Sashe 16
Ba Ni Da Laifi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta b'ata min rai fiye da tunani amma babu abun da zai sauya a k'awancenmu, na zaro wayata na hau what's app, gani nayi wata er course dinmu ta shiga group tana tambayar gaskiya akan called up din engagement dina da take jin rad'e-rad'in anyi, bindawa ta tabbatar mata da hakane amma sai Jalila tace mata ta bita private taji, sai daga baya ta dawo group tace *_oohhh ashe haka abun yake_* Jalila tace *_hakane_* tab'e baki nayi ban sake mata magana ba har muka hau bus, har na koma gida ina mamakin abun da Jalila tayi min....
Washe gari ina zaune Aaryan ya kirani, picking nayi yace,
"Ki fito yanzu ina kofar gidanku".
Sai kuma yayi hanging call din, da mamaki nike kallon wayar, na mik'e tareda zura long hijab na duba fuskata sannan na zura takalma na fice, ina fita waje ya fito daga motarsa, kallo daya nayi mashi na gane yana cikin damuwa, na tsaya gefenshi, yace,
"Baby kinyi fad'a da Jalila ne?".
Da mamaki nace,
"A'a...
Wani abu tace maka?".
Da damuwa yace,
"Cewa tayi in rabu dake bata son in shiga cikin damuwa, na tambayeta idan kina da wani hali na banza ne amma tace a'a baki da damuwa ko kadan".
Na girgiza kai nace,
"Nima haka tace min jiya amma ka rabu da ita kawai...".
Yace, "Baby na tsorata, bana fatan in rasaki heartbeat...".
Ya jima sannan ya tafi while na juya na koma gida, ina shiga daki na jawo wayata na dannawa Jalila call tana picking nace,
"Kin kyauta...".
Daga daya bangaren Jalila tace,
"Baby bana san ku shiga damuwa ne shiyasa, yanzu kam ya rage maki ne ki rabu dashi ki tsallake abun da nike gudu ko kuma ki cigaba da kulashi nan gaba kizo kina nadama".
Tayi hanging call din, nayi jim sai kuma na share koma miye ita ta sani....
Washe gari ina daga daki naji Yaa Ahmad yana fadawa Ummy jiya Mahmud suma ya rinkayi, da yayi wata doguwar suma anyi tunanin ya mutu ne ashe da sauran lumfashinsa, amma yanzu gab zuciyarshi take da bugawa, I feel babu dadi amma babu yadda zanyi sam *BA NI DA LAIFI* saidai nasan kowa haushina yake ji suna ganin laifina, tou daga wannan lokacin ban k'ara jin wani ya kira sunan *Mahmud* a gidan ba....
Bayan kwana biyu ina zaune a daki sai ga kiranshi, yace,
"Ki fito ina kofar gidanku...".
Nace, "Mey?".
Yace, "Yeah ina kofar gidanku".
Nace, "Shine kake zuwa baka fad'a min ballantana inyi maka kwalliya".
Ina ji saida ya saki murmushi sannan yace,
"Surprise ne shiyasa...
Guess what?".
Nayi mashi shiru tareda hanging call din na fizgo hijab na zura koda fuskata ban duba ba, na zura takalma na fice, ina fitowa ya fito daga mota yana smile, Jeep ce baka, mai kyau, daga gani tana da tsada, na jingina da ita tareda bashi baya wai nayi fushi, ya zagayo inda nike tareda had'a hannuwa alamar bada hakuri sai kuma ya ware idanu yace,
"Kinga fuskarki kuwa...".
Na zaro idanu tareda jawo hijab ina goge fuskata, ya mik'o min wayarshi na duba fuskata naga babu komai, na kalleshi na turo baki nace,
"Please miye ka gani a fuskata...".
Shima Aaryan ya turo baki kamar yadda nayi yace,
"Sirri......".
Na shagwab'e fuska, ya kwashe da dariya, nace,
"Miye?".
