Sashe 33
Alqibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fahad ne ya amsa sallamar,ya qaraso ya cilla ledar gefan haidar yana dubanshi
"Ga kaya nan ka tashi ka shirya" ya fada yana zare sau cikin qafarsa,tsaki haidar din yayi yana sake dora qafarshi daya kan daya
"Ka qyaleni haka saif please,already na gaya musu ban shigo kano ba,ba lallai na samu zuwa daurin auren ba"
"Idan baka je ba kuma kayi yaya da sauran abokananmu da su zasu halarta" wani irin zabura yayi ya miqe ya zauna sosai saman gadon,da qarfi ya furta
"What!....waye ya gayyacesu?,waya gaya musu?" Ba tare daya ce masa komai ba ya nuna masa fahad da yatsa wanda keta latse latsensa ba tare daya tankasu ba.
Wani mugun kallo ya jefa masa sannan yace
"Waya saka?,waya aikeka?" Sai sannan fahad ya kalleshi
"Ra'ayi da radin kaina....waikai malam ma tsaya,duk fa wannan botsare botsaren da kake na banza ne da banga amfaninsu ba....qarya ma kake kace tun da can baka son yarinyar nan,in kuma kasan hakane me ya hana ka bamu dama mu da muke muradi?,da munyi magana sai kace mu kama girmanmu kai bakason raini,to yanzu ga qarshen tika tika nan,idan zaka tashi ka shirya kawai ka shirya bamason gulma da pretending"sosai saif keta qoqarin danne dariyarsa saboda ganin yadda haidar din ya zuciyo,ai kuwa basu ankara ba ya kaiwa bayan fahad harbi da qafarsa,Allah ya taimakesa ya goce yana dariya.
Ganin fahad xai jiqa musu aiki yasa saif ya koreshi waje
"Ka bamu waje da Allah malam" ya fada yana hade rai,saiya tattara tarkacensa ya fita yana fadin
"Ana so ana kaiwa kasuwa"
"Ka gaya masa....ni ba abokin wasansa bane wallahi ya shiga hankalinsa....if not zai raina kansa"
"Calm down mana aboki"cewar saif yana zama kusa dashi
"Ni ina mamakin wannan abun da kakeyi....banda abunka ai an wuce wannan qarnin,kada fa ka manta koda baka so kana da right na qara auren wadda kakeso,a yanzu bayan ita akwai uku a gaba ba zata tare maka komai ba,sannan kome zakayi kada ka duba hajja mana,ka duba iyayenka da aljannarka ke qafarsu,kada kayi abinda zaka watsa musu qasa a ido,wannan nasarar qarin girma daka samu duka sirrinta shine yadda kake kyautata musu da binsu,kada ka watsa albarkarka akan wannan minor issue din mana...and mamar zahran,ko yaya uwa uwace,haka ɗa ɗa ne,ko yaya tana son diyarta,ko yaya wani abu mara dadi ya bullo akan diyarta koda ta boye a fuskarta lallai tana jin ciwo a zuciyarta,da kanka ka gayamin matar she mean alort to you....."
"Ya isa" ya dakatar da saif,tsahon mintuna biyar sannan ya aje wayar hannunsa ya miqe kana ya wuce bandaki kai tsaye.
****** *BAYAN WASU WANNI**********
Shudewar wasu qididdgaggun awanni da basu da tsaho unguwar tayi wani irin cikar kwari na ban mamaki,dimbin jama'a masu tarin yawa suka shaida daurin auren ALIYYU MAS'OD DABO da FATIMA SA'ID DABO bisa sadaki naira dubu dari,wanda abban tsakiya shi ya biya lakadan.
