← Book details Alqibla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 69

Sashe 23

Alqibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yanzun ma hira suke masu charting nayi,harda qawayen su batula daga wani dakin,ana tsaka da haka taji mardiyya qawae farida ta luqa ashar
"Ferry....zoki gani....maza maza zo kiga" da sauri farida ta aje tata wayar ta matso kusa da mardiyya,saita zare glass din fuskarta,da qarfi ta furta
"What.....muhsin ne fa,wata fa naga ya dora yana furta kalaman soyayya a qasan pic dinta,kan bala'i" saita fada tana dauko wayarta da sauri tana duba wajen status dinta
"Zo kiga,ni bai nuna ajerin nawa status din ba,babu status dinsa" dariya wata rabi'ah dake zaune kusa dasu tayi,ta tashi ta zauna tana cewa
"Wai baku gane meke faruwa bane,ai na taba gaya miki farida tun kwanaki kika qi yarda,kinzo kina wani jin kin isa kinkai,wai waye ya gaya miki ma cewa a yanzu ana cika baki kan namiji?,ai wannan lokacin ya wuce,lokacin cika baki da alfahari,da basu amanna dari bisa dari.....everybody listen to me" ta fada tana gyara zamanta sosai a tsakiyarsu tare da miqe qafafunta,hakanan maganar da rabi'ah din ta soma fada ta dauki hankalin zahra,bata sauke littafin hannunta ba amma hankalinta na kanta
"Luggar mazan yanzu.....zasu iya yin budurwa dari ko dubu ta watsapp....kuma zasu iya dora hotonta a status...amma kuma,duk sanda zasu dora hoton daya,tofa zasu cire dukkan sauran su sanyasu a jerin wadanda a ranar ba zasuga status dinsu ba,ba zasu ciresu ba har sai hoton yayi disappering,ko kuma ranar naki pic din zasu saka,saisu cilla waccar cikin inda suka ciroki ke kuma a fito dake,donki gani,kiji dadi,ki kuma qara amanna dasu...so dukka abun bugene,duk ta yadda suka biyo miki ki bi musu ta haka,kada ku saurara kunji....kuyita musu yadda suke muku kawai,dakun samu na dauka ku dauka ku watsar dasu" ta qarasa fada tana sheqewa da dariya.

Maganar status din ta baiwa zahra mamaki,wato kullum sabon salo suke fiddawa?,saidai fatan samun shiriya,amma kuma zancan gogayya da samari barkatai sam shawarar batayi mata ba,saita tabe bakinta kawai taci gaba da karatunta,gefe guda hayaniyarsu tana cika mata kunne,da Allah ya taimaketa zuwa wani lokaci suka fara raguwa da kadan kadan,har dakin ya rage daga ita sai hindatu wadda ta haye gado ta kwanta zata dan rage bacci a cewarta kafin ta tashi tayi karatu.

Turo qofar dakin da aka sakeyi da qarfi yasa zahra dagowa tana fatan ba sune suka sake dawowa ba,basu din bane yanzun jannah ce,sanye da straight gown da hill shoes,sai qaramar hand bag da qaramin mayafi data nade wuyanta dashi,kusan shigarta kenan wanda kusan kullum sai sunyi rigima da zahra akan haka.

Yau din fuskarta sam babu alamun walwala,gefan gadonta ta samu ta zube tana zare mayafin kanta cikin masifa take magana
"Ni hisham zaiwa haka?,ni zaiwa wannan akuyancin?" Hindatu dake kwance bacci ya fara dibarta ta daga kai tana dubanta
"Ke kuma meya hadaki da hisham din naki yau?" Iska ta furzar daga bakinta sannan ta zame 'yar hular dake kanta ta sabule takalminta ta zauna sosai saman gadon tana harde hannayenta
"Yau ni hisham zai fito qarara yacemin nayi haquri da maganar aurenmu....shi matarsa ta gida ta isheshi" sosai hindatun ta tashi ta zauna
"Hisham din da kansa da bakinsa?" Kai ta jinjina cikin tsananin jin zafi
"Shi din fa....shi yasa ya kasa zuwa ya gaida dad,ko mami ma danace yaje cewa yayi wasu shirye shirye yakeson ya kammala tukunna...."dauke kanta hindatu tayi zuwa sashen da zahra ke zaune
"Kinji fa zahra?" Saita ture littafinta gefe
"Naji" ta fada tana saukowa daga saman gadonta,ta daura dankwali sannan ta fita zuwa toilet,mintina kadan ta dawo ta samesu suna tattaunawa,ta koma bakin gadonta ta zauna sannan ta dubi jannah.

