← Book details Alqibla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 69

Sashe 8

Alqibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yaro ne yayi sallama yace ana kiran yammatan da suka shigo dazu,murmushi tayi tace
"Kai nuradden" ta tsammaci shi ya aiko,don haka ta yafa mayafinta tace dasu
"Ina zuwa minti biyu" harararta salma tayi
"Kedai kawai sai mun ganki".

A hankali ta tsaya qofar gidan tana waige waigen neman nuraddeen,sallama taji anyi daga bayanta,cikin mamaki ta juya tana duban mai sallamar,don bata son muryar ba bare fuskarshi
"Ni na aika a kirawoku,kuma sai naci sa'a ke din ce ta fito,naga shigarku gidan tun dazu,saina kasa sukuni sai nayi magana dake" dubansa kawai take ba tare data iya cewa komai ba don ta rasa abun cewar,tasan cewa nuraddeen na dab da isowa,kuma tafi kowa sanin halayyarsa na tsananin kishinta,don koda waya ya kira yaji busy ya dinga mita da qorafi kenan yana tambayarta dawa take waya.

Tunaninta ne ya yanke lokacin da taga nuraddeen tsaye daura dasu,a hankali ya tako ya raba tsakiyarsu yana fuskantar saurayin
"Malam me kakeyi a nan?" Yadda ya tsare gida yasa ya tsammaci wani makusancinta ne ko kuma yayanta,don haka yace
"Magana nakeso muyi da ita ne"
"Bace daga wajan nan tun kafin ranka ya baci,don tuni an mata miji,saura kwanaki kadan aurenta"
"Ayyah,ai ban sani ba kayi haquri don Allah,fatan alkhairi" ya fada yana juyawa yabar wajen.

Sai da yayi nisa da wajen sannan ya waiwayo inda take tsaye,fuskarshi da alamun fushi yake dubanta
"Waye wannan zahra?,dama zaki iya tsayawa da wani ki saurareshi bayan ni?" Ya fada yana nuna kanshi da yatsa,kai take kadawa cikin damuwa
"An aika ne ance naxo,na tsammaci kaine,koda na fito ma babu wata magana data hadani dashi,kayi haquri"
"Zahra...kinsan yadda nake sonki?,kinsan yadda nake kishinki kuwa?,da kin sani da ko na second daya ba zaki tsaya da kowa ba"
"Kayi haquri nace,nima ban zaci wani bane daban" sosai nuraddeen ya dinga fushi,da qyar ta lallabashi ya sauko.

Kusan hirar tasu ma batayi tsaho ba yayi mata sallama ya wuce,ta tsammaci zai dade dayawa tunda shine haduwarsu ta farko bayan dawowarta daga makaranta,haka ta shiga gidan tana tunani hannunta dauke da siyayyar daya saba kawo mata lokaci lokaci idan zaizo,basu sake wani jimawa ba suka wuce gida suma,saboda sanin dokar gidansu na hanasu yin dare a waje.

Sanye yake da wadansu irin t.shirt da trouser masu azabar kyau,wadanda suka dace da jikinsa,suka kuma bayyanar da kwarjininsa haiba gami da kyawun surarsa da na jikinsa,kyakkyawar fuskarsa sanye da wani glass mai duhu daya sake qawata adonshi ya kuma qara masa kwarjini wanda yakanyi amfani dashi lokaci zuwa lokaci idan yaso hakan,ko kuma miskilancinsa ya motsa,qafafunsa cikin wani hadadden takalmi both,motarshi na fake daga gabanshi kadan,da alama fita zaiyi,wayarsa daya na a kunnensa,daya kuma yana danne danne da ita,ma'abocin amsa waya ne,da wahala ka sameshi ba kan waya,wanda kusan fiye da rabinta yana yine kan abinda ya shafi aikinsa.

Dab dashi mai adaidaita ya saukesu,saida gabansu dukka ya fadi,musamman zahra data soma gyara yafen mayafinta sanda suka hada idanu dashi,yayin daya kau da kai kamar bai lura dasu ba yana ci gaba da amsa wayarsa.

A gaggauce ta amshi canjinta sannan ta biyo bayan salma zuwa hanyar gate din gidan
"Barka da yamma" salma gadan russuna kanta tana gaidashi,sai itama ta motsa bakinta kamar ta gaidashin tana mintsinin salma,so tayi kawai ta basar su wuceshi tunda waya yake amsawa,gaidashin tana ganin kamar callig attention dinsa ne a kansu.

