← Book details Ba Ni Da Laifi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 32

Sashe 13

Ba Ni Da Laifi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yayi mata sending ta saka a group dinmu na what's app, ita ya fara saukewa a bakin get din gidansu sannan ya wuce, gani nayi ya dauki wata hanya nayi tunanin hanyar zata kaishi unguwarmu ne amma sai naga yayi horn a bakin wani tangamemen get na dubeshi da sauri, yayi banza dani, gani nayi an wangame get din ya shiga da motar cikin katon mansion din mai kama da aljannar duniya, a rayuwata ban tab'a shiga gida mai kyanshi ba, parking yayi a jerin expensive motoci dake parker, na dubeshi yace,
"Gidan auntyna ce, k'anwar Ummana, muga jikkarki ki goge fuskarki kadda ta ganki a haka ta gane kinyi kuka, nasan a jikkunanku na mata ba'a rasa kayan make-up...

Right?".

Na dubeshi kawai, ya dauki jikkata ya budeta yana dubawa saidai babu kayan make-up babu dalilinsu, ya ware idanu yace,
"Handbag dinki kamar bata mace ba, babu powder balle lipstick da blusher aw barbad'a kumatu...

Uhmm handbag dinki babu kayan make-up, tou suna ina?

Uhmm ai en mata suna yawo da kayan make-up ne na sani".

Nayi mashi shiru, ya zaro handkerchief daga pocket din wandonsa ya mik'o min yace,
"Amsa ki goge fuskarki...".

Na kalleshi nayi sai kuma na amsa na nufi fuskata dashi, wani kamshi ne mai sanyi ya ziyarci hancina na tsaya cak da hannuna, na dubeshi nace,
"Kamshi yake....".

Aaryan ya ware idanu yace,
"Aww sorry ashe kamshi yake ba wari ba...

Baby kina da abun dariya, tou miye don yayi kamshi, Uhmm".

Na kalli gefe tareda sakin dariya shima dariya yayi, na goge fuskata na mik'a mashi ya amsa before yace,
"Yeah...

You look lovely...".

Sai kuma ya fita ya zagaya ya bud'e side din da nike na fito ya maida murfin motar ya rufe, yace,
"Let go...".

Nace, "Aha...".

Aaryan yayi gaba na bishi, yana gaba ina biye dashi, kofar shiga ciki ita kanta abun kallo ce, ga punch of flowers masu kyau, ya danna bell, wata yarinya ce ta bud'e door da alama maid ce, ta gaidashi ta gaidani ta matsa, ya shiga nabi bayanshi, a katon parlour mukayi appearing wanda a kalla yana dauke da set din kujeru guda hudu, girmanshi yafi girman gidanmu, babu kowa a parlourn, na dubeshi, yace,
"Ki zauna...".

Na dubeshi ya nuna min kujera mai daukar mutum biyu, na zauna, yace,
"Bari inje inyi ma aunty tawa magana".

Sai kuma yayi min waving hannu yana murmushi sannan ya juya ya haye stirs, nayi shiru ina kallon parlourn wanda yake kamar a turai, babu abun da babu, wata babie ce ta ajiye min drink mai sanyi da ruwa tareda kayan marmari, nidai kallo daya nayi masu nayi gefe da kaina, Aaryan ne ya sauko tareda zama kusa dani, yana murmushi yace,
"Gata nan saukowa...".

Tuni na d'age niqab dina, nace,
"Ka tashi kadda ta sauko ta ganka kusa dani".

Aaryan ya ware idanu yace,
"Tou miye?".

Wata cute hajiya ce ta sauko daga stirs cikin shiga ta alfarma tana zuba kamshi, tasha gold, tana murmushi ta zauna akan doguwar kujera, Aaryan yace,
"Sai mom...".

Da kamilalliyar muryarta tace,
"Boy gaskiya ka kyauta daka kawo min surukata, Maa shaa Aallah...".

Nayi kasa da kaina nace,
"Ina wuni?".

Tace, "Lafiya lau daughter...".

Aaryan yace, "Baby...".