"A inda kullum muke fada dake kenan fadan gaskiya....ita kuma gaskiya daci gareta,hakanan fure take bata 'ya'ya,ita kuma rayuwa duk abinda ka shuka shi zaka girba,ba zaka taba shuka qaya ba kace inibi kakeson cira,jannah.....na dade ina miki nuni da waye hisham,illa da dafin dake tattare dashi,hisham yayi amfani da son da kike masa yayi fooling naki,ya kuma yi amfani da damarsa a kanki,a yanzu ya gaji dake ne shi yasa ya fito miki ta wannan hanyar kai tsaye,don ya ajjiyeki ya kuma lalubi wata mai tsautsayin me qaramin tunanin....kiyi haquri da harsh word da nake amfani dasu a kanki,kawai ni duk inda gaskiya irin wannan tazo gittawa ta gabana saina fadeta,abinda yasa na kira dame qaramin tunani shine....babu ta yadda wanda yakeson ya aureki ki zame masa uwar yaransa kuma mace ta gari abar alfahari ya daukeki cikin motarsa yana yawo dake,ya daukeki ba cikin gidanku ba,ba gaban iyayenki ba,ku hadu a wani waje ya saki gaban mota kuna yawo,yaje ya killace 'yarsa,yaje ya killace matarsa,yaje ya killace mamarsa....amma kefa?,saboda baki da wani daraja,baki da wani matsayi da za'a baki,shi yasa bai dauki hakan a bakin komai ba,daga sanda wanda yace miki yana son aurenki yazo miki da magana kan matarsa qazama ce,matarsa bata iya soyayya ba,matarsa yar qauye ce,kece kika iya komai,matarsa ta gaza ta kowanne fanni,amma kuma ko yaushe yana nanuqe dake,yana fasa miki kai,ta wani sashen kuma a dabarance yana qoqarin ku dinga hulda ta hada jiki romance da kissess amma kuma ko sau daya bai taba tunanin kiyi aure ba,ke koda ya taba tunanin hakan ko furtawa toba shakka na yaudara ne,daga sannan kuma kin samu babbar matsala,a haka da kike yawo dashi janna,cikin irin wannan shigar da wannan rayuwar kike tunanin zaya daukeki yakai gidansa a matsayin matar aure?,me zaya killace?,me zai burgeshi har yakai ga aikata hakan?,bakayi haka bama da sautayi a wannan zamanin ya kuka qarke dashi bare ace kinyi?,ni na isheki manuniya da ishara,kafin kice hisham ya yaudareki ya kamata ki fara cewa kin yaudari kanki,idan maganata ta miki zafi jannah kiyi haquri"sosai taga yadda jikinta yayi masifar sanyi,saita kasa cewa komai,sai dogon nazari da tunani data fada,bama ita kadai ba har hindatu dake kwance.

********** ******** ********

*_ƘADDARA....ta riga fata_*

Cikin sati sunyi CA sa yawa kamar yadda ta zata tun wancan satin,to satin gaba ma kusan akwai sauran tarin karatuttuka,hakan ya sanya kowacce ta sake haqura da zuwa gida weekend,saidai kuma sun shirya zuwa daya daga cikin masaukan baqi hotel don su huta a can a cewarsu.

Sanda suke shirya tafiyar zahra na zaune tana jinsu bata tanka ba,tadai yanke idan sun tafin gida zata wuce ko kwana guda ne ta rage ta dawo.