Hannu kawai ya daga musu ba tare daya dubesu ba,tuni zahra ta zagaye ta wuce salma,tayi gaba zuwa cikin gidan tana murnar da baice komai ba.

Saidai kafin takai ga shigewa ta jiyo sautin dakakkiyar muyarsa mai cike da kwarjini irin ta soja yace
"Ke!,zonan" kasa waiwaya tayi sai salma ce ta nuna kanta
"Ni?" Banza ya mata yana latsa wayarsa,hakan yasa ta waiwaya tana yiwa zahra inkiya akan taje da ita ake.

Tilas tunda su biyu ne a wajen ya sanyata nufar inda yake tsaye,daga can gefansa ta tsaya,tana motsa bakinta,cikin ranta tana fadin
"Allah ka rabamu da masifa da jaraba,Allah ka kadashi wannan mutumin ya koma inda ya fito,yaje can ga qaraci baqin ranshi"tambayar daya jeho mata kan mayafin jikinta ya katse dukka tunaninta,ta soma bin jikinta da kallo,kafin ta gama nazarin abinda yace ya sake fadin
"Idan basu gaya miki ba nida kaina zan gaya miki,daga yau....kinji me nace?" Kai ta gyada kawai sannan ya sake cewa
"Daga yau sai yau,kada na sake ganinki da mayafi irin wannan na jikinki,bazan tsawaita bayani ba,amma idan kunne yaji jiki ya tsira" daga haka ya soma takawa yana yin gaba,hannunsa daya soke a aljihun wandonsa.

Miqews tayi da sauri gana gunaguni qasa qasa ta yadda bazai jiyota ba,tana shiga taga salma tsaye jikin gate,da sauri ta iskota tana cewa
"Bai dai miki komai ba ko?"
"Nifa gsky na soma qosawa da halinsa,fisabilillahi yayita bamu doka da order kamar ance masa a brrack ake ko a filin daga,shikenan a gidan nan baka da damar sakewa kamar a sansanin bada horon sojoji" dariya salma ta saki harda riqe ciki
"Kece son rayuwar 'yancin naki ne yayi yawa,hala shi yasa duk yawan qorafinki yafi namu"
"To a prison muke da zamu dinga rayuwa haka,Allah na kusa fara murje idona ina masa musu" dariyar salma fin ta dazu tayi
"Kema kinsan mafarki kike,amma....dama zaki gwada wallahi" ita kanta saita murmushi ya subuce saman fuskarta duk da yanayin bacin ran da take,hakanan bata shiryawa hakan ba
"To muguwa,ya azabtani kina gefe ko haquri babu lallai ki bayar".

Zahra suka hango na tahowa cikin shigarta tako yaushe hijabi mai hannu,a hankali take tafiya,tadan janyo hijabin kadan yadan rufe mata rabin fuska
"Lover yaaya ina zuwa haka?" Salma ta fada cikin salon tsokana,murmushi mai sanyi tadan saki,hakanan muryarta da sanyi tace
"Asibiti xanje"
"Waye ba lafiya?" Inji xahra tana dubanta,sai data dan dafe kanta kadan sannan tace
"Nice wallahi,ciwon kaine ke damuna tun jiya"
"Ke kadai xaki,ko nazo na rakaki?"
"Yauwa,da kin taimakeni kuwa,tare da yaa haidar zamu,ni kuma kunyar fita mu biyu nakeji,banda ya matsanta ma dasai gobe kawai nahau adaidaita ta kaini ta dawo dani" baki salma ta wangale
"Kaga shugabannin masoya,saikun dawo Allah ya kiyaye hanya,amma wannan rakiyar tafi qarfin salamatu" waiwayawa tayi ga zahra
"To takwara ke taimaka don Allah" fuska ta yatsina ta nuna kanta
"Ni?,Allah suturu buƙui inji kishiyar me doro,idan kin ganni a lahira kaini akayi,yanzu ya gama cimin mutunci,a dawo lafiya" murmushi zahra tayi tana kama baki
"Na gode dacin fuskar da kukemin Allah,babu komai watarana saina rama dukka akan mazajenku,har yanzu kun kasa fahimtar yayanku,amma ina da yaqinin wataran idan kukayi aure zaku fahimceshi kamar yadda su anty asiya suke ganeshi kadan kadan yanzun,kuma gaba zaku gane cewa he is the best and d most kindly gentle man in d world" dariya sosai suka sanya,zahra tace
"Kekam ai dole ki yabeshi,ai masoyi baida laifi sam a rayuwar masoyinsa,ta nan kam banga laifinki ba" daga haka tayi gaba abinta.

