka da sallah, tou idan kina akan what's app kiyi min magana inyi maki sending document dinshi, idan kuma facebook kawai kike, tou kiyi hakuri har kuzo karshen*
Page. 3
Ummy tana zaune tsakar gida na gaidata na wuce dakina, raina a b'ace na rage kayan dake jikina na jawo zani na daura sannan na fito na dauki bucket na bud'e rijiya na jawo ruwa na wuce bayi nayi wanka, bayan na fito na dauki buta nayi alwalla, saida nayi sallar zuhr sannan naci abinci, wai ashe bayan na shigo gida Mahmud zubewa yayi kasa ba ya lumfashi aka wuce dashi asibiti, ban sani ba, kuma babu wanda ya sanar dani....

Da marece ina zaune daga dakina na jiyo Yaa Ahmad yana cewa Ummy ta bashi abinci ya kai asibiti, bayan ya wuce, na fito na dubeta da mamaki nace,
"Ummy wanene bashi da lafiya...".

Ummy tayi jim tana kallona saidai bata ce komai ba, nima kuma ban sake mata maganar ba...

Washe gari tunda muka shiga lectures har muka fito call yana shigowa a wayata, Aallah ya soni na sakata silent, tou before kowace lecture ina saka wayata silent, muna zaune a bus na jawo wayar nayi zuru ina kallon kiran dake shigowa, Jalila tace,
"Kiyi picking mana...".

Na girgiza kai nace,
"A'a...

Ammi ce take kira, mahaifiyar Mahmud...".

Jalila tace, "Tou ki kashe wayar mana...".

Na k'ara girgiza kai nace,
"A'a...

Bazan iya ba...".

Sannan nayi typing message da sauri na tura mata....

"Ammi kiyi hakuri, *BA NI DA LAIFI* Sam".

Shine abun da nayi typing na tura mata....

Jalila tace, "Miye?".

Nace, "Message na tura mata".

Tace, "Better, ai d'an nata shine ya jawa kanshi".

Nace, "Har yanzu tana da k'ima a idanuna...

Ammi wacece mai kirki, bata da damuwa".

Jalila tace, "Indeed?".

Na kalleta kawai saidai ban ce komai ba, tou har na koma gida Ammi bata sake kira ba, bayan na fito daga wanka, wani yaro d'an makotanmu ya shigo wai ana kirana, jim nayi sannan nace,
"Ka sanshi ne?".

Yaron ya girgiza kai, wannan ya tabbatar min da ba Mahmud bane don idan shine zaice min ya sanshi tunda yasha aikoshi kirana, tou waye?

Oho, jim nayi sannan nace,
"Ka je ka ce mashi gani nan....".

Yaron yayi nodding kai sannan ya juya ya fice, nayi jim sannan na shige daki, vaseline kawai na shafa na goge fuskata da powder sannan nayi applying kwalli na zura long hijab na fito tareda zura takalman rubber na fice, sai naga ashe abokin Mahmud ne, sunanshi Ibrahim, bayan mun gaisa yace,
"Baby kin san Mahmud bashi da lafiya?".

Na girgiza kai, yace,
"Tou bashi da lafiya yana can rai a hannun Aallah...

Jiya bayan kin shiga gida ya zube kasa ba ya lumfashi...".

Nayi jim sannan nace,
"Tou Aallah ya bashi lafiya...".

Ibrahim yace, "Baby, ina ganin ya kamata kuyi magana...".

Da sauri na girgiza kai nace,
"A'a....".

Yace, "Amma mey yayi maki?".

Nace, "K'arya yayi min...".

Da mamaki yake kallona, na lura duk wanda yasan Mahmud idan na fad'a mashi yana mamaki amma wannan ba damuwata bace, na cigaba da cewa....

"I have already made of my mind, magana ta k'are, ni bazan aureshi ba, ni ba mayyar kudi bace, tunda k'arya halinshi ne sai yaje ya nemi mak'aryaci irinshi, not mariam, over my dead body, amma kayi hakuri NI *BA NI DA LAIFI* wannan shine abun da zan cigaba da maimaitawa duk da mafi yawa ba zasu fahimceni ba, amma da in auri mak'aryaci gwara ace saboda bashi da kudi na gujeshi, Aallah yasan zuciyata, yasan *BA NI DA LAIFI* indeed".

Na juya na shige gida na barshi a tsaye, a bakinshi naji rashin lafiyar Mahmud sai a lokacin na fahimci shine wanda Yaa Ahmad ya kaima abinci asibiti, jim nayi na d'age kafad'a na shige dakina na zauna tareda jawo wayata naga wata number ta turo min message....

"I love so much and you are part of my prayers...

Ina da barkwanci ke kuma kina da daukar abu da wasa...".

Wannan shine abun da aka turo, Aaryan ne, message na hudu kenan yana turo min tun bayan rabuwarmu amma bai tab'a kira ba, ni dai abun da na sani shine na fara sonshi, wani message ya k'ara turowa saida na saki murmushi sannan na bud'e, ga abun da ya rubuta....

"Ga kyauta daga gareni, kiyi farin ciki".

Sallama naji na fita ina rik'e da waya a hannuna, wani yaro d'an makotanmu ne ya mik'o min wani karamin kit da aka yi wrapping, daidai rik'ewa a palm....

"Wani mai mota ne yace in kawo maki...".

Saida na amsa sannan nace,
"Ina mai motar yake?".

Yace, "Ya tafi...".

Smile ne ya sub'uce akan fuskata nace,
"Na gode, kace ma Naja'atu ina gaidata...".

Yaron yayi nodding kai sannan ya juya ya fice, nayi tsaye ina murmushi, ina juyawa na hango Ummy tana kallona saidai bata ce dani komai ba, da sauri na shige daki na zauna na soma cire wrapping din, wow wani karamin kit ne, daidai rik'ewa a palm, ina bud'eshi naga ashe madubi ne a ciki, murmushi nayi, ranar wuni nayi ina kallon fuskata a madubin ina murmushi, washe gari throughout bamu da lectures, ina zaune gida, ina zaune a daki ina k'ara karanta message da Aaryan ya turo min ina murmushi, Jalila ce ta fad'o, na d'ago da sauri nace,
"Kai besty har kin bani tsoro".

Jalila ta rik'e kugu sannan tace,
"Aaahhh lallai wato har bakin magana gareki, ina sallama amma baki amsa ba, kin zubawa wannan gwaramar wayar taki idanu kina murmushi kamar wacce ta fad'a soyayya da wayar salula...".

Nayi mata wani kallo sannan nace,
"Mey...

Phone din tawa kike kira gwarama?".

"Ehh.....".

Nace, "Ohhhh, tou naji, ai d'an guntun gatarinka yafi sari ka bani....".

Mukayi dariya, nace,
"Ki zauna mana...".

Jalila ta harareni sannan tace,
"Ai nima gidanmu ne, idan zan zauna ai zama zanyi".
Chapter 3 · 0% Book details