← Book details Ba Ni Da Laifi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 32

Sashe 6

Ba Ni Da Laifi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nayi zuru baki daya yanayina ya sauya saida na bud'e hotunan Aaryan ina kallo sannan farin cikina ya dawo na manta da komai, soyayyar Aaryan tayi nutso deep a cikin zuciyata, i can't abroad loosing dinshi, d'an halak, ina saukowa daga napep na hangoshi yana zaune a cikin wata cute mota kirar Benz ya zuro kafarshi daya waje wadda take rufe da wasu expensive cover shoes, Aaryan ne, fitowa yayi yana murmushi, expensive suit ne a jikinsa saidai babu cot, shirt ce, necktie da trouser da wasu expensive cufflinks dake a sleeve dinsa, tareda wata expensive wristwatch, he looks breathtaking, yana taking steps yana smile yana k'ara appearing handsome, sumarshi baka wuluk tana kwance, yalwatacciya, ina k'ok'arin ciro hamsin in baiwa mai napep kudinsa, ya karaso tareda ciro wallet ya zaro sabbin en dubu-dubu guda biyu ya mik'a mashi, kallonshi nayi yana min smile, sama nayi da niqab dake fuskata tareda escaping murmushi, muka jera zuwa wurin motarsa, na jingina da ita while ya tsaya a gefena, na kalleshi yace,
"Kin san mey?

I missed you...".

Nayi murmushi kawai, yace,
"Nazo ne kawai in ganki kuma na ganki daga wurin aiki nike, am leaving".

Na ciro wayar da ya bani na mik'a mashi, ya ware idanu yana kallona, saida nayi dariya sannan nace,
"Selfie...".

Ya shafi sumar kansa sai kuma yayi murmushi har cute dimples din dake a b'oye a left and right cute cheek dinsa sukayi appearing, na kalleshi na kalli wayar dake hannuna yace,
"Ooohhh....".

Ya amshi wayar saida yace,
"Cheese...".

Sannan ya kashe mamu selfie yayi kyau sosai, ya zaro wayarshi ya tura har da daurawa akan dp, yace,
"Inga handbag dinmu...".

Na kalleshi, yace,
"Yeah, ai handbag dinki tawa ce".

Nayi murmushi sai kuma na mik'a mashi ya tura hannunsa a pocket din wandonsa ya zaro sannan ya zura min wayata a bag yayi zipping ya mik'a min, wai ashe wani karamin kit ne mai kyau ya saka min a ciki, Yaa Ahmad ne ya shigo santar a bike dinsa, kallona yayi saida gabana ya fad'i, ya wucemu yayi parking dinsa ya shige gida, nace,
"Shine Yaa Ahmad".

Aaryan yace, "Ooohhh kuna kama sosai".

Nayi murmushi tareda nodding kai, da murmushi yace,
"Am leaving, ki saka zaiyi maki kyau...".

Yayi min waving hannu ya juya ya shige motarsa ya jata, ina tsaye saida motar ta b'ace min daga gani sannan na juya na shige ciki, nayi crossing din Yaa Ahmad zai fito saidai baice min komai ba, yayi crossing dina ya fice, da kallo na bishi, a hankali nace,
"Kuyi hakuri NI *BA NI DA LAIFI* sam".

Na wuce ciki na shige dakina zan ciro wayata na lura da wani karamin cute kit, ciroshi nayi na bud'e wani karamin cute ring din diamond ne yayi appearing, jim nayi sai kuma nayi murmushi na bud'e akwati na turashi kasan kayana na maida akwatin na rufe....

Washe gari bayan na dawo daga school, ina saukowa daga napep naci karo da wata katuwar expensive Jeep parker opposite da gidanmu, wata farar babie ce ta fito tana sanye da fitet gown wadda ta matseta kanta tamke da kallabi, babu hijab a jikinta amma ta d'aura veil a kafad'a, gani nayi ta nufo inda nike kuma ni ban santa ba, wata yarinya ce ta k'ara fitowa daga motar, k'anwar Mahmud ce, Safeena, cikin raina nace,
"Ooohhh wai for how many time suke so inyi keeping ce masu NI *BA NI DA LAIFI* bazan iya auren makaryaci ba...".

Nayi crossing dinsu na shige gidanmu na wuce dakina sallama sukayi suka shigo suka zauna, yunwa nikeji kuma na gaji, na debo ruwa na ajiye masu na dauki zani da shirt na fita, rijiya na bud'e na jawo ruwa na cika bucket tareda daukar kwandon wanka na wuce bayi nayi wanka na sauya kayan dake jikina da zani da shirt, na fito na shiga daki na samesu zaune kamar yadda na barsu, vaseline na shafa na goge fuskata nayi applying kwalli, yunwa nike ji so badly, tamke kaina nayi da veil na fice na shiga kitchen na zubo zazafen tuwo na koma daki tareda masu bismillah suka girgiza kai, gyara zama nayi naci nayi nak sannan na kora da ruwa, na fita tareda ajiye kwanon a kitchen na kuskure bakina na koma dakin na zauna na dubesu nace,
"Yauwa ina jinku, da mey kuke tafe?".

Daya babie din ta dubeni a fusace tace,
"How dare zaki shanya mu...".

Na kalleta na ware idanu sannan nace,
"Ooohhh I see, amma ai ban gayyatoku ba ballantana kuce na kiraku kun zo nayi maku wulakanci, ku tashi ku tafi mana ai ban tsayar daku ba, na dawo daga makaranta da gajiya da yunwa ai bazan tsaya in wahalar da kaina ba akan maganar da an riga an gamata, wai don Aallah mey kuke so inyi maku, sau dubu nawa kuke so in cigaba da ce maku kuyi hakuri NI *BA NI DA LAIFI* bazan auri mak'aryaci ba...".