Dab da zasu shige sassan hajja sukaci karo da hafsat
"Kun dawo kenan?"
"Mundan tsaya ma da yaa zahra,tana ta koda masoyinta,wai asibiti yaa haidar zai kaita take neman dan rakiya....wa zaije?" Salma ta fada tana kama haba
"Ah haba don Allah,ai ko bari naje na mata kara" daga haka tayi gaba da sauri,zahra ta bita da kallo tana son hanata amma tuni tayi gaba,dole ta barta ta wuce sassan hajja,salma ta wuce nasu sassan,tana son ta fara watsa ruwa sannan takaiwa mamanta saqon da abban gwammajan ya bata ta kawo mata.

Tana tsaye tana gayawa hajja ta dawo saiga hafsat ta shigo,kallo daya tayi mata ta sheqe da dariya
"Allah ya qara,hala an tallo qeyarki ne?" Cikin fuskar takaici ta bata amsa tana miqewa saman doguwar kujerar hajjan
"Inda qeyata ma ya tallo kawai da da sauqi,yarfani yayi kawai gaban abu sufyan(abokinsa)" dariya sosao zahra tasha harda buga qafa,ta samu abun tsokana,bata qyaleta ba har sai data yunqura takai mata dundu sannan ta wuce dakinta da gudu hajja na musu addu'ar shiriya.

Cikin kwanakin hutunta tayi hutunta kamar yadda ta saba cikin ahalinta,saidai abu daya daya mata tarnaqi a wannan hutun,ya kuma zame mata baqon lamari wanda bata saba dashi ba shine,rashin samun cikakken lokaci daga wajen nuraddeen,duk wasu qa'idoji na yaa haidar da matsinsa sam bai dameta kamar yadda take samun rashin cikakken lokaci tare da nuraddeen din ba,koda yause cikin bashi uzuri take a karan kanta,bata son ko daya zuciyarta ta tuhumeshi,tunda ada ba haka yakeyi ba.

¶¶¶¶¶¶ ¶¶¶¶¶ ¶¶¶¶¶¶ ¶¶¶¶¶

Kwanaki uku duka duka suka rage hutunsu ya qare su koma makaranta,anata mata shirye shiryen komawa makaranta kamar kowanne lokaci,hakanan itama ta hada kusan duk abinda tasan zata tafi dashi,saidai duk wani abu da takeyi jikinta a sanyaye yake,saboda tabarbarewar tarayyarta da nuraddeen,wanda har yanzu batasan dalili ba,batasan meya kawo hakan ba,bata minti goma cikakke bada wannan tunanin a ranta ba,hakan ya janyo raguwar walwala da karsashinta.

Da yammacin ranar suna sassan abba babba,dan malele suka hada nadiya na kitchen din tana musu,mama nata mitar suyi su gama za'a dora abincin dare,saura na zaune a falon suna hira,hafsat na yiwa zahra kitson komawa makaranta.

Duk wannan hirar da ake zahra na jinsu,rabin tunaninta yana kan nuraddeen,wanda a baya duk lokaci irin wannan da take gab da komawa makaranta basa rabo da yin waya,hakanan bai gajiya da aiko mata da siyayya na abubuwan qwalama don tsarabar komawar,duka ba wannan ne ya dameta ba kamar rashin jinsa da kuma rashin samun kulawarsa a gareta kamar baya,duk sanda ta masa qorafi yakan bata lokaci yana rarrashinta kan cewa busy ne yayi masa yawa,ta masa uzuri,yana son ya kammala ne,komai zai daidaita in sha Allah.

Yadda yake lallamar nata ya dan sanya take samun relief kadan.

Suna tsaka da kitson wayar tata dake tsakiyar cinyarta ta dauki ringing,tuni ta gane waye,saboda kida na musamman ta saka masa.

Dan qwace kanta tayi daga hannun hafsat cikin hanzari tana cewa
"Ina zuwa" ta miqe da sauri ta nufi dakinsu hafsat.

A gyare kuma atsaftace dakin yake kamar yadda kusan dukkansu haka aka horar dasu sanin muhimmancin tsafta,duk da girman gidan da girman kowanne sashe amma zaiyi wuya ka shiga ka tadda qazanta.

Salma ce kawai a dakin,da alama itama waya take,saita samu gefan katifar ta zauna tana amsa wayar.
Chapter 8 · 0% Book details