← Book details Ba Ni Da Laifi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 32

Sashe 17

Ba Ni Da Laifi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga daya bangaren Ayan yace,
"Baby nayi magana da Abba amma ya nuna min ya riga ya yanke hukunci, bai damu ba koda zaki mutu bayan an daura auran...".

Na fashe da kuka nace,
"Aaryan fa?".

Yace, "Kece ya kamata ki fad'a mashi komai, kiyi hakuri ki rage damuwa muna sonki...".

Nace, "Ni sunfi sonshi dani kawai...".

Nayi hanging call din, na danna digit din Jalila da yake ina da digit dinta of head, tana picking na fashe da kuka tace,
"Jiya nazo baki farka ba...".

Nace, "Jalila...

Abba yace dole sai na auri Mahmud ni kuma Aaryan nike so...".

Daga daya bangaren Jalila tace,
"Wannan magana ce wadda na riga na santa tuntuni, Abba ya hada ni da Yaa Ahmad ya fad'a mamu maganar aure tana nan amma ba yaso keda Mahmud ku sani, yace muje mu cigaba da shirye-shiryen biki a madadinku shiyasa nace maki ki rabu da Aaryan amma kikayi watsi dani, daman wannan ne abun da nike guje maki, kinga yanzu dole ki bi umarnin mahaifinki sannan babu damar ki rabu da Aaryan farat daya, dole ki cigaba da kulashi saboda yana da damuwa a zuciyarshi, idan kika rabu dashi lokaci guda zai iya rasa ranshi, yanzu ina school amma idan na fito zan biyo in dubaki...".

Na mik'a mashi wayarshi tareda fashewa da kuka, wannan wacce irin rayuwa ce, babu wanda na sake yi ma magana, da da marece Jalila ta shigo ta jima sannan ta wuce, mutane suna zuwa dubani saidai wasu gulma ce take kawosu musamman en unguwarmu, tou en course dinmu sunzo dubani har da suhail, Yaa Mustapha saidai kira yayi aka bani yayi min ya jiki na fasa mashi kuka, shima cewa yayi inyi hakuri babu yadda zaiyi, tashin hankalina ban san halin da Aaryan yake ciki ba, yau kwanana ukku a asibiti saidai har zuwa yanzu babu wani cigaba saboda naqi kwantar da hankalina kullum cikin damuwa nike, Ummy ce take jinyata amma Abba yana zuwa kullum hakanan Yaa Ahmad da Nadiya....

Ummy ta fita ne, motsi naji na juyo Mahmud ne tsaye, wani kallo nayi mashi na juya mashi baya, yayi taking steps tareda tsayawa bayana yace,
"Baby why?".

Sai kuma yace,
"Ke haka za'ayi auren ina maki magana kina banza dani...".

A fusace na juyo tareda durowa daga saman gadon na nunashi cike da tsiwa nace,
"Get out...

You speak hausa...

Right?

Tou ka fita nace...".

Mahmud ya ware idanu yace,
"Baby baki iya tsayuwa amma yanzu kin tsaya akan kafafunki, ashe nine maganin...".

Wani kallo nayi mashi, Ummy ce ta shigo ta kalleni ta kalleshi, na juya tareda komawa akan gado na kwanta tareda rufe idanuna, ko fita Ummy tayi nidai ban sani ba, yazo yana min magana nayi banza dashi, ni ban san lokacin da ya tafi ba don bacci ne yayi awon gaba dani....

Washe gari aka yi discharging dina, Ummy ta tattara komatsanmu muka wuce gida a kekenapep, wanka nayi na wuce dakina na kwanta, magulmata suna ta shigowa, tou gulma suzo suga yadda nike a samu na fad'i, handbag na jawo na zaro wayata na duba abun mamaki na tarar da miss call da yawa amma babu na Aaryan hakanan bai turo min message ba, na duba what's app na samu ya jima ba ya online, Ummy ce ta lek'o tace,
"Ki zo inji Abbanku...".

Wayata dake bayana na kalla sannan na dauketa na zura a handbag na mik'e na fice na sameshi a dakinshi na durkushe kasa nayi shiru, yace,
"Mariam dole ki auri Mahmud koda zaki mutu, ehhh na yarda a dalilin wannan auren ki mutu, wanda kike gudu yafi wanda kike kuka a kanshi, ai shi Mahmud da ya ganki ni ya fara zuwa ya tuntuba da zancen sannan ya fara zuwa wurinki amma shi wancen fa, saidai yazo ya kiraki ki fita amma babu wanda ya tuntuba ya nemi izini, ni bazan hanaki kuka ba idan kika tashi kiyi na jini, idan kika tashi ki suma sai in daukeki a wuce dake asibiti amma wannan auren baki isa ki tsaidashi ba...".

I feel in sanar dashi gaskiya akan nice na hana Aaryan ya gabatar da kanshi amma no point tunda yace koda zan mutu sai na auri Mahmud kuma na sanshi nasan halinshi idan yace ehh ko a'a babu mai sauyashi sai ikon Aallah, tashi nayi na wuce, ranar wuni nayi a daki ina kuka, na kwana ina kuka, bayan nayi sallar subh na koma bacci nice ban farka ba sai wurin karfe sha biyu na rana, na dafe kaina da yake min wani azababben ciwo, na mik'e na fito tsakar gida na dauki bucket na wuce bayi nayi wanka na fito tareda komawa dakina, na jima before nayi kalaci....

Washe gari da rana ina zaune Yaa Ahmad ya shigo yace,
"Ki shirya yanzu Mahmud zaizo wurinki...".

Nayi shiru ban motsa ba, can wani yaro ya shigo yace,
"Ance baby tazo...".

Nayi shiru, Ummy tace,
"Je ka ce gata nan...".

