← Book details Ba Ni Da Laifi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 32

Sashe 14

Ba Ni Da Laifi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta mik'e ta haye sama, jim kadan ya sauko, suhail ne yana sanye da wasu breathtaking jeans da shirt, he look cute more and more, kallo daya nayi mashi na maida idanuna akan expensive android dake hannuna, da smile yace,
"Baby...

Yau ina zan saka kaina baby tazo har inda nike, amma kinyi kyau, you look muah, but hala b'atan kai kikayi...".

Nayi mashi banza na kalli suhailat dake tsaye akan stirs, waving hand nayi mata na mik'e tareda wucewa na nufi door, ya biyo bayana, na fice na tsaya a compound ya karaso tareda tsayawa gefena, na had'e hannuwana da alamar bada hakuri sannan da pity face, nace,
"Don Aallah suhail kayi hakuri ka yafe min, ka soni so na gaskiya, ka nuna min so matuk'ar so amma na gujeka, wani lokacin ina making fun of you ne, har kuka kayi min amma na dauki abun wasa, kace kana sona na dauki abun da wasa, saboda kana da kudi ne amma yanzu na gane kuskurena na gane a both masu kudi da talakawa akwai na kirki akwai na banza, wasu ne suke b'atawa wasu suna, na rokeka da girman Aallah kace ka yafe min a bakinka har zuwa zuciyarka...".

Suhail ya kama hannuna yace,
"Baby ni ban tab'a rikeki a raina ba amma tunda so kike ince tou na yafe maki...

Naji engagement dinka was called up, sorry...

Mariam!".

Yadda ya kira sunana ya saka na kalleshi da sauri, ashe suhailat tana tsaye daga saman bene tana kallonmu, suhail yayi murmushi yace,
"Mariam har yanzu ina sonki...

Please kice kina sona, zan aureki...".

Da sauri na fizge hannuna tareda fashewa da kuka nace,
"No...

Kayi hakuri lokaci ya kure...

No way...

I wish ace zan iya maida hannun agogo baya, tou zan karbi soyayyarka kuma in aureka amma yanzu lokaci ya kure, kawai kayi hakuri...

Kaji...

Don Aallah kayi hakuri...".

Da karfi yace,
"Baby....".

Sai kuma yayi kasa da murya yace,
"Please mana...".

Na girgiza kai tareda fashewa da kuka na durkushe kasa, suhail ya dafe kai yace,
"Baby why!?".

Sai kuma ya duk'e tareda kamoni, na fizge tareda wucewa na bud'e pampo dake gefe can, na wanke fuskata, gani nayi ya mik'o min handkerchief na rufe pampon sannan na amsa na goge fuskata na mik'a mashi nace,
"Na gode daka yafe min...".

Na wuce na barshi tsaye yana kallona, mai guard ya bud'e min door na fita tareda tsayawa bakin titi wanda yake wayam ina jiran kekenapep saidai babu ita babu alamarta, da alama abun hawa yana wahala akan road din....

Yaa Ahmad ne yazo wucewa akan bike dinsa ya hangoni, na zaro idanu, yayi parking gabana yace,
"Ina kika zo?".

Nayi shiru, yace,
"Hau muje...".

Saida gabana ya fad'i na hau ya jashi, akan hanya yana tambayata inda naje nayi shiru, can yayi shiru da alama ranshi ne ya soma b'aci, yana isa kofar gidanmu na sauko na shige ciki, Ummy tace,
"Ke kuma daga ina?

Kin barni inata nemanki...".

Nayi shiru, Yaa Ahmad ne ya shigo da bike dinsa, Ummy tace,
"Ohhh ashe tare kuke...".

Yaa Ahmad yayi parking bike dinsa sannan yace,
"Ummy ina tace maki zataje?".

Ummy tace, "Ai ni babu inda tace min zata...

Nemanta nayi na rasa...".

Yaa Ahmad yace, "Tou G.R.A na ganta...".

Ummy tayo waje da idanu tace,
"Tou ina taje?".

Yace, "Shine nike tambayarta tayi banza da ni...".

Sai kuma yayo inda nike a fusace, yace,
"Ke ina kikaje...".

Nayi shiru, tou mey zance mashi, ai da ace zan iya fad'i da tun kafin in fita zan sanar da Ummy, a fusace yace,
"Ina kikaje?".

Nayi shiru, yace,
"Tambayarki nike...".

Nayi shiru, kwasheni da mari yayi ya k'ara kwasheni da mari, na fashe da kuka don marukan guda biyu sun shigeni, yace,
"Yanzu fad'a min inda kikaje ko kuma in saka belt in zaneki...".

Nayi mashi shiru, yayi min maganar duniyarnan amma bance komai ba, yayi kwafa sannan yaja bike dinsa ya fita, Ummy tace,
"Maganinki kenan, ai da ya tsaya ya zaneki".

Ta mik'e ta shige dakinta, Ummy bata bugun yaro, tunda na tashi wannan shine karo na farko da aka dokeni a gidan nan, saida nayi kukana na gaji sannan na koma dakina nayi shiru saida na gaji before na mik'e na rage kayan dake jikina na d'aura zani da shirt na fito tsakar gida ina duba note, Yaa Ahmad ne ya shigo yayi parking bike dinsa ya dubeni yace,
"Wato kin san inda kikaje shine ina tambayarki kikayi banza dani kika kyale, don kinga muna nuna maki so shine kike nema ki botsare wato taurin kai, aiko shine zai wahalar dake don bugu yanzu na fara".

Ummy tace, "Ina taje ne?".

Saida ya zauna sannan yace,
"Course mate dinsu wanda yayi aure kwanaki, ashe gidanshi taje amma saboda ta rainani shine ina tambayarta tayi banza da ni...".

