← Book details Ba Ni Da Laifi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 32

Sashe 5

Ba Ni Da Laifi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na kalleshi, yace,
"Yeah, aro na baki ba kyauta ba, don amsar abuna zanyi".

Duk da na gane inda ya dosa, dubara yake so yayi min amma babu yadda zanyi, ya cigaba da cewa....

"Na tura maki pictures dinki, and na bud'e maki what's app, nayi maki sending apps daga wayar Adla irin naku ne na mata, bestie, beauty camera, tou na mance sunan sauran...".

Nace, "Idan na fasa maka screen fa?".

Aaryan yayi dariya sannan yace,
"Then sai in sauya wani ai muna da kudi".

Dole na amshi wayar, ya mik'o min cup yace,
"Ki maida shi...".

Na lura yayi hakane saboda yana avoiding inyi mashi maganar wayar, amsa nayi na maidashi gida na dawo, gani nayi ya mik'o min wayarsa, na amsa, picture dina ne akan screen lock amma mey?

Akan wallpaper picture dinshi ne shi da wata chocolate yarinya mai kyau, baki daya munyi smile, sun bada perfect match, saida gabana ya yanke ya fad'i na d'ago da sauri na dubeshi da alamar tambaya, gani nayi baki daya yanayinsa ya sauya, cikin damuwa yace,
"Sunanta Aalima, cousin dina ce, a gidanmu ta tashi, I love her so much, ta b'ace har yanzu bamu san inda take ba, tana raye tana mace bamu sani ba, first love dina ce, I love her and I love you...".

Nayi jim, yace,
"Baby zaki yadda min waya".

Na dubi wayar da sauri, ya ware idanu yace,
"Kinga wurin Umma zan kaiki ince mata ga Inlaw dinta, in rama abun da Jalila tayi mamu".

Na ware idanu da sauri, yayi dariya yace,
"Sorry, wasa nike maki".

Kiran sallar zuhr aka soma da yake garin akwai lullumi ne shiyasa mutum bai fiye fahimtar lokaci ya ja ba, na ware idanu ya duba silver wristwatch dake daure a wrist dinsa, yace,
"Lokacin sallah yayi...".

Na fito muka wuce tareda Jalila na fiddo masu butoci guda biyu suyi alwalla, Jalila ta hakime akan katifa tana danna waya, nace,
"Besty ki tashi kiyi sallah...".

Tace, "Am off...".

Nace, "Ohhhh...".

Na fito na tarar sun aiko wani yaro ya maido botocin, na dauki buta na shiga bayi na fito nayi alwalla na koma daki nayi sallah, can Jalaludden ne ya kira Jalila, mun fito tsakar gida Affan ya mak'ale mani dole na daukeshi muka fito, Jalila tana mashi wasa koda kallonta baiyi ba, Aryan yace,
"Affan...

Right?".

Nace, "Ehh shine...".

Ya mik'o mashi hannu, mak'ale kafad'a yayi yaqi zuwa, ai daman nasan za'ayi haka, Affan kenan, da en gidanmu kawai yake yarda, ba ya yarda da bakuwar fuska, Aryan yace,
"Ya qi yarda dani...".

Nace, "Ba ya yarda da bakuwar fuska...".

Aaryan ya ware idanu, Jalila tace,
"Ina yawan zuwa amma ba ya yarda dani, wani lokacin ina shiga ya ganni zai hau kuka, may be gani yake kamar zan tafi dashi namu gidan ne in rabashi da nasu".

Mukayi dariya, Affan d'an drama ne, indeed, tou muna sallama ya mik'o hannu yana tab'a Aaryan amma yana juyowa sai yayi sauri ya makalkaleni, wai kadda ya daukeshi, ya mik'o hannu kamar zai daukeshi, ya k'ara mak'ale min yace,
"Ba-by...

Abba...

Ummy...".

Mukayi dariya, Aaryan yace,
"Baby...".

Nace, "Sunana Mariam...".

Yace, "Maa shaa Aallah...

Wow...

Nice name...

Oohhh tou besty dinki bata fad'a min sunanki ba saidai tace baby, I thought rowar sunan kuke min shiyasa ban tambaya ba...".

A tare mukayi dariya suka shiga mota, na lek'a ta glass nace,
"Besty, wacece admin a group dinmu?".

Tace, "Bindawa admin ce...".

Nace, "Then ki tura mata numbata kice nice ta sakani a group, muga zata sakane ko har yanzu tana bin bayan d'an unguwarsu".

Ina tsaye saida motar ta b'ace min sannan na matsa, Aaryan kenan har da cewa bai siyo chocolate ba ballantana yaba Affan amma ga dubu daya, ya zaro sabuwar dubu daya ya mik'o mashi amma ya mak'ale min yaqi amsa, Affan kenan, murmushi nayi ina kallonshi yana kiran....

"Ba-by...

Ba-by...

Ba-by...".

