← Book details Alqibla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 69

Sashe 57

Alqibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dawowarta ba jimawa aka soma jarrabawa,wanda daga ita din watanni kadan suka rage musu suyi jarabawar kammala makarantar,kamar kowanne lokaci dai bata daga qafa ba,ta bada himma wajen karatunta sosai,duk da cewa lokaci zuwa lokaci tunaninsa yakan fado mata a rai,har yakan tsaidata na wasu mintuna kafin ta dora,tun tana yaqin ture zuwan tunanin kwanyarta harta haqura ta bashi dama,saiya zame mata jiki,don kusan duk sanda tazo kwanciya bacci shine abu na qarshe da zatayi kafin baccin ya dauketa,kaf xamansu na abuja sai tayi bitarsa,ranar da zasuyi sallama na qarshe da sauran moments nasu.

Batasan me yasa a kwanakin take yawan duba wayarta ba,koda yaushe tana kan cheaking sms da watsapp massages fiye da yadda ta saba,batasan dalili ba,sai randa zuciyarta tayi mata wata tambaya,wanda a take ta girgiza kai alamar a'ah
"Kina tsammanin samun kira da gareshi ne?" Wannan itace tambayar data yiwa kanta,wanda ko sau daya bata taba yarda da hakan ba.

Jarabawar wannan karon suna samun intervals sosai,don haka duk sanda taga akwai interval mai yawa saita tafi gida,tafiya gidan yakan sa mata nutsuwa,kuma yakan sanya taji kamar tadan rage nisan dake tsakaninta da wani abu wanda ada yake nesa da ita.

Sannu a hankali ta tabbatarwa da kanta damuwa ce,damuwa ce ta rashin ganinsa ko rashin jin muryarsa na tsahon tagwayen sati,har ana neman shiga sati na uku,hatta a gida hajja ta fara qorafin shuru haidar,bai kira ba,koda an kira ba'a samunsa,to Allah yasa dai lafiya,addu'ar data sanya gaban zahran mugun faduwa,saboda tuna maganar daya gaya mata
_"zanyi tafiya me nisa.....waje me hadari,zan iya dawowa....zan iya salwanta a can.....ki yafemin idan na saba miki a tarayyarmu"_,kawai sai taji kuka ya subuce mata,ta danneshi har sai data kai daki sannan ta sakeshi.

Kuka tayi sosai wanda ta kasa yarda da dalilin kukan nata da zuciyarta keta bata,saidai ko ba komai ta danji nauyin dake qirjinta ya ragu,ranar sama sama tayi karatun jarrabawar da zata zana a jibi,washegari ta hada kayanta ta koma makaranta,wanda jarabawar kawaidai tasan saidai Allah ya tsallakar da ita,amma ita kanta bata gama tantance abinda take rubutawar haka yake ba,ko akwai kusakurai da gyararraki ba.

Hajja kuwa bin zahra tayi da kallo tun sanda taga tayi daki da sauri sanda take jajjabin kwanakin da haidar din ya shafe babu shi babu labarinsa,murmushi ta saki,duk da tana cikin fargaba,saita daga hannunta sama tana cewa
"Allah na gode maka,Allah na gode maka,ko yau na mutu ubangiji ka cikamin dukka burina,Allah ka qara hada kan zuria'ata da iyalina,Allah ka qarawa annabi muhammad S A W wasila da fadila" daga haka ta sauke hannun nata,zuciyarta na mata dadi,ba shakka komai yayi dai dai yadda takeso,tasan cewa da zarar ya dawo komai zai kammala dai daita.

Ranar da suka kammala jarrabawarsu suka samu hutu na wasu kwanaki ba masu yawa ba,saboda zasu dawo ne suyi maza su dora sabuwar semester ta qarshe,tana kwance a dakinsu kamar ba wadda ke shirin tahowa gida ba,tana kallon su hindatu sunata shiri.

Tun sanda ta dawo daga abuja ta lura da wani abu,dabi'un su hindatun su canza gaba daya,abubuwa da yawa sun daina yinsu yanayin shigarsu ya canza sosai,wanda hakan ya bata mamaki,saidai bata taba tambayarsu ba.