Saida suka gama hayaniyar yadda zasu gudanar da ranakun qarshen makon sannan suka soma raguwa sannan hindatu ta iso kusa da zahra ta zauna
"Amini....ko sau daya baki taba karar binmu bafa" kallonta tayi
"Ko sha'awa wajen banayi,me zai kaini nikam,kuma ina mamakin yadda kuka maida wajen kamar ba'a bakin komai ba zuwanshi" dariya sosai hindatu tayi
"Kinga,mufa mutanenmu ne suka yiwa wajen mummunan fassara,amma a qa'ida wajene da iyali ma suke iya zuwa su kama daki suyi dukka iya kwanakin da sukeso,su huta daga hayaniyar gida data jama'a,ni kusan duk qarshen wata bazan manta ba kafin nakai haka,sannan abubuwa basu yiwa daddy yawa ba muna zuwa muyi kwana biyu haka ko uku,ba wani abu bane me muni,saidai idan mutum dama da mummunar niyyarsa yaje,don Allah kizo muje wannan karon,sau daya dai tak" kai zahran ta girgiza
"Naji bayananki,amma am sorry bazan iya zuwa ba hindatu saikun dawo" ranta ta bata da alamun bataji dadi ba
"Shikenan....tunda baki yarda dani ba,komai kika fadamin ina qoqarin yi dabi,bana tsallakewa shawararki saboda nina aminta dake....na gode,dama sunatamin dariyar cewa ni kadai na damu dake,yau na gasgata hakan" saita sauka daga gefan gadon ta koma nata tana hada kayan da zasu je dasu.

Ganin yadda harta gama hada kayan bata kalleta ba dakin shuru yasa taji duk babu dadi,ba kaifi hindatun tana daukar duka shawarin zahran da qoqarin ganin tayi abinda zahran keso,da gaske taji haushinta kenan sosai,har ta isa bakin qofa zata fita zahran ta kira sunanta
"Haushi kikaji kenan?" Kafada ta daga
"Saboda me?,bayan baki yarda dani ba?,akanme zan takuraki kiyi abinda baki niyya ba" kaita kada tana murmushi
"Zanje....shikenan ko?" Cikin murna ta dawo
"Na gode sosai....ina mai tabbatar miki zakiji dadin tafiyar da zamuyi,gobe da kanki zaki ce muje" murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba.17

*KIJI TSORON ALLAH ☝🏾☝🏾☝🏾,karki taba kayan da ba naki ba ba kuma mallakinki bane*

Ƙarfe hudu na yammacin ranar suka dunguma su shidda cikin motar gidansu hindatun suka tafi.

Ɗaya daga cikin tsadaddu kuma qawatattun hotel sukayi masauki,suka kama daki guda babba wanda zai ishesu a wadace,itakam tana zaune daga gefe tana kallonsu yadda suka sake tamkar suna cikin gida ko cikin makaranta,ita kam har cikin ranta bata jin wani walwala ko karsashi ko kuma wani jin dadin zuwa wajen,sai take ji acikin zuciyarta duka wani irin babu dadi,sai takejin kamar ta aikata wani mummunan abu mara kyau,haka kawai takejin babu dadi har qasan ranta,har sai da farida ta ankara da haka
"Ki sake mana haba zahra,mu kadai ne fa a dakin,babu wanda yake shigo mana ko ya isa ya shigo" murmushi kawai ta musu,sai tabi lafiyar lafiyayyen gadon dake dakin tayi kwanciyarta akai,don kafin su fito tasha karatu sosai,tana son ta huta kafin ta sake dora wani,don ta taho da dukka litattafanta,har suna tsokanarta cewa ba hutawa zataje yi ba kenan,tunda ba zata bar qwaqwalwarta ta huta ba.

Suna ta hayaniya da walwalarsu har zuwa sanda akayi knocking qofar aka kawo musu abincin dare,kowa ya fara diban nasa duk da cewa akwai sauran lokaci kafin ma ayi sallar magariba din,hindatu ce ta dubi zahran
"Zahra....ga abinci,ki sauko kowa nacin nasa" kaita kada tana hamma
"Kai a'ah,sai an idar da sallah" daga haka ta sake gyara kwanciyarta,tun tana jin hirarrakinsu sama sama har ta fara daina jiyosu,babu jimawa kuwa bacci mai nauyi ya debeta.
Chapter 23 · 0% Book details