← Book details Alqibla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 69

Sashe 37

Alqibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da ɗaya da ɗaya take duba kayan da ilham ta hada mata,gaba daya haushin duniya ya cikata,tabbas da ilham na kusa saita mammaketa,gaba daya riga da skert dinta wanda bata sakasu saita dora after dress akai,sannan babu bra ko pant a ciki sai qwara daya,gefe daya taje ta debo mata kayan bacci cikin wadanda ta fara tarawa a baya,sanda take saka ran aurenta tare da 'yan uwanta
"Lallai yarinyar nan ta rainani....Allah saita raina kanta,bari muje gida" ta fada tana cire daya daga cikin kayan baccin doguwar riga ce wadda kadan ya rage ta isa idon sahunta,ita kadaice me dama dama,saita dauki aron hijabi daya cikin hijaban hajja ta zumbula bayan ta shafe jikinta da turaruka kamar yadda ta saba duk sanda zatayi shirin bacci.

Falo ta dawo ta iskesu suna hira,mama da umma su suka fara tashi,dama tuni abba babba suna waje,da suka shigo kuma sai suka musu sallama,don abba babba yace ya kama musu masauki acan zasu kwana,ya rage a falon daga hajja sai zahra sai musty,sai a sannan zahran ta samu sukunin zubo abinci ta zauna tanaci suna kwasar dariya,saboda wata drama da ake haskawa,hajja ta dage saita fahinta abinda akeyi,musty na fassara mata yana hadawa da yi mata tsiya suna kwasar dariya abunsu harta gama,ta maida farantin ta dawo sukaci gaba da hirarsu.

Qarfe goma na dare aka sake bude gate din mota ta shigo,zahra dake zaune daura hajja sai taji tasha jinin jikinta,dukkansu sunji shigowar motar,saboda haka babu damar tace zata waske ta tashi,tilas taci gaba da zama a wajen,har zuwa sanda muryarsa ta fara ratso falon yana amsa waya kafin isowar gangar jikinsa,hannunsa daya dafe da waya,dayar kuma baqar leda ce dauke da tambarin wani wajen saida abinciccika.

Musty ne ya miqe ya amsa ledar yana masa sannu da zuwa,da hannu ya amsa masa yana qarasowa,ya samu waje ya zauna yana yin sallama da wanda suke wayar ya kashe ya maidata aljuhun gefan wandonsa yana duban hajja bayan yadan sauke ajiyar zuciya,da alamu a gajiye yake sosai
"Sannu da gida....ya naji gidan shuru?"
"Duk sun kwanta saura mu,babanka kuma yaqi kwana,yaa kama musu masauki sun tafi can" goshinsa ya dafe
"Ya Allah....daya fadi hakan yakeso ai da nayi waya an basu daki"
"Wallahi....sun jima aida tafiya".

"Ina wuni" ta furta idanunta na kallon qasa,don ta fuskanci hajja ta sanya musu idanu sosai,saiya waiwaya kadan ya dubi inda take ya dauke kai kana ya amsa tare da cewa mustapha ya bawa hajja ledar,wanda ke ido biyu suyi amfani dashi,karba tayi tana masa godiya,saiya miqe yana wucewa zuwa ciki
"Inajin sai da asuba zamu hadu,am very tired hajja....mustapha.....idan ka tashi da asuba ka nemi ni,don zan fita da wurwuri akwai kuma aikin da zan baka"
"To yaya" ya amsa masa.

Bai rufe minti goma da shiga ba hajja ta dubi zahra tana hade rai
"Ke inna wuro....hada abinci ki kai masa" kamar zata musa saita fasa,ta miqe tana jin kamar ta bace hajjan ta daina ganinta,ta isa bakin dining din ta hada komai saman wani qawataccen babban tray ta durfafi dakin.