Mom tace, "Baby kuma?

Daughter ya sunanki".

Nace, "Mariam....".

Mom tayi murmushi tace,
"Mairo...

Maryamu...

Ya Mamanki?".

Nace, "Tana nan lafiya lau".

Mom tace, "Ki sha ruwa...".

Nayi kasa da kaina, Aaryan ya tsiyaya ruwa a glass cup ya mik'o min na kalleshi nayi banza, Mom tace,
"Kyaleshi amsa ki sha...

Kai son ka kyaleta ko kuma in koraka...".

Na amshi cup din na kafa lips nasha ruwan kadan sannan na ajiye cup din, Mom tace,
"Tubarkallah boy ka iya zabi...

Daughter ya kike?".

Nace, "Lafiya lau...

Mun sameku lafiya?".

Tace, "Lafiya lau...".

Wasu yara ne guda biyu mace da namiji suka rugo suka haye Aaryan, da alama jikokinta ne, daya namijin ya dubeni yace,
"Uncle...

Who is she?".

Aaryan yace, "She is my fianc
Yaron yace, "I like her".

Aaryan yace, "Greet her sultan".

Yaron wanda Aaryan ya kira da sultan yace,
"Ina wuni?".

Nace, "Lafiya lau...".

Itama macen tace,
"Ina wuni?".

Nace, "Lafiya lau...".

Macen tace, "Kina da kyau...".

Nayi murmushi kawai, yaran suka wuce, namijin yana cema macen....

"Sultana tsaya...".

Mom tace, "Daughter zan baki numbata kadda kiji komai idan yayi maki laifi ki kira fad'a min, ni da ummarshi same father same mother muke".

Nayi nodding kai kawai, tace,
"And kadda kiyi hurting dinshi kinji".

Kunya naji sosai, tace,
"Zuciyarshi tana da damuwa...

Kici Apple...".

Na girgiza kai, Mom tace,
"Gardama zakiyi...".

Da sauri na dauki apple guda daya na gutsira kawai, ta mik'e ta haye sama, nace,
"Ka tashi muje...".

Aaryan ya mak'e kafad'a ya kira yaran nan sultan da sultana, namijin ya tsaya wurina while macen ta tsaya wurinshi, yaba wata maid wayar tayi mamu snapping pictures, ya amsa ya kashe mamu selfie sannan yayi min, yayi min dasu, pictures din baki daya sunyi kyau, ya jasu suka haye sama, jim kadan ya sauko tareda Mom, da smile tace,
"Aaahhh daughter har zaki wuce, tou na gode ki gaida Mamanki, Aallah ya kiyaye hanya...".

Nace, "Aameen na gode...".

Ta koma sama ya matso kusa dani ya dauki apple guda daya, na tashi yayi gaba ina biye dashi, sultan da sultana suka rakamu har bakin mota, ya bud'e min side din mai zaman hakanan na shiga ya maida murfin ya rufe before ya zagaya bangaren direba, yaron ya lek'o yace,
"Ki k'ara zuwa kinji...

Uncle ka k'ara zuwa da ita...".

Suna tsaye suna mamu waving hannu har motar ta fice, nace,
"Mey yasa kayi min haka?".

Yace, "Daga na kaiki kin gaida Aunty na...".

Nayi mashi banza, can nace,
"Tana da kirki, I like her, bata da damuwa".

Yace, "Hakane....

Yanzu kuma wurin Ummana zan kaiki ki gaidata...".
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
*Update Of June, 2019*
In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen
*Eid mubarak our greatest doctor and your cold friend, tabbas bashi da damuwa....*
*Hope kunyi sallah lafiya dearies, wish you all the best....*
Page. 12
Da sauri na dubeshi idanuna a waje, yace,
"Wasa nike maki...".

Na maida lumfashi, yace,
"Matsoraciya...".

Nace, "Nice kai, ai naji komai lokacin da kuka fara zuwa".

Aaryan ya ware idanu na kwashe da dariya, yana parking opposite da gidanmu ya mik'o min wata katuwar leather yace,
"Gashi mom ta baki...".