Yaron ya juya ya fice, mik'ewa nayi na zura takalma na jawo long hijab daga saman door na zura na fice, Mahmud ne yana jingine da wata bak'ar mota kirar Benz, shadda ce a jikinsa wadda tasha aikin hannu, komai na jikinsa expensive ne, tab'e baki nayi na karasa tareda kallonshi, ya saki murmushi yace,
"Ya kike...".

Nace, "Ai kana da idanu ko ka ganni a gutsire ne, I don't think I look somehow bad...".

Mahmud ya girgiza kai, nace,
"Ashe kasan amsar....".

Yace, "Ohhh baby rigima...".

Nace, "Ohhh kai kuma k'arya ba...".

Mahmud ya rik'e hab'a yana dariya, yace,
"Relax mana baby, baki son mai guard, na daina guard nayi kudi, kawuna yayi min wankan talauci, ai kin ganni...".

Nace, "A banza aikin banza katoton zero a gaban decimal point ai bashshi da amfani...".

Na zaro baby Nokia dake kuguna yasa hannu ya wafceta yace,
"Zan siya maki expensive waya... iPhone 7plus kike so ko kuma iPhone 8...".

Wani kallo nayi mashi, haushi ya bani, nace,
"Ai ni ba mayyar kudi bace, abun duniya ba ya gabana, koda arzikin duniya zaka bani ba amsa zanyi ba, zan iya tafiya...".

Mahmud ya ware idanu yace,
"A'a ai zance nazo, kin manta ne...".

Nayi banza dashi, wata expensive Jeep ce tayi parking kallo daya nayi mata na gane ta Aaryan ce, taking steps nayi zuwa inda motar take na bud'e front seat na shiga na rufo na dubeshi kuka yake saida gabana ya yanke ya fad'i, I thought yaji komai ne, nace,
"Kayi hakuri kaddara ce...".

Aaryan yana kuka at the same time yana smile, yace,
"Kukan murna ne, Aallah ya bayyanar mamu da Aalima, yanzu haka tana gidanmu, naji dadi ki tayani murna, I love her and I love you zan aureku baki daya...".

Da sauri nace,
"No...

Aaryan kayi hakuri akwai damuwa...

Aurenmu bazai yiyu ba...".

Da mamaki yake kallona, yace,
"Baki son kishiya ne?".

Nace, "Itama kishiyar damuwa ce, opposite da gidanmu mata biyu ne daya tana da hakuri da kauda kai shiyasa suke zaune lafiya, nan kuwa kusa da gidanmu kowace bata da hakuri sune kullum cikin fad'a...".

Kallona yayi sai kuma yaja motar yayi reverse yayi gaba da ita, da mamaki nike kallonshi saidai ban ce komai ba, gudu yake sosai, ya tsaya a bakin wani katon get yayi horn aka wangame mashi get ya shiga tareda parker motar, ya bud'e ya fice ba tareda yace dani komai ba, ina gani akan idona ya shiga ciki ya barni ni daya a mota, can ya fito tareda wata babie, Aalima ce saida gabana ya yanke ya fad'i ganinsu tare, wannan ya tabbatar min da gidansu ya kawoni, a jere suka tafo ta bud'e side din da nike na fito ya juya ya koma ciki, Aalima ta dubeni da damuwa sai kuma ta had'e hannayenta alamar rik'o, tace,
"Don Aallah baby kadda kiyi mamu haka, Yaa Aaryan yana matuk'ar sonki kuma yana da matsalar zuciya idan kika rabu dashi zamu iya rasashi, zan iya hakura dashi in bar maki saidai nima yana matuk'ar sona, yace kince baki son kishiya, damuwa ce, tashin hankali ake, tou ni naji zan rink'a hakuri ina kauda kai kinga shikenan za'a zauna lafiya...".

Da sauri nace,
"A'a baki gane bane, akwai damuwa, aure na da shi bazai yiyu ba saboda...".

Muryar twins naji daga bayana suna fadin....

"Ga Aunty Mariam...

Ga Aunty Mariam...

Sannunki da zuwa...

Zo mu je wurin Umma...".

Suka jani har parlour inda wata cute mata mai kama dasu take kishingid'e akan kujera, a tare suka ce,
"Umma...

Surprise...

Ga baby...".

Kallona tayi ta saki murmushi tace,
"Ahhh wa nike gani kamar surukata...

Aaahhh lale marhabun, sannunki da zuwa, zauna and feel free nan ma gidanku ne...".

Na zauna tareda gaidata ta amsa da fara'a tana tambayata mutan gida, a kunya ce nike, tace,
"Mariam...

Right?".

Nayi nodding kai, tace,
"Mariam ki saki jikinki nan ma gidanku ne...

Maa shaa Aallah...

Cwtheart ya iya zabe...".

Aaryan ne ya sauko daga stairs ya kwanta akan kujerar da Umma take tareda pillow da cinyarta yayi lamo, Umma tana shafa sumar kanshi tace,
"Cwtheart...

Miye?".

Da shagwab'a yace,
"Umma kaina ne yake ciwo...".

Da damuwa tace,
"Ayya amma banda ciwon zuciyar ko?

Cwtheart ka daina sakawa kanka damuwa, Aalima ta bayyana then what kuma?".

A hankali ya bud'e idanunsa ya kalleni sai kuma ya maida idanunsa ya rufe....
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
*Update Of June, 2019*
In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen
*Eid mubarak our greatest Usman Mujaddadi, wish you all the best....*
*Hope kinyi sallah lafiya Ummu-khalil, our greatest salma, wish you all the best....*
Page. 16
Adila ta dubeni sannan tace,
"Baby tashi muje bedroom dina...".
Chapter 17 · 0% Book details