← Book details Alqibla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 69

Sashe 31

Alqibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karku manta mace Mai gyara kanta Bata boranci taku ce maman yusuf Yar mutan sokoto 07069711327
.
Don Allah wadda Bata shirya ba tabari sai ta shirya sannan tayimun magana🙌🏼🙌🏼🙌🏼🙌🏼🙌🏼ngd

07069711327
_____________________________

Sanda ya koma daki ma kasa zama yayi,yakai ya kawo tamkar wanda ake kadawa kugen yaqi,cikin qanqanin lokaci idanunsa suka kada suka sauya launi.

Da sauri da sauri ya dinga sauke numfashi,har ya soma jin a hankali zafin da zuciyarsa ke masa yana raguwa,saidai gaba daya jikinsa babu qwari,daya laluba da kyau sai ya fahimci yunwa ce yakeji,bazai iya kuma cin abincin da ya siyo din ba,don haka ya yanke zuwa wajen ummi,don ita bata rabo da irin abincin da yakeso din,musamman ma yawancin lokuta takan aje fridge saboda shi idan yana gari,duk sanda ya buqata koda darene zata dumama masa shi ya koma kamar sabo ta bashi yaci abinsa hankalinsa kwance.

A gaggauce ta koma sashen abban babban,ta dubi nasma dake falo yin wani assigment da aka basu,gefanta mommy ce zaune tana duba wani dan qaramin english novel da yake meson karance karance ce,duk da shekaru sun dan tura
"Ke ina tsohuwarki?" Ta tambayeta,saita daga kai ta dubeta da mamaki,tunda tasan bata jima da fita daga sassan ba
"Tana dakinta" sai kawai ta wuce zuwa ciki,mummy tadan bita da kallo sannan ta dauke kanta ta maida ga abinda take.

Tana shiga maman na fitowa daga wanka,gefe daya kuma tana sauraren wata lacture ta dr malam umar sani fagge,gefan gadon maman ta zauna tana cewa
"Lallai hadiza,ke har kina da lokacin sauraron karatu ma ruwa yana shirin cimmaki kina zaune dafa'an" da mamaki maman ta dubeta
"Ruwa kuma uwani?,wanne irin ruwa?"ta fada tana dakatawa daga goge jikinta da take wanda takeson ya bushe ta shafa mai
"Hmmm.....wai dan Allah da saninki koda amincewarki za'a bawa danki auren sangartattar yarinyar can zahra'u?"murmushi ne ya subucewa mama
"Ni wallahi tsoro kika bani ma uwani.....na sani,zahra'u ai diyata ce itama kamar yadda yake dana,sannan kuma gwara hakan,ai ina ganin hakan shine kawai maganinsa tunda bashi da niyyar yin aure" matsowa anty uwani tayi kamar wani na kusa dasu zai iya jin abinda zata fada
"Amma dai hadiza don Allah banda abinki.....kaf 'yammatan dake cikin dangi tsala tsala,dama wadanda ke yawo a gari,a rasa wadda za'a bashi sai yarinyar da kowa yazo guduwa yake ya barta yaqi aurenta,ke ko kishin kanki dana danki bakyayi?,kin taba tunanin meye ya hanata auruwa ma tukunna?,tunda dai banza bata kai zomo kasuwa,haka nan ruwa baya tsami banza,sannan bakiyi tunanin idan ma hadasun akeson yi saboda Allah da ma'aiki ba....me ya kawo wannan gaggawar?,daura aure nan da kwanaki bakwai kamar wadda ta aikata wani abun kunya da ba'a so ya fito?,haba hadiza,kiyi tunani mana,ga yara nan masu sonshi wadanda babu wani kokwanto a kansu?,ko suwaiba wannan tawa bakiga yadda take son yaron nan ba,kwanaki har jiyya ta kwanta,tsabar kamun kai da kunya ne yasa ta kasa bayyanawa".