Dashi da zahra dake cikin gida dukkansu jin sanarwar daurin auren suke kamar a labarin tatsuniyoyi,kamar wani mafarki suke da babu dadewa zasu farka suga ba gaske bane,don haka shi haidar dinma ana gama dauraws maimakon ya shiga cikin gidan saiya shiga mota kawai,ya umarci drivern daya fara yawo dashi ya kaishi wani masaukin baqi na musamman ya kama daki na kwana biyu,babu irin nema da duban da ba'ayi masa ba babu shi babu dalilinsa,koda aka gayawa hajja cewa tayi
"Da ita data kwanta ciwo,dashi daya gudu duk ku qyale 'yan kan uba,duk zasuyi su ware,ƴaƴan yau ne fa?,muna nan daku zasu baku mamaki,munafukan banza" haka suka gaji suka haqura da neman nasa,tunda sunsan koma ina yaje yana sane ya tafi din kamar yadda hajjan tace.
***** *_BAYAN KWANA BIYU_*********
Tuni gidan ya zamana babu kowa sai mutanen gidan,kai kace ba'ayi wani taro bama daya danganci biki,ta bangaren zahra tuni ta tattara auren da aka daura mata ta aje lamarinsa gefe,ta auna ta auno bata ga ta inda zai takura ta koya zame mata matsala ba,saidai dama da zai bata ko kuma ya zame mata tsani ko matattakala da zata taka ta cimma burinta na qarasa karatunta da take kan gaba,baya ga haka kuma sasan yadda zasuyi da sauran matsalolin,don dai bata manta da maganar hajja wadda ta sake sanya mata relief a rai ba,indai har haidar din ya kasa shiga zuciyarta to ta mata alqawarin amsar mata takardarta,maganar ma dariya take bata,don bataga ta wata hanya da haidar din zai shiga zuciyarta ba,ta yaya ma?,yadda yake jin kanshin nan,saidai kuma an samu arashin yadda yakeji da kansa itama dai dai take dashi,da ire iren wadan nan tunanukan yasanya ta sawa auren nata suna MATACCE,ta kuma fara tsara yadda zata koma makaranta abinta ba tare da wata damuwa ba.
******************
Kimanin qarfe takwas da wasu mintuna na dare,ita da hajja zaune a falon hajjan suna taba jira,ta tanqwashe qafafunta saman kujera tana yankan farcenta da nail cutter,ilham da husna na zaune daga gefe sun bada himma a kallo.
Kadan kadan kuma kamar daga dan nesa kadan da qofar shigowa sassan hajjan take jiyo muryarsa,tayi tsam da ranta,tabbas shine,don haka ba tare da kowa ya lura da abinda ta jiyo din ba ta miqe ta nufi dakinta,hajja da batasan wainar da ake toyawa ba ta dubeta
"Ke kuma meye haka?,wanne irin tashine haka kamar wadda ake kira?"
"Ina zuwa hajja" ta bata amsa tana shigewa dakin gami da turo qofar.
Ajiyar zuciya ta sauke ta samu waje tana zama,ita sam bataso ma su hadu,saboda idan ta tuna cewa yana amsa sunan miji ne a gareta ita kadai tasan me takeji,ta kuma sha jan kunne wajen umminta kan kada ta qara yarda tayi wani abu akan haidar din da zai sosa ran hajjan,shi yasa tayi gaggawar barin wajen ma tun kan hajjan ta ankara da dalilin da yasata barin falon.
Ko minti uku batayi ba kuwa ta jiyo muryar nan tasa yana sallama cikin falon,a dake muryar take wanda hakan zai alamta maka fuskarsa na nan yadda kowa ya santa koma fiye da haka,babu digon fara'a ko walwala kenan,saita lumshe idanunta tana sakin tsaki,ta koma ta kwanta rigingine tana jin yadda zuciyarta ke daka.
