← Book details Alqibla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 69

Sashe 32

Alqibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaba daya fuskarta ta kode ta jeme kai kace zaman takaba takeyi,saidai abinda ta fuskanta shine babu wanda ma ya damu da damuwarta,tun bayan da zancan ya soma zaga gidan duk wanda ta kalla sai taga fuskarshi a sake take da walwala,bugu da qari kuma saiga kira daga hafsat yusra yasira da salma,duk wadda ta kira tana kiranta ne da ihun murna gami da tambayarta ya akayi haka ta faru?,baqinciki bai iya barinta cewa komai,saidai ta datse kiran,kuma ba zata sake daga kiran su ba,saidai suyita kira su gaji,daga qarshe saidai ta jisu suna waya da hajja daga falo,daga nan babu me sake kiranta,da alama ta gaya musu yadda aka qulla abunne ba bisa son ran kowannensu ba.

A kullum idan gari ya waye dama bata da wani aiki zaman daki tun daga wancan lokacin,saidai wanka sallah da kwanciya,abinci kuwa sai taji kamar cikinta zai hade da bayanta sannan zata dan tsakura ta koma ta kwanta.

Yauma kamar kullum,tana nan zaune gefan katifarta bayan ta gama wanka ta saka riga da zani na atamfa hajja ta turo qofar dakin ta shigo dauke da kwanukan abinci,wanda kullum ita da kanta ke kawo mata koda ba zata kulata ba,zata kawo mata ta ajjiye ta juya ta fita abinta ta barta.

Yau din data dora abincin saman inda take ajjiye mata saita qaraso inda zahran ke zaune ta zauna gefanta
"Ki zauna dai kiyita sanyawa ranki damuwa....ki hadu da wani ciwon tunda qananun shekarunki" karon farko tun bayan zancan da hajjan tabi ta kanta harma ta tanka ta,sai qwalla ta cika mata idanu,ta zumbura baki murya a dasashe tace
"Idan ma ciwon ya kamani aiba damuwa kikayi dani ba,kinga saina mutu kowa ma ya huta" murmushi ne ya kunbcewa hajjan
"Au Allah....saboda na miki gata na baki dandasheshen jikana....shine zaki ce haka?,au ashe?,sakayyar ma da zakimin kenan,maimakon ki bani danqwalelen goron albishir?"
"Ni so nake.....haka kawai ina zamana....saboda Allah bai kawomin miji ba shine za'ayi sadakata" ta fada tana fashewa da kuka,jikin hajjan sai yayi sanyi,saita koma cikin seriouse dinta bayan ta dafa bayan zahran
"Zahra'u,ki tsaya ki nutsu kiji abinda zan gaya miki,na tabbatar dama da farko zakiji babu dadi,zakiji na takuraki,zakiji ban miki adalci ba,saboda kaf cikin 'ya'yana ko jikokina babu wanda na taba yiwa irin hukuncin dana miki....amma abinda nakeso ki sani shine,soyayya da qauna ce tasa nayi miki hakan,na tabbatar ko ba dade ko bajima zakimin godiya,zakiji kuma dadin wannan abun dana miki,alfarma daya nake nema a wajenki idan har na isa,idan har ina da kima da mutunci a idanunki" shuru hajja tayi tana kallon zahra da kukanta ya tsagaita,saita dora
"Na sani cewa a yanzu baki da wani daya shiga zuciyarki bare kice na miki karan tsaye....da wannan nake neman alfarma daga wajenki daki sassauta zuciyarki,ki cire wannan quncin takura da takunkumin da kika sanyawa ranki,ki yi juriyar maida komai ba komai ba....ki bawa aliyyu dama....na miki alqawarin cikin shekara daya indai ya kasa shiga zuciyarki da kaina zan amsar miki takardarki kije ki auri dukkan wanda yayi miki,kuma babu wanda zai tada hukuncina....abinda nakeso shine kawai ki kwantar da hankalinki" shuru tayi tana nazarin maganar hajjan tare da kokwanto,saidai cikin hikima da dabara irin tata ta tsofaffi ta samu tadan sauketa kadan,aka samu canji duk da ba wani me yawa bane.

