← Book details Ba Ni Da Laifi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 32

Sashe 11

Ba Ni Da Laifi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yaa Ahmad ne ya shigo santar suka gaisa, yace,
"Babynmu zance kike?".

Nace, "Kai Yaa Ahmad...".

Yace, "Uhmm babynmu ta girma...".

Ya shiga gida yana dariya, a lokacin ne na tambayeshi saidai a wannan karo baiyi min k'arya ba saidai yayi shiru akan wani abu....

Na dubeshi nace,
"Abokinka ne?".

Yace, "Wai Ahmad?".

Nace, "Ehhh....".

Yace, "Wurin aikinmu daya...".

Daga nan baice komai ba, tunda yace wurin aikinsu daya na gane wurin aikinsu daya da Abba kenan tunda da Abba da Yaa Ahmad wuri daya suke aiki, Yaa Ahmad yana da degree akan Bsc.

Mathematics, guru ne sosai akan maths....

A lokacin ban tambayi Mahmud matakin da yake ba, shi kuma bai fad'a min ba, abubuwa da yawa sun faru a soyayyata da Mahmud saidai zuwa wannan lokacin da wadannan abubuwan suka faru sam ban san tuna wadancen lokuttan, ni dai abun da na sani shine naso Mahmud iya so, na nuna mashi so matuk'ar so amma daga baya ai kunga abun da yayi min, k'arya, wai k'arya, idan na tuna raina b'aci yake, tou ban san maraya bane sai wata rana da yake fad'a min cewa both iyayenshi en batsari ne dake nan jihar katsina amma mahaifinsu ya rasu tunda tsohon cikin k'anwarshi Safeena, na tausayi mashi sosai, rashin mahaifi babban ciwo ne, tabbas, don wani abun idan ya tsaya maka a wuya hmmm, wani lokacin zaka duba kaga ga abu da yake maka amma lokaci yazo da ba ya nan ballantana yayi maka, mun dauki lokaci muna soyayya na lura yana da hali mai kyau, sam bashi da damuwa, ina sone in gane idan yana da ilimin addini, wata rana yazo muna cikin hira nace,
"Kaga bari in dauko Alk'ur'ani ka duba min hardata...".

Na mik'e na shiga ciki, da yake a zaure (soro) muke zance sai in dauko mashi sallaya ya zauna while ni kuma sai in zauna daga gefe, na dauko Alk'ur'ani mai girma na dawo zaure (soro) tareda zama na mika mashi Alk'uranin, shi a lokacin suratul ma'ida na bud'e mashi wurin tsakiya shima na lura a lokacin yana da sani akan Alk'ur'ani mai girma tunda duk inda nayi b'ata yana gyara min, bayan mun gama yace,
"Ashe matar tawa mahardaciyyar Alk'ur'ani ce, kinga ni na sauke ne amma banda hadda".

Nayi murmushi kawai nace,
"Na gode, karanta min inji kira'arka".

Ya mik'o min yace,
"Then bud'e min duk inda kike so".

Na amsa na bud'e na mik'a mashi yayi auziya sannan yayi bismillah before ya soma rero karatu, yana da karatu mai kyau saidai tsakanin kira'ata da tashi banbancin a bayyane yake, ya burgeni sosai, kamar yadda kuka sani bayan hakan ne ya soma hadda, wata rana muna making call kamar da wasa yace,
"Zan kawo maki kanwata ku gaisa...".

Nace, "Ina jiran zuwanta".

Na dauka da wasa yake....

Bayan kwana biyu ina zaune ya kira, murmushi ne ya sub'uce min nace,
"Aaahhh yanzu wayar nan sai tayi recording komai, wow...".

Sai kuma nayi picking tareda amsa cikakkar sallamar da yayi min, yace,
"Ya kike...".

Nace, "Kamar yadda kake...".

Yace, "Ashe kina fama ne da ciwon kaine...".

Da sauri nace,
"Mey...

Inji wa?".

Mahmud yayi dariya sannan yace,
"Aaahhh ai da bakinki kika ce yadda nike haka kike, manta da wannan, gani a kofar gidanku na kawo maki Safeena...".

Da mamaki nace,
"Aallah?".