Hindatun ce ta qaraso ta taba zahran dake kwance rub da ciki,saita daga kai tana duban hindatu,hijabi ne dan madaidaici a jikinta wanda ta dorashi saman abayarta,wadda ta rufe jikinta ruf
"Tunanin me kike mrs haidar?" Murmushi ta saki,ta tashi ta zauna tana duban hindatun,fuskarta qunshe da murmushi
"Ina mamakin me ya canza qawayena haka tashi guda" murmushin itama hindatun tayi,ta zauna gefan zahra
"Tasirantuwa mukayi da qawar qwarai,hakan shiya canza mu,sannan kuma mukayi aiki da hankali da tunanin da Allah ya bamu,muka ga cewa,babu wata rayuwa ta wayewa face wadda addininmu ya tsara,hakanan kome zakayi kayi abinda zai kauda mummunan tunani a kanka,mukayi karatun cewa samarin yanzu sam basu da ALQIBLA....ko kuma ince ALKIBLARSU mafi yawansu bame kyau bace,ba miqaqqiyar ALKIBLA bace,kowanne yana amfani da yanin shigarmu yana mana hukucin cewa mu din lalatattu ne,duk wanda zai durfafemu zai durfafemu ne da mummunan niyya.....,suna tunanin cewa mu din mazinata ne,mun saba kowacce harka data saba addini da al'adarmu,mukaga meye ribar rayuwar diya mace?,ki killace kanki,ki tsare mutuncinki dana iyayenki,kikai qimarki gidan miji,qima kuma bawai ta budurci kawai ba,harda ta kyakkyawar shaida da kyakkyawan tarihi,abun yabo,abun alfahari da zaki barwa 'ya'yanki da jikokinkin ba,rayuwarki kawai ta zame mana abun misali,yanayin rayuwarki bazai hana a kiraki wayayya ba,saidai komai naki bisa tsari ne,irin tsarin daya dace"murmushi sosai zahra keyi cikin jin dadi da Allah yasa ta zama silar gyaruwar halayyar wasu,ta kuma sake jin dadi qwarai data sake samun tabbacin babu wadda ta saida mutuncinta a cikinsu,sai tace
"Na godewa Allah da yamin baiwar da mutum hudu suka gyara tsarin rayuwarsu saboda ni,Allah yaci gaba da tabbatar damu akan shiriya"
"Amin zahra" hindatu ta fada tana ci gaba da shiryawa,jifa jifa suna taba hira da zahran da har yanzu take kwance
"Wai ba zaki koma gida bane naga babu alamun shiri tare dake?" Baki ta kwabe tana gyara kwanciyar tata,sam sam batajin wani doki ko murnar zuwa gidan
"Zanje,so nake rana tayi sanyi ne"
"Amma zahra....sai nakega kamar akwai abinda ke damunki kwanakin nan" murmushin qarfin hali tayi
"Me kika gani?" Sai data rufe akwatinta sannan ta dawo gefanta ta zauna
"Yanayinki ba kamar yadda na sanki ba,don ba haka mukeyi dake ba....like kamar akwai damuwa a ranki" qaramin tsaki taja
"Ba wani damuwa,kawai yana yine"
"Yanayin kewar soja ko?" Ta fada tana qunshe dariya,cikin qarfin hali da son qaryatawa tace
"Kamar da can na sanshi ne da yanzun zan damu kaina,karki sake wannan batun don bashi bane,stress ne kawai na exam" tabe baki hindatu tayi tana miqewa
"Tunda wannan shine karon farko da kika fara yin exam din,maji ma gani" ta fada tana dariya abunta,batason dogon magana sai kawai ta barta a hakan taci gaba da kwanciyarta.

******** *** *********

Cikin babban mayafinta data yane ilahirin jikinta ta shigo falon,cotton ne mai zanen adon furanni masu kyau,wanda kusan shine mayafin da hajjan tafi amfani dashi tuntuni har yanzu,saboda kaurinsa da suturta jiki,duk siyayyar da za'a mata na sutura tofa sai an nemo mata shi.

"Ashe ka iso,lale maraba" ta fada tana murmushi gami da samun wajen zama,murmushi shima abu sufyan yayi yana saukowa qasa ya gaida hajjan,tana tsaka da amsawa zahra tayi sallama dauke da jakarta
"A'ah.....kamar tare kuke" cewar hajja tana duban zahra,saita saki gajiyayyen murmushi ta samu kujera daya ta zauna
"Ni hajja yaushe rabona da naga ya abu sufyan ma,sai yau" murmushi yayi
"Ku dinne ai kukayi tsada,daga ke har xaki,ganinku nan gaba sai munyi da gasken gasken" murmushi tayi tana rufe bakinta da tafin hannunta
"A'ah bamu isa ba"
"Har kunyi yawa" datse zancan tayi ta hanyar soma gaidashi,don sam ita a kwanakin nan bata jin wani armashi wajen yin raha ko walwala,ita kadai tasan takurar da ranta da zuciyarta ke ciki,suna gama gaisawa ta miqe,taja jakarta zuwa ciki tana tambayar hajja abinci,don tun break din da tayi da safe na zallar ruwan tea bata sake cin komai ba
"Akwai raguwar na rana,don gaje bata nan,saita dawo zata dora na dare".

