← Book details Ba Ni Da Laifi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 32

Sashe 1

Ba Ni Da Laifi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Root Entry
WordDocument
0Table
Data
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
*Update Of June, 2019*
In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen
*Assalam Alaikum sis, complete ne nayi maku shi a matsayin barka da sallah, tou idan kina akan what's app kiyi min magana inyi maki sending document dinshi, idan kuma facebook kawai kike, tou kiyi hakuri har kuzo karshen*
*Aallah ya isa duk wanda yayi min editing novel ko kuma ya sauyashi ta kowane bangare*
*Bismillahir Rahmanir Rahim*
Page. 1
Durkushe nike ina rusar kuka kamar wacce tayi loosing both iyayenta saidai ni a durkushe a gabansu nike rusar kukan, the more nike kuka the more nike ganin idan basu yarda da muradina ba, rayuwata ta shiga garari, kuka nike ina shedding tears babu ji babu gani, a karo na farko Abba ya dubeni yace,
"Baby mi ye yake damunki?".

Ban yi uttering koda word guda daya ba, gani nike the more na tsaida hawayena the more Abba zaiyi watsi da muradina, I feel inta kuka more and more koda ya yarda da abun da zan sanar dashi....

Ummy ta dubeni sannan tace,
"Baby ba kya ji ne, Abbanku yana magana?".

Na d'ago ina mai cigaba da shedding tears nace,
"Abba ni bazan iya auran Mahmud ba, bazan iya auranshi ba, a baya nace ina sonshi amma yanzu bazan iya ba".

Na mik'e na juya na bar dakin a guje ina gumjin kuka, wani k'aramin daki dake kusa da kofar da na fito na shiga na zube kasa nayi zaman en bori tareda fashewa da kuka, na had'a kai da gwuwa ina sharar hawaye, the more nike tuna abun da Mahmud yayi min the more nike shedding tears, wannan wacce irin alaka ce, wannan wacce irin soyayya ce, wannan wacce irin dauka ce yayi min....

Abba yace, "Ta fada maki wani abu da ya faru tsakaninsu ne?".

Ummy tace, "A'a sam babu abun da tace min".

Abba yace, "Shikenan zan kira Mahmud din inji ta bakinshi".

Sai kuma ya mik'e tareda goya hannayensa a baya yana kaiwa da komowa....

Ina kunshe a daki ina shedding tears, ina busy kuka autanmu ya shigo ya d'ane bayana yana kiran...

"Ba-by....

Ba-by....

Ba-by....".

Na zura hannu na jawoshi gaba yana kiran sunana ina tayashi, ina fara kiran Ummy....

Abba....

Da sauran brothers dinmu guda ukku ya soma wangame baki yana dariya, shekararshi daya da watanni hudu amma gudu yake sosai, ga baki, ga shi yana da zakin murya, yana gudu yana kiran Ummy....

Abba....

Baby....

Ayan...

Sauran brothers dinmu guda biyu kiran sunayensu wahala yake mashi, tou kwaranci yake, na biye mashi muna dariya har na lallab'ashi yayi bacci, nayi jim ina tunani, wasu yadda ka daukesu ba haka suka daukeka ba, ban tab'a tunanin Mahmud zaiyi min haka ba, kallabi na jawo na tufke yalwataccen gashin kaina, wani kodadden zani ne a jikina da shirt, bani da wadatattun kaya, idan nace zan rink'a sakasu tsakar gida zasu kod'e ne in rasa na sakawa in fita shiyasa na yanko fallaye guda-guda na atamfa rubber ina had'awa da shirt ina sakawa a tsakar gida, fitowa nayi na tarar da Ummy tana tankad'en garin tuwo, nace,
"Ummy kawo inyi...".

Ummy ta girgiza kai sannan tace,
"A'a je ki had'a wuta...".

Na wuce kitchen na had'a kan itace (woods) sannan na banka masu wuta na daura tukunya na tsaida ruwa, ina fitowa naci karo da Yaa Ahmad ya dawo daga wurin aiki yana sanye da suit, kallona yayi saidai baice komai ba, da alama ya ji komai tunda ba haka muke ba, amma nayi mamaki da baiyi min maganar ba, ina ganin Abba ne ya hana kowa yayi min magana, tunda gashi itama Ummy ba tace dani komai ba, dakinshi ya shiga, ni kuma na zauna bakin rijiya na jawo mashi ruwan da zaiyi wanka sannan na soma tara wadanda zanyi wanke-wanke dasu, ina ji yana fama da Affan wato autanmu saida ya samu ya likama Ummy shi sannan ya zo ya dauki bucket da na cika mashi ya wuce bayi, ina wanke-wanke ya fito nace,
"Yaa Ahmad ba magana".

Yaa Ahmad ya juyo yana smile ya ja kumatuna yace,
"Akwai magana mana babyna, ai ni dake ba baki bane".

Mukayi dariya yace,
"Munyi magana da Ayan yana gaidaki".

Nace, "Aallah sarki mutanen London".

Affan yazo ya rik'e mashi hannu yana kiranshi...

"A-mad....".

Mukayi dariya, Yaa Ahmad yayi mashi wayo ya wuce, na lura yanayin kowa ya sauya a gidan har sauran brothers dina sunji komai amma babu yadda zanyi, tabbas an dauki lokaci da saka ranar wannan aure saidai yanzu wannan aure ba mai yiyuwa bane, bayan na gama sallar isha'i ina zaune tsakar gida ina cin tuwo da miyar kuka, wani yaro d'an makotanmu ya shigo yace,
"Baby wani yace kizo".