Na juya na koma gida saidai zaro tsohuwar gwaramar wayata nayi nai zuru da ita, tou na gaza nuna wadda Aaryan ya bani tou ban san abun da zance ba, wai ashe har VTU yayi min sannan yayi min sending data, almost eleven thousand na samu a account dina, I feel inyi transfer din kudin a bani in sayi less din nine thousand in dinka in samu na shiga mutane, da daddare ina bud'e data na samu bindawa ta sakani group dinmu har da wani rubuta....
*_Welcome Mrs Aaryan to be_*
Wasu da suka sanni da Mahmud suka ce Mahmud dai, har gani nayi wata ta rubuta...
*_Babie ai har engaged anyi mata da Mahmud ko baki sani bane_*
Bindawa tace ai mun rabu, ita yanzu tana side din Aaryan ne, da alama akwai wata a kasa, daga nan abun ya zama topic of discussion, wadanda sukayi min sallama nayi masu reply na duba dp naga picture dinshi, yana sanye da wasu breathtaking k'ananan kaya, a London yayi selfie din, indeed he is damn cute, handsome, breathtaking, charming, alluring and mesmerizing, smile nayi na duba naga *Babie* ya saka min a sunan dake appearing a group, ban sauya komai ba, gani nayi yayi min sallama, da *heartbeat* yayi saved din numbarsa, murmushi abun ya bani, na amsa sallamar da yayi min, mun jima muna chatting, tou yana da murya mai d'ad'i amma bai tab'a kirana ba, koda yanzu typing kawai yake ba ya sending voice, sallama mukayi na kwanta saboda ina da lecture 8am, tou ya kamata in kwanta da wuri, tabbas hakane....

Washe gari tunda na tashi da asuba ban koma ba, bayan nayi sallar asuba nayi wanka na shirya tsaf sannan nayi kalaci a gaggauce, na mik'e tareda wanke bakina nayi brush, shadda ce blue a jikina lokacin naso nayi mata surfani saidai bamu da hali, lokacin saidai aka dinka min ita hakanan aka ratsa dark blue net a gaban shaddar sai dinkin yafi kyau sosai fiye da idan aka yi mata surfanin, long hijab har kasa na zura na rufe fuskata da niqab naja handbag dina nayi ma Ummy sallama na fice na tari keke napep, karfe bakwai da mintina ashirin tayi min a bus, hakanan naji ina sha'awar in shiga gallery, zaro wayar nayi na kunnata, wow, ashe har da pictures dinshi ya turo gasu nan birjik, looking breathtaking a kowane picture, har da hoton k'annanshi en biyu masu kama dashi, har da hoton wata cute mata ina ganinta na gane mahaifiyarshi ce, cin karo nayi da hotunan wannan chocolate din yarinyar, Aalima ce, saida gabana ya yanke ya fad'i, tabbas hakane ya faru da ni lokacin da na fara ganin hotonta, nayi gaba da sauri, tou bana son kasancewa a wannan yanayin, har da hoton wani babban mutum na gani wanda nike ganin shine late father dinshi, cin karo na k'ara yi da hotunan wannan chocolate yarinyar, da sauri na fice daga gallery din tareda bud'e data....
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
*Update Of June, 2019*
In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen
*Assalam Alaikum sis, complete ne nayi maku shi a matsayin barka da sallah, tou idan kina akan what's app kiyi min magana inyi maki sending document dinshi, idan kuma facebook kawai kike, tou kiyi hakuri har kuzo karshen*
Page. 5
Messages ne suka soma rushing, suna gudun wuce mate, ashe bayan na sauka hirar maganarnan suka cigaba da yi a group, saboda kusan kawayenmu sun sanni da Mahmud kuma sun san anyi mamu engaged, nikam ban damu ba koda za'a ce saboda kudi na guji Mahmud na so Aaryan, ai Aallah yasan zuciyata, Jalila ce naga tayi magana, rufe data kawai nayi na maida wayar a bag, before eight ina zaune a lecture hall, bayan mun fito daga lectures, ni da Jalila muna zaune a bus, macpolo ce kuma mutane kadan ne a ciki, ta zaro kwalin waya tareda tsohuwar wayata ta mik'o min, daman na san za'ayi haka, dubara kawai yayi min ta yadda dolena in amsa, amsa nayi na saka a handbag, nace,
"Dubara kawai yayi min...".

Jalila tace, "Aaryan yana sonki sosai, abokin Jalal ne sosai, ba ya da damuwa, Jalal ya sanshi ciki da bai...".

Sai kuma tayi dariya tace,
"Ya love din?".

Nima nayi dariya sannan nace,
"Har na mance da wani Mahmud".

Tace, "Kuma kika kira sunanshi...".

Mukayi dariya, tace,
"Kin san kuwa Aaryan miskili ne, magana wahala take mashi, da alama jiya zancen kurame kukayi".

Mukayi dariya, nace,
"Nima na lura da haka amma ba haka yake ba, yana da barkwanci, farko da smile da nodding kai kawai nike amma saida ya saka nayi magana, yana da surutu a gabana...".

Jalila tace, "Ooohhh...

Unbelievable...

Don yana sonki ne, ya nuna maki miskilancin ya gani ai sai ki barshi da miskilancinshi ki nemi wani...".

Mukayi dariya, tace,
"No more shedding tears kenan...".

Nayi rolling idanu nace,
"Yeah, soyayyar Aaryan ta kawo man farin ciki a rayuwata".

Tace, "Ooohhh ai na gani, mik'o wayarki in kashe mamu selfie".

Na zaro wayar na mik'a mata, tace,
"Cheese...".

Ta kashe mamu selfie a different style, ta jawo wayarta tace,
"Bari kiga inyi sending...".

Wayata ce ta soma ruri, saida gabana ya fad'i, Ammi ce take kira wato mahaifiyar Mahmud, ban yi picking ba, saida kiran yayi yawa sannan na tura mata sakon text message....

"Ammi koda na dauka ban san abun da zance ba, amma Ammi kiyi hakuri *BA NI DA LAIFI* Indeed".
Chapter 5 · 0% Book details