Kayan jikinta ta cire ta sauya wasu bayan ta shiga daki,saboda taji inna gaje bata nan,tana tunanin ta karba girkin daren tunda Allah ya dawo da ita,kafin nan umminta ta dawo,don ta fara leqa sassan nasu bata taras da ita ba,su ilham din ma suna islamiyya,duk da sun fara zama 'yammata,gidansu sam babu wasa da karatun addini,ita kanta da take boarding duk sanda tazo hutu akwai islamiyyar da take zuwa har a koma hutu,don haka babu wani karatu da yake hanasu karatun addini tun suna qananunsu har a aurar dasu,ko samarin gidan yanzu haka akwai makarantar dare ta maza manya da suke zuwa duk dare,har kwanan gobe.

Fitowarta kenan zata wuce kitchen din taji muryar abu sufyan yana cewa
"A matsayinsa bashi zaije wajen ba....shi xai tura,amma kishin qasarsa yana ya saka kanshi sahun masu shiga wajen,waje ne mai hatsari,wanda yawanci ko rashi aka samu sai randa suka dawo ake qididdige wadanda suka mutun a bada sanarwar mutuwarsun a hukumance.....amma kuma abun daure kan shine,shi din yana da 'yancin fita ai yayi wayarsa,ko ya sauka a masaukin daya zaba.....amma shurun yayi yawa,ace har yanzu babu wani motsi daga wajensa" kamar an buge mata gwiwoyinta haka taji,sai taji kamar ba zata iya qarasawa kitchen din ba,zata zube ne a wajen,daqyar a daddafe dai ta samu takai kitchen din,saita dafe kantar kitchen din ganin tana niyyar zubewa
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" abinda ta dinga maimaitawa kenan,sai taji hawaye na sauko mata,zuciyarta ta shiga gaya mata ya mutu,ya haidar ya mutu kawai.

Kifewa tayi saman kantar ta soma kuka sosai,kuka mara sauti,mai dauke da rashin madafa,batasan iya lokacin data shafe a haka ba,sai data tsinci muryar hajja na fadin
"Ke,lafiyarki kuwa?" Dago kanta tayi da fuskarta ke jiqe jage jage da hawaye ta dubi hajja,cikin muryar kuka
"Hajja....." Saita kasa.magana,ta juya da sauri ta fice a kitchen din,hajjan ta bita da kallo kawai.

Tun daga lokacin bata kuma fitowa a dakin ba bare ta tambaya wani abinci,har zuwa washegari data sake jin abinda ya daga mata hankali,tara su abba yusuf da hajja tayi cikin damuwa tanason su nemo wani labari daga bangaren haidar din,wata kusan biyu shuru?,wannan shi yasa ta qara rafkewa,saiga zazzabi mai zafi ya rafketa.

Ba wanda ya sani saida hajja taji shurun yayi yawa sannan ta leqota,hankali tashe hajjan ta kira mustapha ya kira mata abban tsakiya tun baikai ga fita da motarsa su kai zahran asibiti,koda akaxo tafiya ma kasa tashi tayi,Allah yasa sadiq yana gidan yazo hutu daga wajen aikinsa,shiya dauketa ya kaita bakin motar suka wuce asibitin.

Taimakon gaggawa suka bata,aka daura mata ruwa bayan allurai,ba jimawa bacci mai nauyi ya dauketa.

****** ***** ****** *****

Zaune take saman gadon asibitin,inda ta jingina bayanta da bango,ta kuma miqe qafafunta saman gadon,cup din tea ne a hannunta take kurba kadan kadan,tanayi tana yamutsa fuska,saboda anty aliya ce ta sanyata a gaba akan sai tasha din,tana ta fada gami da bambamin ta yaya zata samu lafiya taqi abinci sai magani da aketa dirka mata,bayan ga ulcer nan itama da takeson tayar mata.
Chapter 57 · 0% Book details