Yace, "Wasa nike maki, babu komai akan fuskarki...".
Nayi mashi wani kallo, yace,
"Surprise...
Juya ki gani...".
Ya juya tareda knocking akan glass, wata cute babie mai kama dashi ce ta fito daga side din mai zaman hakanan sannan wata mai kama da ita sak ta fito daga backseat, twins ne, Adila da Adla, kowacensu tana murmushi, murmushi nayi na dubeshi yace,
"Surprise, kawo maki su nayi suyi maki wuni...".
Wani expensive less ne suke sanye dashi, komai nasu iri daya, hatta handbag, heel shoes, jeweleries, veil duk iri daya ne, murmushi na saki nace,
"Aaahhh...
Adila...
Adla...
Sannunku da zuwa...
Amma na gode da wannan surprise heartbeat...".
Aaryan yayi murmushi tareda waving min hannu yace,
"I love you...
Bye...
Take care...".
Sai kuma ya dubi tagwayen yace,
"Idan kun gama ku kira direba yazo ya daukeku...".
Ya shiga mota ya jata, en gulma idanunsu suna a kai, na jasu muka shiga ciki, Ummy tana zaune tsakar gida, suka gaidata ta amsa tana kallonsu nasan taga kama, na jasu dakina suka zauna na d'age masu labule saboda ana zafi, na kawo masu fan tareda zama nace,
"Sannunku da zuwa amma naji dadin zuwanku, kun kyauta, nasan twins ne saidai ban san wacece Adila ba, wacece Adla...".
Sukayi dariya ta kusa dani tace,
"Nice Adla...".
D'ayar tace, "Ni kuma Adila...".
Nace, "Bari in kawo maku ruwa...".
Adila tayi murmushi tace,
"A'a mun hutar dake, da ruwanmu a bag, ai ba zamu wahalar da babyn broz ba".
Nace, "Kunzo lafiya?".
"Lafiya lau...".
"Ya su Umma da Mom?".
"Suna nan lafiya lau...".
Nace, "Gaskiya kuna kama dashi sosai...".
Suka saki murmushi, nace,
"Ga shi bai fad'a min zuwanku ba ballantana in tanadar maku da wani abu amma akwai tuwo, hope zaku ci".
Adila tace, "Zan ci...".
Adla tace, "Nima zanci amma idan miyar kuka ce...".
Nace, "Baki da damuwa itace, ai koda ba ita bace na shiga kitchen in kad'a maki...".
Na mik'e naje na zubo masu na had'o masu da spoon saida na shiga makotanmu na sawo man shanu na zuba masu a miyar sannan na kai masu, bowl din da miya take daban wanda tuwo yake daban, suka ci abunsu, Adila tace,
"Ruwa...".
Na dauko masu buta suka fita suka kuskure bakinsu suka koma daki kowace ta fiddo rubbar swan daga bag ta kafa lips, naji dadin zuwansu, muka sha hira, suna da kirki, basu da damuwa, har kayan da Mom ta bani na dauko masu suka gani, sun yaba, farat daya naji sun shiga raina, na rasa abun da zan basu, wani d'an karamin kit Adila ta zaro daga bag ta bud'e, wow sakar ce mai kyau daga gani zatayi tsada, tace,
"Da mukaje Dubai tareda Umma muka sawo maki ita...".
Adla tace, "Kuma zatayi maki kyau".
Na amsa nace,
"Kai amma sunyi kyau, na gode sosai".
Adila tace, "Saka mu gani...".
Na saka kuma tayi min kyau na cire na maida, har hotuna mukayi, nayi excusing kaina na shiga makotanmu nayi amfani da kudin da Aaryan yaba Affan wadanda Ummy ta maido min, na siya masu kayan snack tare dasu aya mai suger, gyad'a da sauran kayan makulashe, na basu aiko sunji d'ad'i, suka kira direba koda yazo call ya danno ya sanar dasu, Adila tace,
"Kinga direba yazo...