Kai mama ta girgiza
"Toh...koma meye Allah ne masanin gaibu,amma abinda na sani shine,hajja ba zata taba yin abinda zai cutar da yaran nan ba,kuma dukkanmu ta isa damu,saboda haka duk abinda ta fada dai dai ne,duk hukuncin data yanke kuma yayi dai dai" baki anty uwani ta kama tana duban mama
"To ai dama ita zatayi ne da kyakkyawar niyya,amma da za'a zurfafa bincike za'a gane akwai matsala"
"Ni bani da iko dashi tunda bani kadai na haifeshi ba,ikonsa naga mahaifinsa uwani,kullum addu'a muke Allah ya yiwa rayuwarmu zabi mafi alkhairi,kuma shi zamu ci gaba da yi,kema ki tayamu" daga haka ta juya tana ci gaba da shiryawa,gami da kokawar kauda dafi da mugun tunanin da uwani keson cusawa cikin zuciyarta haka siddan,ba gaira ba dalili.

"ƙnnnn,ai shikenan,wanda ke sonka dai shi zai hango abun cutarwa ya gaya maka tun baikai ga cutar dakai din ba,idan kinji haushina kiyi haquri"
"A'ah wallahi,ba wani haushi uwani,haba aliyyun da inna wuron ai duka yaranki ne kema" jin haka bata sake cewa komai ba sai kai data sanya ta fice.

Ajjiye man hannuta maman tayi ta koma ta zauna shuru na wami lokaci tana tunani,kafin ta miqe tana fada a sarari
"Dukkan alkhiairi ubangiji ya tabbatar dashi,ya kade dukkan wani sharri,yayi mana jagora" sai taci gaba da shiryawa abunta.

Da sallama ya shiga falon ummin,ta amsa masa tana daga zaune saman kujera,sanye da hijabi hannunta kuma riqe da carbi tasbih counter,wanda bata rabo dashi.

Yana gaidata su ilham suna gaidashi,ya amsa yana riqe da hannun sulaiman
"Ummi nace don Allah zan samu wani abu haka da zan iya ci?" Dan murmushi ta fitar
"Ai kuwa mutuminka muka dafa....ilham....tashi maza ki hadowa yayanku abinci"
"To" ta fada tana aje littafinta ta miqe ta mufi kitchen.

A dabarance haidar ke satar kallon ummin,duk yadda takai ga boye damuwar dake shimfide saman fuskarta amma hakan yaci tura,matuqar ka qware wajen karantar halayyar mutum kuma kayi mata farin sani zakasan cewa akwai damuwa tattare da ita da taketa yunqurin boyeta,saiya saukar da idanunsa wani sashen daban yana son boye nashi qwayar idanun kada ta karanto nashi yanayin.

Ba jimawa ilham ta dawo da komai a shirye,sai ummin tace
"Ajjiye masa yaci a nan basai yasha wahalar fita dashi ba" yasan ummin farin sani,zai iya cewa tun quruciyarsa suke tare,yadda yake iya karantarta haka itama take saurin karantarsa,a nan gabansa ilham ta duqa ta aje,ta duqa kuma ta zuba masa komai,sannan ta miqe ta kwashe litattafanta ita da sulaiman suka bar falon,kamar sunsan hakan ummin keda buqata.

Sai daya nutsa sosai a cin abincinsa sannan ummin tace cikin yanayi na nutsuwar nan tata
"Haidar.....dama inatason na aika ayimin kiranka" kanshi yadan daga kamar zai dubeta saiya fasa,shima anutsen yace
"Ba wata matsala bane ko ummi?" Kaita girgiza
"Matsala ce....kuma wadda na jawo maka,inason na baka haquri ne bisa matsalar dana ja maka,wanda inda nasan alfarmar dana nema wajen hajja sakamakon zai juye ne a wuyanka da ban nema ba,gaba daya maganar ma da nasan zata ja maka zargi wajen hajja da ban tadata ba....."
"Ummi....don Allah karki sake cewa komai" ya fada cikin matuqar jin nauyinta,anya kuwa bata karanci duk abinda ke cikin zuciyarsa ba?,anya bataji maganarsu da hajja ba,wani irin nauyinta ya dabaibayeshi,yana iya tuna tun daga zuwanta gidan a lokacin da take amarya,yana iya tuna yadda ta riqeshi da,ɗan data tsugunna ta haifeshi,ta nuna masa qauna sosai,irin qaunar da sai daya baro dakin mamanshi ya dawo sassanta,bai bar sassan nata ba har sai daya kai munzali sannan ya koma sashen da aka tanada saboda yara maza na gidan,duk da cewa a sannan shine da namiji na farko a gidan,bayan kuma ta samu tata haihuwar babu abinda ya canza,qauna da kulawar da take nuna masan bata ragu ba,kuma har kwanan gobe hakane....bayajin ya kamata ko sau daya tayi wannan furuci na ban haquri agareshi komai bata masan da tayi,bare ma babu wani laifi nata guda daya da ya gani kan lamarin gaba daya.