Ummy ta girgiza kai sannan tace,
"Baby wannan halin da kika tsurowa kanki ba hali bane, ace ki shirya kiyi tafiyarki ba tareda kin ce dani ga inda zaki ba...".

Kamar zata sake magana sai kuma ta kad'a kai tayi shiru kawai, washe gari tunda safe na shirya na wuce school, bayan kwana biyu ina chatting da Aaryan shine yake cemin shi so yake ya ganni kawai, ji yake kamar yayi tsuntsuwa ya ganshi gabana, karanta nayi amma naqi tura reply, ya kara magana *_am serious gobe in shaa Aallahu zanzo_* na k'ara karantawa naqi reply, ya k'ara turo wani *_Baby kin karanta amma babu reply_* shima na karanta amma babu reply, ya turo min alamar kuka na kunshe dariya shima nayi the same, can sai ga call dinshi ya shigo, dama don ya kira nayi mashi haka, nayi picking da murmushi akan fuskata, daga daya bangaren cikin husky voice dinsa mai sanyi yace,
"Assalamu Alaiki...".

Saida na saki murmushi sannan nace,
"Wa-alaikas-salam...".

Saida yaja lumfashi sannan yace,
"Shine ina magana kika shareni...".

Na kwashe da dariya sannan nace,
"Aaahhh muryarka nike son inji shiyasa".

Aaryan ya saki murmushi har ina jinsa sannan yace,
"Aaahhh indai wannan ne kin tara kin samu amma kadda ki manta gobe in shaa Aallahu ina nan zuwa, so nike kawai in ganki...".

Nace, "Aallah ya kawoka lafiya...".

Yace, "Aameen....".

Ji nayi yayi hanging call din, da mamaki na kalli expensive android din, wai ashe komawa yayi akan what's app yayi recording muryarsa yayi min sending, ban tab'a sanin expert ne akan kalaman soyayya ba sai a lokacin, ina sauraron recording din bacci yayi awon gaba dani....
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
*Update Of June, 2019*
In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen
*Eid mubarak our greatest Fateema and Fateema, aw Fateema and Teema, wish you all the best....*
*Hope kayi sallah lafiya Abbas Abubakar, wish you all the best...

Lemme see idan zan iya guessing daya sunan, uhmm, kai no aw uhmm, a'a ba haka bane, tou na gaza tunawa, hhhh lols....*
Page. 13
Washe gari wurin karfe biyu na mik'e na jawo ruwa na cika bucket na shiga bayi na durje jikina sosai sannan na fito na shiga dakina na zauna kamar wacce zata shafe fiye da hour biyu tana applying make-up amma vaseline kawai na shafa na goge fuskata n
ayi applying powder sannan nayi applying kwalli, wata cute gown na zaro daga akwatina tana kyau, wata sallah ce har na fidda rai da zan saka kayan sallah saboda lokacin Abba bai d'ad'e da yi mamu registration ba, ba ya da kudi, ya buga gabas ya buga yamma amma ba shi da kudin da zaiyi min kayan sallah, ni har na hakura, ranar daren sallah ina zaune brothers dina maza suka kawo min, wai ashe suna tara kudi shine suka sayi wani farin yard mai cute pattern suka dinka babu surfani babu komai, ni kuma suka siya min ita, gown din tana da kyau, hawa biyu ce, ta kasan tana da circle neck sannan rufe take with yard marar pattern marar design while ta saman take a bud'e kamar after dress tana da madauri sannan kuma tana da pattern, wow, so cute, indeed tana da kyau, zurata nayi tayi matuk'ar suiting dina, na samu dakyar na tattara gashina nayi mashi gammo na d'aura kallabi sannan nayi rolling veil, Maa shaa Aallah nayi matuk'ar kyau more and more, wayata ce tayi haske, tou kullum silent take, na jawota tareda picking na kanga a kunnena....

"Assalamu alaiki wa rahamatullahi wabarakatuhu...".

Saida na saki murmushi before na amsa....

"Wa-ailaikas-salamu wa rahamatullahi wabarakatuhu...".

Daga daya bangaren Aaryan yace,
"Guess what?".

Nace, "Kana kofar gidanmu...".

Yace, "Tou fito in ganki heartbeat...".

Yayi hanging call din, saida na bud'e akwati na zaro diamond ring da ya bani na saka a yatsana kuma yayi suiting dina sosai, tou na zura takalma flat, ba ni saka takalma masu tsini, ina da tsayi duk da ni ba doguwa bace hakanan ni ba gajera bace sannan babu wanda zai kalleni yace min tsaka-tsakiya, kawai dai ina da tsayi daidai nawa wanda yayi suiting structure dina, indai diri ne ni kaina nasan both front and back ba ni da damuwa, komai yaji, kirjina a cike yake hakanan ina da kugu, sometime idan ban saka hijab ba sai a rink'a cewa ina tafiya kamar wata model, hakane kuma, fitowa nayi tsakar gida na fice waje na hangoshi yana jingine da wata expensive car wadda koda sunanta ban sani ba, yana jifata da murmushi har cute dimple dake mak'ale a both cheeks dinsa sukayi appearing, yana sanye da brown kaftani wanda yayi suiting dinsa, cute qube, expensive wristwatch, expensive shoes, wow I feel in sureshi in zura a bag kadda sauran mata su kalle min abuna, lol, na karasa gefenshi ina taking steps sannu a hankali tareda dropping kowace kafa a inda na sauke dayar, na tsaya gefenshi da murmushi nace,
"Ina wuni?".

Da murmushi akan fuskarsa yace,
"Lafiya lau baby...".

Sai kuma ya ware idanu yace,
"Baby amma kinyi kyau you look....".
Chapter 14 · 0% Book details