Yana shirin xama su husna na gaidashi,ya amsa musu,duk sai suka miqe suna barin falon,sai ya zamana daga shi sai hajjan a falo,muryarshi a dake ya soma gaidata
"Barka da dare hajja....an yini lpy"
"Qalau muke" ta amsa masa a kaikaice
"Ka gama guje gujen naka?" Ta tambayeshi tana tsareshi da ido,dubanta yayi kafin ya amsa mata
"Gudun me fa?...ba inda naje,kawai shiryen shiryen bikin qarin matsayin nan ne ya sanyani gaba,yazo kuma ya hade da wannan"
"Kai ka sani,nidai ina sake jadda da maka wallahi ka fita idanuna....ka kuma kiyaye ni,idan ba haka ba...bakai kawai ba,har tsohonka bazai ji da dadi ba" ta furta maganar tana kanne ido gami da nunashi da yatsa,sumeshi ya shafa yana furzar da iska
"Ya salam....to nikam hajja bansan me kikeso ba dani kuma,duk abinda kika tsara anyishi,saura me kuma?,me ya rage?" Zamanta ta gyara sosai tana kallonshi
"Ai kafi kowa sani,tunda dai kasan cewa cikin satin nan matarka zata koma makaranta ko?"
"Matata?" Ya tambaya yana jin kalmar wata banbarakwai,da confidence dinta ta gyada kai
"Eh,matarka zahra'u.....kana nufin mu ko dangin uwarta ne zamu ci gaba da dawainiya da ita?,ko bakasan haqqoqin mata akan mijinta ba na kira malami su karanta maka?" Ta qarashe da tambaya gami da zuba mishi idanu,idanunsa kawai ya dauke daga kanta ba tare da yace komai ba,kamar bazai magana ba sai kuma ya amsata
"Nima cikin satin nan zan koma,saboda 'yan kwanaki ya rage na karba sabon matsayina" kafada hajjan ta daga
"Oho maka....kaika jiyo,ka fara sallamarta tukunna da dukkan abinda ya dace,idan yaso kafi ruwa ma gudu"
"Hajja hajja" ya kira sunan nata har sau biyu,tsohuwar tana son takai masa iya wuya,itama sai tace
"Ali...ina jinka,da magana ne?" Kai ya kada yana miqewa
"A bani abinci idan akwai"
"Zakaci iya na kwanakin dana diba maka ne kawai wlh,don bazanci gaba da aikin baban giwa ba" ta fada kamar me qunquni,yaji me ta fada amma sai yace
"Magana kike hajja?"harara ta dalla masa,saboda ta fuskancin yanzun so yake ya tsiro da wasan jika da kaka tsakaninsu
"ban sani ba,nace ka quce dakinka za'a kawo maka"
"Godiya nake" ya fada yana ciro wani turare daga aljihunsa ya aje gabanta,tabi turaren da kallo kana ta raka aliyyun da ido.
Turarenta ne da take amfani dashi,take kuma matuqar so,aliyyun yasan lagonta lokutta da dama,ba banza ba take sonshi duk cikin jikokinta,koda tayi fushi ta ruwan sanyi yake sauketa,sai tasa hannu ta dauka turaren,tana qwalawa inna gaje kira.
Cikin sakanni ta bayyana
"Gani hajiya"
"Shiryawa Aliyyu abinci maza gaje"
"Toh...toh,yanzu za'a kai masa?" Kai ta girgixa
"A'ah....ki hada kawai,matarsa ce zata kai masa"
"To toh,hakan yayi kyau" ta fada tana juyawa zuwa cikin kitchen din tana murmushi,ko ita abun yayi mata sosai,ta jima a ranta tana qiyasta auren aliyyu da xahra,ta dade tana sha'awar haka,amma bata taba furtawa ba,sai gashi Allah ya haskawa hajja,don haka cikin kuzari ta shirya komai cikin wani foldable basket mai kyau,sannan ta dawo ya shaidawa hajjan ta hada,ta amsa mata sannan ta turata ta shiga daki ta kira mata zahra,sai a sannan ma abunda ya faru dazu ya dawo mata kai,wato bisa dukkan alamu tajiyo maganarsa ne tun kafin ya shigo shi yasa tabar falon?,saita saki murmushi kawai cikin ranta tana addu'ar Allah ya shiryesu,ya kuma hada kansu.
Tare da inna gajen suka fito,tana dan rarraba idanu a falon ga zatonta yana nan saboda qamshinsa daya barwa falon,sai data tabbatar baya nan sannan ta qaraso tana sakin jikinta.