_hello assalamu alaikum zafafa fans,kuyi haquri da jina shuru jiya,bana jin dadine,yauma da qyar na hada wannan,so idan kun jini shuru gobe kuyimin uzuri,amma in sha Allah ma zan qoqarta,kuci gaba dai dayi mana uzuri kamar yadda kuka saba,mu din 'yan adam ne kamar kowa,mun gode da yadda kuke fahimtar damuwoyinmu_🙏🏽🙏🏽🙏🏽🥰🥰🥰22

_*LAVENDER RESTAURANT..*_
_(Palace of mouthwatering food/delicacies)_

_IDAN KUKAJI GANGAMI DA LABARI, INA MASU SON INDA ZASU SAMU INGATACCEN ABINCI MAI DADI DA LAGWADA? KAI BA ANAN MUKA TSAYA BA, INA SABBIN AMARE? MAMAs, YAYYU? DA KANNEN MU MASU SON KOYAN GIRKUNAN YAN GAYU NA KASAR NIJERIYA DA KETARE?_

_*TO KU MATSO...! AT LAVENDER RESTAURANT GOTS YOU COVERED. ABINCIN KASASHE DA DAMA MUKE KOYARWA,,COME LETS UPGRADE YOUR FOOD TIME TABLE, MATSO KUSA YAR UWA GA DAMA DA ZAKI CANZA YANAYIN ABINCIN GIDAN KI, KOWA YASAN IYA SARRAFA ABINCI NA TAKA RAWAR GANI A GIDAJEN AURE. KAI KO BUDURWA CE INDE KIN IYA GIRKI ZAKIGA KOWA YANA HABA HABE DAKE.._*

_*UNCLES, DADDIES, BROTHERS., NEWLYWED HUBBYS..! KU ZO KU YIWA ‘YAYAN KU, MATAN KU DA KANNEN KU RAJISTAR WANNAN HARKA TA KOYAN GIRKI.._*

_*Lavender catering school zamuyi practical class. zamuyi 30 dishes continental,snack & desserts, traditional dishes, drink. Fee din 40k NE. phone number WhatsApp and call 09080299283 akwai discount na 5% ga mutum uku farko wadanda sukai register aranakun independence 1/10/2021 to 3/10/2021 Nigeria @ 61_*

_*ZA’A FARA CLASSES RANAR 14/10/2021. WATO SHA HUDU GA WATAN OKTOBAR DA MUKA SHIGA YAU._*

_*GIRKE GIRKE GUDA 30😫😨AKAN DUBU 40 KAWAI, HARDA BONUS NA SNACKS, DESSERTS, TRADITIONAL AND MODERN DRINK, GARGALIYA DA ZAMANI🥂WATA DAYA CHAS ZA’AYI ANA KOYAN GIRKE GIRKEN. _*

_*KU SAKE KARANTA WANNAN BONUS DIN👇🏾RIGIJI GABJI_*

_*Nigeria @ 61 _*
_*COOKING COMPETITION!!!_*

_*from lavender Catering ina masu son koyon girki ga dama zaku shiga gasarmu ta girki bayan kunyi register damu akan 10k,wanda yazo na 1zai shiga ajin mu free hade da wasu prize din na 2 da na 3 kuma zasu bayar da rabin kudine da wasu prize suma saura kuwa zasu ayi musu ragin 5% da wasu prize wannan gasa zamu yita ranar lahadi ne 3/10/21 zamu rufe registration na gasar ranar asabar_*

_*LAVENDER RESTAURANT: NA GARIN KANO, CLASSES DIN AKWAI PRACTICAL AND ONLINE CLASS GA WANDA KE NESA_*
________________________________

Cikin kwanakin ikon Allah kawai zahra take kallo,yadda aka tada shirye shiryen daurin aure gadan gadan,saiga dinkuna hajjan tayi mata na shaddodi da atamfofi,ko kallon inda suke ita dai batayi ba,saboda ta fuskanci kamar ma kowa goyon bayan abun yakeyi.

Ta fannin aliyyu kuwa shiryen shiryen qarin girma da za'a masa ya janye hankalinsa sosai,don har wani lokacima yakan sha'afa da batun idan ba wani bane daga gida ya tada masa zancan,baya ma samun zama sosai,wani lokacima ba'a gidan ko a garin yake kwana ba.

Ana ya gobe daurin aure saiga baqi sun fara cika gidan,tun zahra na daukar abun me sauqi harta fahimci babba ne,saiga su yusra ma duka sun hallara,salma ta soma mata zancan itako ko qunshi da gyaran kai mana ayi mata a ranar dai.

Yadda ta rufe ido tayi ma salman tas da duk wanda ya goyi bayan zancan salman ya tabbatar musu da cewa lallai a wuya zahran take,ta dinga balbala masifa da bala'i har sai da kowa ya dare ya barta,ta buga tsaki ta sakawa dakinta key tayi kwanciyarta,bata sake bude dakin ba har zuwa washegari da safe,data tashi tana jin yunwa,sassan hajjan kuma akwai baqi,sa'annan haushin kowa takeji,batason yiwa kowa magana bare ta buqaci abinci a wajensa,don haka ta zurma hijabinta babu wanka ko kwalliya tattare da ita,kamar ba ita ake shirin daurawa aure ba tayi sassan umminta.