Na mik'e na karasa gefen katifa na zaro wata karamar waya mai gidan memory, before da ita nike amfani amma daga baya ta samu matsalar speaker idan ina magana ba'aji shine na ba wani d'an unguwarmu dubu daya ya sawo min waccen karamar Nokia din, ko lokacin da aka kawo min ita taci duniya, jim nayi ina juya wayar abun da ya faru shine a lokacin da nike amfani da ita duk wayar da nayi tana recording shiyasa sau da yawa idan bani aikin komai nike kunna recording call din da nayi da Mahmud ina ji ina murmushi, idan mutum yaci karo da ni a lokacin sai yayi tunanin radio nike saurare, tayi recording komai, kunna masu nayi sukaji komai, da alama suma sunyi mamaki, na gani a fuskokinsu, d'ayar babie din tace,
"Kai impossible....".

Na kalleta sai kuma ta sauya yanayi, a hankali tace,
"D'azu na b'ata maki rai, nayi maki ihu amma kiyi hakuri, Mahmud means a lot to me ne, kiyi hakuri ki koma gareshi, tabbas akwai kuskure a wani wurin amma sam wannan ba halinshi bane...".

Nayi mata shiru, Safeena kanwar Mahmud ta fashe da kuka tace,
"Don Aallah kiyi hakuri ki tausaya mamu shi daya muke dashi, Ammi kwana take kuka, yana can kwance akan gadon asibiti fighting for his life...

Kin sani na sani kowa ya sani he love you so much...".

Nace, "Indeed he love me so much but I don't either said sai mai kudi zan aura, tou miye dalilin k'aryar, Aallah ya bashi lafiya, Aallah ya tsareshi daga kamuwa da ciwon zuciya amma ni babu ni babu shi, duk da yana can fighting for his life and please kadda kuga laifina NI *BA NI DA LAIFI* I don't think I deserve yayi min k'arya tunda ai ban ce sai mai kudi ba, ko miye ya faru shi ya janyowa kanshi NI *BA NI DA LAIFI* sam...".

D'ayar babie din ce ta daka min tsawa ta mik'e tareda zaro bandir din en naira dubu-dubu ta jefeni dasu tace,
"Kawai ki fito fili kice you are after abun duniya, don kina fara shine kike tunanin sai mai kudi zaki aura, kodadda kawai, no wonder kin tashi kina cin wannan dirty so called abincin da kikayi mamu tayi d'azu, aikin banza aikin wofi, dubi wannan gugurarran dakin babu komai a cikinsa sai talauci a haka kike nema ki wulakantamu, Mahmud yafi karfin wannan, dole sai kin aureshi koda kina mutuwa kina dawowa, mayyar kudi kawai, kudi kike so ko tou ai gasu nan dauka, kina banzar cima a gida shine kike burin idan kinje gidan ki sauya cima, kina so ki daina cin tuwo miyar kuka ki koma cin tea da bread da wainar egg, fried rice da pepper chicken, kina so ki daina shan ruwan tulu ki koma shan ruwan gora da drinks masu sanyi, kin gaji da wahala kina so saidai kina kwance ayi maki komai, mayyar kudi kawai, wato kin saba da wanka da ruwan rijiya wadanda sai kin jawo kin zuba a bucket kin cika sannan ki dauka kije bayi kiyi wanka shine kike dreaming din wanka a katon bathroom mai towel, bathtub da shower wanda kina juya makunni ruwa zasu zubo maki shaaa, kin tashi a wannan gurrurarran gidan kina so ki koma katon mansion mai garden, swimming, ac, upstairs, manya-manyan bedroom da parlours na alfarma wadanda daya daga ciki yafi girman wannan so called gidan...

Idan ba wannan ba, miye abun kyama a auran mai guard...

Yaa Mahmud yafi karfin yayi maki k'arya, bazai maki k'arya ba, kawai ki fito fili kice dreaming din auran mai kudi kike, ai mai kudi kike so ko?

Ahhh tou kin samu, Mahmud cousin dina ne, Abbana attajiri ne, mai kudi na gasken-gaske, waccen motar da muka zo a kanta, zan iya siyen guda goma irinta ba tareda na girgiza ba...

Mahmud yana da gatanshi, Abbana yana sone ya samar mashi da aiki mai kyau shi kuma ba ya son takurawa wani shiyasa yake guard, yana da diploma ya ajiyeta yana aiki da secondary, koda kina so koda baki so sai kin aureshi...".

Kallon gefe nayi tareda maida kwolla dake neman zubo min, bana san inyi kuka a gabansu, mik'ewa nayi na nuna mata kofa nace,
"Get out...

Mahmud ne bazan aureshi ba...".

Safeena ta duk'a ta dauki kudin tace,
"Baby kiyi hakuri....".

Da sauri na katseta tareda nuna mata kofa nace,
"Babu abun da za ki ce min, ai kece kika kawota taci min mutunci, tou jata ku fice min daga gani, ai kina da brain ko?

Tou Mahmud ne bazan aureshi ba, nice Mariam nace ba nayi sai kubi wani sarkin...

Ai bani daya bace mace a gari, akwai babies da yawa...

Nace ba nayi ai sai ku kyaleni...

Aikin banza aikin wofi...".
Chapter 6 · 0% Book details