Sashe 28
Ba Ni Da Laifi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wata ranar alhamis wadda bana tunanin zan manta da ita, Mahmud ya shirya zai tafi kauyensu, har bakin mota na rakashi, hankalina sam bai kwanta da tafiyar nan ba, nace,
"Yanzu ba zaka fasa tafiyar nan ba...".
Mahmud yayi murmushi sannan yace,
"Baby zumunci zanje kuma zumunci yana da lada...".
Sai kuma ya sunkuya tareda sumbatar cikina yace,
"Ki kula min da little princess dina".
Nace, "Sure...".
Smile yayi yaja kumatuna yace,
"Yauwa good girl...".
Na turo baki sannan nace,
"Lallai wato erki princess ni kuma girl".
Mahmud ya ware idanu yace,
"Baby rigima...
Uhmm kishi...
Kin boni da erki kike kishi...".
Nace, "Ehhh ai so kake ta zama kishiyata tun kafin tazo duniyar".
Mahmud ya fashe da dariya yana kallona, yace,
"Tou nidai na tafi...
Bye...
Take care...
Ki yafe nima na yafe maki...".
Nace, "Na yafe...
Aallah ya kiyaye hanya...
Aallah ya tsare...".
Yace, "Aameen...".
Tareda waving hannu ya bud'e mota ya shiga ya jata, ina tsaye ina waving mashi hand har motar ta fice daga get, na koma na zauna hakanan naji gabana yana faduwa sai kuma na fashe da kuka, jina nike babu dadi daga baya baccin wahala ne yayi awon gaba da ni, bayan na tashi na duba lokacin sallar zuhr baiyi ba, na bud'e *data* shine nike ganin labari cewa wasu mahara kimanin mutum talatin wadanda suke dauke bindigu sun shiga wani kauye a saman bikes sun kashe mutane sannan suka kwashe kudiyoyinsu, saida gabana ya yanke ya fad'i ganin sunan kauyensu Mahmud a matsayin kauyen da aka kai harin, neman kuka nayi na rasa nayi zuru kawai...
Yaa Ahmad ne ya fad'o gidan daga ganinshi ba ya cikin hayyacinsa, na fashe da kuka, ya wuceni ya haye sama jim kadan ya dawo yana rik'e da hijab, ya mik'ar dani ya zura min ita sannan yaja hannu muka fice ya sakani a mota while shi kuma ya zagaya side din direba yayi horn mai guard ya wangame mashi ya ja motan tareda ficewa da ita ya nausata akan flat kwalta dake shimfid'e akan road din, wannan itace fita ta karshe da nayi daga gidan ban k'ara komawa ba, yana driving ina kuka, kusan lokaci guda muka isa tare dasu Ammi, gawarwaki ne a kwance, na mak'ale a baya ina tsoron abun da zan gani, Ammi ta wuce tana taking steps cike da damuwa, yanayinta ya nuna itama ta daure ne kawai amma ita kanta tana fargabar abun da idanunta zasu gane mata, cin karo tayi da Mahmud kwance a cikin gawarwakin shima ya rasa ranshi a hannun wadannan mahara, baya tayi da sauri sai kuma tayi zuru saidai gani aka yi ta zube kasa bata lumfashi, ana dubawa aka ga she is dead ta mutu babu rai a tattare da ita, Safeena k'anwar Mahmud ta kalli gawar brother dinta sannan ta kalli gawar Ammi, yanke jiki tayi ta zube itama ana dubawa aka samu she is dead babu rai a tare da ita, zuru nayi na kasa koda hawaye, a hankali na soma tafiya gawar Mahmud na fara gani then ta Ammi sannan ta Safeena, Aallah sarki Safeena an saka mata biki da d'an uncle dinsu, wata daya ya rage ma bikin, durkushewa nayi yayinda jini yake bin kafafuna, tafiya nayi gajeran hutu na dawo daidai sai kuma na sume saidai farkawa nayi na ganni akan gadon asibiti har na kwana daya....
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
*Update Of June, 2019*
In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen
*Eid mubarak to all Muslim all over the world....*
*Hope kunyi sallah lafiya dearies, wish you all the best....*
Page. 25
A hankali na bud'e idanuna, nayi zuru kawai, a bakin Ummy nike jin cewa cikin dake gareni ya zube har wankin ciki aka yi min, daga baya take sanar da ni mutuwar both Safeena da Ammi, tun jiya aka sallaci gawarwakinsu sannan aka wuce dasu gidansu na gaskiya, duniya kenan, shikenan baki dayansu sun mutu they were no more, na fashe da kuka, yanzu shikenan Mahmud, Ammi da Safeena duk sun mutu, matsawa nayi likita yayi discharging dina, kai tsaye na wuce gidan uncle din late Mahmud, a can ne ake zaman makokin, zama nayi nai zuru bana magana saidai idanu, ni kadai nasan yadda nikeji, ga mutuwar nan ga kuma ciwon ciki da mara, zaune kawai nike ina amsar gaisuwar amma bana magana, moment din da na kasance da late mijina Mahmud kawai nike tunawa, gashi yanzu ya mutu ba ya nan, he is no more, cikin da muke tattali ya zube, ashe bayan da maharan suka tafi ne aka kwaso gawarwakin aka tafo dasu cikin gari, a nan aka yi masu wanka, a inda mutanen garin katsina da kewaye dake tattare da wannan alhini suka halarci sallatarsu tareda wucewa dasu gidansu na gaskiya (wanda suke ganin cewa mutuwar Mahmud, Ammi da Safeena baiyi masu dadi ba, tou nayi hakane domin ku fahimci yadda dukkanin wadanda suka rasa en uwansa a wadannan hare-hare sukeji...