Yace, "Idan baki so sai na koma da ita".

Nace, "Aiko da kaima idan ka dawo ban fitowa".

Na mik'e na shiga daki na zura long hijab na duba fuskata a madubi sannan na fito na lek'a dakin Ummy tana zaune akan kujera nace,
"Ummy zan fita, Mahmud
ne ya kawo min k'anwarshi...".

Ummy tace, "Tou kije ki shigo da ita".

Na gyad'a kai tareda juyawa na fice yana zaune akan rubber-rubber ta sauko, suna kama sosai, yarinya ce don na girmeta, tou shekarunta ba zasu wuce goma sha shidda ba, Mahmud yace,
"Ga k'anwata na kawo maki...".

Nace, "K'anwarmu dai, kaji fin karfi...

Safeena sannu, ya hanya?".

Tace, "Alhamdulillah...".

Yace, "Wato na kawo maki ita shine kika manta da ni".

Nace, "Tou naga k'anwata wa yake ta kai".

Ya ware idanu, nace,
"Ehhh...".

Yace, "Ai zamu hadu...

Safeena kinga an kirani, tou idan kin gama ki wuce a kekenapep".

Safeena tayi nodding kai, yayi min waving hannu yana murmushi sannan ya burka bike dinsa ya wuce, na jata muka wuce ciki ta gaida Ummy sannan na wuce da ita dakina, ana zafi don haka na d'age mata labule, nayi mata magana sannan na fita na shiga makotanmu gidan maman en biyu, na amso mata pure water da zobo tareda snack na dawo na jera mata a plate sannan na kai mata na zauna tareda zare hijab din dake jikina, nace,
"Sannu Safeena kunsha hanya...

Ya gida...

Ya su Ammi...".

Tace, "Suna nan lafiya lau...".

Nace, "Gaskiya naji dadin wannan zuwan naki, kin kyauta, ga ruwa da zobo da snack...".

Tana murmushi tace,
"Na koshi...".

Nace, "Ohhh har ana koshi da ruwa, tou bari in kirashi ince mashi na kawo maki abunsha kince a'a...".

Ta girgiza kai tace,
"Tou zan sha...".

Nace, "Mey ai har da snack zaki ci ko kuwa yanzu in danna mashi call...".

Wuni tayi sannan tayi ma Ummy sallama na rakata har bakin titi na tare mata kekenapep na fad'a mashi unguwarsu na biya mata kudin ta shiga suka wuce sannan na juyo, ban koma gida ba, na shiga gidansu wata childhood bestie dita, ina zaune a can na kirashi nike tambayarshi Safeena, yace ta isa gida lafiya....

Washe gari muna lecture bindawa ta soma ganin jiri muka wuce da ita clinic ta amshi magana muka wuce da ita hostel, bayan mun tafo ashe ciwo tayi kamar zata mutu, da sukaga abun yafi karfinsu aka wuce da ita general hospital, har asibiti mukaje ganinta tareda en course dinmu, tou bayan sunyi discharging dinta ta koma gida before ta ida murmurewa, Jalila ce take cemin ya kamata muje mu k'ara dubata, nace tayi fixing lokaci, shine washe gari bayan mun fito daga lectures, muka biyo bus, daga national muka tari kekenapep ta wuce damu unguwarmu bindawa wato filin samji, ya saukemu muka wuce da yake mun san gidansu, gida ne mai kyau yasha paint ga tale malale a kasa abun saidai hamdalah....
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
*Update Of June, 2019*
In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen
*Eid mubarak online writers and publishers, wish you all the best....*
*Hope kinyi sallah lafiya mariam dabai, Aallah ya albarkaci rayuwarki....*
Page. 10
Muka tadda Mamansu ta fito daga kitchen muka gaidata ta amsa da fara'arta ta sanmu....

"Ya mai jiki?".

"Jiki yayi sauki...".

"Aallah ya k'ara sauki...".

"Aameen...

Ku shiga tana dakinta...".

Muka wuce muka sameta kwance ta mik'e zaune tana murmushi tace,
"Sannunku da zuwa...

Bari a kawo maku ruwa...".

Jalila tace, "Kamar kuwa kin san daga school muke".