Na gane wanda yake nufi duk da kuwa ba wai ya fad'a min bane, bana da lokacin sauraren duk wasu maganganu na Mahmud don haka nace,
"Ka je ka ce mashi na ce a'a, yauwa kace ma Mairo ina gaidata".

Yaron ya juya ya fita, Yaa Ahmad da Ummy suna tsakar gidan kuma sunji abun da nace saidai babu wanda yace dani komai, yaron bai dawo ba, saidai Yaa Ahmad da yayi picking call ya mik'e ya fice ya jima sannan ya dawo, duk da nasan Mahmud ne ya kirashi amma sai naga baice dani komai ba, tsame hannuna nayi daga cikin akushin da nike cin tuwon a cikinshi na daukeshi na wuce rijiya na wanke komai, Ummy macece mai tsafta bata tolerating k'azanta, kayan da aka b'ata da dare basu kwana a gidan nan, saida safe nayi masu na dora da sanar da Ummy lokacin da zan wuce school....

"Ummy gobe idan Aallah ya kaimu karfe goma zan wuce school, lecture daya gareni".

Tace, "Aallah ya kaimu....".

Nace, "Aameen....".

Na wuce dakina wanda yake wayam, tsohuwar katifa ce kawai a ciki, sai karamin akwati da kayana masu kirki suke a ciki then tsohon bedsheet dake gefe wanda na kulle kayan da nike sakawa tsakar gida a ciki, already ina da alwalla kwanciya nayi saidai na kasa bacci, waya ta isheni da k'ara, nasan wanda yake kira kuma ni bazan dauka ba, na yarda Abbana ba mai kudi bane, saidai bazan yarda da abun da yayi min ba, bazan dauka ba, sam ba haka nike ba, karshe da wayar ta isheni da ringing na jawota na maidata silent na turata a bag, sai wurin karfe daya na dare sannan na samu nayi bacci, da asuba a daddafe nayi sallar subh na koma bacci, nice ban farka ba, sai karfe tara na safe, wata zabura nayi na mik'e, a gaggauce na wanke bakina nayi kalaci, tou ba na shan koko, kosai naci tareda zazafen tuwo na jawo ruwa nayi wanka tareda da brush na wuce daki ina d'aure da zani nayi mashi d'aurin kirji, vaseline kawai na shafa na goge fuskata da powder, na shafawa idanuna kwalli, wasu riga da skirt na atamfa na saka, na shafa humra, most of the time ina b'ata lokaci ne wurin tamke yalwataccen gashin kaina, dakyar na samu nayi mashi gammo na zura long hijab har kasa na rufe fuskata da niqab, kusan kullum haka dressing dina yake, bag dake dauke da materials dina na jawo na zura dari biyu da hamsin tareda zura takalma na fito na lek'a nayi ma Ummy sallama, kullum Ummy tana bina da addu'a, yauma bata fasa ba, cikin ikon Aallah ina fita daga santarmu na samu kekenapep, naira hamsin ya kaini national, na samu saura kadan bus ta cika na samu seat, babu jimawa bus din ta cika kasancewar coaster ce bata da wahalar cika, shiru nayi yayinda bus din ta dauki hanya, akwai en course dinmu saidai tunda muka gaisa ban k'ara uttering koda word guda daya ba, saida wata er course dinmu ta tab'ani sannan na lura da bus din tana tsaye ne a bus-stop dake gefen faculty dinmu ne, mik'ewa nayi muka fito, sunanta Zaynerb Abdul'aziz, duk da bamu magana irin sosai din nan amma mun san juna tunda course daya muke karanta wato BCH (Biochem) muna a 400 Level, degree muke had'awa, a hankali tace,
"What wrong with you mariam?".

Naji wayata dake a bag ta soma tsuwwa, waving hannu kawai nayi mata ta wuce tareda wasu course mate dinmu, zaro wayar nayi wadda ta kasance baby Nokia ce, taci duniya har rubberly na saka na nannad'eta, picking call din nayi tareda yi mata sallama....

"Hello babie...

Yeah na shigo...

Gani nan a tsallaken bus stop...

Ohhh kina a medicine classes...

Alright then, ki fito gani nan zan tafo...".

Saida na maida wayar a bag sannan na soma tafiya, ina gab da library na hangoshi yana tafowa daga bayana, kamar wanda aka jefo, ba ya tare da nutsuwa ko kadan, da alama kekenapep ya biyo, daga nesa na kalleshi ya kalleni, Mahmud ne, Jalila zata fara min surutu na jata tareda k'ara sauri, wuf muka shige library, na sani duk nacinshi ba za'a barshi ya shigo library ba, upstairs muka haye, Jalila tace,
"Mahmud na hango ina maki magana kika wani jawoni".

Na zauna akan kujera ina hango waje ta glass nace,
"Na hangoshi shiyasa na jawoki nan".

Da alama tayi mamaki sosai tace,
"Mahmud nike nufi...

Suitor dinki...

Wanda zaki aura...".

Nace, "Of course shi...".

Da mamaki tace, "Kunyi fada ne...".

Bana san tattaunawa akan maganar a lokacin don haka nace,
"Ki bari kawai idan na shirya munyi maganar".

Jalila tace, "Alright then amma abun da mamaki".

Daga sama muna hangoshi ya duk'e kasa tareda dafe kai, bayan wani lokaci ina lekawa naga wurin wayam, ashe wani friend dinshi dake masters ne ya zo wucewa ya ganshi shine ya jashi suka wuce, wayata na duba tareda dafe kai nace,
"Gosh, lecture....".
Chapter 1 · 0% Book details