Wadanda kuma suke jin cewa sunji haushin zubewar cikin da baby take dauke dashi, tou kamar hakane mutane da yawa suke rasa abun da suke matuk'ar so a dalilin wadannan hare-hare).....
Ranar lahadi aka yi sadakar ukkunsu wanda ya samu halartar mutane masu dumbin yawa, babu wanda zaice maka ga adadin mutanen, mutane ne bila adadin, Mahmud yayi mutane kuma duk wanda zai bud'e baki tou halinshi na kirki zai fad'a, kowa halayenshi masu kyau yake fad'i, tabbas Mahmud bashi da damuwa, ina kukan mutuwarshi ina mashi addu'a, idanuna sun koma wani iri, kallo daya mutum zaiyi min yasan nasha kuka ba kadan ba....
Washe gari da daddare na wuce gidanmu kusa da Ummy na, duk wanda zaiyi min godiya a can yake samuna, kullum ina daki sanye da hijab, daga wanka sai wanka babu kwalliya ko kadan, ba wai ina takaba bane, tou babu takaba a kaina, en uwanshi dake nuna basu sona tou ga mutuwa nan tazo ta daukeshi tareda mutane biyu da nike samun sauki daga gunsu, Aallah sarki duniya lokacin da ina yarinya karama ina yawan tunani akan idan na girma nayi aure koda mijin yana dukana ne zan hakura in zauna saboda kadda in fito a kirani bazawara, tou yanzu miye sunana amsar itace bazawara, kowace mace tana da kaddararta a rayuwa, kowane mutuwar aure yana da sila, wani lokacin baka da laifi, en course dinmu sunzo sunyi min gaisuwa....
Washe gari suhail yazo yayi min gaisuwa tareda matarshi suhailat, cikin hakane en uwan Mahmud suka fara maganar rabon gado, tou koda basu fad'a ba, na sani daga ni sai kayan jikina iyayena suka kaini sai kuma gara, tou lefena da sauran kayan sawana, motocina da sauran wasu k'ananan abubuwa kamar waya, laptop, iPhone, iPad, laptop, tou sune nawa sauran tarar dasu nayi....
Brothers dina tareda Nadiya sukaje suka dauko min kayana wadanda suka had'a da lefe, sauran kayan sawa, ATM card, laptop tareda sauran k'ananan kayan suka zo suka jibge min su, ina da ilimi koda ba'a fad'a min ba, na sani gadon Mahmud kawai gareni kuma both Ammi da Safeena suna da gadonshi tunda ya rigasu mutuwa, shi ba ya da gadonsu while Ammi take da gadonshi kawai while Safeena take da gadon dukkaninsu while ita kuma basu da gadonta tunda sun rigata mutuwa, ni duk maganar gadon nan ba ita bace a gabana, damuwa da nike tattare da ita ta mutuwar mijina itace take damuna har yanzu, kullum cikin damuwa
nike da tunani, koda aka raba gado aka bani nawa fili Yaa Ahmad ya siya min a kusa da filin da ya siya min da sadakina, sauran kudin ya siya min gida, wadanda suka rage ya saka min a account....
Abba yana yawan zaunar dani yayi min nasiha akan hakuri da dangana, hakanan itama Ummy, Nadiya tana zuwa ta zauna tare da ni, hakanan brothers dina guda ukku suna yawan zama tare dani, Affan ya girma har an sakashi school, wasu lokuttan nakan dauko wayata in rink'a kallon hotunan da late Mahmud ya daukemu gasu nan da yawa sune suka cike wayata, damuwar dake raina ta taru ta saka na rame na koma kamar yadda nike lokacin da ina budurwa, tou yanzu na koma baby na tashi daga bebilo....
Ranar wata talata ina zaune akan kujera ina sanye da hijab, Jalila da Jalaludden ne suka shigo, na ajiye waya dake hannuna na d'ago kai, na bud'e baki da muryata wadda ta koma some how mai sanyi, nace,
"Jalila kece...
Sannunku da zuwa...
Sweety...".
Suka zauna a separate kujeru, sukayi min gaisuwa tareda jerowa Mahmud addu'o'in samun rahama a wurin Aallah, nace,
"Aameen...
Na gode...
Ansha biki babu ni...".
Jalila tace, "Abun nan bai jima da faruwa ba aka yi bikin, naje har can gidan saidai lokacin baki gane mutane...".
Na gyad'a kai kawai, can nace,
"Sweety don Aallah ka bar Jalila a wurina har zuwa dare...".
Jalaludden yace, "Indai wannan ne baki da damuwa...".
Tafiya yayi ya barta muka wuni, naji dadin zama da ita, har take cemin da ace cikin da nike dashi ya zauna sai in wanko hotunanmu ni da Mahmud dake a wayata, inyi album dinsu idan macece idan ta tashi aure sai in batasu kyauta, hakanan idan namiji ne idan ya gama karatu sai in bashi shi kyauta, saidai kash cikin ya riga ya zube, muna tare saida dare sannan yazo daukarta har mota na rakata wannan itace fitata ta farko daga gidan tun bayan dawowata, sai naga unguwar ta sauya ta koma man wata iri, saida naga tafiyarsu sannan na juya na koma gida....
BAYAN SHEKARA DAYA....
Ina zaune a daki, Yaa Ahmad ya shigo, kamar kullum hira muka sha, har ina tambayarshi matarshi da yake yayi aure, wata cousin dinmu ce mai kirki da ita ga kyau, har yayi min sallama ya mik'e sai kuma ya koma ya zauna, yace,
"Mariam....".
Na dubeshi, yace,
"Mariam zuwa wannan lokacin ya kamata ace yanzu kin sake aure...".