Abinda ya sake daure mata kai haushi ya cikata shine samun ummin nata da tayi tayi wanka abinta ta shirya cikin dinkin shadda sabuwa gal,daga ita har ilham da yusuf da sulaiman dukka iri daya.

Can dinma akwai baqi,duk da baikai cikar sassan hajja ba,saita gaisa dasu suna kiran amarya amarya,ba wanda ta tankawa,abincinma ji tayi ya fice mata a ka,don haka ta koma da baya zuwa sassan hajjan.

Mutane ta tarar yanxun a dakin nata ciki harda suwaiba,koma bayan dazu data fita babu kowa a ciki,hasina dake zaune gefan katifarta ce tace
"Ah,hala sabani mukayi,ummi tacemin kina nan,na shigo kuma ban tadda ki ba"
"Eh" ta amsa a taqaice tana isa bakin madubi ta dauki brush da maclien tayi bandaki,da hanzari hasina ta miqe tabi bayanta cikin bandakin.

Ta sameta harta soma brush din,saita jingina da qofa tace
"Wai zahra me kike yine haka?,nida salma ta bani labari na zaci iskancinki ne kawai,ai koda za'a miki auren da bakiso yanzun ai an daina wannan duhun kan,da iliminki fa?,barema miji irin Aliyyu....hmmm wallahi kukan dadi ma kike,hadadden mutum gentle man irinsa?,tsada fa irinsu suke wallahi" kamar jiran hasinan itama zahran take,saita hau kuskure bakinta sannan ta waiwayo ta dubeta
"Tunda ya miki me yasa baki magantu ba tun wuri ke an baki shi ba?"dariya hasinan ta saki tana daga hannayenta sama alamun surrender
"Kai ina....babban goro ai sai magogin qarfe,wallahi yafi qarfina tako ta ina,ya haidar ai sai irinku....yanzu dai ki maida wuqar....don Allah zahra,kodon ki farantawa umminki rai ki saki ranki kiyi abinda ya kamata,wallahi wallahi tun shigowata gidan nan na fara ganin fuskokin 'yan baqinciki muraran,ko a dakinkin nan ma yanzu akwai yan baqinciki da yan saka idanu zaune suna aikinsu,don Allah karki fito sai kinyi wanka....na roqeki" ta fada tana hada hannayenta waje guda,harara zahran ta jefa mata sannan tace
"Naji....ki bani waje,ko kuma a gabanki zanyi wankan" dariya ta saki tana girgiza kai,haka kawai ta zama wata rigimammiya ta gaske,fita tayi gami da ja mata qofa.

Tana zama saiga anty alawiyya ta shigo itama dauke da qaramin yaronta
"Ina amaryar?" Ta tambaya suwaiba,saita yatsina fuska ba tare data amsa ba,hasina dake danna waya ta dago kai
"Tana wanka anty alawiyya"
"Toh....bari ina zuwa" ta fadi tana fita.

Kusan minti ashirin sannan zahran ta fito,wanda yayi dai dai da dawowar anty alawiyya,ta nema duka mutanen dakin su bata waje,sai hasina ce kawai ta rage.

Fada ta soma yiwa zahran sosai kan yadda ta maida kanta,ta kuma tilasta mata ta shirya,hakanan tana baqin rai da dacin rai ta shirya din,abinda yadan rage mata baqincikin shine zuwan hindatu,wanda bata tsammaci zuwan nata ba,tana bata labarin yadda suke kula da komai nata na makaranta,harda su CA da suke mata,wanda taji dadin hakan,saidai hindatun ta tambayeta dama zahran tasan aure zatayi shi yasa bata kula kowanne namiji,amma kuma koda wasa bata taba gayawa wani ko bashi labarin auren nata ba,harda ita karan kanta,duk da yadda suke?
"Uhmmm" kawai ta iya cewa hindatun ba tare data bata amsa ba.

Su ukune rak cikin katafaren dakin hotel din da suka sauka a daren jiya,haidar dake kwance rigingine hannunsa riqe da waya yana dannawa,sai Fahad dake zaune a gefansa yana latsa system din dake gabanshi.

Turo qofar akayi aka shigo,saif ne dauke da wata baqar leda dake dauke da tambarin wani kamfanin dinke dinke daya shahara a nigeria,inda suke saida kaya ready made kowanne iri.
Chapter 32 · 0% Book details