A hankali kamar wadda ta shigo sata ta tura qofar dakin,tana saka qafarta cikin dakin ta lume cikin wani kallausan carfet daya rine da sanyi,baya ga qamshi na musamman daya ziyarci kafofin hancinta,zata iya cewa dakinsa nacan gida kango ne akan wannan,duk da bata da nutsuwar da zata iya tsaiwa qarewa dakin kallo amma a kallo daya kawai idanunta sun kaiwa qwaqwalwarta saqo da dama game da kyau da tsaruwar dakin,qarar ruwa da takeji daga wata qofa dake hannun hagu na dakin ya tabbatar mata yana bandaki,kamar an mata rahama haka taji,don haka da dan sassarfa ta isa ga wani dunqulallen qawataccen table ta dora plate din,ta koma da baya tana ficewa daga dakin da sauri.

Sanda ta koma tana ankare da irin kallon da hajjan ta bita dashi,amma batace da ita komai ba,itama saita share kamar bata gani ba,hajjan bata jima ba ta tashi ta barsu ita da musty sukaci gaba da hirarsu,ba'a jima ba itana taji bacci ya soma daure mata idanu saita miqe tana masa sallama,shima kayan kallon ya nufa yana kashewa gami da cewa
"Nima kwanciyar zanyi,saboda gobe na tashi fresh,kinsan goben nan fa babu sauqi,zamu hadu da manyan mutane....Allah yasa nayi babban kamu nima...." Harararsa tayi
"Ai anan kuka fi kauri"
"Kinga laifina?" Saita saki dariya tana yin gaba,sau tari sai ta dinga ganun mustapha kamar ba cikinsu daya da haidar ba,saboda tsananin sauqin kansa.

Da sallama ta tura qofar,sai taga duhu,qwayayen dakin a kashe,lalube ta soma yi don kunna qwan,taji muryar hajja na fadin
"Waye anan?"
"Hajja nice fa" ta fada dai dai sanda tayi nasarar ganin makunnin ta kunna,haske ya gauraye dakin
"Me kikazo yi kuma?,salon ki hana jama'a bacci ku da baku gajiya da surutu" saita miqe ta zauna sosai tana kallon zahra,mamaki maganar hajjan ta bata,don haka tace
"Nima kwanciyar zanyi ai,bacci nakeji sosai wlh"
"A ina zaki kwanta din?,badai a nan dakin ba" saroro tayi tana duban hajja,murya qasa qasa saboda karsu tashi sauran tace
"To a ina hajja?,akwai wani dakinne bayan wannan?"
"Eh....dakin mijinki me yake?,ko ce miki nayi na daukoki ne kizo ki kwanta gotai gotai a gabana?,ko kuma kiji dadin jirgi ki koma?" Idanu ta zaro,wato hajja da manufarta kenan a ranta tasa aka daukota takanas daga makaranta?,kwanan dakin haidar dai dai yake da kwana kusa da maqabarta,ta inama zatace wai taje su kwana daki daya?,saita karyar da murya kamar zata saki kuka
"Haba hajja....haba hajja don Allah"
"Au ba zaki fita ki tafi ba dogon bayani kikeso kenan?,toni bari na baki nawa makwancin naje mu kwan tare dashi" ta fada tana qoqarin miqewa duk da ciwon qafar da take fama dashi.

Abun saiya girmami kan zahran,da mugun sauri ta juya ta fice daga dakin,don tasan indai hajjan ta miqe to taja mata jagwal,don sai ansha daga kafin a sha kanta.25

_*LAVENDER RESTAURANT..*_
_(Palace of mouthwatering food/delicacies)_

_IDAN KUKAJI GANGAMI DA LABARI, INA MASU SON INDA ZASU SAMU INGATACCEN ABINCI MAI DADI DA LAGWADA? KAI BA ANAN MUKA TSAYA BA, INA SABBIN AMARE? MAMAs, YAYYU? DA KANNEN MU MASU SON KOYAN GIRKUNAN YAN GAYU NA KASAR NIJERIYA DA KETARE?_

_*TO KU MATSO...! AT LAVENDER RESTAURANT GOTS YOU COVERED. ABINCIN KASASHE DA DAMA MUKE KOYARWA,,COME LETS UPGRADE YOUR FOOD TIME TABLE, MATSO KUSA YAR UWA GA DAMA DA ZAKI CANZA YANAYIN ABINCIN GIDAN KI, KOWA YASAN IYA SARRAFA ABINCI NA TAKA RAWAR GANI A GIDAJEN AURE. KAI KO BUDURWA CE INDE KIN IYA GIRKI ZAKIGA KOWA YANA HABA HABE DAKE..*_