Bindawa ta kira k'anwarta tace,
"Soffi dauko masu ruwa daga fridge...".

Nace, "Daga gani k'anwarki ce...".

Tace, "Ehhh...".

Nace, "Tubarkallah kuna kama...".

Yarinyar ta kawo mamu abinci da gorar ruwa tareda cup guda biyu, ruwan masu sanyi (but not as cold as ruwan da nasha a school, I feel idanuna zasu samu damuwa, lols...) fried rice ce wadda taji vegetables muka ci muka kora da ruwa muka sha hira abunmu, tace,
"Watakila next week in koma school...".

Da muka tashi tafiya mukayi ma Ummarta sallama, bindawa ta rakamu har bakin kofa muka fito ta koma, muna tafiya na d'age niqab din dake fuskata, ji nayi wata muryar mace tana kirana....

"Baby....".

Ina juyawa naga Safeena k'anwar Mahmud a kofar wani gida, I feel da ban d'age niqab dita ba, don ba ni da excuse din da zai hanani shiga gidansu ni kuma kunya nike ji, Jalila tace,
"Wacece?".

Nace, "K'anwar Mahmud ce...".

Tace, "Aikuwa naga kama....".

Nace, "Please bata uzuri kadda mu shiga, kunya nikeji...".

Jalila tace, "Ai bamu da uzuri".

Safeena ce ta karaso, nace,
"Safeena sannunki...".

Tace, "Da wucewa zakiyi?".

Nace, "K'awarmu muka zo dubawa da jiki...".

Tace, "Ohhh Haulat...".

Nace, "Ehhh bindawa...".

Tace, "Hakane...

Muje ki gaida Ammi ko kuma ince mata kinzo kin wuce baki lek'ata ba".

Na nuna mata Jalila nace,
"Wannan k'awata ce tare muke karatu, sunanta Jalila...".

Safeena tace, "Hakane...

Tou muje...".

I feel some how amma babu yadda zanyi, nace,
"Tou muje...".

Muka jera tayi mamu jagora zuwa wani gida, gida ne daidai rufin asiri, dakuna biyu ne sai rijiya, gidan ba ya da girma sosai, daidai-daidai yake, ta wuce daya dakin wanda da alama shine yafi girma, wata dattijuwar mata ce zaune akan kujera tana karanta husnil muslim, nayi kasa da kaina, Safeena ta nuna mamu kujera amma muka zauna kasa, matar ta d'ago tace,
"Ku koma akan kujera...".

Kallo daya nayi mata naga basu kama da ita, da alama mahaifinsu suka biyo koda yake ga hotonshi can suna kama sak, muka zauna akan kujera muka gaidata ta amsa da fara'a, tun wurin Mahmud nasan cewa da Ammi suke kiranta, Ammi tace,
"Safeena k'awayenki ne?".

Safeena tace, "A'a.....".

Sai kuma ta fita....

Ammi tace, "Sannunku da zuwa yaran nan".

Safeena ta dawo da ruwa pure water guda biyu daga gani a fridge ta daukosu, ta ajiye mamu tace,
"Ammi baki gane wannan ba?".

Tayi pointing dina, nidai kaina yana kasa, Ammi ta kalleni tayi jim sai kuma tace,
"Kuma kamar na wayeta....".

Safeena tayi dariya tace,
"Baby ce, budurwar Yaa Mahmud...".

Ammi ta saki murmushi tace,
"Sai yanzu na gane, hotonta na gani, kice surukata ce...".

A lokacin ji nayi kamar kasa ta tsage in shige, tace,
"Ku sha ruwan mana...".

A kunya ce nasha, tou bazan iya mata gardama ba, tace,
"Ya Ummarki?".

Nace, "Lafiya lau take...".

Tace, "Kice ina gaidata..".

Nayi nodding kai, a kunya ce nike zaune, gwara Jalila ta fini sakin jiki, da muka tashi tafiya tace,
"Ni mey zan ba surukar tawa, baby gashi dakin nawa babu abu irin naku na en mata amma Safeena dauko mata wani littafi yana cikin locker ta kaima Ummarta zaiyi mata amfani".
Chapter 11 · 0% Book details