"Kina sani jin nauyi da jin cewa kamar kinga wani abu tattare dani dake sakaki tantamar baki isa....komai daya faru rubutacce ne kuma ya riga ya wuce" kai ta kada
"Nasan na isa haidar....amma lamarin aure ba qarami bane da za'a ce an yankeshi haka katsam babu nutsuwa ko yardar zukata...."
"Ummi....don Allah kiyi shuru kada ki sake cewa komai,kiyi mana addu'a"kai ya rausayar
"Shikenan.....ubangiji ya shiga lamarin" abu na qarshe data fada kenan.

Sanda ya koma daki sake shiga rudani yayi,sai yanzu yake hango girman dabaibayin da hajja tayi masa,tako ta ina shidin a qulle yake bashi da wata mafita,ya jima gaban window din daya fita waje daga dakinsa yana kaiwa hunhunsa sassanyar iskar dake kai kawo cikin fadin duniya,kafin ya samu nasarar waftar qanqanuwa daga yankin nutsuwa,sannan ya dawo cikin ainihin dakin.

Sai a sannan idanunsa suka sauka ga envalope din da general ya bashin,sam ya manta da batunta,don tunda ya shigo da ita ya aje bai kuma bi ta kanta ba.

Yakai hannu zai dauka idanunsa suka sauka kan dan qaramin hoton marigayiya zahra dake cikin wani qawataccen frame ruwan gold,saiya fasa daukan envalope din,ya soma kai hannunsa ya shafi fuskar hoton dake dauke da fuskar zahran,sannan qasa qasa ya furta
"Rest in peace" ya miqa hannu ya dauki takardar ya koma saman kujera guda daya dake dakin ya zauna ya farketa ya zaro takardar dake ciki.

Girman saqon da takardar ke dauke dashi ne ya sanyashi miqewa tsaye qyam cikin mamaki,gefe daya kuma wani farinciki na son kunnuwa tsakiyar bacin ran da yake ciki ya kuma shafeshi cikin mintuna qalilan.

Takarda ce ta qarin girma,wanda sam bai taba kawo hakan ba a ranshi,saboda shekarunshi da shekarun daya dauka yana aikin basu isa bashi wannan matsayin ba,a qalla saiya shekara ashirin da hudu sannan zai taka wannan matakin,amma sai gashi lokaci daya!,dare daya ya samu wannan matsayin.

Har ya nufi qofa da niyyara isa ga hajja da wannan albishir din sai yaja ya tsaya saboda tuna abinda ke wakana,rasa wanda zai raba labarin dashi yayi,don haka ya zauna ya lalubo wayarsa yana neman su abu sufyan,yana da yaqinin labarin bai fasu ba tsakanin manya da qananun sojoji da tuni sun kirashi.

Ya dan jima suna waya dasu,kafin wani lokaci kuma sai wayoyin mutane suka soma turereniyar shigo masa,da alama labari ya fasu,dole ya katse duk wani kira,ya shiga cikin gida ya shaidawa mama da abba babba,amma saiya share 'yar tsohuwar bai shiga ya gaya mata ba.

Kafin ya kwanta sai daya kira general yayi masa godiya sosai bayan ya hadashi dasu abba sun masa tasu godiyar,jin bai tada masa batun su haisam ba yasa ya share shima baici komai ba,saidai ya gaya masa ana buqatarsa a office saboda wasu akwai shirye shirye na amsar office da kuma bikin qarin girman,shi a gobe zai koma wajen aiki,ya amsa masa da yana tafe da yardar Allah.

*********washegari***********
Chapter 31 · 0% Book details