_*UNCLES, DADDIES, BROTHERS., NEWLYWED HUBBYS..! KU ZO KU YIWA ‘YAYAN KU, MATAN KU DA KANNEN KU RAJISTAR WANNAN HARKA TA KOYAN GIRKI.*._

_*Lavender catering school zamuyi practical class. zamuyi 30 dishes continental,snack & desserts, traditional dishes, drink. Fee din 40k NE. phone number WhatsApp and call 09080299283 akwai discount na 5% ga mutum uku farko wadanda sukai register aranakun independence 1/10/2021 to 3/10/2021 Nigeria @ 61*_

_*ZA’A FARA CLASSES RANAR 14/10/2021. WATO SHA HUDU GA WATAN OKTOBAR DA MUKA SHIGA YAU*._

_*GIRKE GIRKE GUDA 30😫😨AKAN DUBU 40 KAWAI, HARDA BONUS NA SNACKS, DESSERTS, TRADITIONAL AND MODERN DRINK, GARGALIYA DA ZAMANI🥂WATA DAYA CHAS ZA’AYI ANA KOYAN GIRKE GIRKEN.*_

_*KU SAKE KARANTA WANNAN BONUS DIN👇🏾RIGIJI GABJI*_

_*Nigeria @ 61 _*
_*COOKING COMPETITION!!!*_

_*from lavender Catering ina masu son koyon girki ga dama zaku shiga gasarmu ta girki bayan kunyi register damu akan 10k,wanda yazo na 1zai shiga ajin mu free hade da wasu prize din na 2 da na 3 kuma zasu bayar da rabin kudine da wasu prize suma saura kuwa zasu ayi musu ragin 5% da wasu prize wannan gasa zamu yita ranar lahadi ne 3/10/21 zamu rufe registration na gasar ranar asabar*_

_*LAVENDER RESTAURANT: NA GARIN KANO, CLASSES DIN AKWAI PRACTICAL AND ONLINE CLASS GA WANDA KE NESA*_
_____________________________

Tsayawa tayi a tsakanin dakunan da falo tana kalle kalle,tare da tunanin me ya kamata tayi,tabbas kome hajja zatayi mata saidai tayi mata amma ba zata taba yarda ta shiga dakinsa da sunan kwana ba,sai kace wadda ake neman kai da ita?,ko kuma itace mijin shine matar?,sam bazai yiwu ba,saita qarasa ficewa,ta isa wajen tvn da dazun musty ya kashe ta kunna,ta koma kan kujera ta zauna tana rungume pillow gami da sauya tasha.

Kusan a qalla awa daya ta kwashe a zauna,gidan ya dauki shuru,sai tsoro ya fara cikata,don haka ta kashe tvn ta miqe a hankali ta nufi dakin nasu.

Sadaf sadaf ta tura qofar dakin,yan nan da duhunsa da alama kashe qwan hajja ta sakeyi bayan fitarta,saita kunna fitilar wayarta ta haska a hankali ta isa bayan hajjan tayi kwanciyarta nesa kadan da ita,ta tofa addu'o'in baccinta ta rufe idanunta tana addu'ar kada Allah ya farkar da hajjan.

Washegari tana kallon yadda hajjan ke maka mata harara,saita maze ta kuma dauke kai kamar batasan abinda ke faruwa ba,tasan idan tayi fushinta ta gaji dole ta sauko,shirye shiryen tafiya wajen gabatar da taron ma saiya janye hankalinta zahran ta sake samun sukuni.

Fitowarta daga wanka sukaji ana kada qaraurawar qofar falon
"Kai wannan abu sam babu hikima a ciki,wai wannan iblishiyar abar ke gaya maka kayi baqo....ke zahra'u...jeki ki duba kiga waye" hijabinta ta zura saman zanin jikinta ta fita falon.
Chapter 37 · 0% Book details