Yauwa don Aallah Aunty ki kula mamu da broz kinga tunda Aalima ta b'ace yake cikin damuwa saida ya hadu dake sannan walwalarshi ta dawo...".
Saida gabana ya fad'i, tace,
"Broz yana da damuwa, abu kadan zai iya sakawa zuciyarshi ta buga...".
Adla tace, "Please ki tayamu tattalinshi, shi kadai garemu...".
Nace, "Kadda ku damu...".
Suka yafa veil suka dauki bag tareda leather da na basu, muka fito sukayi ma Ummy sallama na rakasu har wurin mota suka shiga saida naga tafiyarsu sannan na juya na koma gida....
Washe gari ina zaune hakanan a daki na jawo wayata na kira Aaryan, yayi picking mukayi exchanging sallama and greeting, yace,
"Baby you called me, na gode...".
Nace, "Baby I miss you...".
Saida yayi dariya sannan yace,
"Nine baby kuma?".
Nace, "Ehhh mana...
Kaga kai baby nima baby mun koma babies...".
Daga daya bangaren Aaryan yayi dariya sannan yace,
"Baby kin san mey?
I love you...".
Sai kuma naji wayar tayi dif ina magana babu respond, kuma bata tsinke ba....
Abba ne naji yana kirana....
"Mariam...".
Saida gabana ya yanke ya fad'i na mik'e tareda tura wayar a bag sannan na fito, shi da Ummy ne zaune akan tabarma na durkusa a gefensu, Abba ya dubeni yace,
"Mariam maganar aurenki da Mahmud tana nan babu abun da ya sauya, lokacin da kika sameni da maganar kin fasa aurenshi na fad'i maki ne kawai shima na fad'i mashi maganar aure sai idan kun daidaita kanku amma na fad'i ma waliyanshi maganar aure tana nan babu fashi, tabbas nasan Mahmud nasan halinshi abun da ya faru can tsakaninku ne, ni miji na gari nike nema maki kuma Mahmud ya cika miji na gari, ina gani bazan bari ki rasa wannan mijin ba, kuma ina gani bazan bari ya rasa ranshi saboda ke ba, Mahmud yaron kirki ne, before sai kin gama bautar kasa sannan za'ayi auren amma yanzu kina gama karatu za'ayi...".
Tunda ya fara magana naji jikina ya zama very weak, mik'ewa nayi na tafi luu, next duhu ne, daga nan ban kuma sanin abun da ya faru ba, saidai bud'e idanuna nayi na ganni akan gado a asibiti....
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
*Update Of June, 2019*
In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen
*Eid mubarak our greatest babies, tou ina nufin wadanda ake kira baby, ehe, tou wish you all the best....*
*Hope kunyi sallah lafiya dearies, wish you all the best....*
Page. 15
Na d'aga idanu Ummy na gani then Yaa Ahmad da Nadiya, fashewa nayi da kuka, suna min magana amma nayi shiru sai idanu kawai, Ummy ce fita jim kadan ta dawo tareda likita, dakyar ya samu nayi shiru ya dubani ya fita saidai kafafuna rawa suke koda mik'ewa bana iyawa, cire min drip aka yi, tou daga zaune nayi alwalla na rama sallolin da ake bina ashe kwana nayi, aka bani abinci naci sannan na koma na kwanta ina hawaye, Yaa Ahmad ne ya mik'o min wayarsa, Yaa Ayan ne akan layi, na amsa tareda fashewa da kuka, daga daya bangaren Yaa Ayan yace,
"Baby yi shiru zamuyi magana...".
Cikin kuka nace,
"Kana ji Abba yace dole sai na auri Mahmud, ni kuma Aaryan nike so and kasan Aaryan kasan halinshi tunda na bashi numbarka har gaisawa kuke, Yaa Ayan ka taimaka min ni bazan auri makaryaci ba...
Tabbas shi makaryaci ne...".