Na dafe kai, yace,
"Yane...".

Nace, "Ban mata godiya ba".

Yace, "Kawo wayarki in saka maki digit dinta, mantawa tayi bata saka maki ba".

Na zaro expensive android da ya bani na mik'a mashi ya saka min numbarta yayi min saving tareda mik'o min wayar yace,
"Bari in gani miye a ciki...".

Ya bud'e, expensive perfumes ne kala-kala har guda hudu da wani hadaddan expensive less da atamfa super English tareda wasu gown masu tsad'a guda ukku, yace,
"Aahhh gaskiya mom ta kyauta, yanzu wannan less da atamfa zan tafi dasu in kaima tailorn da yake ma twins dinki ya dinka maki".

Ya zarosu ya wulla backseat, nace,
"Na gode...".

Ya d'aura yatsanshi akan lips sannan yace,
"Shhhhh keda kika bani zuciyarki fa?".

Dariya ya bani na amshi leather din tareda b'alle murfin motar na fito ina dariya, na shiga gidanmu na samu babu kowa a tsakar gida na wuce dakina na bud'e akwati na saka leather din kasanshi sannan na rufe, already nayi dropping handbag dina, na zare hijab tareda rage kayan dake jikina na d'aura zani a kirji na fito na bud'e rijiya na jawo ruwa na cika bucket na daukeshi na shiga bayi, tou ina daukar bucket amma bana daukar jarka kwata-kwata, ina fitowa, Ummy tace,
"Baby har kin dawo kenan...".

Nace, "Dawowata kenan na shiga bayi".

Daga nan bata sake cewa komai ba, taja buta ta shiga bayi, saida nayi alwalla sannan na wuce daki, tou an fara kiran sallar magrib, saida nayi sallar isha'i sannan na fito naci abinci nasha ruwa na koma daki ina chatting da Aaryan, bayan wasu mintina mukayi sallama na fito na dauki buta nayi alwalla na k'ara cikata na wuce da ita daki na kwanta.....

Washe gari bani da lectures, da marece bayan nayi wanka na shafa vaseline tareda goge fuskata nayi applying kwalli, wani material na saka dinkin gown ne k'irar bubu, naja dogon gashina wanda idan ya bazo har gwuwata yake wucewa, haka yake, gashi wara-wara kamar rubber, dakyar nayi mashi gammo na d'aura kallabi yayi zororo a baya, nayi rolling veil na dauki poss tareda applying humra na zura takalma flat na fito, Ummy bata a tsakar gida kuma ni bazan iya fad'a mata inda zanje ba don haka na fita kawai ba tareda na fad'a mata ba, bakin titi na tsaya na tare adaidaita na shiga tareda fad'a mashi inda zai kaini, bakin wani katon mansion yayi parking na bashi kudinshi sannan na fito tareda matsawa nayi knocking akan door dake gefen get, wani mutumi ne ya bud'e door din yana kallona, nace,
"Suhail yana ciki...".

Yace, "Ehhh....".

Tareda matsawa na shiga, mansion ne babba, ginin masu kudi da suka amsa sunansu masu kudi, an zuba naira babu k'arya, direct hanyar door nayi na danna bell, suhailat ce ta bud'e door kallona tayi na kalleta sai kuma ta matsa tareda cewa....

"Ashe kece...

Shigo...

Barka da zuwa...".

Na shiga ta rufe door din tayi gaba, na bita ina k'arewa parlourn kallo, babba ne, komai yaji, abun ba'a cewa komai, ta nuna min kujera na zauna ta kawo min ruwa na dubesu kawai, wasu matan yanzu bakin kishi garesu, tace,
"Ki sha...".

Na girgiza kai kawai, nace,
"Wajan suhail nazo idan yana nan...".

Jim tayi sannan tace,
"Ehhh yana nan...".

Nace, "Wajenshi nazo, please kiyi mashi magana".

Kallona tayi tai jim sai kuma tace,
"Alright then, bari inyi maki magana dashi".
Chapter 13 · 0% Book details